KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   26 / 49

75K to 78K   out of 146.5K words

da hantsi Mammah”.
   Ya faɗa cikin tausasawar data katse mata tunaninta. Wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta shafa addu'ar data kammala sannan ta fuskanceshi tana gyara zama da faɗin, “Wannan tafiyar daren dai bazaka dainata ba, ko tsoro baka ji Muhammad”.
       Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana ɗan sunkiyar da kansa. “Kiyi haƙuri Mammah, tafiyar daren ce tafi sauƙi a garemu kodan yanayin rayuwar”.
       “To ALLAH ya rufa mana asiri, ya baku kariya ya tsare mana ku da tsarewarsa”.
     “Amin ya rabbi Mammah ina kwana. Na sameku lafiya?”.
            “Komai lafiya lau Alhamdullah. Fatan kuma kuna cikin ƙoshin lafiya?”.
       “Alhamdulillahi, sai kewarku”.
   “Kewa kam muma a cikin taku muke akoda yaushe. Amma ya za'ayi tunda haka UBANGIJI ya tsara”.
     Murmushi yayi nan ma kawai, ita kuma ta jawo ƙaramin flaks dake gefenta da wani kyakkyawan mug, shayin dake ciki ta zuba ta miƙa masa.
        “Mammah kamar kin san nayi kewar shayin nan naki kuwa”.
     “Ai gashi sai kaita sha har ka koma. Jiya muke zancenka da Momy ashe kana tafe?”.
      “Tafiyar tazo ne kawai nima. Bata daina yawon nata ba kenan dai”.
         “A'a yanzu kam ta rage ai, tanata fama ma da laulayin ai yawo dole a barshi”.
     “Mammah baki son laifinta dai kawai”.
    Karo na farko Mammah tai dariya, dan kusan su duka haka suke gaya mata akan Momy idan suna faɗan yawonta tana kareta. Sun cigaba da hirarsu cikin nutsuwa, anan ma yake jin Ma'aruff da Ja'afar sun wuce Chaina. Dan su harkar kasuwanci suke yi. Tun dai kasuwar daya zama sanadin kafawa itace ALLAH ya sanya ma albarka zuwa yanzu har suna da manyan shaguna kusa shida da zamu iya cewa ma sune sanadin arziƙin da suke ciki a yanzun haka. Dan haka Ja'afar da Ma'aruff tagwayen Mammah ke kula da su, sune suke zuwa ƙasashe kawo kaya kuma da kansu.
        Sunyi nisa da hira akan dai lamarin sauran ƴan uwan nasa da bikin su Ja'afar dake tunkarowa Biebah tai sallama. Amsa mata sukai da bada izin shigowa. Ta shigo ɗauke da tire yaron nan na ɗazun biye da ita. Sai da ta durƙusa a gabansa sannan ta ajiye tiren, yaron kuwa yaje kusa da shi ya zauna. Dukan abinda Zak-Shadow zai ci yanada ƙa'ida da tsarinsa, baya cin abinci sai mai amfani da gina jiki, shiyasa kayan ganye, nama, ƙwai, kifi, vegetables, fruits sunfi yawa a abincinsa. Sauran kuwa yana cin komai dai-dai misali da kuma tsari. Kwata-kwata baya shan suger, baya cin magi da yawa da gishiri. Baya cin mai da yawa koda nama mai kitse ne, hakama duk wani drinks.
     Yanzun ma ƙwai ne guda huɗu da nama sai vegetables wadatacce a ciki da agada ta kawo masa. Sai fruits salad data haɗa masa kaɗan. Fuskarta washe da murmushi ta ce, “Dada idan kaci abincin nan yau nasan har ƙyauta sai kayi mini”.
       “Ko kuma kisha zana ba idan babu daɗi”.
     “ALLAH Dada akwai daɗi, ai Mammah ma ni nake mata girki yanzu ko?”.
     Tai maganar tana juyawa ta kalla Mammah ɗin cike da shagwaɓa. Dariya Yaron nan ya sanya, dan haka ta maida dubanta kanshi tana harararsa. Dai-dai Zak-Shadow na kai naman bakinsa. Kusa da shi ta koma cike da ƙosawa tana jiran ya yaba mata, harda yin tagumi fuska a shagwaɓe. Sai da yay lauma ta biyu sannan ya ɗago kyawawan idanunsa yana kallonta, sai ta waro masa idannunta. Harararta ya ɗanyi, tai saurin risinar da su. Ya ɗan girgiza kansa da faɗin,
         “Irin wannan sakani a gaba Auta, shike nan yayi daɗi, tashi ki bani waje karna ƙware”.
     Ai da wani irin murna ta miƙe ta fita, yaron nan da Mammah ta kira Mu'azz ya bita yana tayata. Kansa kawai ya girgiza nan ma, Mammah kuwa tai murmushi.
       “Ai daga nan kuma munga boni a gidan nan wajenta, yanzu zata fara bazama sauran ƴan uwan a waya duk da nasan tunda ta ganka ma ta kira kowansu. Amma kai miyasa ba zaka saka matarka tai maka girkin ba, nifa bana son ana tauye mutum ka sani”.
          “Kiyi haƙuri Mammah nima bana tauyeta bane, idan tayi na rana ba sai naci ba, itama Autan ina son ganin farin cikinta, tana son tayi bai kamata na sare mata gwiwa ba”.
      “Shike nan, a dai dinga kula”.
    “In sha ALLAHU”.
 
          Kamar yanda Mammah ta faɗa kuwa tuni Biebah ta bazama sauran ƴan uwan batun zuwan Dadan, kafin 12 har sun cika gidan. Idan ka cire Ma'aruff da Ja'afar da basa nan. Hatta Ammar dake Zaria yana makaranta yace sai yazo gida komai dare.........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 37_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t


UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta
+201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1FEkjc/
__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Taron yara ne a filin da ake kira dandali a ƙauyen. A wannan dandali duk wani abun kwalam da maƙulashe ana saidawa, da daddare kuma nan ƴammata ke taruwa yin gaɗa da hira da samari. Yanda ƙura ke tashi da ihun yaran da suka taru zai baka tabbacin faɗa akeyi. Gashi hantsi ne maza duk suna gona, kusan duk ta inda ka zagaya yaran ne sai mata masu satar fita anguwa ganin mazan basa nan.
      Tafe take tana ƴan waƙe-waƙenta da ƙaramar galon fara mai cin kwalba uku ta mai an zuba man gyaɗa da zai iya kai kwalba ɗaya da rabi a ciki, sai leda baƙa a ƙulle. Yanda aka ɗaure bakin galon ɗin harda leda zaka gane anyi haka ne dan karta zubar. Harta kama hanyar da zata sadata da gidansu ta canja saboda hango ƙurar dake tashi a dandali da ihun yara irinta. Sauri-sauri gudu-gudu kuwa ta nufi can, dan a duniya babu abinda ke burge Nimrah irin damben tsiya, iyayen sunyi faɗa har sun gaji, ga kawunta Tanimu na ɗaure mata ƙugu, da anyi magana yace a barta dan ita *_Zakanya_* ce soja ma zata zama. Tsabar fitinar Nimrah idan nace kowa ya santa a ƙauyen nan banyi ƙarya ba.
      Cike da rigima ta fara kutsawa ta cikin yaran dan son ganin abinda ke faruwa, ko tsoron a zumar da man gyaɗan dake hannunta batayi. Bako ta tsaya ko'ina ba sai tsakkiyar filin faɗan. Tana shiga kuwa ta ajiye galon ɗin man da ledar ta cire ɗan hijjabinta taci ɗammara ta koma tsakkiyar masu faɗan ta tsaya.
Cikin tsiwa da rawar kai ta ce, “Ke Abubu matsa na sayi faɗan nan, dama haushin wannan shegiyar Ɗaharen nake ji. Babu musu Abubu ta matsa ta bama Nimrah waje, dama ba ƙarfi gareta ba tun ɗazun Ɗahare ke jibgarta, dan kuwa ta girmeta har ita Nimrah ɗin ma. Ɗahare zata kai shekara tara ma.
     Ɗahare dake kallon Nimrah tana huttai ta nunata da yatsa tana faɗin, “Ke Nimrah wlhy ki fita a wannan faɗan ba ruwanki, dan sai na haɗa ke da Abubun naci uwarku a filin nan”.
      “Sai dai kici uwarki”.
  Cewar Nimrah cike da tsiwa tana girgije-girgijen jiki ita a dole mai ƙarfi, sai kuma ta duƙawa ta dimtsi ƙasa a hannu biyu, ta sake matsawa gaban Ɗahare sosai ta nuna mata. “Gata tsiya gata arziƙi ki zaɓa”.
     Cikin takaici Ɗahare ta kaɓe ta tsiyar, ai ko sai kokawa ta kacame tsakaninta da Nimrah. Nan fa ihun yara ya ƙaru dan kamar wasa sai ga mutuniyar taku takai Ɗahare ƙasa ta dimbiji ƙasa ta cika mata baki da ita. Dambe yay dambe aka tambaɗar da man gyaɗar Nimrah, ledar ma dake ɗauke da ƙuli-ƙuli ciki tuni yara sun saka mata wawa. ALLAH ne ya kawo wata mata ta raba wannan tsiya da ƙyar bayan ta kori yaran wajen da bulala. Nimrah na huci tayi buɗu-buɗu da ƙasa har cikin gashin kanta ta fara neman galon ɗin mai da ledar ƙuli, yayinda Ɗahare ke kuka da zaginta da cewa sai ta rama. Da ƙyar matar nan ta janyeta ita kuma Nimrah ta ɗauki galon ɗin manta data kimbiɗe matar ta sakata a gaba suka wuce. Sai lokacin kuma kuka da tsoro sukazo mata. Amma taƙi bari kukan ya fito har matar ta rakata ƙofar gida tace ta shiga ita kuma ta wuce...
         Hassatu da a yanzu Nimrah ke kira Umma nata aiki da kallon yanda rana ke ƙarayi zuciyarta cike da tunanin ina Nimrah ta tsaya, ta ajiye iccen data ɗebo zata ƙarama wutar dambu da take yi. Gidansu gidan yawa ne mai sassa daban-daban dan haka ta shiga ƙwala kiran sunan ɗan facalarta da take jiyo suritunsa a sashensu. Daga can ya amsa yana fitowa, yazo gabanta yana faɗin, “Umman Nimrah gani”.
        “Lawwali taimakeni dan ALLAH ka bimin sawun Ninrah gidan Inna Yalwa na aiketa sayen mai da ƙulli tun gama karin kummalo ga shi har sha biyu ta wuce bata ba labarinta, maza ka duba min ita kaji”.
     “To”.
Ya faɗa yana nufar hanyar babbar ƙofarsu, sai ga Nimrah dake jin duk abinda ma ke faruwa rakuɓe a bango da galon a hannu.
      “Ke Nimrah kizo Ummanki na kira”.
    Harararsa tayi, cikin son huce haushin faɗan da tayi a kansa ta ce, “Baza'azo ba ɗin, munafuki”.
        “Kece munafuka dai, minai miki zaki ce min munafiki?”.
     Duka takai masa da galon ɗin man, ya koma cikin gidan da gudu.
    “Lawwali ina aikar da nai maka kake shigowa da gudu?”.
        Nimrah ce zata dakeni, tana zaure”.
     Umma najin hakan tasan tayi tsiyar ne, in dai har ba'a zubar mata da mai ba to an zubar da kuɗin ne. Batace komai ba ta cigaba da aikinta. Sai da ta kammala ta shiga wanka ganin azhar ta gabato sannan Nimrah ta lallaɓo ta shigo cikin sanɗa ta ajiye galon ɗin. Ta juya zata koma da gudu Umma data fito a bayin ta manta sabulu ta kamata caraf. Wani ihu ta fasa mata kuwa.
       “Wayyo ALLAH na shiga uku Umma dan ALLAH kada ki dakeni, Inna ku kawo ɗauki Umma zata tumurmusa ni, wlhy kunkuru na da kafaɗata ciwo suke, na mutu na lalace a taimakeni.”
     Tsayawa kawai Umma tai tana kallon yanda take ihun da dire-diren iskancin. Sai ko ga kakarta da wasu a matan gidan sun shigo. Dai-dai Umman ta kai hannu zata mangareta surukar tata ta dakatar da ita.
         “Karki sake ki taɓata Hassatu, ke wai baƙya tausayin yarinyar nan ne kullum duka dai duka dai, gata abu ba abuba ko jikin kirki ta gagara yi saboda masifarki”.
     Ran Umma a ɓace ta ce, “Inna nagaji da al'amarin Nimrah a gidan nan, tun gama karin kummalonta fa na aiketa sayen mai gidan Inna Yalwa sai yanzu take dawo min da galon ɗin babu man babu kuɗin, dan iskanci kuma ta shigo ta faɗa min yanda akayi shine ta laɓe a zaure har tana shirin dukan Lawwali dana aika ya nemo min ita. Wannan wace irin rayuwa ce, jiba jikinta daga gani dambe taje tayi yarinya kamar wata namiji”.
       “Koma dai miye dukan ai ba shine magani ba addu'a ce, sannan kowane yaro da irin ƙuruciyarsa”. Inna tai maganar tana ƙwace Nimrah a hannun Umma. Dole ta sakar mata ita, tanaji tana gani ta wuce da ita sashensu aka barta da takaici, sai sake bada wasu kuɗin tayi aka sayo mata wani man. Ba kuma ta sake saka Nimrah a idonta ba sai dare da babanta ya dawo gidan....

>>>>>>★<<<<<<

          Sai da suka je sallar azhar massalaci suka dawo sannan ya koma sashensu. Ƴammatan ɗazun kawai ne a falon, suna ma jin motsinsa suka shiga rige-rigen faɗawa bedroom ɗin kwanansu. Sai dai hakan bai hanashi fahimtar suna a gidan ba har yanzu. Sai da ya shige ɗakinsa ɗaya daga cikinsu ta fito cikin sanɗa ta shiga bedroom ɗin matar gidan. Tana zaune a bakin katafaren gadonta da yaji shinfiɗa ta alfarma kamar yanda jikinta ke cikin kwalliya. Ɗakin ya haɗu matuƙa, komai tsaf babu wani tarkace. Waya ce a kunnenta alamar magana take da wani, sai dai ganin yanda ƙanwar tata ke tsaye a bakin ƙofa fuska a marairaice ya sata ɗan kauda wayar a kunnenta ta rufe speaker ɗin da hannu.
         “Miya faru?”.
     “Aunty ya dawo fa, dan ALLAH kije ki bashi haƙurin”.
     Hararta ta ɗanyi da faɗin, “Naji. Fita ki bani waje.”
   Sai da ta tura baki gaba sannan ta juya fuuu ta fita. Ita kuma tai ƙaramin tsaki tana janye hannunta. “Mommy Please ina zuwa, wai ya dawo sashen. Bari naje kin san shi da baƙar zuciyar tsiya, duk yanda mukai zan kiraki. Amma dan ALLAH ki kwantar da hankalinki babu inda zasuje”.
     Banji mi akace mata daga can ba, ta dai yi ɗan shiru alamar saurare kafin ta yanke kiran ta ajiye wayar. Gaban ƙaton mirror ɗin ɗakin taje, ta ɗauka wasu turare ta ƙarama jikinta tare da mouch freshener sannan ta fito. Dining ta nufa ta ɗauki wani ƙyaƙyƙyawan basket ƙarami da aka shirya abinci a ciki ta nufi ɗakinsa.
Shigowarta dai-dai da fitowarsa a bayi jikinsa na raɓar ruwa farar fatarsa tayi wani fayau sai towel ɗaure a ƙugunsa. Tabbas Zak-Shadow murɗaɗɗen mutum ne bana wasa ba, dan ko wasu ƴan wrestling ɗin albarka. Sarai yaji sallamarta da motsinta, amma yay biris ko kallon ƙofar baiyi ba yama wuce bakin gado abinsa yana ɗaukar wayarsa dake a bed side drawer tana vibration. Kiran ya ɗaga tare da kai wayar kunnensa. Dai-dai lokacin ta ƙaraso wajen itama bayan ta ajiye basket din acan saman table dake a tsakiyar kujerun ɗakin. A hankali ta manna jikinta da bayansa, ta zagayo da duka hannyenta biyu, ɗaya a ƙirjinsa ɗaya a saman shafaffen cikinsa mai manyan layukan six-pack.
      Sai ko daya ɗan lumshe ido saboda yanda ta fara zagaya hannun a jikin nasa, sai dai ya dake abinsa, yana cigaba da wayarsa hankali kwance. Bai kuma ajiye ba sai da ya kammala. Yana cireta a kunnensa yay ƙoƙarin janye jikin nasa daga riƙon datai masa, sake ƙanƙameshi tai cike da shagwaɓa ta furta, “Please my Cool one, I really miss you wlhy. I'm so sorry, dan ALLAH kada kaimin hukunci da laifin daba nawa ba. Bance kazo dan na ɓata maka rai ba”.
        A hankali ya ɗan saki huci, batare da yayi maganar da take son yayin ba yasa hannu ya cire hannayenta dake a jikinsa. Da sauri ta dawo ta gabanshi ta rungume shi tsam-tsam, tare da sakar masa kuka. Karo na farko ya ɗan ciji gefen lips ɗinsa, shiru kamar bazai kulata ba sai kuma a hankali ya ɗaura duka hannayensa biyu akan bayanta shima ya zagayeta yana sake matseta. Cike da farin ciki ta sake ƙanƙameshi da bashi kissis masu zafi a saman ƙirji, kafin ta ɗago tai ɗiɗɗishe da ƙafafunta dan ya fita tsawo kawai ta haɗe lips ɗinsu waje guda.
      (Ehem-ehem nai gyaran murya dan ganin al'amarin babbane), dan kuwa tuni ya ɗagata cak ya ɗora a gadon ta yanda tsahonsu yay dai-dai, tun abun nasu na iya tsayen ana sumbatar juna har takai suka zube a gadon gaba ɗaya...........✍🏼



_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 38_

__________________

🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH?mode=ems_copy_t

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF 'YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a

26 / 49