KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   41 / 49

120K to 123K   out of 146.5K words

ganshi ba akace yana kan aiki, daga nan suka dawo, shi sai ya samu hanyar barin ƙasa zuwa turai, akan shima Jeo zai biyoshi daga baya, sai dai Joe bai bishi ba daya tambayi wanda yayi musu hanyar sai yace shi tun ranar bai sake ganin Joe ba ma”.
       “Yanzu ina abokin nashi?”.
    “Ya koma turai, dama yazo tafiya da Mamansa ne. Ga gidansu anan bayana kaɗan harma ya rushe saboda babu kowa”.
       “Mama kince kamanin Joe da Ojo mai tsanani ne har mutane basa banbance su, kema wani lokacin suna ruɗar dake. Amma da wane irin banbanci kike banbance su a sauran lokaci?”.
      Ɗan shiru tayi na wani lokaci, kafin ta nisa tana jinjina kai.........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 58_

__________________


Ina mata ma'abota ado da kwalliya maryam's all-in-one emporium ta tanadar muku Mayafai masu kyau da aminci kama daga plain chiffon veils masu kyau kamar daga Egypt suka sauko🥰 jersey scarfs , beaded and stoning veils, Chantilly, 2D to 10D Turkish veils Dubai d.s Kuma abun farinciki muna bada sari da siyan dai dai ina Kano Ina tura kaya ko'ina cikin Aminci da yardar Allah ga number ta 09064960666

https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt


A cikin duniya ta gayu da burgewa mayafi shine ya ke daukaka ado da aji

Maryam's all-in-one emporium 09064960666 Kano
Anan ne gayu yake tarar da qawa.

Ki more hadaddun Mayafan mu da suka hada da
Plain chiffon veils (soft & flowy)
Italian Chantilly veils (pure elegance
Jersey Veils (comfort meets class)
Lafaya and many more.

Each piece tells a story of grace, crafted for women who understand beautyin simplicity.🤍

🖤 Premium quality
💛 Affordable luxury
🖤 Available in elegant shades
💛 Delivery 🚚 duk inda kike a fadin duniya

Ba mayafi kawaii kike bukata ba you deserve a statement of class.👑

Wholesale group
https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

..........“Jeo yafi Ojo sauƙin kan zama da mutane, dan Ojo nada saurin fushi kuma bai son mutane sosai. Dan ko aboki da wuya kaga Ojo da shi. Shi ko Jeo na kowa ne. Sannan akwai wani ɗan tabo a bayan kunnen Jeo da Ojo bashi da shi, suna jarirai wani abu ya ciji Joe a wajen shine ya zama ciwo har sai da mukaita zuwa asibiti kafin a samu ya warke da ƙyar, daga nan ne ya zama tabo, shine abu na biyu bayan waccan halayyar da nake banbance su da shi.”
     Kafin Dabo ya bata amsa ta miƙe ta shiga bedroom, babu jimawa ta dawo da albom na hotuna ta miƙa masa. Amsa yay ya kuna fitilar wayarsa dan akwai ƙarancin haske a ɗakin. Gaba ɗaya albom ɗin hotunan su Ojo ne a jiki, tun suna jarirai har lokacin da Ojon yay mata gyaran gida harda budurwarsa ma kamar yanda ta faɗa, sai biyun ƙarshe shi da Jeo lokacin an kammala aikin gidan, ɗaya su biyu, ɗaya su huɗu harda budurwar Ojo da ita maman, wani kallo da Jeo kema budurwar Ojo ya ɗauki hankalin Dabo sosai. Ya jima yana kallon hoton kafin ya ajiye albom ɗin yana ɗan murmushi.
       “Mama naga hotuna, na kuma gode sosai”.
    “Nima na gode da kazo min da labari akan yarona, bayan shekara biyar ban sake jin komai akansa ba. Yanzu ka gaya min yana ina?”.
        Samun kansa yay da yi mata ƙarya. Ya ce, “Ojo yana nan lafiya, jinsa da bakiyi ba na tsawon shekaru an turashi aiki ne wata ƙasa. Kin san mu sojoji akan aikinmu sai haƙuri. Amma ki kwantar da hankalinki yana gab da dawo wa. Yanzu ma saƙo aka sakani zuwa na kawo miki. Sai dai yanzu dare yayi, zan koma can babban garin naku na kwana zuwa safiya sai na dawo...”
        “Miyasa bazaka kwana anan gidan ba?”.
    Ta faɗa cikin damuwa. Daɗi ne ya kama shi dan dama abinda yake so kenan, amma sai ya danne tare da faɗin, “Karki damu Mama zanje can, anan ai sai na takura ki”.
     “Ni bazaka takura ni ba, ga ɗakin su Joe kullum sai na gyara Dan Kada wani yazo a cikinsu ya ganshi da datti, na roƙeka ka kwana anan”.
         “Shike nan Mama Nagode zan kwana.”
    Sosai ta nuna jin daɗi da amincewarsa....

>>>>>>%<<<<<<

         Imran na ƙoƙarin yin parking kiran Dabo ke shigowa a wayarsa. Bai ɗaga ba sai da ya kashe motar, Zak-Shadow dake baya ya fita ya buɗe ma Mammah dake riƙe da Nimrah, dai-dai nan shima ya fito yana ɗaga wayar da kaita kunensa. Sunan Dabo daya ambata ya saka Zak-Shadow juyowa yana kallonsa. Dai-dai kuma lokacin ake kiran sallar isha'i. Dan haka Imran yace ma Dabo ya bari su dawo salla sai suyi magana.
        Ba wanda ya cema ɗan uwansa komai shi da Zak-Shadow ɗin suka fice massalaci, dama shi Uncle a gida suka ajiyeshi kafin su ƙaraso. Suna fita a gate ɗin ne motar Momyn Nabeeha ke shigowa. Ko kallon inda motar take Zak-Shadow baiyi ba suka fice. Koda aka idar da salla suka dawo gidan anan compound suka zauna. Imran yay kiran Dabo. Bugu ɗaya ya ɗauka kamar dama abinda yake jira kenan..
        “Kamar dama ni kake zaman jira Dabo?”.
    “Wlhy Sir a ƙage nake kamar ka sani, dan ji nake kamar nayi tsuntsuwa na ganni a gabanka.”
            “An samu abinda ake so kenan?”.
     “Kusan hakan sir, dan yanzu haka ina a cikin gidan su Ojo, a ɗakinsu ma mahaifiyarsu tai min masauki zan kwana”.
        “Masha ALLAH Dabo, shiyasa na yarda da aikinka sosai. Yanzu ya akayi?”.
     “Sir tabbas akwai alamar tambaya akan Ojo, dan kuwa ta tabbata shi twins ne, sunan ɗan uwan nasa Jeo..........” ya kwashe labari tsaff ya sanar masa. Kuma komai Zak-Shadow shima yaji saboda wayar a hansfree take. Dan haka Zak-Shadow ɗin ya amsa ya ɗan yi masa tambayoyi.
         Bayan ajiye wayar ne Imran ya kalla Zak-Shadow da yay shiru alamar yana nazari. “Mika fahimta a wannan labarin Zak...?”
      Shiru kamar bazai amsa ba, dan yafi minti biyu kafin ya nisa yana sake gyara zamansa. Kai tsaye ya maidama Imran tambayar da “Kai mika fahimta?”.
             “Babbar alamar tambaya akan Ojo gaskiya”.
     Ƙaramin murmushi Zak-Shadow yayi idanunsa na kallon wani waje daban, sai kuma ya juyi yana kallon Imran ɗin hannayensa harɗe a ƙirjinsa. “Imran dole a cikin biyu ɗaya ya kasance a tunani na. Kodai tun farko Ojo ya shiga aikin soja da manufa, ko kuma Jeo shine Ojo a yanzu”.
       “What! Taya hakan zata faru Zak.. idan ma tunanin farko zai yiwu taya na biyu zai yiwu? Ta yaya Ojo zai zama Jeo? Kuma ya saka rigar soja babu tsoro har wannan shekarun baya ganosa ba?”.
      “Ta yanda hasashenka ke baka bazai yiwu ba....”
    Zak-Shadow yay maganar yana kai wayarsa kunne. Idanu kawai Imran ya zuba masa cike da tsoro. Dai-dai yana amsa gaisuwar da ake masa daga can a taƙaice. Cikin bada umarni ya cigaba da faɗin, “Yusuf kana ina?”.
         Daga can cike da girmamawa akace “Sir! Ina barrak?”.
     “Ina Ojo?”.
“Tun ɗazun ya fita wai zai yi shopping saboda zaije gida gobe na hutun da muka samu”.
        Ɗan jimmm Zak-Shadow yayi na sakani, sai kuma ya ce, “Daga yanzu zuwa goben duk wani motsinsa ina son na sani”.
    “In sha ALLAHU sir”.
Yanke wayar Zak-Shadow yayi, sai kuma ya juya yana kallon Imran dake kallonsa. “Yana barin cikin barrak a kama shi”.
      Kai Imran ya jinjina masa. “Haka shine dai-dai”.
    Ganin Zak-Shadow ɗin zai miƙe Imran ya dakatar da shi. “Ina zaka kuma bamu gama magana ba”.
             “Miya rage?”.
       “Case ɗin yarinyar nan da iyalinka”.
    Murmurshi mai ƙayatarwa yayi, sai kuma ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa hannayensa duka biyu na cikin aljihu. “Karka damu na gama yanke hukunci”.
     Aɗan tsorace Imran ya miƙe. “Wane irin hukunci ka yanke?”.
“Zaka gani a goben”.
“Haysam dan ALLAH kada ka aikata abinda Mammah zataji babu daɗi. Koba komai Uncle Nasiru nada muhimmanci a wajenta shiyasa ma kaga tana iya shanye komai. Tasha faɗa a gabanmu Shine Yayanta daya rage take ma kallon uba duk duniyar nan a yanzu”.
        Sosai Zak-Shadow ya zuba masa ido, sai kuma ya sake murmusawa kaɗan yana kauda su gefe. “Kafi kowa sanin waye ni, kada kai banzan tunani”. Daga haka yabar wajen. Da kallo kawai Imran ya bishi harya shige sashensa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Addu'a yake a ransa ALLAH ya yayafama wannan masifar ruwan sanyi da wuri, dan yasan wanene Haysam idan aka ƙure haƙurinsa, ya fahimci kuma Nabeeha ta fara ɗakko hanyar ƙure haƙurin nasa a yanzu, komai kuma zai iya faruwa idan tai wasa. Da wannan tunanin ya nufi sashen Mammah domin yi mata sallama shima ya wuce nashi gida....

★>><<>><<★

            GIDAN GWAMNATI.

       A Ƙaramin ɗakin taro dake ƙawace da sanyin ac da haske mai sauƙi. Shugaban ƙasa da ministan tsaro sai General da wasu manya uku ne ke zaune cikin nutsuwa da hali irin na masu girma. Babu komai a gabansu sai manyan files guda uku a teburin tsakiyarsu sai ruwa. Shiru mai nauyi ya ratsa ɗakin tun bayan gaisuwa kowa ya nutsu. A karo na farko shugaban ƙasa ya nisa cikin nuna damuwa yay ƴar gyaran muryar data sakasu sake maida hankali sosai da nutsuwa suma duk da hankalinsa akan General yake alamar shi zaima magana, “General rahotannin da suka fito daga bangaren Arewa maso yamma sun fara girgiza mana tsarin tsaro gaba ɗaya. Muna bukatar gaskiya daga gare ka, a wane hali zamu iya kira ko auna Zak-Shadow a yanzu bayan abinda kukazo mana da shi a zahiri da wanda muka gani game da nagartarsa a wannan makon har mukai zaman shirya karramawa a garesa?”.
       Iska General ya ɗan furzar tare da  jan numfashi kafin ya amsa da, “Your Excellency, Zak-Shadow ba sunan da ake ambata kai tsaye a cikin runduna bane kawai. Zaki ne na gaskiya dake aiki da ZUCIYA DA ƘWANJI akan duk wanda ya tare masa gaba da sunan GIRGIZA ƘASARSA. Ni kaina shaida ne akan hakan batun yanzu ba. Amma na fahimci ana son alamta wannan nasarar tasa ne ta jiya-jiya da cewa yana da alaƙa da tsohon skasin ɓangare na Special Recon Unit, wanda aka rufe shekaru uku da suka wuce…...”
      Cikin nuna fusata Ministan tsaro ya katse General da faɗin, “Kana nufin ana iya samun haɗin kai daga cikin mu ne General?”.
     Cikin ɗan kausasa harshe shima General ya bashi amsa da, “Ba zan tabbatar ba, amma abubuwa na nuna akwai waɗanda ke ƙoƙari ko son ƙirƙirar wani labari daga sama a kan sadaukarwar tasa shiyasa suke son dawo da abinda ya faru jiya su haɗa dana yau dan cimma manufa.”
       Cikin matuƙar fusata Minista ya sake yunƙurowa zai yi magana. Amma sai shugaban ƙasa ya ɗan buga table ɗin, hakan yasa ya nutsu yay shiru. Kai shugaban ƙasa ya ɗan girgiza, tare da yin baya ya jingina da kujera, ya fahimci ministan tsaro da Janar kowa na kan gaskiyarsa ne. Iska ya ɗan furzar tare da gyara zamansa yana duba takardar gabansa.
“Rashin nuna fahimtar juna tun a farkon tafiya ba shike bada nasara ba. Ya kamata mu kula dan karkacewarmu tamkar rasa ƙashin bayan al'amarin ne kai tsaye. Wannan bincike yana buƙatar a tafiyar da shi cikin sirri da kulawa. Ba na son ƙarin jita-jita a cikin jama’a. General, zaka jagoranci wannan aikin, amma kai kaɗai zaka san asalin manufarsa. A kafa kwamitin bincike da gaggawa dan kwanaki uku ne damu rak, sai kuyi aikin haɗin gwiwa da ministan tsaro..”
      Daga haka shugaban ƙasa ya miƙe abinsa. Duk miƙewar sukai suma cike da nuna girmamawa, har sai da ya fice dogarinsa biye da shi sannan suma sukai yunƙurin fitowa..........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 59_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

..........Cikin damuwa General ya koma office, tunda ya baro gidan gwamnati babu abinda yake maimaitawa sai sunan Zak-Shadow a fili. Zama yay a kujerar office ɗinsa tare da ɗan ja numfashi mai nauyi. Dai-dai nan mutane biyu daya buƙaci gani suka shigo office ɗin.
     Koda suka ƙame da sara masa alamar su zauna kawai yay musu. Cikin damuwa ya sake furzar da iska mai kauri yana kallon su. “Aikin nan ba ƙarami ba ne fa. Kuma idan rahoton da na gani gaskiya ne… to akwai wanda ya karya alkawari cikin runduna.”
       Cikin matsanancin tashin hankali ɗaya daga cikin hafsoshin nashi Colonel Haydar dake gefen damansa ya ce, “Sir! duk mai hankali zai fahimci hakan musamman yanda komai ya taso da zafi. Kenan za mu sake tuntuɓar sashen Recon Unit da aka rufe a baya? Akwai tsoffin bayanai da zasu taimaka nake ga.”
       Cikin ƙwafa General ya ce, “Ai mu ake hara kai tsaye ba Zak-Shadow kawai ba Colonel. Shiyyasa wannan binciken zai gudana a cikin inuwa ne kawai. Dan haka ko ɗaya daga cikin Recon Unit bai kamata ya san munayi ba. Saboda Zak-Shadow yana cikin su, idan muka motsa da ƙarfi zai iya kallonmu daga nesa duk da nasan ita gaskiya gaskiya ce.”
       Ɗayan ne yay magana a yanzu cikin jinjina kai da gamsuwa. Ya ce, “Haka ne sir, zamuyi komai a yanda ya dace.”
        “Wannan shine dai-dai, “Ku shirya min jerin waɗanda suka yi aiki da sashen nan a shekaru uku da suka wuce. Ina so in san inda suke, koda kuwa wasu a cikinsu sun yi murabus.”
     “Yes, Sir.”

<<><>>★<<><>>

        Dare yayi nisa, shiru ya ƙara ratsa ko ina a garin na Abuja. A duka ɓangarori biyu na gidan daren yau yazo musu da wani yanayi ne. Sai dai kowa da manufar tasa damuwa. A ɓangaren Mammah ta maida hankalinta ne ga ibada, yayinda Nimrah ke barci ɗai-ɗai a gadon ɗakinta dan tunda suka dawo daga asibiti tana nane da ita. A can kuwa Bilal, Yaya Ma'aruff, Yaya Ja'afar da Ammar ne suka ƙule a ɗaki suna sake tattauna abinda ke shirin faruwa a gidan nasu. Tun ɗazun Mammah ta kora su Aunty Ummi gida badan sun so tafiya ba, dan haka tattaunawar ta koma a tsakaninsu su iya mazan sai kuma waya da su matan ke kiransu dan suji ko akwai wani motsi. Amma kasancewar Mammah ta haɗe girar sama data ƙasa na hana kowa damar cewa wani abu yasa su zamewa suka koma ɗakin barcinsu suna tattauna iya abinda suka ji da tunanin mi ya faru da su Mammah ɗin suka je asibiti? Sun so zungurar Nimrah ta faɗa musu tunda sunga tanada surutu amma Mammah ta kafa ta tsare ta hana yarinyar zuwa wajensu kamar tasan mi suke shiryawa.

       ★Anan ɓangaren ma Momyn Nabeeha da Nabeeha ɗinne a ɗakinta sun kulle kansu suna sake tattaunawa. Dan suma tunda suka dawo gidan Momyn keta sake tunzura Nabeeha, hakan ne yasa Jiddah yin fushi tabar musu gidan ko jiran zuwan mijin nata ma batai ba. Dan ta riga ta fahimci al'amarin Momynsu a wannan karon yayi babban tasiri a zuciyar ƴar uwarta Nabeeha. Tana tafiya Momyn ta koma zaginta, sai hakan ya ƙara tunzura zuciyar Nabeeha ta ƙullaci ƴar uwar tata da sake tabbatar da ba sonta da ƙaunarta take ba daman, tunda bata kishinta bata tayata baƙin cikin abinda ke faruwa da ita. Hasalima goyon bayan mijin nata take saboda neman duwawun zama. Sai hakan ya sake jagorantarta shagaltuwa da huɗubar Momy da dake jin zafin Zak-Shadow matuƙa..

       ★Zak-Shadow kam tun bayan wucewar Imran daya koma sashen ɗakinsa kawai ya shige ya rufe kansa. Shi sam ba wani

41 / 49