Author : Billyn Abdul Category : Adventure
dake tafiya amsa kiran suma a babban filin taro. Bayan sun gama hallara kaf kowa yana daga tsaye a nutse babban Officer ya tsaya a gaban su da takarda mai ɗauke da jerin sunaye ya fara jawabi kamar haka..
“Today, you will be assigned to your permanent Companies. Once your name is called, move to your Company’s block. That will be your new home.”
A tare suka amsa da kalmar, “Yes Sir!”.
An fara kiran sunaye ɗakunan da sunayen wanda zasu kasance a cikinsu ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda aka kira zai amsa ya nufi inda aka nuna masa. Kowane ɗaki da iya adadin mutanen da ake buƙata. Kasancewar ana binsu a jere ne a kiran sunayen har aka zo kan H, Haysam na cikin H ɗin ƙarshe, cikin sa'a kuma Imran na cikin I ɗin farko. Kamar yanda ake kiran kowa aka kira sunan, Haysam Abdul-rasheed Shehu.”
Cike da nutsuwarsa ya amsa yana mai miƙewa tsaye, “Yes, Sir!”, ya faɗa yana nufar inda aka nuna masa an rubuta Alpha room. Kamar abin almara sai ya sake jin an furta, “Imran Abbas.”
Haysam ya juyo cikin mamaki, Imran ma yana kallonsa cike da farin ciki har murmushi na ƙoƙarin bayyana kansa akan fuskarsa. Shi kansa Haysam sai da ƙaramin murmushi ya bayyana kaɗan a saman tashi fuskar. Dan bayan ƙanensa Imran shine na biyu daya ji yana so tamkar jininsa. Gashi dai suna matsayin sa'anni ne a shekaru, amma raunin Imran dake a bayyane yasa yana jinsa kamar ƙaninsa daya kamata ya bama garkuwa. Badan Imran ya bashi labarin shine yake son aikin soja da kansa ba da ya ce an tilasta masa ne da tsiya saboda yanda yake a raunane. An ƙaro mutum biyu cikinsu, dan kowanne ɗaki na ɗaukar mutane huɗu ne. Gado biyu ne sama da ƙasa. Biyu a sama biyu a ƙasa. Sai lockers da sauran abin amfani kowa da nashi da ma sunansa a jiki.
Kowane group an haɗa su da Officer ɗin da zai kula da su. Bayan sun shigo nasu ɗakin wanda ya jagorancesu ya nuna musu ɗakin da faɗin, “Each room, four cadets! You are brothers now. You eat together, you fight together, you win together.”
“Yes Sir”.
Sunan Haysam ya fara kira yana nuna masa nashi gadon. “Haysam Abdul-rasheed Shehu bunk na ƙasa, Imran Abbas kuma gadon saman Haysam. Da wani irin farin ciki Haysam da Imran suka kalli juna suna murmushi kamar ɗazun, wannan lokacin ya tabbatar musu cewa rayuwarsu zata ci gaba da tafiya a tare kenan, abotar da aka ƙulla batare da tabbacin rayuwar waje ɗaya ba bisa rahamar UBANGIJI da dubin zuciya ta tabbata..
Suma sauran kowa an bashi nashi. Basu zauna ba suka fara shirya abubuwansu a inda ya dace da yanda suke buƙata. Musamman ma abokai biyu da farin cikinsu ya kasa ɓoyuwa.
★Da daddare bayan kowa ya kwanta, sai Imran ya ɗan leƙo daga sama, yana magana a hankali da kallon fuskar Haysam da yay kwanciyar rigingine a gadonsa yay filo da hannayensa duk biyu.
“Zak... kana jin kamar rayuwa ta canza ko?”
Buɗe idanun Haysam yayi a hankali ya sauke su kan fuskar Imran daya leƙo ta sama. Wani ɗan guntun murmushi yay masa. Kamar bazai ce komai ba sai kuma a ciki ya furta, “Imran!. Tabbas rayuwa ta canza, canjawar data nisanta mu da ahalinmu da su kaɗai muka sani a rayuwar jiyanmu. Amma da kai tare a nan sai ta zama mai ɗebe kewa da koyar da sabon darasi”
Ƴar dariya Imran ya yi cike da jin daɗin kalaman sabon abokinsa Haysam. Hankali kwance kuma kai tsaye cikin son fidda abinda ke zuciya ya ce, “Ni ma haka nake ji My Zak-Shadow, kamar kai ne garkuwata, ɗan uwana jinin jikina da ya ɓuya sai yanzu ne ya bayyana min kansa”.
Hannu Haysam ya miƙa masa, shima Imran ya miƙo nashi suka riƙe juna. Cike da tabbatarwa ya ce, “Ni kuma ba zan bar ka ka faɗi ba in sha ALLAHU Imran. Ba'a nan kawai ba, a ko inama. Ka sani kana cikin lagona da in har aka hareni ta hanyarka tabbas zan faɗi, faɗuwa irin ta kwanciyar da babu juyi a ciki. Ka riƙe alƙawari, ka riƙe amana, ka tuna wannan koda anan gaba”.
A hankali hawayen da suka cika idon Imran suka gangaro suna ɗiga a fuskar Haysam. Bai share ba, bai sakar masa hannu ba kuma har wani lokaci. A wannan daren kafin su rufe idonsu, sautin bugun tambarin alƙawarin riƙe amanar juna ya gama zagaye zuciyoyinsu. Rayuwar soja ta gaske ta fara a cikin ƙwaƙwalensu, sun yarda su biyu sun riga sun zama abokai, aminai, kuma ƴan uwan juna a cikin ɗakin Alpha dake wannan makaranta ta NDA.
Ƙarfe 4:30 na asuba aka busa ƙararrawa mai ƙarfi. Duk da har yanzu duhu ne muryar ɗaya daga cikin senior cadets ta farkar da su Haysam kamar sauran ƴan uwansu sabbin ɗalibai.
“Wake up, gentlemen! You’ve got 5 minutes!”
Imran sarkin tsoro kuwa ya zabura yana neman faɗowa a gadon, jikinsa sai rawa yake saboda tsoro. Haysam kuwa ya tashi da natsuwa kamar yanda ya saba a gida idan Mammah ta tashe sa. Gadon ya dafa cikin sanyi da muryar wanda ya tashi a barci ya furta, “Ka nutsu Imran, ka sauka a hankali. Ka tsaya a gefe na, ka koyi komai a hankali da nutsuwa, gaggawa taɗiye mutum take daga cimma burin nasara, haka Abiy na ke gaya min sanda ina yaro”. Ya ƙare maganar yana kama hannun Imran ya taimaka masa ya sauko a hankali.
Suna fita daga ɗakin iska mai sanyi ta bugi fuskokinsu, sai ƙarar ƙafafun ɗalibai kake ji a kan ƙasa. Wani senior mai ƙarfin jiki ya tsaya a gaban su da fitilar hannu yana ta faman haskesu cikin ido da faɗin, “Down for push-ups! Let me see soldiers, not boys!”
Gudu suka fara iya ƙarfi kamar yanda aka basu umarni. Tun ba'ai rabin filin ba wasu suka fara kukan gajiya. Imran kam da ba ƙarfin zuciya yana neman kaiwa ƙasa ne ma, amma Haysam ya matsa kusa da shi, yana faɗin, “Ka cigaba, kada ka tsaya Imran. Ka kalle ni kaji. Idan ka faɗi ka sani nima zan faɗi”.
Wannan magana ta ƙarfafa shi sosai har ya yi mamakin kansa, ɗan daga nan yaji kawai ya ƙara ƙaimi har suna tafiya a jere da Haysam, Alhamdullah cikin nasara suka kammala round ɗin farko. Koda aka ɗan huta aka koma kuma nan ma bai sare ba sam. Dama shi oga kwata-kwata ko'a jikinsa. Komai Haysam na yinsa ne da ƙarfin jiki da zafin nama kasancewar zuwa yanzu ya saba da wahalar rayuwa, to tallar da yake yi ɗin nan zagaye kasuwa ai ba wasa ba. Wankau ɗin Mammah, ɗibar ruwa. Hatta daka idan ta amsa tare sukeyi in dai yana gida. Wannan wahalhalu sun taka rawar gani a rayuwarsa ƙwarai da gaske har yake jin wannan ƙwarin gwiwar a yanzu da son ƙarfafa irin su Imran masu rauni da gata yasa basu saba da wahala ba.
Bayan an gama sunyi sallar asuba, suka dawo wajen rarraba breakfast packs. Imran yana jin kamar ƙafarsa bata motsi da ƙyau, sai Haysam ya karɓi nasa kwanon ya riƙe masa zuwa wajen zama. Sannan ya taimaka masa ya zauna yana jera masa sannu. A gefe ɗaya, wasu senior cadets suna kallon Haysam cikin mamaki, sauran ƴan uwansa duk a galabaice, amma shi a tsayensa yake kamar ma baiyi komai ba yana a nutsuwarsa da karfin hali, ga kuma yana da tausayi fiye da kowane sabo a cikin su. Wani daga cikinsu ya ce, “Wato wannan yaron akwai wani abu daban a idanunsa, ku kula sam bashi da tsoro ko fargaba balle jin karaya kamar yanda sauran suka nuna”.
Wanda ke kusa da shi ya ce, “Ƙaryar banza, yo mi aka fara da mazan. Yau kawai kake masa wannan yabon. Ka bari suci watan farko dan Babansa wlhy sai ya rusuna wannan zafin kan nasa yabi iska”.
Dariya suka sanya suna mai tafawa cike da shaƙiyanci. Duk abinda suke faɗa kuwa a kunnen Haysam, amma ya basar kamar ba jinsu yake ba yana maida hankalinsa ga Imran dake shan ruwan zafi a wahale. Koda Imran ya kallesa sai ya sakar masa murmurshi, baki Imran ya ɗan tura tare da faɗin, “Ka bar yi min wannan murmushin naka mai kama dana ƙeta. Wlhy da kai ne kawai nake jin karfin hali a nan, amma ji nake kamar na fasa na gudu gida”.
Haysam ya sake murmusawa yana daidaita beret ɗinsa a saman kai. “ Haba mazan fama wane gudu kuma ana zaune ƙalau, ai in ka ganka a waje hutu zamu, in sha ALLAHU kuma mu dawo da ƙafafunmu a ɗora daga inda aka tsaya. Daga yau ka ɗauka mu biyu ne a tare, wani bazai bar wani a baya in sha ALLAHU. Ba zan a taɓa barin wani ya cutar da kai ba. Kaima bazaka taɓa barin wani ya cuta min ba”.
“Yes Sir! Ina sha ALLAHU”.
Imran ya faɗa yana salute ɗinsa. Dariya Haysam yayi yana kai masa naushi. Da sauri ya kauce shima yana dariya. Idan ka gansu dole su birgeka, dan a kallo ɗaya zaka tabbatar da aminci mai tsafta ya shiga zukatan waɗan nan matasan zakunan guda biyu. Kuma ina sha ALLAHU zasu kafa tarihi mai ban mamaki da taɓa zuciyar duk wanda zai bibiyi labarinsu.........✍🏼
__________
TALLAH
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7
Mmn surayya me kayan kamshi
Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa
Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada
Turaran wuta na danal banat
Kajiji
Turaran kaya watau abbasiyya
Kabbasa spray
Humra
Kwallacca
Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu
Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇
08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 29_
__________________
https://wa.me/+23408067422528
Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba.
Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa.
Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka
Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne.
Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki.
Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.
https://wa.me/+23408067422528
“Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar ’ya’yanki a gida ba?” ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne
Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇
https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........WASHE GARI su Haysam suna tsaye a layi, jiki a sharɓe da zufa, wasu har suna rawar tsoro saboda an ce yau ce the real beginning. Major Adetunji, babban jami’in horo, ya tsaya a gaban su da ƙarfi, yana ta kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamar mai tantance fuskokinsu. Kafin cikin buɗaɗɗiyar muryarsa mai kaɗa hanjin marasa ji ya shiga faɗin, “Welcome to the Nigerian Defence Academy. From today, you are no longer civilians! You are cadets, and you will either become men here or quit!”. Sai kuma ya ƙara ƙarfin muryarsa cikin sabon ihu ya sake faɗin, “Drop down! Ten push-ups… No, make it twenty!!”.
Cike da zafin kai irin na farkon balaga da jin kansu su maza ne wasu a cikinsu suka fara gunaguni ƙasa-ƙasa. Sai dai babu damar cewa baza'ayi ba. Dan haka suka fara kamar yanda aka umarcesu a tare kuma. Ai ba'a wuce 7-8 ba wasu suka fara zubewa ƙasa saboda gajiya. Sai ƙalilan a cikinsu irin su Haysam masu taurin zuciya da sabon wahala ne suka cigaba da yi har ƙarshe. Haysam da idanunsa ke a rufe yana kammala nashi push-ups ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa daram, kamar wanda yake numfashi ne kawai, ba wahala yayi ba.
Cike da mamaki Senior cadet ɗaya ya zo da fuskar tsoro, yana ƙoƙarin tsoratar da shi, “You think you’re tough, new boy?!!”.
Haysam dai bai ce komai ba. Yana tsaye kuma akan ƙafafunsa yana kallon sa kai tsaye idanu ƙyam babu alamar jin shakka. Kawai sai Senior ɗin ya ɗan tsaya yana kallonsa shima cikin ido, ganin fa Haysam bazai janye nashi ba sai shi ya janye nasan yayi murmushi mai cike da ma'anoni yana girgiza kai da faɗin, “Hmm… we’ll see how long you last”.
Nan ɗin ma ko gezau Haysam baiyi ba. Imran kuwa yana gefensa yana rawar jiki, a ransa yana mamaki taurin kan Haysam. Bashi akema tsawar ba amma ji yake ƴan cikinsa na motsi wlhy. Amma kalla shi wanda akemawa ɗin ko a slippers ɗinsa ma. Ba Imran kawai ba, sauran mate ɗin nasa ma da Seniors ɗin hankalinsu ya koma kan Haysam ɗin, sai dai babu wanda ya sake cewa komai aka cigaba da basu horo.
Bayan horo na farko, aka shiga weapon drill. Ana koya musu riƙe bindiga da tsaye kamar sojoji na gaske. Wasu sai mutsu-mutsu suke sun kasa daidaita hannayensu, amma Haysam yana gefe yana riƙe da bindigarsa tamkar wanda ya shekara yana yi. Tsayawa Captain Adetunji wanda yake lura da su yay a kusa da shi.
“You! what’s your name, cadet?”.
“Cadet Haysam Abdul-rasheed Shehu, sir!”
“Good stance. Good grip. You’ve done this before?”
“No, sir. But I learn fast.”
Captain ya ɗanyi shiru yana masa kallon mamaki, sai kuma ya ɗan murmusa da ba kasafai yake yin haka ba dan irin mutanen nan ne da sam basa fara'a basa wasa.
“Keep that spirit. Nigeria needs men like you”. Ya sake faɗa yana ɗan bubbuga kafaɗar Haysam ɗin. Kai Haysam ya jinjina masa cike da girmamawa.
Bayan an kammala an sallamesu suna shiga hostel, Imran ya jingina da gado yana magana cike da raɗa idonsa akan Haysam.
“Kai Haysam kana bani tsoro wlhy, ni kam ban taɓa ganin wanda yake da karfin zuciya da rashin tsoro irin naka ba.”
Ɗan harararsa Haysam ya yi da murmushi mai sanyi kawai yana girgiza kai. Sai da ya kai zaune a bakin gadon su yana cire takalmin ƙafarsa sannan ya bashi amsa da, “Ba ƙarfin zuciya bane ko rashin tsoro Imran. Imani ne da abin da nake so in zama, tare da son cika burin Abiy na”.
Zama shima Imran yayi yana sauke ajiyar zuciya. Ya ce, “Gaskiyar ka kuma Zaki na. Nima in sha ALLAHU zan dinga jin ƙarfi da ƙarfin son cikar burina kamar kai. Da yardar ALLAH wataran sai mun tuna hakan munyi dariya tare munyi kuka tare”.
“ALLAH ya tabbatar”.
Cewar Haysam yana kaiwa kwance a gadon.
__________★
Da daddare gari ya yi sanyi sosai a NDA. Ko ina ya cika da shiru sai ƙarar iska dake kaɗawa da motsin fallen langa-langar rufin ɗakunansu. An kashe fitilun waje, sai hasken ƙaramin bulb da yake haskaka ɗaki na 17 Alpha room da sautin minsharin room mate ɗinsu biyu masu saurin barci. Haysam yana kwance kan gadonsa, jikinsa har yanzu na ciwo amma zuciyarsa cike da natsuwa. Imran kuwa yana daga sama shima ya kasa barci sai faman juyi yake a gadon, yana gumi alamar wanda ke mafarki mai nauyi.
Can kuwa sai ga muryarsa na fita kamar cikin kakari irin na wanda yasha shaƙa a hannun wani. “Ka barni… don ALLAH kar ka sake min haka… Mama… Mamaaa!”.
Da sauri Haysam ya tashi, ya sauka daga gadonsa cikin sassarfa. Tsaye ya miƙe tare da kai hannu kan Imran ya shiga jijjiga kafaɗarsa, “Imran… hey, wake up. Lafiya kuwa? Kaga tashi…”
A firgice Imran ya buɗe ido da sauri, sai kuma ya zabura zaune jikinsa na rawa. Idonsa cike da hawaye, numfashinsa na fita da sauri kamar wanda aka fito da shi daga ruwa. Hannun Haysam ya damƙe tare da matsowa sosai kusa da shi cikin muryar kuka ya ce, “Na… na sake ganin su.. sun sake kamani Haysam”.
Kallonsa Haysam yake cikin tausayi, sai kuma ya ɗan dafa kansa kamar mai dafa kan Bilal.
“Shhhh… ka yi shiru. Mafarki ne. Ba kowa a nan. kai da ni ne kawai da su Peke. Kayi addu'a ka canja kwanciyarka ta wannan ɓarin”.
Sai kuma ya juya ya ɗakko ruwa ya miƙa masa. “Ka sha ruwa, ka huta. Kada ka bari mafarki ya firgita ka.