KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   35 / 49

102K to 105K   out of 146.5K words

wanda yayi magana a ɗakin kowa yana kallon Nimrah da son jin ƙarin bayani a bakin Zak-Shadow ɗin ko Imran. Sai dai suma duk sunyi shiru. Sai da aka kusan mintuna biyu sannan Zak-Shadow yay ma Nimrah magana a karo na farko.
         Idanunta dake tara ƙwalla ta zuba masa batare data amsa ba, sai kuma ta fashe da kuka da faɗin, “Baba ɗan sanda nika kaini wajen Ummana. Bana son nan”.
       Kallonta kawai yake yi shi dai, sai Imran ne cikin lallashi ya duƙo yana mata magana. Kafaɗa ta maƙe masa. “Ni dai bana son nan”. Ta sake faɗa tana ɓarkewa da kuka harda fara buga ƙafa, ƙarshe ma ta zube ƙasa zata fara musu borin data saba yima Ummanta a Bankaura. Zak-Shadow bai ma san ya daka mata tsawa ba.
           “Kika mana bori anan sai na karya ƙafafunki, maza tashi”.
    A mugun razane ta miƙe jikinta na rawa, ta gumtse baki domin hana kukan dake son kufce mata fita. Imran zai riƙota rawar jikinta ta ƙaru.  A karo na farko Mammah dake kallonsu kamar kowa na ɗakin tai ƴar gyaran murya, sai kuma cikin lallashi ta miƙe ta ɗauki Nimrah cak ta ɗaura a saman cinyarta. Rungumeta tayi a jikinta. Kamar kuwa tana jira sai ta ƙanƙameta ta fashe da kuka. Cikin dabara irin ta uwa Mammah ta dinga shafa kan Nimrah da bayanta har barci ya ɗauke ta a haka. Dai-dai lokacin kuma likitan dake kula da Zak-Shadow ya shigo. Dole kowa ya miƙe domin tafiya.
     Mammah dake kallon ƙyaƙyƙyawar baƙar fuskar Nimrah dake barci ta ce, “Gashi tayi barci, ko nan kusa da kai za'a kwantar da ita ne?”.
        “A'a Mammah ku tafi da ita gida, dama nan za'a kawota”.
      Babu wanda a ɗakin bai kalla Zak-Shadow mai maganar ba, idan ka cire Imran dake normal. Tsulum Nabeeha ta ce, “Gida kuma D. A dalilin mi? Ina iyayenta da baza'a kaita wajensu ba sai gidan mu?”.
      Bashi da niyyar bata amsar tambayoyinta. Dan haka Imran ya katse shirun da faɗin, “Kuyi haƙuri idan ya samu lafiya zakuji bayanin komai a kanta.....”
      “Bayani kamar ya? Kai miyasa baza'a kaita naka gidan ba to? Ko dole shike da alaƙa da ita?”.
     Naneeha ta sake maganar cikin rufewar idanu. Dan tana da matsanancin kishi na tashin hankali. Shiyasa ko ƴan uwan Zak-Shadow take jin kishi idan sun raɓe shi. Matar mahaifinsu Uncle Nasiru kanta saboda kishin uwarsu basa ko gaisheta, shiyasa da suka shigo ma ko kallonta basuyi ba balle ƴaƴanta duk da kuwa bata haɗa zama da uwarsu a gidan su ba, tunda sai da ta fita a dalilin auren Nabeeha da Zak-Shadow ɗin sannan ya aureta. Da aka sasanta su ta dawo tace bazata koma ba sai ya saki matar tasa, shiko yace tai zamanta, shi da matarsa mutu ka raba dan yana samun kwanciyar hankali a wajenta fiye da sanda yay rayuwa da ita. Hakan ya ƙara mata tsana a wajen su Nabeeha ɗin, ita ko ta kame kanta daga garesu sai dai su zageta a bayan idonta, agaban ta kam babu dama dan shakkarta ma suke yi...
Ganin mugun kallon da Zak-Shadow ya watsama Nabeeha ɗin Mammah ta katse yunƙurin Imran na son sake magana. “Ya isa haka, kumuje kawai ga likita na jiranmu fa”.
     Kowa yunƙurawa yay da niyyar tafiya banda Nabeeha data cika tai fam. Sai ma yunƙurowa tai zata sake magana Uncle Nasiru ya daka mata tsawa. “Ba'a isa dake ba kenan ko Nabeeha?”.
       Hawayen da suka cika mata idanu ne suka silalo, ta ce, “Amma Abbah....”
    “Bana buƙatar ji, wuce muje”.
  Yanda yay maganar babu wasa balle sassauci ya sakata raɓashi ta wuce tana waiwayen Zak-Shadow dako kallonta bayayi. Suna gama ficewa yaja tsaki mai ƙarfi yana mai zamewa ya kwanta. Ayyanawa yake a ransa Yaya zai yi da baƙin kishin Nabeeha shi kam? Dan yayi imanin tunda ta fara da haka ba ƙaramin badaƙala zaman yarinyar nan zai kawo ba a wajensu. Shi kuma babu gudu babu ja da baya akan yarinyar nan, yanda ya amshi amanarta a hannun mahaifiyarta in sha ALLAHU zai riƙe koda ransa zai zama fansa a wajen bata kariya........✍🏼


       (🤔To babbar magana).
  



_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 50_

__________________

🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH?mode=ems_copy_t

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF 'YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata💃😍

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻

Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi

Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi

Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra

Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327 call or Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Iska kaɗan Imran ya furzar yana kallon fuskar Zak-Shadow daya lumshe idanu. “Zak.. gaskiya akwai matsala, tunda har matarka ta fara nuna damuwa akan yarinyar nan”.
      Shiru kamar bazai tanka ba, sai kuma ya buɗe idanunsa da har sun ɗan sake kaɗewa akan Imran ɗin. “Saboda itace mai aure na?”.
          “Humm bazaka fahimta ba, kasan mata da kishi, bana son maimakon riƙe amanar da bani da haufi a kanka wajen riƙewa al'amarin ya koma wani abu daban. Taya kake tunanin zata riƙe yarinyar nan a wannan yanayin data fara nunawa?”.
      “Sai ta kasheta ai, ince dai ƙarshen kishin nasu kenan ko. Mtsoww, ni kada ka ɓata min rai ma”.
    Shiru Imran yay bai sake magana ba, amma tabbas shi yasan akwai rigima. Dan kishin Nabeeha ba ɓoyayye bane ga kowa. Tunda har akan ƴan uwansa da Mammah ba ɓoyewa take ba. A haka likita ya dawo ya duba Zak-Shadow ɗin, ganin ya ɗakko allurar barci ya dakatar da shi.
       “Ka sallame ni kawai”.
  Cikin girmamawa sojan likitan ya ce, “Kayi haƙuri Sir ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ne, dan jikinka na buƙatar hutu sosai”.
       Wani kallo ya watsa masa kawai. Da sauri likitan yace, “I'm sorry Sir”.
  Murmurshi Imran yayi a karo na farko. Sai kuma ya kalla likitan. “Karka damu ka sallame shi kawai, idan baiji dai-dai ba sai ya dawo”.
      “Okay Sir”.

<<•>>°<<•>>°<<•>>

          A ranar aka sallami Zak-Shadow daga asibiti. Shi mutum ne mai adalci da duba na ƙasa da shi akan komai daya dace. Dan haka maimakon tafiya gida ya samu hutun jiyya da aka basu sai ya koma jihar da ƙauyukan su Bankaura suke ƙarƙashinta ya duba sojojinsu da aka kwantar a asibiti. Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba da ganin irin ɓarnar da akai musu. Dan sojoji da yawa sun jikkata. Hakama ya shiga har inda aka killace gawarwakin waɗan da suka rasa ransu, ciki harda Captain Musa. Lokacin daya ɗora idanunsa akan Captain Musa sai da suka sake juyewa, Captain Musa jarumin soja ne  ɗan amanarsa, ya taka rawar gani matuƙa akan wannan yaƙin, babu abinda zasu masa sai addu'a. Lokaci ɗaya aka harbesu da Major Imran, shi da yake kwana ya ƙare tun a jejin ya rasu, shi kuma Imran ya suma.
         Bayan ya gama zagaya su kaf daga asibitin cikin barrak inda sojojin suke su, babban asibitin jihar ya nufa itama. Nan ko mutanen ƙauyukan ne da suma suka samu raunuka. Kamar yanda yay fata suna samun kulawa ta musamman daga gwamnati, akwai kuma jami'an sojinsu a tare da su, da ƴan sandan farin kaya. Suma ya dubasu. Daga nan ya wuce sansanin da aka samawa waɗan da suka tsira. Ganin yanda aka barsu a wulaƙance sai a tsakar wajen suke kwana damma zafi ne ransa ya ɓaci.
     Dama akwai zaman da zasuyi da Gwamnan jihar da shi da wasu manyansu a washe gari. Ai gaba ɗaya ya tattara takaicinsa ya ajiye har zuwa lokacin zaman. Daga sansanin cikin jejin da nasu sansanin yake suka koma. Komai ya lalace, sai dai anata kafa sabbin tantuna an kuma kawo wasu rundunar sojojin dan bazai yiwu abar yankin a haka babu tsaro mai ƙarfi ba. Har dare suna a cikin jejin, dan har cikin ƙauyukan Bankaura, Gangare, da Marke sai da suka shiga. Anan dama abubuwan sukafi tsamari musamman Bankaura a ƙarshe-ƙarshe. Dan an musu ɓarna matuƙa da zasu daɗe basu maida gurbinta ba. Har a yau ana zaƙulo gawarwaki a cikin jejin da ƙauyen Bankaura irin na wanda suka ɓuya a wasu wajejajen suka kasa fita. A lokacin da suka wuce ta ƙofar gidan su Nimrah ya kwashe mintina uku yana kallon gidan da tuna abubuwan da suka faru tun daga farkon zuwan su Imran da sanda yay kiransu. Randa Nimrah tai musu zancen falawa har zaman da sukayi da Ummanta. Rayuwa kenan, cikin abinda baifi sati huɗu ba komai ya lalace, dan gidan ya rurrushe sosai sakamakon bomb da yaran Dagger suka tayar musu suma tamkar gidan iyayen Umman Nimrah. Shiyasa suma baya jin akwai wani sauran zuri'ar data rage, idan kuwa sun rage to ƙalilan za'a samu kuwa a ciki, suma yara ne ko wanda basa a garin al'amarin ya faru.
        Tunda suka baro jejin zuwa masaukin da aka bashi a cikin barrak na jihar wanka kawai ya iya yi ya zauna yana wasu rubuce-rubuce, bayan ya kammala kuma ya hau salloli. Bai kwanta ba sai da yay sallar asubahi. Zuwa ƙarfe goma dole ya farka dan suna da meeting da zasu zauna da Gwamna akan harkar tsaro.
     Amintaccen yaron nan nasa, kuma munafukinsa a bayan fage da tunda ya iso yake nane da shi ya kira a waya. Babu jimawa ya iso. Bayan miƙa gaisuwar girmamawa tamkar wani mutumin arziƙi kansa a ƙasa ya ce, “Sir! Akwai abinda kake buƙata ne?”.
     Batare da Zak-Shadow ya dubashi ba ya miƙa masa wata ƙaramar takarda da ATM ɗinsa. “Kaje Boutique ka sama min kayan da zanyi amfani da shi. Saura ka ɓata min lokaci”. Ya ƙarashe maganar ƙarshe cikin dakewarsa da rashin ɗaukar raini.
        “I'm sorry Sir, bazan daɗe ba in sha ALLAHU”.
    Zak-Shadow bai sake tanka masa ba, hasalima ya ɗauke kansa ya koma gaban takardun da yay ta rubutu a daren jiya. 

         Koda Ojo ya fito sai ya harari ɗakin da Zak-Shadow yake, kafin ya kalla ATM ɗin daya bashi da takardar mai ɗauke da pin ɗinsa ya taɓe baki. Baiyi yunƙurin komai ba sai da ya fita a barrak ɗin gaba ɗaya. Nesa sosai ya samu waje ya tsaida mai mashin ɗin daya ɗakko shi. Sauka yayi ya bashi kuɗin, ya samu ƙasan wata bishiya ya zauna. Kamar yanda ya saba kai duk wani motsi da bayanan Zak-Shadow ga iyayen gidansa yanzun ma haka yay kira ya rattafa bayani. Tun daga dawowar Zak-Shadow a jiya har komawarsu jejin nan da ƙauyukan, da takardun da yaga ya baza a ɗakin daya kwana.
    Daga can wanda yake gayawar ya ce, “Su kayan daya aikeka ka saya na miye?”.
       “Sakawa zai yi sir! Sai dai kamar akwai inda zasuje shi da wasu manyanmu dan jiya bayan mun dawo barrak ɗin sunyi wani ƙaramin meeting su uku”.
        “Na baka daga nan zuwa awa ɗaya, nasan ina zai je. Idan ba haka ba kada ka kirani. Sannan ka sani, dolene a yanzu sanya idonka yafi na baya, dan mun rasa yara biyu a wannan tafiyar, an kashe ɗaya, ɗaya na cikin wanda aka jima rauni a asibiti”.
      “Babu wata damuwa Sir, komai kuke buƙata zanyi fiye da hakan, kada ka manta na shiga rigar soja ne kawai saboda aikin ku badan zama soja ba. Shiyyasa ma a yaƙin nan ban yarda na cusa kaina a halaka ba”.
          “Good! Da kake tuna hakan. Yaushe zai koma Abuja?”.
     “Bani da cikakken bayani akan hakan shima, amma nasan bazai jima ba tunda yana ƙarƙashin hutun jiyya ne shi da aminin nashi dama sauran Captains ɗin mu. Dan shi kaɗai ma yazo jiyan alamar akwai abinda yazo yi, duk da dai nasan shi mutum ne azababbe akan aiki shiyyasa ake shan wahalar cimmas cikin sauƙi”.
          “Mtsoww! Zai kuwa gane kuransa a wannan karon”. Daga haka ya yanke kiran. Ojo dake dariyar mugunta zaram ya miƙe yana cire layin daya saka a wayar tasa yay kira, ya maida ainahin layinsa da kowa ya sani sannan ya sake tare mashin ya hau ya tafi aiken Zak-Shadow.

★Kai sojan da Zak-Shadow ya saka ya biyo bayansa ke ɗawa tamkar ƙadangare, sai da ya ga mashin ɗin da Ojo ya hau yayi ɗan nisa sannan ya tare wani shima ya hau. Bayan Ojon yasa suka bi, sai dai bai sauka a mashin ɗin ba lokacin da suka iso inda ya sauka a nashi mashin ɗin ya shige wani Boutique. Har yace mashin ɗin ya juya sai kuma yace ya dakata, suna nan kusan mintuna ashirin Ojo ya fito cikin sauri yana kallon agogon hannunsa. Mashin ya sake tarewa ya haye. Yanzun ma sakawa sojan yay suka cigaba da bin bayansa, sai dai ganin ya sauka a ƙofar gate ɗin barrak ɗin shi kuma sai ya sauka can nesa ya biya mai mashin ɗin ya ƙaraso da kafa.
       Bai nufi masaukin Zak-Shadow ba har sai da ya tabbatar Ojo ya kai masa kayan ya baro ɗakin sannan. Cike da girmamawa yayi knocking, Zak-Shadow ya bashi izinin shiga. Cikin ƙamewa da sarawa ya ce, “Sir! Duk inda yaje tare mukaje da shi ina biye......” tsaf ya labarta masa komai da ya gani ya kuma ji daga Ojo. Wani kalar zuba masa ido Zak-Shadow yayi, dan tabbas zuciyarsa ta girgiza. Saboda daga jiya zuwa yau ne kawai ya ɗarsa zarginsa akan Ojo, zargi kuma ba irin wanda ya samu bayani ba a yanzu. Dan kuwa shi zargin ma da yakema Ojon daban, abinda

35 / 49