KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   15 / 49

42K to 45K   out of 146.5K words

wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Tabbas an ɗauro auren Umaru lafiya a garin Barno, dan kuwa shi a can ya ɗakko tashi matar da suka haɗu a wajen karatu a Zaria. Su Abdul-rasheed sunyi gangami sun halarci wannan aure a sabbin motocin daya saya musu shi da yayunsa biyu, akan suma sauran zuwa ƙarshen shekara in sha ALLAHU zai saya musu nasu, sannan ya biya hajji zasuje shi da Babban yayansu. Amma rayuwa bata da tabbas, a yayin dawowarsu Bauchi motar Abdul-rasheed tayi haɗari, a ciki kuma shine da yayansa na uku a ciki, sai abokansa biyu da Haysam.
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, haɗari ne mai gigitarwa da tada hankalin wanda ya gani, dan kuwa babbar mota ce ta hayesu tsaf. A take ɗaya a abokan Abdul-rasheed da Yayansa suka rasu, dan kuwa sune a gaban motar, abokinsa driver, yayansa a gefensa. Sai Abdul-rasheed da ɗayan abokin da Haysam dake tsakkiyarsu a baya. Wani hikima ta UBANGIJI sai akai kamar anyi wurgi da Haysam ta tagar motar, dan can waje gefe aka tsuntoshi babu rai, yayinda nan su Abdul-rasheed mota ya danne su, shi rabin jikinsa a waje ƙafafunsa zuwa ƙugu na ciki ƙarfen mota ya rabasu kaɗan ya rage ƙugunsa ya rabu da gangar jikin. Yana kuka da kiran sunan ALLAH yana kuma ambatar sunan Haysam da roƙon mutane su taimkesa su duba masa yaronsa karya mutu. (ALLAH sarki ɗa da mahaifi kenan😭, yana cikin azabtuwa amma bata kansa yake ba. Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭 🙏🏼, ka yafe musu laifukansu ya rabbi😭😭).
         Da ƙyar aka iya zaro su Abdul-rasheed a wannan mota, akai asibiti da su. Kafin ma a isa ɗayan abokinsa shima ya cika. Shi ko sai da yay kusan awa guda ma likitoci nata kai-kawo a kansa kafin ALLAH ya amshi abinsa. Wannan rana dole ya zama ranar ruɗani da ahalin Abdul-rasheed bazasu manta da ita ba a rayuwarsu. Ranar da ta raba su Haysam da mahaifinsu, ta zo cikin rashin shiri. (Wato mutuwa! Mutuwa! Mutuwa nada tashin hankali ƴan uwana, mutuwa nada gigita ƙwarai da gaske, wlhy bazamu gane wacece mutuwa ba sai randa tazo kammu. Wane shiri kai mata, wane shiri kake mata? Ka kammala baka kammala ba ko bakama fara ba wlhy sai tazo, zuwan da babu ɗaga ƙafa balle jiranka koda na sakan ɗaya danka kammala abinda ka fara😭😭).
       
         Mata ƴan biki nata kai-kawo anan Bauchi, sai dai jikin A'isha dana Yakura duk a sanyaye kamar marasa lafiya. Ga yawan faɗuwar gaba da suke samu da nauyin zuciya. Ita Yakura sai kowa ke ɗauka ciki ne. Itako A'isha ganin tasha jiyya bata ko jima da miƙewa ba sai kowa ke mata uzirin da sauran nauyin jiki. Sai dai ba haka bane ba, mutane kuma basu gane ba haka bane sai lokacin da labari ya iso cikin Bauchi, tun anayi ƙasa-ƙasa kada su A'isha su fahimta lokacin ma da ran Abdul-rasheed har dai ta fasu bayan rasuwarsa. Dan dole aka kwaso gawarwakinsu huɗu reras idan ka cire Haysam ɗan shekara goma sha ɗaya dake gadon asibiti likitoci na ƙoƙarin ganin sun ceto tashi rayuwar. Hakama matar Ayuba Yayan Abdul-rasheed dake fama da tsohon ciki duk tayi sukuku.
         A lokacin da aka shigo da gawar Abdul-rasheed data Ayuba rawa jikin A'isha da ƙus-ƙus ɗin mutane ya fara shiga kunnenta ya fara. Cikin ɗimuwa ta fito daga ɗakinta batare data fahimci inama take ajiye ƙafa da ɗaukewa ba ta durƙushe a gaban gawar mijinta da aka shimfiɗar a ƙofar ɗakin nata, hawaye na zuba kamar ruwan sama da ba ya ƙarewa. Hannunta na karkarwa ta kaishi kan babbar rigarsa da aka rufa masa dake jiƙe da jini ta yaye a hankali, fuskarsa dake da ƴan ƙananun raunuka ce ta bayyana, sai kawai ta tafi luuuu ta kife akan fuskar tashi ta sume musu. Dai-dai faɗuwar Yakura itama data fito daga ɗakinta a guje, ita kam jini ne ya ɓalle mata abinka da mai ciki. Ga matar Ayuba can ma ƙudar dole ta sameta. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ya rabbi ya rabbi mun tuba, mun tuba ya ALLAH 😭😭.
           Gida ya ɗauki koke-koke da ƙyar ake tsawatama mutane. Yayinda aka zubama A'isha ruwa a jiki ta farfaɗo, Yakura kam dole Inna Salame ce a kanta ana ƙoƙarin tsaida jinin daya ɓalle mata. Haka aka shigar da Abdul-rasheed ɗakin A'isha da Ayuba cikin jini babban Yayansu da mai bi masa sukai musu wanka aka shiryasu a tufafinsu na gaskiya. Tufafin da kai da ni suke jiran mu ma. Duk yawan kaya masu tsadar man da kika tara bango guda na drawer da wanda ka tara duk nan za'a barsu dama anan muka samesu. A naɗemu a wannan yankin farin ƙyalle tal kamar yanda a yau akama Abdul-rasheed da Ayuba. Haka ma sauran abokansa biyu an kaisu nasu gidajen ana musu nasu shirin suma...

            ALLAH sarki rayuwa kenan, taron biki ya koma taron makoki, da ƙyar aka samu A'isha ta iya sallama da gawar Abdul-rasheed. Yakura kam ma anata ƙoƙarin ceto rayuwar ta ne da abinda ke cikinta. Hakama matar Ayuba. Sauran ƴan uwansu makusanta sunyi sallama da gawar Ayuba da Abdul-rasheed kafin a fita da su ƙofar gida inda aka haɗe da sauran abokansa akai musu salla, sannan aka wuce da su makwancinsu na gaskiya. Makwancin da yake jiranmu ni dake, yanzu ko anjima ko gobe, koma yaushe ne dai sai tazo😭.
        Babu wanda hankalinsa ya koma kan batun Haysam sai washe gari. A'isha ta ɗan dawo hankalinta duk da a jiyan ma ba wani kukan shirme take ba. Yaran suna zagaye da su ita da Yakura da aka samu nasarar tsaida jinin daya ɓalle mata tun a jiya da dare. Sai Yakura ta ce, “Yaya ni naga kowa amma banga ɗan albarka na ba tunda gari ya waye”.
    A karo na farko A'isha tabi yaran da kallo itama. Su duka biyar suna nan, wanda take goye yana bayan Alawiyya. Cikin girgiza kai ta ce, Mama (dan haka take kiranta kamar yanda yaran ke faɗi) bana jin tun jiya ma ni naga ɗan nan naki ai”.
        A ɗan rikice Yakura ta tashi a zaune jikinta na rawa, idonta cike da hawaye ta ce, “Yaya tun jiya fa? Mun shiga uku ni Yakura, dan ALLAH ku nemo min cikin kawun nan ku, Haysam fa tare suke da Babansu Yaya. Kai Ma'aruff tashi maza kira min Kawu Nuhu”.
        Ba Yakura dake magana jikinta na rawa ba, itama A'isha rawar jikinta keyi, sai dai kamar wadda aka dokema ƙafafu ta gagara koda tashi balle cewa komai daga inda take. Har ita Yakuran ma tai ƙoƙarin daddafawa ta sauka a gadon tasa Ummi ta taimaka mata. Dai-dai nan Khadijah ta shigo, itama ido luhu-luhu alamar ansha kukan rasa ƴan uwa. Ganin halin da Yakura take ya sata saurin ajiye kwanon fura dake hannunta, dan ganin A'isha bataci komai ba tun jiya gashi yanzu har an kusa sallar azhar shine ta nema fura ta damo ta kawo mata nan ɗakin Yakura da taga ta shigo tare da yara duba ta.
         “Yi a hankali Maman Haysam (da yake haka suke ma Yakura alkunya, ita kuma A'isha suce Maman Ma'aruff) kin san da halin da kike ciki, inama zaki ke da akace ba'a son kina dogon motsi”.
     Muryar Fauziyya na rawa tace, “Yaya Khadijah Haysam, kin san fa tare suka tafi da Babansu, amma babu wanda yay batunsa tun jiya”.
       Sosai gaban Khadijah ya faɗi itama, dai-dai nan Ma'aruff ya shigo tare da kawunsu Nuhu, shima yana jin batun da suke tattaunawar hankalinsa ya tashi, sai lokacin ya tuna cewa lallai tare da Haysam aka wuce da Babansa asibiti, duk da shima babu wani alamu daya nuna yana a raye, amma yaji sanda ake sakashi a ambulance likitan na faɗin zuciyarsa na harbawa kaɗan-kaɗan, shiyasa ma ba'a sakashi cikin gawar su Ayuba ba. Ai babu zama ya fita da gaggawa, kai tsaye asibiti suka wuce shi da su Nasiru. Cikin amincin ALLAH suka samu Haysam ya farfaɗo tun da safe, likitoci nata cigiyar ƴan uwansa an duba kaf sun wuce tun juya kasancewar a rikice kowa yake. Tunda suka shiga ɗakin da Haysam yake kalma ta farko daya fara jeho musu shine “Kawu ina Babana?”.
      Babu wanda a cikinsu gabansa bai faɗi ba, amma suka dake cike da mazantaka suka zagaye shi suna lallashi da tambayar jikinsa. Shi ko yaro ne mai wayo, duk da shekarun nashi duka 11 ne a duniya ALLAH ya bashi basira sosai, sai ya ƙi amsa musu ya zuba musu ido kawai. Tausayinsa mai tsanani ya kama Nasiru, dama ga alhinin rasa aboki, kuma amini zagaye da ruhinsa. Sai hawaye sharr suka shiga rige-rigen zubo masa. Kafin ya kauda fuska Haysam ya ganshi.
      Kawai sai ji sukai ya ce, “Baban Kano kuka kake yi?”.
      Da sauri Nasiru ya shiga girgiza masa kai yana share hawaye. Amma sai Haysam ɗin ya ƙara faɗin, “Babanmu ya rasu ko? Irin rasuwar Baba da Inna da Gwaggon Maiduguri. Dama ranar nayi mafarki ai, dana gaya masa yace nai shiru kada na gayawa kowa mafarki ba gaskiya bane, gashi kuma ya zama gask....”
     Ya kasa ƙarasawa sai haɗiyar zuciya. Sai suka ga ya rufe idanunsa kawai. Gaba ɗayansu hawaye suke sosai, amma abin mamaki Haysam ko ɗigon hawaye babu a idanunsa, tunda ya rufe idanun nan shike nan, bai kuma sake magana ba har suka baro asibitin. Koda suka dawo gida mutane nata hamdala da ganin Haysam ɗin yana lafiya sai ƙananun raunuka. Kowa kuma na ƙara jinjina hukuncin UBANGIJI, dan duk wanda ya kalla motar su Abdul-rasheed da yanda su suka kasance, dan su dukansu likafaninsu sharkaf da jini aka bizne su a kabari amma ga Haysam ko babban ciwo babu a jikinsa. Babu wanda zai tunanin za'a samu wani mai sauran rai a motar nan.
         Rungume Haysam Yakura tayi tana kuka, amma A'isha ido kawai ta zuba musu. Koda Haysam ɗin yazo gabanta ya zauna bata iya ce masa komai ba, shima kuma bai iya yama kowa magana ba har lokacin. Duk wanda yace kuma yaga kukan Haysam a zahiri game da wannan rashi yayi ƙarya. Sai da dare A'isha ta kama shi a wani ɗan lungu cikin ɗakin Abdul-rasheed yana kuka shi kaɗai a cikin duhu. Hakan na nufin yazo ya ɓuya ne anan baya son kowa yaga yana kuka. A karo na farko taje kusa da shi ta zauna, tare da kamoshi jikinta ta kwantar da kansa a saman kafaɗarta, sai ya sake fashewa da kuka shima ya rungumeta. Itama kukan take yi sosai.
       Ranar a ɗakin nan suka kwana ita da shi, tana zaune dangan-gan, shi kuma tun yana a kafaɗarta har tai masa dabara ya zame ya kwanta kansa a cinyarta, a haka gabannin asuba barci ya sacesu su duka. Sai kiran salla ne ya farkar da su........✍🏼

Matan da suka rasa mazajensu ALLAH ya gafarta musu, ALLAH ya baku haƙuri bayin ALLAH, ALLAH ya raya muku zuri'arku ya albarkacesu, yasa su zama masu jinƙai a gareku😭😭🙏🏼.


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 22_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._



_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM
👇🏻👇🏻👇🏻
https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
👇🏻👇🏻
wa.me/2349030398006

TIKTOK
👇🏻
https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1




Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Anyi addu'ar uku, ranar addu'a mutane sun cika fal harma da wanda ba'a sani ba abokan aiki dana kasuwanci na Abdul-rasheed daga gari-gari. A washe garin cikon kwana na huɗu mutane suka fara raguwa. Sai ƴan uwa na jiki kawai da danginsu na Maiduguri sai su Innar A'isha ƴan kano. Bayan addu'ar bakwai ma kowa ya wuce sai su A'isha kawai da Innarta da zata zauna da su. Sai wata ana kiranta Gwaggo Laraba ƴar Maiduguri dake matsayin kamar kaka a wajen su Abdul-rasheed ɗin. Zasu zauna da su har su kammala takaba, koda yake A'isha ce mai gama takaban a kusa. Yakura kam sai in ALLAH ya sauketa lafiya kuma. Gashi cikin ƙarami ne zubar jinin da tayi kuma zai iya sakawa ma ya koma baya.
       A yanzu kam Alhamdullah, basu da matsalar abinci da abubuwan buƙatu na rayuwa, dan suna samun ɗauki daga ƴan uwa da abokan arziƙi, musamman ma Nasiru dake yin iya bakin ƙoƙarinsa. Bai gajiya da yawo tsakanin Kano da Bauchi. A haka A'isha ta kammala takaba, sai Yakura dake jan ciki, tana kuma samun kulawa sosai daga Inna da Gwaggo Laraba har ma da A'isha kanta. A tsakanin Haysam ya kammala primary ɗinsa, sai su Ma'aruff kuma daya kamata ace anyi haramar sakasu, amma a ƴan uwan na Abdul-rasheed babu wanda yayi magana. Sai da Nasiru yazo yaga shirun yayi yawa shi ya ɗaukesu ya sakasu, ya kuma ce saura a jira takardar Haysam ta fito shima ya wuce Secondary, ƙananun kuwa Ummi, Mommy, Bilal. Aka sakasu ta allo kamar yanda Haysam ke zuwa. Daga haka ya juya ya koma Kano.
      Watan Abdul-rasheed bakwai a cikin ƙasa ALLAH ya sauki Yakura lafiya. Sai dai kuma haihuwa tazo da tangarɗa da tashin hankali, dan tunda dama cikin ya tsufa gata nan ne dai babu isashiyar lafiya. Yau kuma data haihu sai jini ya ɓalle mata. Abu kamar wasa Inna Salame anguwar zoma zata iya tsaida shi, ga su Innar A'isha da Gwaggo Laraba na taimaka mata har abu yaci ƙarfi akace a wuce asibiti. Amma mi babu isasshen kuɗin zuwa asibitin, A'isha ta fita hankali a tashe zuwa gidan babban Yayan su Abdul-rasheed sanar masa, amma sai ya nuna shi wlhy baida kuɗi, hasalima yau haka ya tashi baida ko sisi, sai dai taje wajen ƙaninsa mai bi masa. Shima koda ta shiga ma sai matarsa tace baya nan. Hankalinta ya tashi ta dawo gida, bama ta iya sanar ma su Inna yanda akai ba ta sake fitowa, abinka da babu waya balle ta kira Nasiru dake tsaye akan al'amarin su. Wajen makwafcinsu dake saida dabbobi ta nufa, tace ya taimaketa ya bata kuɗi zasu kai Yakura asibiti idan sun dawo yazo ya kama akuyarta da take kiyo. Bai musa ba ya bata kuɗin, cikin farin ciki ta juya zuwa gida, tana isa aka ɗauki Yakura aka nufi asibiti. Likitoci sunyi faɗa sosai, daga ƙarshe dai suka amsheta.
     To ashe wasa farin girki, dan kuwa dai Yakura jiyya ce mai girma a tare da ita. Dan abu tun ana ɗaukarsa na marmari har ya wuce gaban kwatance. Tun ƴan uwa na zarya da bada ɗan taimako har kowa ya naɗe hannunsa ya bar A'isha da Nasiru kawai da Innar A'isha akan al'amarin Yakura. Sai Khadijah da autan su Abdul-rasheed angon da sukai haɗari ran aurensa da suma suke nasu ƙoƙarin duk da ba masu ƙarfi bane, dama dai ƴaƴansu Abdul-rasheed ɗin ne taƙamarsu, yanzu kuma ya tafi abubuwa duk sun tsaya musu. Shima Nasiru ƙarfin hali ne kawai ba wani ƙarfi ne da shi ba, gashi yana shirin tafiya ƙara karatu daya samu scholarship a ƙasar waje. Ana cikin wannan kai-kawo maganar tafiyar tashi kuma ta tashi, da farko yace ya haƙura A'isha taita roƙonsa akan yaje dan ALLAH kada ya fasa. Nan dai su Inna ma suka saka baki haka ya tafi bayan ya ajiye musu ɗan abinda zai iya na iya ƙarfinsa, bayan tafiyarsa matarsa da ƴarsa ɗaya Raihana da bata wuce shekara biyu ba sukabi bayansa.
     Tun ana zaman asibiti da Yakura har rashin kuɗi yasa suka tattaro suka dawo da ita gida, Gwaggo Laraba ma ta sulale ta tafi abinta, sai A'isha kawai da Innarta, ga yara har takwas dan yarinyar da Fauziyya ta haifa ma sai A'isha ke shayar da ita. A wannan halin A'isha ta ƙuƙuta ta saka Abdul-rasheed a Secondary school, ta fara sana'ar masa da safe. Sai kuma ƙananun tsogumin ya fara tashi akan zaman Inna, wai ya kamata ya tattara ta koma Kano, rasuwa shekara ɗaya da rabi amma ta tare a gidan ƴarta. ALLAH sarki Inna uwa mai dattaku, haka ta tattara ta wuce A'isha na

15 / 49