KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   34 / 49

99K to 102K   out of 146.5K words

Spider mai kuka ya share hawayensa.
       Da kaushi murya oga Jush ya ce, “Silence. Plan c will begin now. Bana buƙatar Dagger da duka yaransa da aka kama a raye. Zamu sake sabon tsari daga yau. Shi ko tunda yace zai iya wasan zamu zuba. A yanzu ba wasan mutuwa bane ba, wasan gasa masa aya a tsakkiyar tafin hannu ne. Zai rayu, sai dai rayuwa mafi raɗaɗi da ƙasƙanci a idanun ƴan ƙasar tasa dake kambamashi da zuga jarumtarsa. Mu DODANNI ne da KIƊA A RUWA BAYA TADA HANKALIN MU. Zamu ɓoye shi a indanunsa da kunnuwansa zasu cigaba da jin kukan mutanen ƙasar tashi, ya cigaba da kallon gudanar jininsu a cikin ƙasa tamkar kwata ɗin yanka dabbobi. Zakuma mu ɗiba arziƙin ƙasar tasa, kuma ƴaƴan ƙasar tasa ne zasu zama bayinmu masu haƙa, masu kuma kashewa”.
      Raff!! Raff!! Raff!! Kake jin tafi na tashi ga sauran members. Sun san waye ogansu, sun kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari. Dan daga faro tafiyar nan zuwa yanzu bai taɓa faɗa bai cika musu ba. Matuƙar nutsuwa kuwa kalaman nashi suka basu, har suna ji a ransu Zak-Shadow tamkar sauro ne yanzu a dakin kwanansu da baya buƙatar magani sai net kawai domin killacewa. Ga damar shan jini ya samu, amma babu karfin fita domin tsira da rai...
     Sun rufe taronsu da zancen fara horar da sabbin yara da zasu maye gurbin Dagger. Yaran kuwa yaran nan ne da suka rage a hannunsu da suka sace. Daga haka taron ya tashi kowa ya kama gabansa rai fes..

<<•><•>><•><<•><•>>

            A lokacin da can ƙungiyar duhu ke ƙoƙarin haɗa GUDU DA WAIWAYE... anan ɓangaren mazan fama bisa umarnin General ne aka turke Zak-Shadow domin duba lafiyarsa. Dan da farko ya dage akan baya buƙata, duk da kuwa ko'a zahiri jikinsa akwai ƙananun raunika na gumurzun da aka sha, banda cizon ƙwarin cikin jeji kala-kala da farar fatarsa ta kasa ɓoye wa. Shi kansa ba ganin likitan ne baya buƙata ba, hankalinsa da tunaninsa nakan Mammah da ƴan uwansa da matarsa ne gaba ɗaya. Dan ya tabbatar sunfi kowa shiga tashin hankali akan abinda ke faruwa, musamman daya kasance a kwana na uku da hargitsewar yaƙin har an sanar da mutuwarsa, mutuwar da ta ɗauki hankalin mutane sosai duk da kuwa ba daga bakin jami'an soji sukaji ba ko makusantansa, hasalima wani ɗan media daɗi ne ya zauna ya tsara labarin da komai, cikin sa'a kuwa ya samu karkatowar hankulan mutane a kansa har wasu gidajen jaridu wajen saurin son ace su suka fara kawo zancen suka fara yaɗawa. Da yake mutane jininsu a farce yake na son jin yaya Zak-Shadow ke ciki saboda randa ya saka sulken yaƙi da kansa kafafen yaɗa labarai masu girma da sanin yakamata sun sanar cike da alfahari. Shiyyasa fitar batun mutuwar tasa yaso yin tasiri sai da hukumar soji suka ƙaryata hankulan mutane ya kwanta aka cigaba da binsu da addu'ar samun nasara.
       Alhamdullahi UBANGIJI kuwa ya amsa wannan addu'oi tunda nasara ta samu. Duk da wasu sojojin sun rasa rayukansu wasu sun rasa wani sashe na jiki. Musamman Captains da aka rasa kusan guda uku da suka sha gwagwarmaya. Imran ma ya samu harbi a ƙafa, kamar yanda shima Zak-Shadow ɗin ya samu harbi a hannu ta gefen kafaɗa, sai dai da kansa ya cire harsashin ya kuma cigaba da gwagwarmaya, sai kuma a yau ne da komai ya lafa aka sake masa treating ɗin wajen yanda ya kamata...

<<<<<•>>>>>

       Kamar kuwa yanda Zak-Shadow yay hasashe akan tashin hankalin su Mammah hakanne. Dan kuwa tun ranar da ya bar gidan ba kowa ya sake barci mai daɗi ba. Hatta su Ma'aruff dake ƙasar Chaina kawo kaya tunda Bilal ya sanar musu a ranar da Dadan ya ɗauki ɗammarar yin yaƙin da kansa suka tattara komai suka dawo gida cikin tashin hankali. Dan a duk sanda Dada yay irin wannan zuciyar ta saka sulken yaƙi ba ƙaramin ɗagawar hankali suke samu ba, gani suke kamar za'a kashe musu shi a tarnaƙin yaƙi. Sai dai Alhamdullah UBANGIJI na bashi kariya da nasara koda kuwa zai samu wani rauni mai girma, iyaka yayi jiyya ya miƙe ya koma filin daga. To amma wannan karon sai suka ji zukatansu sun karaya sosai.
      Mammah kanta mai ƙoƙarin ƙarfafasu da shanye tata damuwar a wannan karon itama a raunane take, amma maimakon zaman kuka da ɗaga hankali sai ta maida hankali ga addu'a da sadaka, hakan ya ƙarfafa zukatan su Bilal suma suka nutsu wajen gayama UBANGIJI kukansu da fatan nasara ga Dadansu. A randa kuwa akace an kashe shi ɗin nan yanke jiki Mimi tai ta faɗi, jini ya ɓalle mata abinka da mai ƙaramin ciki, hakama sauran babu wanda bai kusa suma ba saboda tarwatsawar zukata. Sai dai Alhamdullah abin bai nisa ba sukaji gaskiyar zance aka koma hawayen farin ciki.
     Yau kuwa suna jin fitowar su daga jejin kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye. Tuni suka bar gida zuwa Headquarter tun ma kafin su Zak-Shadow ɗin su iso Abujan, dan an sanar zai wuce gida ya huta tare da yin jiyya. Suna a cikin barrak ɗin jirgin soji mai saukar angulu daya ɗakko su Zak-Shadow ya sauka, sai dai basu samu ganinsa ba aka shige dasu ciki saboda yanayin da yake ciki na ganin jiri a dalilin jinin daya zubar sosai. Su Imran kuwa dama yau kwanansu huɗu kenan a asibitin cikin barrak ɗin.
     Har bayan magriba basu ji sun gaji da zaman ba, zuwa lokacin ma Uncle Nasiru ya iso shima. Shi da mahaifin Imran ne suka samu ganawa da Gen. Dan son jin yaya Haysam ɗin na raye kuwa?. Cikin mutuntawa Gen yay musu bayanin da sukaji gamsuwa da kwanciyar hankali, ya kuma basu haƙuri da tabbatar musu in sha ALLAHU zuwa gobe za'a basu damar ganin shima Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu ɗin da muƙarrabansa dake a raye dan sunga Imran dama kullum ma suna zuwa dubashi, sannan a sanar da wanda suka rasa rayukansu...
Wannan bayani ya saka su Uncle Nasiru lallaɓa su Mammah komawa gida, sai dai a gidan ma jigum-jigum sukayi babu mai wata walwalar kirki balle jira. Abinci kuwa babu wanda ya nema balle tunanin ci. Nabeeha matarsa kuwa data dinga kuka acan da dagewar acan zata kwana har sai ta ganshi koda suka dawo gidan Mammah bata barta komawa sashenta ba, sai ta taho da ita nan sashensu a bedroom ɗinta. Sosai take jin tausayin Nabeeha ɗin a ranta duk da kuwa ita ta haifi Haysam, ita tafi cancanta aji tausayi da yarda tafi kowa jinraɗaɗi da tashin hankali. To amma mata da miji sai ALLAH, musamman auren soyayya irin na Nabeeha da Haysam, dan tsantsar soyayyar da Nabeeha kema Zak-Shadow a bayyane take ƙwarai da gaske, bata iya ɓoyeta agaban kowa har da ita mahaifiyarsa ma. Shiyasa a wasu lokutan da Nabeeha kan nuna kishinta akan ƙannensa Mammah takanyi murmurshi ne kawai. Haka suma ƙannen nasa basa iya ɓoye kishinsu a kanta wani lokacin, musamman ma idan yazo gidan da nufin yin ƴan kwanaki kowanne najin shine yafi cancanta da samun lokacinsa fiye da ɗayan ɓangaren. Ita dai tana musu addu'a da fatan haɗin kai, dan koba komai itama Nabeeha tasu ce tunda jinin Uncle Nasiru ce, Uncle Nasiru kuwa ya cancanci kowace irin ƙauna da girmamawa a garesu baki ɗaya.

        Washe gari ma basu sami damar ganin su Zak-Shadow ba. Dan allurar barci ake musu saboda su sami isasshen hutu na rashin wadataccen barcin kwana da kwanaki da suka sha. Musamman ma shi uban tafiya commandor ɗin yaƙin da ko bai faɗa ba a kallo ɗaya zaka fahimci a jigace yake da son barci, hasalima shine ya saka shi ganin jirin da har suka iso yana ciki.
      Kwanaki uku cir kuwa suka sami wadataccen barci da nutsuwa yanda ya kamata. Dan basa ganin kowa babu mai ganinsu sai likitoci da wasu manyan soji da ke ɗan zama da su a duk sanda suka ɗan farka musamman a lokacin salla. Suma basa wuce mintuna talatin suke fita su barsu. A kwana cikon na huɗu tunda safe iyalan Mammah kaf suka kammala shirin komawa cikin barrak da su Zak-Shadow ke kwance a asibiti. Mota uku sukayi dan babu wanda ya yarda aka barshi a gida har ƙannen Nabeeha. Ganin sammakon nasu ga ƴan jarida da suma suka matsu da son jin halin da su Zak-Shadow ke ciki dan su isar ma al'umma sai General da kansa ya bada umarnin a kaisu ɗakin da Zak-Shadow yake.
     Nabeeha ce gaba-gaba wajen shiga, cikin takaici Mommy ta balla mata harara da jan ƙaramin tsaki. Ja'afar dake gefenta da shima takaicin Raihana dake nuna kamar ta fisu son Dadan ya kume, ƙasa-ƙasa ya furta, “Itafa ji take kamar tama fimu sonshi mtsowww”.
        “Kabar ƴar wahala Yaya J. Ai mu da ita kar tasan kar ce. Dan wannan da ace ta samu Dada yanda take so wlhy sai ta rabamu da shi ma”.
    “Ita ɗin banza”.
Cewar Ma'aruff ƙasa-ƙasa shima. Dai-dai nan suka ƙarasa shigewa ɗakin. Shi kaɗai ne a ciki duk da kuwa babban ɗaki ne an kuma zuba komai a ciki na more rayuwa kamar ba ɗakin asibiti ba. Babu wanda zuciyarsa bata sosu a cikinsu da ganin yanda Nabeeha taje ta maƙalƙalesa ba. Haba wannan rashin kunya har ina bayan tasan Mammah na tare da su.
       Shi kansa Dadan da alama bai san harda su ba, tunda sai da ta shigo da fin minti ɗaya da rabi saboda gudun da tayi sannan suka ƙaraso. Suna yin sallama yay ƙoƙarin janyeta daga jikinsa, ita ko sai ƙara mannewa take har Momy da Ja'afar ɗin dake a gaba suka fara shigowa suka gansu. Magana yay mata data sakata sakinsa na dole, sai dai cike da takaici da baƙin ciki ta watsama su Mommy ɗin harara. Basu kulata ba, dan basa son koda wasa Dada ya fahimci suna TAKUN SAƘA da matarsa akan soyayyarsa.........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 49_

__________________

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LkEgiP5qOEo9YDYjaeZLLc?mode=ems_wa_t✍️✍️ Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed yar mutan Chadian traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products at home my people bazamafa a kwai zafafan promo damukeyi in Sha allahu zuwa on 15 zamugama sannan gareku Yan Kano free ne kayanki zasuzo miki amma fa karyazo bayan mungama promo kuce kyauta ne aa zakibiya kudi nagode takuce yar mutan Chadian mai gyaran ciki dawaje 💃💃 please banda maza,❌maza❌
In kinada matsala wadda zamu iya taimaka miki 09065504546
Ga PRODUCTS DINMU KAMAR HAKA
MAGANIN SANYI
TSUMIN BOM
MADARAR TABAJE
GORON TULA SYRUP
ZUMAR SHADAMATSIN
GARIN YAUKAYAUKA EMERGENCY
GARIN KINFI KAZA DADI
SIRRIN MALLAKAR KASA
SIRRAN GIDANKI
DAHUWAR KAZA
DAHUWAR CICCIBI
DAHUWAR YAN SHILA
HMM BAZASU IRGUBA INA GODIYA SOSAI MY PEOPLE 🥰🥰

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Cike da girmamawa da soyayyar da suke masa suka zagaye gadon kowanne idanu cike da hawaye, shi ko ya zuba musu ido kawai daga zaunen da yake bayansa jingine da fillo. Sanye yake da wando da riga masu taushi kalar army green na barci. Duk da fatarsa tayi duhu sosai saboda wahalar yaƙi ga raunikan jikinsa hakan bai hana kamilar fuskarsa fitar da hasken kwarjini da bayannanniyar nutsuwarsa da kamun kai ba. Karo na farko ya sakar musu ƙaramin murmushi.
        “Miye haka kunzo kun zagaye ni kamar masu shirin min tambayoyin kabari?”.
      A tare suka saki murmushi suma suna share hawayensu, sai kuma suka shiga rungumeshi abin sha'awa su takwas ɗin duka sukai masa runfa. Yayinda kukan Mimi da Biebah ya ƙara ƙarfi. Kansa kawai ya girgiza, tare da ɗan buga bayan Ammar da Ummi da sukafi kusa da shi. Cikin lallashi ya furta, “It's okay guys! I'm here. Kun san dai bana son kuka. Ina Mammah?”.
       Kamar jira suke ya nema Mammah ɗin suka wani dare daga jikinsa Mammah dake tsaye a farkon shigowa ɗakin ta bayyana cikin idanunsa. Yunƙurawa yay zai sauka ta girgiza masa kai. Shi mutum ne mai tsananin girmama iyaye da basu darajarsu koda a gaban waye. Baya wasa da al'amarin Mammah a rayuwarsa ako wane yanayi....
          “Kaida ke fama da kanka ina zaka sauka”.
   Cewar Mammah tana ƙarasa shigowa ɗakin idanunta akansa. Ƙasa-ƙasa ya ɗan murmusa, koda ta kai zaune a gefen gadon kusa da ƙafafunsa sai yay salute ɗinta. Ƙaramar harara tayi masa, harar data saka murmurshinsa ƙara faɗaɗa ƴan uwansa kuwa na dariya. Da ido yay ma ƙanen nasa alamar suma suyi, ai ko sai suka wani ƙame tare da sara mata a tare.
     Mammah dake girgiza kai ta ce, “ALLAH ya shiryeku to. Da alama na fara zama kakarku kuma”.
     Ma'aruff ya ce, “Mammah ba haka bane, kin san masu iya magana sunce UWAR RAGO akema JAJE, UWAR GWANI kuwa sai dai ai mata SAMBARKA.”
         “Wannan zance haka yake Yaya M.”
   Cewar Bilal yana kashe masa ido ɗaya.
       “ALLAH ya shuryeku”.
Mammah ta sake faɗa tana sake maida hankalinta kan Zak-Shadow daya risinar da kai yana gaisheta.
            “Yaya jikin naka?”.
     “Alhamdullahi Mammah bana jin ciwon komai, kawai dai sun so riƙeni anan ɗin ne suma”.
     “Yin hakan shine dai-dai ai. Ga jiki duk raunika ace ba'a jin komai kuma.”
      Ɗan murmurshi kawai yayi, ta gefen yana kallon yanda Nabeeha ta haɗe fuska, dan tunda ƙannen nasa suka zagaye shi ta koma gefe. Sai su Ismat ƙannenta suka koma gefenta suma duk suka maƙale. Idanunsa ya ta janye, zuciyarsa na masa babu daɗi. Ya jima da fahimtar matar tasa bata son ƙyaƙyƙyawar alaƙarsa da ƙanensa, kai wani lokacin ko tare da Mammah ta ganshi suna hira sai fuskarta ta canja, ya rasa gane ma'anar hakan da take yi. Bayan ita bai taɓa nuna damuwar zaman ƙanenta tare da su ba, dan ko babu ita zai riƙe zuri'ar Uncle Nasiru a duniyar nan duk da kuwa Ismat ce kasai tashi biyun ƴaƴan ƙanwar mamarta ne...
      Shigowar Uncle Nasiru da Baban su Imran da Hajiyarsu, sai matar Uncle Nasiru ɗin da yaranta, dan itama dai yaranta biyar da shi a gidan yanzu, kuma suma duk sun tasa ba laifi. Idan aka haɗa dasu Nabeeha da ƙanenta biyu yaransa takwas shima a duniya. Cikin girmamawa Zak-Shadow ya gaida su, dan kallon iyaye yake musu su duka. Yana kallon Uncle Nasiru tamkar Abiy a gefensa, iyayen Imran kuwa suma sun zama iyaye a gareshi, dan suma suna masa abu irin na ɗan da suka haifa, shiyyasa zuminci ne mai ƙarfi a tsakanin waɗan nan zuri'a uku a yanzu.
      Sun jajanta masa, tare da jinjina da addu'a bisa ga namijin ƙoƙarin da sukayi da jarumtar murƙushe waɗan nan mutane da bayyanar ta'addancinsu ke tada hankalin al'umma. A wannan yanayin Imran da zuwa yanzu shi ya fara takawa dan kwanansa na takwas kenan shi a barrak ɗin tun randa aka harbesa aka kawosu ya shigo tare da wasu soja biyu. Sai Nimrah riƙe a hannunsa tayi fes da ita, sai dai tayi zuru-zuru alamar rashin sakewa da damuwa bayyane akan ƴar fuskarta.
      Kamar yanda Zak-Shadow ya zuba mata ido haka kowa a ɗakin ita yake kallo, yaran sojin suka ƙame cike da girmamawa ga Zak-Shadow, sannan sukai gaisuwa da tambayar jikinsa. Kai ya jinjina musu kawai. Imran ma ɗan ƙamewa yay alamar nuna girmamawar, kawai Zak-Shadow ɗin ya balla masa harara. Bakuna su Ma'aruff suka gumtse suna dariya ƙasa-ƙasa, suko su Mammah murmushi duk sukayi. Imran ya gaishesu, suka tambayi nasa jikin shima duk da kuwa kullum suna shigowa dubashi tun ma kafin a kawo su Zak-Shadow.
        A karo na farko Zak-Shadow dake kallon ƙafar Imran ɗin ya ce, “Yaya kafar taka?”.
      “Alhamdullah saura kaɗan ya rage, dan shekaran jiya na fara takawa sosai. Yaya jikinka kaima?”.
            “Ni lafiyata Lau, kawai anso takura min ne anan”.
     Ƴar dariya Imran yayi, sai kuma ya jawo hannun Nimrah data noƙe gefe tayi kicin-kicin da fuska kamar zata fashe da kuka. Kusa da Zak-Shadow ya matso da ita yana faɗin, “Yanzu su Yusuf suka kawota, itama yau aka sallameta a asibiti”.
         Hannu ya miƙa mata a karo na farko, sai kuma ya ɗaga kai yana kallon su Yusuf ɗin yaran sojin dake tare da Imran. Cikin girmamawa suka ƙara ƙamewa, sannan wanda aka kira Yusuf ya ce, “Sir! Yau da safe suka sallameta gaba ɗaya, bayan an tabbatar babu wata matsala a tare da ita a yanzu. Sai dai sunce lokaci-lokaci zata iya dinga tsintar kanta a yanayin tsorata ko firgici, dan haka za'a cigaba da kaita tana ganin likita da amsar magani”.
         Kansa ya ɗan jinjina, “Sauran yaran fa?”.
    “Duk suna cikin ƙoshin lafiya da kulawa ta musamman ga Captain Ayuba, dan tun ranar su aka miƙasu can hannun jami'an gwamnatin jiharsu. Da ita kaɗai muka taho nan Abuja bisa umarnin Major Imran”.
       “Zaku iya tafiya”.
Kawai ya faɗa bayan ya jinjina kansa. Sai da suka ƙara Sara masa da salute shi da Imran ɗin duka sannan suka juya suka fita. Babu dai

34 / 49