Author : Billyn Abdul Category : Adventure
kuka Yakura dake kwance komai sai an mata da yara nayi ta wuce. Tafiyar Inna baifi da wata guda ba Babban yayan su Abdul-rasheed ya lallaɓo yazo wa A'isha da batun wai yana son ya aureta, dan su haɗu su riƙe ziri'ar Abdul-rasheed. Takaici ya saka A'isha rufe ido tai masa tass, wannan abu da tayi kuma babu bincike mutane da dangin Abdul-rasheed suka sakata gaba saboda shi ya juya maganar a baibai. Haka aka dinga zuwa har gida ana cin mutuncin A'isha, sai dai su haɗe kai da Yakura da bata ɓoye ma komai ba suyita kuka. Ana tsaka da wannan rikicin jikin Yakuran ya rikice matuƙa, A'isha ta dinga bin dangi tana neman taimakonsu amma kowa ya nuna bazai iya ba bai da shi. Sai kawai ta yanke shawarar saida gidan da suke domin takai Yakura asibiti. Abinda ya bata mamaki sai ga ƴan uwan Abdul-rasheed sunyi uwa sunyi maɗaukiya, ƙarshe ma Yayan nan nashi da suke kira da Yayan gandu daya ce yana son aurenta ne ya sai gidan. Haka ta share bata nuna ta damu ba takai Yakura asibiti, ta biya kuɗi za'a mata aiki da tun farko likitoci suka faɗa rashin kuɗi ya hana. Sai dai UBANGIJI mai hikima bayan yin aikin da kwana biyu ALLAH ya ɗauki ran Yakura😭.
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wato gigita da magagin tashin hankalin da A'isha ta shiga da Haysam mai ɗan wayo a cikin ƴaƴan ɓata lokaci ne ma wajen zana shi. Dan Yakura haihuwar Haysam ne kawai batai ba. Amma komai da uwa take ma ɗa ta masa. Haka tsakanin Yakura da A'isha zamane na amana da ba'a batun wani kishi. A ranar da Yakura zata koma ga ALLAH ta kama hannun A'isha dana Haysam ta jaddada musu ta bar musu amanar ƴaƴanta. Bata yarda A'isha ta bama wani su Ma'aruff ba a duniya koda ƴan uwanta ne da suke uwa ɗaya. Tace ta baiwa A'isha har abada, ta kuma bama Haysam dake matsayin Babban yaya ya koma Uba a yanzu. A haka ALLAH ya ɗauki rayuwarta hannayensu riƙe a hannunta.
A wannan rasuwa A'isha ta sake tabbatar da lallai suna cikin halin shiga uku ita da waɗan nan yara har takwas, dan kuwa Yakura batai wata biyu da rasuwa ba Yayan gandu ya sake zuwama A'isha da batun auren da yay mata a wancan karon, da tace bata yarda ba yace to ta tattara yara ta bar masa gidansa, ya bata sati ɗaya kacal. Hankalinta ya tashi, ta kira Jamilu autan su Abdul-rasheed ta sanar masa komai dake faruwa, harna sharrin farko da Yayan gandu yay mata, shima hankalinsa ya tashi, dan basu taɓa sanin gaskiyar zancen ba sai yanzu, amma sai yace su koma gidansa dan babu yanda zai yi tunda yayansa ne. Dan haka suka shiga tattare kayansu, abinda zai zama kaya A'isha ta saida shi, sai kayan sakawarsu da abubuwa masu muhimmanci kawai suka koma gidan Jamilu da zama. Sai dai ko wata basu cikaba sabon kalubale ya ɓullo daga matar Jamilu, dan ƙiri-ƙiri ta nuna ita bata yarda da wannan zama ba. Taya tana amaryarya haihuwa ɗaya (dan zuwa yanzu itama ta haihu) ace azo a cika mata gida da ƴaƴa. Rikici ita da mijinta A'isha taga aurensu na neman mutuwa ta shiga tsakani da roƙon Jamilu ya barta ta wuce Kano. Zai tada hankalinsa ta lallaɓasa da nuna masa muhimmancin yin hakan. Badan yaso ba haka A'isha ta hau shiri, da taimakonsa da rakiyarsa A'isha da ƴaƴanta takwas tai bankwana da garin Bauchi ta koma garinta na haihuwa Kanon dabo....
Babu zato babu tsammani Inna ta wayi gari da baƙin Bauchi. Al'amarin ya girgiza mata zuciya, duk da kuwa kullum dama addu'arta ALLAH ya kawo ma A'isha mafita, dan tunda taje rasuwar Yakura ta sake tabbatar da Bauchi bazata zaunu ga ƴar tata ba. ALLAH sarki rayuwa, bayan shekaru goma sha shida A'isha ta dawo gidansu babu Abdul-rasheed a duniya. Tayi aure tana da shekara sha huɗu. Shekararsu goma sha huɗu da Abdul-rasheed, yanzu yana shekara biyu da wasu wattani da rasuwa. Haysam nada shekara goma sha uku da wasu watanni a duniya. Ja'afar da Ma'aruff nada shekara takwas, Bilal nada shida, Ummi nada biyar. Mommy nada huɗu da wata takwas, Ammar nada uku da wata huɗu, sai ƴar da Yakura ta haifa a ƙarshe da taci sunan A'isha suna kiranta MiMi nada ɗaya da rabi. A yanzu A'isha nada shekara talatin da ɗaya ne cif a duniya.
Inna ma ba mai ƙarfi bace, dama Abdul-rasheed ne ke mata komai a yanzu, hatta da karatun su Bashir, dan tunda ya rasu suma su Bashir ɗin karatun ma ya nema taɓarɓarewa sai da Nasiru ya shiga ya fita ya samar musu wani taimako sannan. Ƴar sana'ar koko Inna keyi da safe yanzu, sai daddawa, da itace take ruƙe su ita da su Tasi'u da yake ba zama suke ba a gida koyaushe suna ma makaranta ne a Zaria, yanzu ga A'isha da iyalanta sun ƙaru. Lissafin ya canja ƙwarai da gaske. Ita kanta A'isha tunda ta shigo gidan take tattauna abubuwa a zuciyarta, da yanda rayuwa zata sake kasancewa. Amma dai tasan zama bashi yiyuwa, babban tashin hankalinta karatun yaran, duk rintsi bata fatan karatun yaran ya tsaya musamman Haysam dake jss 2 zai tafi jss 3 ne nan da ƴan watanni. Haka taita lissafi tun a daren da suka iso Kano ko rintsawa batayi ba. Washe gari karatun ya fara mata maimaicin kansa a cikin ƙwaƙwalwa. Ga Haysam tunda suka zo ya tsangwami kansa sai dai ka gansa zaune gefe shiru. Koda yake tunda Yakura ta rasu rashin maganarsa ta sake girmama fiye da bayan rasa mahaifinsu. Ya sake zama mara fara'a da yawan walwala.........✍🏼
_Rayuwa kenan, akowane motsi bawa baya rabo da jarabawa da sabbin ƙaddariri, ALLAH ya baki wuyan ɗauka A'isha🥲._
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 23_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp
07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.......Zak-Shadow da su Mammah sun wuce Kano, zasuyi hutu na makwanni har shida. Ashe walima Mammah ta shirya masa. Dan haka suka iske gida cike da danginta anata girki. Ƴan Bauchi dai iya kawunsa ne kawai sai Khadijah da Alawiyya suka zo. Bai damu ba, wanda ya gani ɗin ma sun wadatar. Anci ansha an masa addu'oi kala-kala harda mutanen anguwa.
Bayan kwanaki biyu gida ya koma sai su kaɗai, Zak-Shadow ya sake fahimtar rayuwa ta canja ga mahaifiyarsa, ta tabbata dai bata tare da sabon mijinta. Sai dai yanzun ma bai tambaya ba saboda girmamawa har sai da Mammah ta sanar masa komai a wannan karon da bakinta. Tabbas zuciyarsa ta hasala matuƙa, amma bai ce komai ba dai a zahiri. Itama Mammah data fahimci yanayin nasa sai tai masa nasiha da gargaɗinsa akan kar taji wani abu daga garesa. An riga anyi ya wuce sai a tari gaba. Badan yaso ba yay shiru kamar yanda ta gargaɗe san.
A cikin wannan hutu ya samu damar bibiyar karatun ƙanensa, har zuciyarsa kuwa ya gamsu da yanda komai ke tafiya Alhamdullah. Musamman ma su Ja'afar ƴan Secondary. Ya ji daɗin kuma ganin yanda kasuwar Mammah tai tasiri a gida. Ya ziyarci Malam Zayyanu da abokinsa Malam Datti. Sun masa addu'a sosai da nuna jin daɗin nasarar da ya samu a NDA.
Duk da yana cikin hutu bai daina yin motsa jiki da safe da yamma ba, kamar yadda suke yi a NDA. Wani lokacin idan yana fama Mammah har faɗa take masa ya huta. Yakan yi murmurshi ne kawai ya ce, “Mammah idan banyi ba jikina zai yi ciwo ne”.
Haka dole ta ƙyaleshi har hutunsu ya ƙare, kamar kuma yanda yay alƙawari yaje Bauchi tare da su Ma'aruff cikin weekend. Sun ziyarci kabarin mahaifinsu da Umma har ma da kakaninsu su Malam. Babu wanda yasan yaje a ƴan uwan mahaifinsu sai kawunsu Jamilu kawai, dan basu kwana ba a ranar suka juyo Kano.
A watan Agusta ya koma Jaji, domin yin Young Officers Course, inda ya sake haɗewa da Imran, a wannan karon ma a ɗaki ɗaya suka zauna, dan sai da sukai duk yanda zasuyi aka haɗasu cikin amincewar UBANGIJI. Alhamdullahi sun kamalla course ɗin su a farkon shekarar 1999, daga nan kowa aka turashi inda zai fara aiki. sai dai an samu matsala dan anyi posting ɗinsu waje daban-daban shi da Imran, amma da yake suna da oganni tuni suka nema oga Adetunji suka sanar masa damuwarsu. Shine yay ta kai kawo har aka haɗasu waje ɗaya yanda suke fata, antura su aiki zuwa 82 Division Enugu, inda suka fara rayuwar soja ta zahiri. A can suka gane cewa aikin soja ba na jarumtaka kaɗai ba ne, aikin zuciya da sadaukarwa ne.
★Su Zak-Shadow na Enugu cikin sabuwar rayuwar aikin soja, anan rayuwar Mammah da marayun ƴaƴanta na neman canja salo da fuskantar sabuwar jarabawar rayuwa. Domin kuwa Zak-Shadow bai wuce watanni uku a Enugu ba Tasi'u ƙanin Mammah ya zo kwatsam. Zuwan daya saka Mammah a farin ciki dan tayi tsammanin har abada ta rasa dukkan ƴan uwa a duniya.
Da farko dai kamar abin arziƙi tsakaninta da Tasi'u, dan harda zama ya bata labarin rayuwar da yake ciki ta tashin hankali. Yarinyar daya aura basu ko ƙulla shekara ɗaya ba a rayuwar aure suka rabu, ya shiga halin rayuwa mai tsanani a sabuwar ƙasar da bai san kowa ba, haka ya jure saboda karatun da yake yi. To zuwa yanzu ya kammala, acewarsa har ya samu aiki, yanzu ma yazo gida ne domin wani aiki da zai yi na wata uku ya koma. Mammah ta jajanta masa ta kuma tayashi farin ciki.
Sunyi sati kamar uku a wannan farin cikin kwatsam rana tsaka sai ga Tasi'u da lauyoyi har biyu da wasu mutane, wai yana son a raba gida a bashi nashi kaso. Mamaki ya kama Mammah, ta kalla gida ta sake kallo, tabbas gidansu babba ne, gashi a bakin titi, kusan a yanzu ma gidan yafi duk wani gida na layin ƙyau saboda gyaran da Alhaji Nura yay masa lokacin daya aureta. Da farko ta ɗan so tirzawa tai masa faɗa, ya nuna mata shifa ba yaro bane, sannan gidan nan dai yana da hakki ai kuma dolene a bashi nashi hakki. Ganin yana son su zubar da mutunci a anguwa tace ba damuwa yayi duk yanda yaso, ko ɗaki ɗaya ta samu ALLAH ya amfana zata zauna da yaranta. Haka kuwa akai yayta shiga da fita batare daya bari tasan yaya komai yake tafiya ba. Kwatsam a cikin wata na biyu da zuwansa ta nemeshi ta rasa. Duk inda ya kamata ta bincika kuma tayi amma babu shi. Hankalinta yaso tashi kawunsu yace karta damu kanta, ta barshi duk ma inda yaje zai dawo tunda ba yaro bane. Haka dole ta haƙura ta share. Abin mamaki cikar wata ɗaya saiga wasu mutane wai sunzo gidan nan da take ciki nasu ne an sayar musu, suka nuna mata takardu harma da shaidun gani da ido da akai ciniki da su. Hankalin Mammah ya tashi kwarai da gaske, sai ta rasa inama zata saka kanta dan tashin hankali, kawai ta yanke jiki ta faɗi sai da aka kaita asibiti. Kwananta biyu aka sallamota, abu dai kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba Tasi'u ya saida gida ya gudu. Masu gida kuwa sun bata wata ɗaya kacal suna buƙatar gidan akwai abinda zasuyi da shi.
Wannan tashin hankali ya saka Ma'aruff da Ja'afar sulalewa suka tafi Enugu suka sanar ma Zak-Shadow. Kwatsam babu zato ya gansu, mamaki ya kama shi ya balbalesu da faɗa domin a ganinsa ai kasada ce zasu kamo hanya batare da sanin gari ba su taho. Su dai haƙuri suke ta bashi, Imran dai ya kwacesu da ƙar, shine ya basu abinci sukaci ya basu wajen kwanciya. Zak-Shadow bai saurarensu ba sai dare, anan ne suka sanar masa abinda ke faruwa da halin da Mammah ke ciki, suka tabbatar masa a yanzu ma sunzo ne bada saninta ba, dan sun tabbatar tana can tana nemansu ƙilama hankali a tashe..
Jin wannan zance ya sake ɗaga hankalin Zak-Shadow, haka ya samu da ƙyar da kamun ƙafa aka bashi damar zuwa gida kwana uku kawai. Ya taso ƙanensa gaba suka nufi Kano. Aiko hasashen su ya tabbata, dan sun sami Mammah cikin tashin hankalin rashin sanin ina su Ja'afar ɗin suke, sai kuma gashi ta gansu harda uban gayya Haysam. Kukan dake danƙare da ƙirjinta sai a lokacin ne ta samu ta yi shi. Wannan al'amari ya sosa zuciyar Zak-Shadow matuƙa. Wanda ma bai san fushinsa ba a wannan karon ya gani kwarai da gaske.
Ɗan kuɗin albashinsa da yake faman ajiyar taro da kwabo a account ya kwashe domin sayen fili, sai dai a karo na farko Kano ta fita masa a rai gaba ɗaya, yana son yin nesa da ita nisa mai yawa ko mahaifiyarsa zata samu salama tamkar yanda ta baro Bauchi, amma kuma bai san ina zai maidasu ba, dan haka ya nema shawarar Imran ta hanyar kiranshi a wayar landline. Babu wani ja'in-ja Imran ya bashi shawarar zuwa Abuja kawai, ya kuma haɗashi da yayansa.
A ranar Haysam ya bar Kano zuwa Abuja. Inda da taimakon yayan Imran suka samu fili suka saya. Sauran kuɗin daya rage ya sayi siminti da bulo aka fara ginin ɗakuna ƙwara biyu kacal. Kwana uku aka bashi kawai a wajen aiki, dan haka dole ya koma Kano yabar sauran aikin wajen yayan Imran. Yana zuwa Kano ya sanar ma Mammah komai, mamaki ya kamata sai kuma ta shiga yi masa faɗa akan dammi zai yi hakan. Shi dai kansa a ƙasa kawai yana bata haƙuri ne. Sai da ta kammala yace su fara shiri kawai, nan da kwanaki kamar goma zasu koma can shi kuma ya shirya ya koma Enugu.
Haka kuwa akayi, kwanaki goma bayan komawar Zak-Shadow yayan Imran yazo har Kano da mota ya kwashi su Mammah da yaranta. Tafiyar data sakata kuka sosai, jikin ƴan uwanta yay sanyi da rashin taimakonta da basuyi yunƙurin yi ba har Haysam ɗin ya yanke hukunci. Dan sun so hanata da nuna mata zasu ɗauki mataki tace ba komai zata koma Abujan kawai dan itama bata son zaman Kanon a yanzu.
Wannan shine sanadi kuma mafarin barin Kano dasu Mammah sukai suka dawo Abuja. Ɗaki ne guda biyu kawai, sai aka zagaye gidan da kwanon langa-langa. Dan Zak-Shadow ya nuna baya son taimakon komai daga wani saboda Yayan Imran yaso yin hakan. Shima kuma Imran ɗin yaso yin hakan amma ya haƙura dan yasan wanene Zak-Shadow, idan yace baya son abu to kawai baya so ɗin da gaske.
Yana sake ɗaukar albashin watan ya nufo Abuja, kuɗin yay amfani da su wajen maida ƙannensa duk makaranta, su Ammar ma da ba'a saka ba ya sanya su. Dama Mammah tunda suka dawo bata zauna ba, haka ta dinga shiga tana fita wajen nunama mutane kayan sana'arta ta koli. Sannu a hankali aka fara ganewa, kasancewar sabuwar anguwa ce kafin mutum yaje kasuwa sai yafi ganewa zuwa wajenta sayen abu a sauƙaƙe. Ganin haka ta fara haɗawa da kayan miya, da wannan sana'ar da albashin Zak-Shadow suka cigaba da rike rayuwarsu, idan an samu ɗan rarar kuɗi a sai siminti a ɗan ɗora gini. Kwatsam sai kuma ga wata ƙaddarar ta sake afkawa Zak-Shadow lokacin da yake shekara biyu da fara aikinsu, wai ya buɗe wata gaskiya wani ogansu yayi kutun-kutun an saka shi a prison. ALLAH sarki rayuwa, a wannan gaɓar ALLAH dai ya ƙaddara Mammah kam bazata rasa ranta ba. Dan bama ita kawai ba hatta su Ma'aruff sun shiga wata irin gigitar rayuwa.
Haka Mammah ta dinga bin duk wanda ta sani cikin roƙo da magiya don ganin Haysam ya kuɓuta. Amma ina, Imran ma iya bakin ƙoƙarinsa yake amma al'amarin kamar da wani babban shiri a cikinsa. Hatta su Adetunji sunyi iya yinsu Zak-Shadow bai fito ba. Ga baƙar wahala suna bashi ta tashin hankali kamar sun sami criminal, duk mai hankali yaga wannan al'amari yasan akwai lauje cikin naɗi a ciki, sai dai kai tsaye basu san wa zasu fuskanta suce yayi ɗin ba..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na