KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   25 / 49

72K to 75K   out of 146.5K words

amfanin gona, amma fa da ance ruwa ya zuba zaka gansu sunata dawowa gida. Maza na fita neman kuɗi a lokacin rani, da damina suyi noma. Mata kuwa kanyi ƙuli-ƙuli da mai da man-kaɗe da sabulun salo su kaishi manyan ƙauyukan dake kusa da bankaura domin siyarwa. Da damunar ma dai ba'a barsu a baya ba, masu himma kan yi noma suma nasu na kansu ko suyi ƙwadago a gonakin wasu. Zagaye da ƙauyen bankaura akwai wasu ƙauyukan da zasu iya kaiwa bakwai ma. Suma kuma kamar hakan ne basu da wani cigaban rayuwa da duniya ke kallo. Haka suke rayuwa tsawon shekaru, sai a shekarar 2002 wani matashi mai suna Tanimu yay sanadin wani tagomashin arziƙi ma ƙauyukan yankin ba Bankaura kawai ba, duk da kuwa shi ɗin haifaffen ɗan bankaura ɗin ne.
         Tanimu irin mutanen nan ne masu wayewar kai tamkar a jinin jikinsu, dan kuwa baiyi karatun boko ba sai na allo kawai a cikin garinsu. Yana da shekara sha takwas ya shiga cikin matasa masu tafiya neman kuɗi zuwa Lagos. Tun fa a fitar farko Tanimu ya fahimci duniya tayi nisa mai yawa ta barsu, ya dinga ji a ransa basu da maraba da dabbobin dake rayuwa a jeji sai dai suci su kwanta suyi barci. A take zuciyarsa ta fara sosuwa da jin kishin yankinsa da al'ummarsa. Dan haka ya shiga bincike a iya ɗan tunaninsa da hangen nesan sa, sai ya fahimci idan fa har suna son irin cigaban da al'ummar birni ke ciki dole-dole sai sun tashi daga barci da suka jima sunayi, su cire tsoro, su cire gidadanci. Yaransu su shiga makarantar addini data boko ba noma kawai da fita neman kuɗi cikin birane ana musu kallon ƙasƙantattu ba.
       Tun a Lagos ya fara latsa tunanin ƴan uwansa, ƴan garinsu dama ƴan wajen garinsu akan al'amarin. Kai tsaye wasu ke bashi goyon baya, yayinda wasu ke ɗaukarshi mahaukaci. Bai damu ba ya cigaba da son fahimtar da su har lokacin da ruwan damina ya fara sauka suka koma gida. Kowa ya duƙufa noma, shi ko ya duƙufa nazari da tuntuɓar manyan ƙauyukan musamman masu gari. Kai tsaye ba kowa ke fahimtar Tanimu ba, dan wasu ma kance yana son zuwa musu da kafirci ne kawai da lalata tarbiyyar yaransu da al'adarsu. Sai dai baya nuna jin haushi ko ƙosawa, sai ya zauna yay musu bayani na gamsuwa da nuna musu ai a yanda ɗin suke bai hana yaran nasu su lalace ba, dan akwai da yawan matasan da tunda suka fita neman kuɗi birni a ƙauyukan sunƙi su dawo gida, wasu ma sun faɗa mummunar hanya acan birnin. Kamar wasa sai al'amarin ya fara tasiri, a shekarar 2007 da akazo zaɓe sai suka haɗe kai suka nuna bazasu kaɗa ƙuri'arsu ba suma. Sai ƴan takarar dake ƙasa-ƙasa sun musu alƙawrika sannan. Shi ɗan siyasa babu abinda yafi ƙauna musamman a lokacin zaɓe sai kuri'a, idan kuma za'a haɗa ƙauyen bankaura da sauran ƙauyukan dake makwabtaka da shi dole za'a samu ƙuri'a mai yawa. Aiko sai ga ƴan takara kowanne na nashi alƙawarin musamman ƴan takarar chairman da kansiloli. Sunko cika alƙawari, dan cikin dabarun Tanimu aka samu tsara yanda za'a kaɗama kowanne ƙuri'ar, kunga duk wanda ya dace yaci bashi da bakin cewa basu zaɓesan ba.
    Bayan gama zaɓe da samun sakamako chairman ɗin da yaci da kansiloli suka nema saɓa alƙawari, Tanimu bai gajiya ba ya cigaba da zungurar masu gari shima yana haɗa gangamin matasa zuwa garin da chairman ɗin yake suna masa tini. Da suka ga anƙi ɗaukar abin da muhimmanci sai suka nuna ai zaɓe zai sake zagayowa. Daga haka suka watsar da batun su suka koma kan harkokinsu.
    Wannan abu da sukai ta farkar da masu wayon cikin ƴan siyasar, musamman ma kansiloli sai suka fara ƙoƙarin yin fanfon tuƙa-tuƙa a kowane ƙauye. Fara kuma wannan fanfuna ya saka ƙauyukan a farin ciki sosai, sai dai kuma masu aikin fanfuna suna fahimci kauyen bankaura da ƙauyikan gefensa akwai wasu ma'adanai dake rayuwa a wajen. Ma'adanai ne kuma masu ɗunbin daraja da zasu zama dukiya. Waɗan nan ma'aikata sune suka tsogunta batun ga wanda suka sakasu aikin fanfunan nan, suka nuna idan aka basu dama zasu dinga tonowa da wayo ana kashe muraba.
     Kuɗi ƙunbar susa, dan danan kuwa suka amince musu. Aka sake zuba ayyukan fanfuna tuƙa-tuƙa tako ina. Su ƴan gari na farin cikin ana masu aiki masu aiki na farin ciki da ɗibar ganimar dukiya. A hankali-ahankali zance ya kai ga kunnen manya irinsu chairman da ɗan majalisar yankin, ai babu ɓata lokaci hankalinsu ya fara dawowa ƙauyukan. Amma sai basu nuna a fili ba aka cigaba da yaudarar su da ayyuka. Dan kuwa babu wani jimawa akai musu makarantun primary, aka kuma musu asibiti ƙarami, hanyar ma an gyara amma ba kwalta aka zuba ba. Ba'anan aikin ya tsaya ba sai ga wutar nefa an jawo musu. Bayan yin waɗan nan ayyuka ne wasu a manyan garin suka fara farga, nan fa ƙaramar rigima ta tashi har abu dai ya kai ga manya, sai ga baƙin fuska sun fara shigowa ƙauyukan harda ƴan ƙasar waje. Wannan al'amari ya fara tada hankalin mutanen wannan yanki, sai kawai suka miƙe da addu'a tamkar anyi ruwa an ɗauke masu haƙar ma'adanai dama shugabannin yankin dai suka ja baya.
     A shekarar 2008 kwatsam wasu mutane daban suka shigo yankin suka cigaba da aikin haƙa, sai dai suna a ƙauye guda ne ba duka ƙauyukan ba. A ƴan ƙananun magana suka fahimci akwai bakin wasu a manyan garin, sannan masu wannan haƙa sun sha banban da na baya. Akwai kuma kasuwa babba a yankin da ake cinikin amfanin gona da dabbobi tamkar ba'a so itama al'amarinta ya fara canja salo. Wannan kasuwa dai itace taƙamar wannan yanki gaba ɗaya bama ƙauyikan ba, kai arewa ma kasuwa ce ta alfahari ga kowa. Dan haka suka shirya ɗaukar mataki dan basa son rasa kasuwarsu, batun ma'adanai ma bai canja ba, dan yaransu sun dawo sune masu haƙa ana biyansu maƙudan kuɗi, ta wani fannin kuma basu san darajar ma'adanan ba sam.
    Ƙoƙarin hana taɓarɓarewar kasuwar nan da daina fitar yara neman kuɗi ne ya fara jawo rikici, rikici babba da ya kai har gwamnatin jiha ta shiga, daga ƙarshe ma aka turo sojoji domin kwantar da tarzomar su kuma tarwatsa ƴan ta'addar. Haka kuwa akayi dan wannan shine sanadin zuwan su Zak-Shadow cikin dajin yankin a karo na biyu. A lokacin yana matsayin Major Haysam Abdul-rasheed Shehu. Akwai runduna a ƙarƙashinsa, rundunar tasa kuma itace ta kawo dai-daiton cigaban kasuwar da har ya zamto an ƙaramasa muƙami na bayan abubuwa sun lafa gaba ɗaya. Sun bar jejin har na tsawon shekara ɗaya da wasu watanni da tunanin komai ya dai-daita, sai dai a shekarar 2010 wasa na biyu ya nema fin na farko, dan kuwa horarrun ƴan ta'adda da ba'asan daga ina suke ba sunzo sun ragargaza jama'ar wani ƙauye da ake kira Gunda gaba ɗaya, an kashe wasu an jikkata wasu. Wannan rikici shine yay sanadin sake dawowar sojoji a yankin, ba kowa kuma aka maido ba sai Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu Zak-Shadow ganin shine ya dai-daita rikicin farko.
        Zak-Shadow ya kafa ya tsare a wannan yanki matuƙa, ta yanda ƴan ta'addan nan sun kasa ko numfashi mai ƙarfi, dan tarwatsawar da yay musu ta ƙarshe sai da ya samu nasarar kashe shaƙiƙin ƙanin shugaban ƴan ta'addar. Maganar tonon ma'adainai kuwa tuni ya dakatar da shi sai a ɓoye, a ɓoyen ma yana musu wuya sosai.

       Wannan ƙauye na Bankaura shine ƙauyen su matar nan mai ciki da su Zak-Shadow suka haɗu dasu a shekarar 2006 da suke shigowa jejin. Ita da mijinta duk asalin ƴan ƙauyen ne. Mijinta Maude, shine yaya ga Tanimu da yayta gwagwarmayar jawo cigaba a wannan ƙauye. Ita ko sunanta Hafsatu, amma ana kiranta da Hassatu a gaba ɗaya ƙauyen. Shekararsu tara da aure ALLAH bai basu haihuwa ba, sai daga baya kwatsam ta samu ciki, cikin daya saka duk wani masoyansu a farin ciki da su kansu.
     Kamar yanda Hassatu ta faɗa tana jin labarin aikin sojoji ne a rediyon ƙanin mijinta Tanimu idan ya kunna musu, yakan kuma bata labarai irin na birni da abubuwan cigaba da ƙoƙarin da jami'an tsaro musamman sojoji keyi a yankin nasu kan ta'addacin dake faruwa dan su ƙauyensu lafiya lau yake zaune har lokacin. A hankali zuciyarta ta dinga kwaɗaituwa da son abinda zata haifa ya zama soja, kullum wannan shine fatanta, har mutane kan mata dariya a kan hakan da ɗaukarta shashasha, burinta ya sake girma da faɗi a lokacin data haɗu da su Zak-Shadow, haka ta dawo gida cike da farin ciki a wannan ranar, ta bama mijinta Maude labarin komai daya faru. Shi mutum ne mai sanyin hali da rashin yawan magana, sai kawai yay dariya dan ya ɗauki zancen nata kawai shiririta irin ta mata ne. Ita kuwa tun daga ranar ta addabeshi da labarin sojoji da fatan haihuwar namiji ɗanta ya zama soja. Tun yana mata dariya har ya fara jin haushin hakan yana mata faɗa, da taga haka sai ta daina masa maganar kawai. Cikin aminci UBANGIJI kwanaki goma sha shida da haɗuwarsu da su Zak-Shadow a daren juma'a ta haihu, sai dai kash maimakon ɗa namiji da take fatan haihuwa dan kawai ya zama soja sai aka samu mace........✍🏼



_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 36_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Duk da namiji Hassatu taso batai baƙin cikin samun macen ba, sai ma farin ciki mara misali ta shiga, tare da addu'ar ALLAH ya bata namijin a can gaba. Ranar suna shagali akayi sosai saboda wannan haihuwa ta farin ciki ce a garesu, hidimar da Maude yayi da danginsu har ba'a magana. Yarinya taci suna *_NAJA'ATU_* sunan mahaifiyar su Maude, dan haka sukai mata alkunya da Ummi, sai Tanimu yace tsohon yayi ne a dinga kiranta *_Nimrah_*. Tun mutane na kananun magana akan sunan aljanu Tanimu ya sakama Naja'atu ƴar Hassatu har suka haƙura, dan kuwa itama uwar ƴar Hassatu sunan ya mata daɗi.
        Bayan haihuwar Nimrah burin haihuwar ɗa namiji da zai zama soja bai bar zuciyar Hassatu ba, sai dai wani ikon ALLAH har Nimrah takai shekara biyar ko ɓatan wata Hassatu bata sake yi ba. Sai dai bata fidda rai daga rahamar UBANGIJI ba ta cigaba da addu'a da fatan samu.
     Nimrah yarinya ce ƙyaƙyawa. Irin black beauty ɗin nan da baka gajiya da kallo, akwai dogon hanci da manyan idanu masha ALLAH. Sai ƙaramin bakinta na surutu da tsiwa. Dan kuwa idan kaji ance shugaban rashin ji da rikici to Nimrah na layin farko ne. Ga gata kawunta na mata Tanimu, hakama iyayenta kasancewar sun jima basu haihu ba kuma ita kaɗai ce. Koda yaushe zaka sameta tsaf cikin kayan kwalliya irin na zamani, dan Tanimu baya gajiya da saya mata kaya duk da shima yana da yaran amma duk maza ne su biyu. Amma yanda yakema Nimrah gata sai ka ɗauka shine ya haifeta, dan har abun na damun matarsa shiyasa ta tsani Nimrah da iyayenta, kullum cikin son raba mijinta take da su amma shi ya tsaya tsayin daka akan bata isa ba. A kwana a tashi yau ga Nimrah na shekara ta bakwai da wasu watanni a duniya....

>>>>>>•<<<<<<

         Cikin takunsa na nutsuwa da ƙarfin jiki ya shigo falon. Babba ne sosai, dan ya ninka falon sashen matarsa sau biyu girma. Amma duk da haka a gyare yake ƙal ga wani ƙamshi mai saka zuciya nutsuwa na tashi da sanyin ac. Shiru babu hayaniyar komai sai ta ƙarar ac da tv dake kunne tashar mbc 3. Duk da babu kowa sai da yay sallama sannan ya shiga, sai lokacin idanunsa suka sauka akan yaron dake zaune hankalinsa gaba ɗaya a kan tv. Yaron bazai wuce 9years ba, yana da ƙiba gashi ƙyaƙyƙyawa masha ALLAH. Tvn ya ɗan zubama ido shima, kafin ya maido su kan yaron yay ƙaramar gyaran murya.
       Da sauri kuwa yaron ya juyo inda yake, suna haɗa ido ya zabura tare da dirgowa a saman kujerar yayo kanshi da gudu cike da farin ciki. A karo na farko ya saki wani ɗan murmushin gefen baki, sai kuma ya ɗan kai dirƙushe gwiwar sa ɗaya a ƙasa ɗaya a zaune ya tokare ya warema yaron hannayensa ya shige. Gaba ɗayansa ya rungumeshi, hakama yaron yay masifar ƙanƙamesa cikin matsanancin farin ciki yana faɗin, “Oyoyo Dada na”.
         Murmushi ya sake yi yana rungume da shi, dai-dai ya ɗagoshi daga jikin nashi wata ƴar budurwa da bazata wuce 17years ba ta fito daga wata ƙofa hannunta ɗauke da ƙaramin bowl dake tururi alamar abinci ne a ciki. Sosai itama farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ƙaraso wajen da sassarfa tana faɗin, “Dada sannu da zuwa”.
       Kansa kawai ya jinjina mata, sai itama tai saurin sake risinawa tana gaishe shi. Bai amsa ba sai da ya miƙe tsaye hannunsa riƙe dana yaron, sai dai idanunsa a kanta shiyasa ta sake nutsuwa sosai amma har lokacin fuskarta da murmushin farin cikin ganinsa.
          “Miya hanaku zuwa makaranta?”.
     Ya faɗa cikin buɗaɗɗiyar muryarsa. Da sauri ta ce, “Anyi hutu ne jiya Dada”.
       Nan ma kansa ya jinjina da maida kallona kan yaron daya amshe zancen yana bashi labarin yazo na biyu a ajinsu. Hannunsa yaja suka ƙarasa cikin falon sosai, zama yay a kujera ya zaunar da yaron a kusa da shi. Itama budurwar da yaron ya kira Aunty Biebah bowl ɗin hannun nata mai ɗauke da dafaffiyar indomie ta ajiye a gaban yaron.
     Ta miƙe zata bar wajen ya ce, “Ina Mammah?”.
        “Tana ciki Dada, tayi sallar walha ne dama zan gaya mata kazo ne”.
     “Barta, haɗa min breakfast, bana son jagwalgwalo kuma”.
    “Yes Dada, yanzu fa na iya duk irin abincin da kake ci, tunda ka tafi na dage inata koya. Da Yaya Ma'aruff yaga na dage shine ya sani makarantar koyon girki ma”.
        Shi dai idanu kawai ya zuba mata tana zuba surutu. Dukan ƴan uwansa yana son su ƙwarai da gaske. Amma tausayin autar tasu Biebah mai girma ne a zuciyarsa saboda ita kaɗai ce ba mahaifinsu ɗaya ba, sannan kamaninta daban da su. Mahaifinta na raye, amma bata da maraba da su da suka rasa nasu, dan har yanzu Alhaji Nura yaƙi karɓarta a matsayin ƴarsa, duk da kuwa har yanzu ba'a sake masa haihuwa ba bayan ita. Tunanin nasa ya ture gefe, sai kuma ya miƙe yana faɗin, “To akku sarkin magana jeki min abinda na saki”.
     Daga haka ya nufi wata hanya, itama dake tura bakin shagwaɓa sai ta juya hanyar kitchen cike da farin cikin yau zatama Dada abinci mai daɗi. Dan a wani zuwa da yay ya taɓa sakata ta haɗa masa salad kawai tai masa shirme, tako sha faɗa, shiyasa ta dage da burin duk randa ya dawo zata faranta masa rai da abinci.
      
       Dai-dai ƙofar farko ya tsaya, a buɗe take sai labule dake a sake, cike da nutsuwa yay sallama. Daga ciki wata dattijuwar murya ta amsa masa a tausashe. Labulen ya ɗaga ya shiga cikin ɗakin, mamallakiyar muryar na zaune akan sallaya alamar salla ta idar take addu'a ta ɗago tana kallonsa. Tabbas shekaru sunja, fata ya canja daga mai laushi da santsi zuwa mai ɗan tattarewa da hasken kwarjinin ibada, bazamuce da ita tsohuwa ba, amma zamu kirata dattijuwa dan kuwa a sittin kaɗan ne babu. Tana nan da hasken fatarta da annurin fuska. Tunda tai masa kallo ɗaya ta ɗan kauda kanta tana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. A duk sanda yay nesa da su kewarta gareshi mai girma ce, idan ya ziyarcesu tana jin nutsuwa amma takan danne da yanayi irin na masu dattako. Gaba ɗayansa a halittar jiki Abdul-rasheed take gani, duk da kuwa ya fishi buɗewa da ginannen jiki, dan Zak-Shadow irin mutanen nan ne masu ƙirji gashi a murɗe sosai musamman daga sama, cikin nan a lafe tamkar ba'a zuba masa abinci. Sai hasken fatar ta daya ɗauka kawai, da halin rashin yawan magana irin tata data kakarsa mahaifiyar Abdul-rasheed. Dan tun yana ƙarami Baba yasha faɗin halayyar Haysam ta rashin yawan magana da murɗin hali irin na Inna ne, kawai shi dan ya haɗa biyu ne dana mahaifiyarsa shiyyasa abin yay masa yawa.....
         “Barka

25 / 49