Author : Billyn Abdul Category : Adventure
ke bakinta ta cigaba da matsa yatsun hanun nasa, kafin a ɗarare ta ce, “Dan ALLAH wannan karon ka yarda muje muga likitan nan mana. Ta hakanne zamu fahimci idan wata matsala ce a tare damu mu tashi mu nema magani. Shekara goma sha fa ba kwana goma sha bace My D. Dan ALLAH kai baka jin wani abu a ranka idan ka kalla ƙannenka da yaransu? Ga su Ja'afar suma zasuyi nasu auren, nan da shekara ɗaya sai kaga duk suma da yaransu. Haka kake son suma matansu suzo a bayan bayana su haihu ina kallo....”
Shiru ya mata yaƙi tankawa. Sai hakan ya ƙara ƙular mata da zuciya, dan haka yake mata a duk sanda ta kawo masa batun zuwa ganin likita. Kuka ta fashe masa da shi mai ratsa zuciya. Kafin ta yunƙura fuu ta miƙe da nufin bar masa wajen, batare daya kalleta ba shima ya riƙo hannunta, tare da fisgota ta faɗo jikinsa gaba ɗayanta. Kici-kici ta fara nason tashi tana ƙara ƙarfin kukanta, amma riƙon da yay mata da hannu ɗayan nan kawai ta gagara tashin. Ganin ba iya ƙwatar kan nata zatai ba da gaske sai kawai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta cigaba da raira masa kukan.Tsawon lokaci suna a hakan idanunsa a rufe tamkar bai san tanayi ba, ganin ba dainawa zatai ba ya ɗagata a jikin nasa ya miƙe da nufin bar mata ɗakin gaba ɗaya.........✍🏼
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 41_
__________________
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LkEgiP5qOEo9YDYjaeZLLc?mode=ems_wa_t✍️✍️ Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed yar mutan Chadian traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products at home my people bazamafa a kwai zafafan promo damukeyi in Sha allahu zuwa on 15 zamugama sannan gareku Yan Kano free ne kayanki zasuzo miki amma fa karyazo bayan mungama promo kuce kyauta ne aa zakibiya kudi nagode takuce yar mutan Chadian mai gyaran ciki dawaje 💃💃 please banda maza,❌maza❌
In kinada matsala wadda zamu iya taimaka miki 09065504546
Ga PRODUCTS DINMU KAMAR HAKA
MAGANIN SANYI
TSUMIN BOM
MADARAR TABAJE
GORON TULA SYRUP
ZUMAR SHADAMATSIN
GARIN YAUKAYAUKA EMERGENCY
GARIN KINFI KAZA DADI
SIRRIN MALLAKAR KASA
SIRRAN GIDANKI
DAHUWAR KAZA
DAHUWAR CICCIBI
DAHUWAR YAN SHILA
HMM BAZASU IRGUBA INA GODIYA SOSAI MY PEOPLE 🥰🥰
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Zaram tasha gabansa, sai dai ta gagara kallonsa kamar yanda shi yake kallonta. Zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗi, shawarwarin mahaifiyarta na bata ƙwarin gwiwa ta ce, “Haysam kana saka min shakku a zuciyata da jin yarda akan maganganun mutane. Kodai baka son haihuwa ne kamar yanda kowa ke faɗa?”.
Ya daɗe bai ji abinda ya sokar masa zuciya kamar kalamanta ba. Cikin wani irin yanayi mai girman gaske ya zuba mata idanu yana mata wani irin kallo mai zafin gaske. Zuciyarsa kuwa tuni ta yinƙuro ta tokare maƙoshinsa. Ya tabbata in dai ya buɗe baki akan bata amsar kalamanta zai iya gaya mata mai zafin gaske da zata ninka wadda ta gaya masa sau dubu. Dan haka sai kawai ya zagayeta ya fice a ɗakin gaba ɗaya.
Fashewa tai da wani irin kuka tana kaiwa ƙasa ta zube. Jifa ta fara yi da duk abinda ya tare mata gaba. Babu abinda ke ƙara ingiza fushinta sai kalaman mahaifiyarta. Tabbas ta yarda gaskiya Momy ke faɗa akan mijinta. Dan ita kanta a wasu lokutan takan zauna taita tunani game da al'amarinsa. Yanda yake mutum mai yawan buƙatar iyali miyasa idan ya tafi wajen aikinsa in ba ita ta takura masa da magiyar yazo tana missing ɗinsa ba dan kansa baya shiryowa yazo dan yin hakan. Sannan ko zuwan yayi idan ba ita da kanta ta kawo masa kanta ba bazai nema ba. Da tana ɗauka tsabar girman kansa ne ke sashi yin hakan. Sai da mahaifiyarta ta fara fargar da ita ne akan kodai yana neman mata ne sannan ya ɗan fara taba tunaninta, sai dai zuciyarta bata amince ba tana wasi-wasi dan tasan sa da ƙyanƙyami. Amma zuwa yau zuciyarta kamar ta fara jin aminci da wannan zance, musamman idan ta tuna maganar wasu ƙawayenta da kance ta tashi tsaye akan mijinta dan wasu sojojin akwai son matan tsiya, shiyasa ma basu cika son haihuwa ba dan kar aima ƴaƴansu abinda sukema wasu.
Waɗan nan tunane-tunane Nabeeha ta cigaba da tasirantarwa a wannan dare suna ƙara tunzurata da rikita mata sissafi. Koda ta sake kiran mahaifiyarta ta gaya mata yanda sukayi da mijin nata sai ita kuma ta sake tabbatar mata hasashensu ya zama gaskiya dai, Zak-Shadow baya san haihuwa a gaske. Kuma tabbas dole ta miƙe tsaye da bincikensa dan ta tabbatar shin baya neman mata. Ai ko haka ta ƙara hawa ta zauna. Da safe har ya shirya ya fito bata leƙashi ba. Sai shine ya shigo ɗakin nata.
Yanda ta faffasa abubuwa kawai ya tsaya yana kallo, kafin ya maida idanun kanta. Tana kwance a kan gado da waya a hannunta. Sarai kuma ta ji shigowar tasa amma tai biris. Uffan baice mata ba ya juya ya fice a ɗakin. Sai ta raka bayansa da harara tare da jan tsakin daya shiga kunnensa a bazata, dan ya juyone da nufin dawowa ɗakin ya mata magana. Cak ya tsaya tamkar wanda akai ma tsawa, sosai fuskarsa tayi masifar sake haɗewa fiye da yanda take, idanunsa sun wani juye alamar zuciyar ƴan maza ta motsa, dan ni kaina na tsorata addu'a kawai nake kar yace zai koma ɗakin. Ganin ya bar wajen ya sani sauke ajiyar zuciya.
Sashen Mammah ya nufa, a kallo ɗaya kuma ta fahimci ransa a ɓace yake. Sai dai batayi magana ba saboda ƙannensa. Shima cikin dannewa da haƙuri da ALLAH ya bashi ya fuskanci ƴan uwansa ya ajiye batun Nabeeha gefe.....
>>>>>★<<<<<
Gaba ɗaya wannan yinin su Major Imran sun yishi ne akan ƙafafunsu wajen binciken son sanin su wanene suka kawo musu wannan harin, ta wani ɓangare kuma hankalinsa a tashe yake matuƙa akan son samun Zak-Shadow kafin zancen harin da aka kai musu ya kai Headquarter asan baya jejin tunda yayi fita ne irin ta sirri. Amma har wani daren bai samu mafita ba. Sai dai sun sake shiri na musamman akan kowane sansani dama jejin gaba ɗaya. Dama haka wannan munafukai ke buƙata, wato karkatar da hankalin su Imran ɗin, sun ko samu nasara zamuce, dan ana cikin sallar isha'i suka sami nasarar kai hari a ƙauyuka uku. Bankaura dake babban ƙauye na wannan yankin, sai wani ƙauye da ake kira Gangare, sai kauyen Marke.
Wannan sabon tashin hankali ne da waɗan nan ƙauyuka basu taɓa fuskanta ba a baya, dan rikicin shekarun baya daya faru a sauran ƙauyukan ne banda nasu. Ruwan fitar harsasai da ƙarar tashin nakiya ce ta fara jan hankalin wasu a yaran su Imran. Cikin gaggawa wani haziƙin matashin soja ya silalo yabaro inda suke da bayi da nisa da ƙauyukan ya sanar da Imran. Ai babu ɓata lokaci ya zabura da wasu tawaga suka nufi wannan waje. Ƙauyen Gangare suka fara shiga kasancewar shine farko. Tun a farkon shiga suka fara cin karo da gawarwakin mutane. Hankalinsu ya tashi dan sun fahimci al'amarin da lallai babba ne. Ai babu wani maganar ɗaga ƙafa suka buɗe ma yaran su Dagger wuta, nan fa sabon wasa ya koma tsakaninsu, mutanen gari kuwa tashin hankali yasa sun watse cikin jejin, wasu kuma a cikin gidajensu suka samu wajen ɓuya.
Matuƙar bata kashi akasha a wannan dare, kowane ɓangare sun gama jigata musamman mutanen gari da sukafi fuskantar ƙalubale, an kashe mutane da yawa, a wannan ƙauye. Ba'a samu lafawar wannan hargitsi ba sai zuwa ƙarfe shida da rabi na asuba gari ya fara haske, daga ƙarshe dai su Dagger suka gudu, an kashe wasu a cikinsu suma, an kama mutane biyu kuma, kamar yadda wasu a cikin yaran su Imran suma aka ji musu ciwo, sai dai soja ko ɗaya bai mutu ba. Sojoji na tattara mutanen da suka jikkata Imran ya samu waya ta wani da aka kashe, gefe ya koma ya shiga neman layin Zak-Shadow, a lokacin kusan ƙarfe tara na safiya. A kuma dai-dai wannan time ɗin ne Zak-Shadow yake a sashen Mammah tare da ƴan uwansa bayan ya baro nashi sashen da ɓacin ran matarsa.
★ Bilal ne yaga wayarsa na haske, dan shi hankalinsa ya tafi kan magana da Mammah.
“Dada kamar ana kiran wayarka”.
Bilal ɗin ya kalla, sai kuma ya juya yana kallon wayar dake a gefensa. Baƙuwar number ce, shi kuma baya ɗaga baƙuwar number. Dai-dai nan kiran ya katse, har zai ɗauke kansa sai kuma wani kiran ya sake shigowa a karo na biyu, cikin takaici ya ɗauki wayar zai kashe gaba ɗaya dan zuciyarsa sam babu daɗi...
“Ya kamata dai ka ɗauka kasan waye”.
Maganar Mammah ta dakatar da shi daga kashe wayar, cikin bin umarni ya ɗaga tare da sakawa a hansfree. Jigatacciyar muryar Imran ta daki kunnensa, “Imran ne Sir!.........”
Wayar ya ɗauka yana miƙewa tare da cireta daga hansfree ɗin gaba ɗaya. Cikin wata irin razananniyar murya ya ce, “What! Shine sai yanzu kuke sanar dani. Imrannn!!!”.
Yanda ɗakin ke amsawa da amon muryarsa yay matuƙar tada hankalin ƴan uwansa, a zafafe ya yanke kiran yana mai isowa gaban Mammah. Kai tsaye ya ce, “Mammah zan wuce akwai matsala”.
“Ya rabbi, miyake faruwa?”.
“Ba lafiya Mammah, hari aka kai mana. Kiyi haƙuri zamuyi waya”.
Daga haka ya fice daga falon kamar wani yunwataccen zaki. Hankalinsu a tashe duk suka miƙe suna kallon juna, sai kuma duk sukayo waje suma. Dai-dai nan yake fitowa daga sashensa da jaka a hannu, sai hular mashin ɗinsa. Gaban Mammah yazo ya ɗan rungumeta, ta shafa kansa tana mai masa addu'a, dan yanayinsa kawai ya tabbatar mata al'amarin babba ne sosai. Hakama ƙannensa a tare suka zo suka rungumesa tare da masa addu'a. Da sauri yabar wajen ganin su dukansu suna faman sharar hawaye, har Mammah duk jarumtarta sai da ta kauda kai gefe, yana hawa ƙaton mashin ɗinsa da in yana tafiya baka jin ƙara Bilal ya zabura ya nufi gate da gudu ya buɗe masa. Ai ko a guje ya fice daga gidan shima, dan ji yake kamar ya rufe ido ya gansa a jejin...
Ganin kowa ya fito babu Nabeeha ƙanwarta ta tafi da gudu tana buga mata ɗaki da kiranta.
“Aunty!. Aunty! Ki buɗe dan ALLAH Dada fa zai tafi”.
Wani irin dukan zuciyar Nabeeha kalmar zai tafin tai a karo na farko. Cikin sauri ta diro a gadon da take kwance. Yanzu fa taji yana buga mata ƙofa da kiran sunanta tai banza da shi, a zatonta kan maganar jiya ne yazo ko fitinarsa ce ta motsa, duk da tasan kome yake ji idan yana fushi zai iya danne abinsa ya haƙura, shiyasa taƙi buɗewa. Tana buɗe ƙofar ƙanwarta taja hannunta kawai suka fito, sai dai rashin sa'a suna fitowa tsakar gidan ana rufe gate alamar harya wuce. Sharrr hawayen da suka cika mata ido suka shiga rige-rigen zubowa, sai kawai jikinta ya kama rawa har tana neman faɗi sai da ƙanwarta ta riƙeta. Ciki suka koma, dan su ma su Mammah sun shige nasu sashen. Bedroom Nabeeha ta shige tana mai fashewa da kuka, dan ita duk tunaninta abinda tayi jiya ne da ƙin buɗe masa ƙofa a yanzu ya fusata shi.
“Aunty dan ALLAH ki daina kukan nan, kimasa addu'a kamar yanda sauran ƴan uwansa ke masa. Dan ita yafi buƙata a garemu baki ɗaya”.
“Ismat bazaki gane ba, laifina ne, nasan nina fusatashi ya tafi. Miyasa daya buga ban buɗe masa ƙofar ba....”
“Anya haka ne kuwa Aunty. Kamar fa kiransa akai daga wajen aiki inaga wani abu ne ya faru”.
“Wajen aiki?”.
“Tabbas haka ne Aunty, amma ki bincika wajen su Mammah”.
Hawayenta ta shiga sharewa da sauri. Sai kuma ta jawo wayarta ta shiga kiran number ɗinsa. Amma harta katse bai ɗaga ba. Ta jera masa fin kira goma no answer, sai ta sake fashewa da kuka tana yin jifa da wayar, ALLAH ma ya sota bata faɗi ƙasa ba Ismat ta cafe..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 42_
__________________
https://wa.me/+23408067422528
Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba.
Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa.
Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka
Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne.
Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki.
Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.
https://wa.me/+23408067422528
“Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar ’ya’yanki a gida ba?” ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne
Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇
https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Mahaukacin gudun da yay a hanya, wanda UBANGIJI ne kawai ya tsaresa kusan ƙarfe biyu na rana ya iso cikin jejin. Tun daga sansanin farko da aka kaima hari a daren shekaran jiya ya fara cin karo da tashin hankali, dan gaba ɗaya sansanin a hargitse yake, an fasa tantunan da harsasai tako ina huji ne, ga karnuka nan kusan huɗu kwance a mace an harbesu. Shiru babu kowa alamar mazaje nakan aiki. Sansaninsu ya ƙarasa da sauri, tuni ƴan tsirarun sojojin da ke a sansanin suka tareshi tare da miƙa gaisuwa.
Ajiye mashin ɗinsa yay a wajen da yake ɓoyewa, tare da canja kayansa zuwa uniform ya zubama bindugu biyu bullets sannan ya fice. Kai tsaye inda baradan karnukansa suke yaje ya buɗesu. Ai ko suna ganinsa suka fara wani mahaukacin haushi. Bayan mota dake fake irin ta sojoji dake shiga kowane kwazazzabo saboda ƙarfin tayoyi ya buɗe musu duk suka shiga, shima ya zagaya gaba inda aka buɗe masa kusa da mazaunin driver, cikin sauri wanda zai tuƙa shin ya fice a wajen a guje zuwa ƙauyen Gangare inda su Imran suke.
Da tarin gawarwakin mutanen garin fin arba'in ya fara cin karo su Imran sun taresu a waje guda. Sai sojojin da suka samu raunuka ana duba su da wasu a jama'ar gari da suma suka sami raunukan. Garin tsit mutane duk sun ɓuya, sai su sojojin kawai da kallo guda zai tabbatar maka duk a jikace suke, wasu suna gyara bindiga, wasu kuma suna ta duba ƙananun raunikan jikinsu.
Motar na tsayawa duk suka miƙe. Tare da ƙamewa suka sara masa. Yayinda Captains ɗinsa suka iso gabansa da sauri, ilahirin fuskokinsu suma na nuna gajiyawa da damuwa.
Zak-Shadow da idanunsa sukayi ja, muryarsa cike da ƙarfi da zafi idonsa akan Major Imran Abbas ya furta, “Na bar sansani na kwanaki biyu kawai, amma ku kai sakacin da komai ya rushe haka? What the hell is this?! Are you ladies or soldiers?!”.
Yanda yay maganar idanunsa na sake rikiɗewa kamar garwashin wuta yay matuƙar hargitsasu. Kowa ya kasa magana, dan babu ma mai wannan zarran bare gigin, garama Major Imran, dan haka a yanzu ma shine yay magana.
Cikin matuƙar girmamawa Major Imran dake tsaye a kusa da shi jikinsa da kura, ya ce, “I'm sorry sir. Mun yi iya ƙoƙarinmu. Amma mun ji kamar makiyan suna sanin duk motsinmu ne kafin mu yi. Kamar ana gaya musu abin da muke shiryawa ne kai tsaye. Sannan hari ne na bazata. Mun rasa haɗin sadarwa tun daren shekaran jiya. An kai hari biyu lokaci guda a Arewa da Yamma. Sojojinmu sun watse, mun rasa mutane da yawa. Wannan dalilin ne ya janye hankalinmu da sansanin mu, ashe shiri ne na musamman, hari ne na kauda hankali aka kaima sansanin nan shine ainahin target ɗinsu”.
Sosai zuciyar Zak-Shadow ke hanƙoro a cikin ƙirjinsa, wani irin raɗaɗi da zafi mai ƙuna yake ji a ransa. Dan ya fahimci bayanin Imran fiye da yanda yayi masa shi, tabbas yaji a ransa dole ne harin ya kasance shiryayye, sannan an tsarasa ne ta hanyar amfani da fitarsa a jejin. Sanin fitarsa kuwa dole tana da nasaba da munafiki a cikinsu.