Author : Billyn Abdul Category : Adventure
jeji baƙa mummuna”.
Nimrah dake kuka cike da ihu da cika kunne ta ce, “Niba shegiya bace ba, kuma ba arniya bace muguwa mai yanka mutane. Wayyo Ummana zata yankani kizo Umma, Kawu Tanimu na....” numfashinta ya wani jaaa alamar ɗaukewa saboda kafta da Nabeeha ta sake kai mata da wuƙar cikin rufewar idanu. Hakan kuma yayi dai-dai da isowar Zak-Shadow gabanta yay ƙoƙarin janyeta amma ina UBANGIJI ya riga ya ƙaddara sai ta sami Nimrah sai ko ta shata mata wuƙa a cinya. Ya rabbi, wani irin gigitaccen ihu da Nimrah ta saki Zak-Shadow bai ma san ya wanke fuskar Nabeeha da wani wawan mari guda biyu ba a lokaci ɗaya, wajen yin taga-taga zatai baya saboda gigita shima ta sharɓeshi a hannu, saboda kaifin wuƙar sai da ta fasa rigar shaddar jikinsa ta ratsa fatarsa. Amma bawon ALLAH bata kansa yake ba, ƙoƙarin zaro Nimrah data maƙale a lungu yake yi dan yarinyar tayi ɗif alamar ta suma. Ga jini tuni ya wanke rigarta ta dai-dai cinya inda Nabeeha ta yanke ta.
Gaba ɗaya hankalin su Mammah ya gama tashi, Zak-Shadow dake rungume da Nimrah yana gama sauketa Mammah ta ɗaga rigar, ai a rikice tace, “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” dan yanka ne babba sosai damma jini ya jiƙe ƴar cinyar tata ba'a iya ganin girmansa da zurfinsa.
“Muhammad karka sauketa muje asibiti”. Mammah ta faɗa cikin tashin hankali. Suma su Uncle Jamilu gaba ɗaya sun gama rikicewa. Hatta Momyn Nabeeha rawa jikinta yake yi, tama kasa zuwa inda Nabeehar ta kife kan kitchen cabinet itama alamar taji marin maza. Sai da suka fice Uncle Nasiru da gaba ɗaya yay sumar tsaye ya tafi taga-taga zai faɗi, da ƙyar ya iya laluben bango ya dafe. A haka ya fice a kitchen ɗin shima yabar Momyn Nabeeha da jikinta ke rawa zuciyarta kamar zata fashe. Dan kasancewar a ƙarshe tazo sai idonta ke nuna mata akan ciki Nabeeha ta yanki yarinyar, kai tsaye ta kasheta...
Acan compound ma su Ja'afar gaba ɗaya sun gigice saboda a yanda Dadansu ya fito da Nimrah shaddar jikinsa duk ta ɓaci da jini abinka da fara kawai sun ɗauka ta mutu ne. Hankali a tashe suke tambayar miya faru? Basu sami amsar kowa ba, sai kawai suma suka fara rige-rigen shiga mota....
★ Duk da raɗaɗin da hannunsa ke masa bata kansa yake ba, yana riƙe da Nimrah har aka gama mata ɗinki bayan an tsaida jinin da ƙyar dan anyi allura takai uku kafin aci nasara. Ya rabbi, duk mai imani dole yaji tausayin yarinyar, dan kuwa yankane bana wasa ba, gashi ya shiga sosai har ana iya ganin ƙashin ta. Su kansu asibitin da farko tsoron taɓata sukai sai da Zak-Shadow ya nema gigitasu da ihu. Dole suka dawo hayyacinsu sukai abinda ya dace. Tana sume akai komai aka gama, sannan suka farfaɗo da ita da dabarunsu. Allurar barci suka sake mata dan da ihu ta farka.
Imran ya maida Zak-Shadow dake neman miƙewa ya zaunar yana ma nurse ɗin nuni da hannunsa. Ƙoƙarin nuna shi baya buƙata yayi, dan haka Imran ɗin ya ɗaure fuska ya kafa ya tsare kuma. Dole ya haƙura ya tsaya. Nashi ma da sauƙi amma fa ya yanku shima babu laifi, sai dai bai kai ko kwatar na Nimrah ba. Amma shima duk da haka sun masa ɗinki a wajen.
Sun so riƙe Nimrah yace kawai a sallamesu za'a kula da ita a gida. Dole aka basu sallama da magunguna da dokar kawota ana dubawa suka wuce gida. Yanzu ɗin ma shine ya ɗauketa, ko'a mota tana riƙe a jikinsa har gida. Anan kuma suka tarar da tashin hankalin Uncle Nasiru, su Ismat da Biebah data dawo makaranta zagaye da shi suna kuka, sauƙin ma Biebah tai hankalin kiran matarsa, shine fa ta iso a rikice da likitansu datai kira a waya. Shine yaketa ƙoƙarin ganin nunfahsinsa ya daidaita sanda suke shigowa.
Kai sukam dai wannan family sai dai suce Alhamdullah a wannan tsakani. Ganin al'amarin zai ƙwaɓe dole aka ɗauki Uncle Nasiru zuwa asibiti. Ga kuma Nabeeha can ta kulle kanta a ɗaki tana ihun kuka da rantsuwar idan Zak-Shadow bai saki Nimrah ba sai ta kashe kanta itama. Takaici ya saka babu wanda yabi takan haukan nata sai uwarta dake magiya da lallashinta su Amima na tayata. Da ƙyar da ƙyar dai suka samu ta buɗe. Uwar ta wani rungumeta tana kuka itama wai miyasa zatai mata haka. Miye-miye dai nan sukaita surutasu.....
★
“Tunda barci take kaje ka raba kayan nan da jikinka Muhammad, sam basu da ƙyan gani duk jini abinka da farin abu ƙara tada hankali yake”. Mammah ce mai maganar cikin damuwa da sanyi, dan kuwa babu abinda ke mata kai-kawo idan ta kallesa sai lokacin da Abdul-rasheed ke shinfiɗe a ƙasa an lulluɓa masa babbar rigar shaddarsa data jiƙe da jini.
Dama su kaɗai ne a ɗakin nata, daga ita sai shi sai Nimrah daya shinfiɗar a gado. Kansa ya jinjina yana miƙewa. Har ya fara tafiya ta sake dakatar da shi. “Dan ALLAH na roƙeka kada kace musu komai?”.
A karo na farko ya zubama Mammah hargitsatstsun idanunsa da suka mugun kaɗewa kamar wanda ya busa cocaine. Ita kanta Mammah sai da taji zuciyarta ta motsa saboda yanda idanun nasa suka koma. Magana yake son yi amma zuciyar ƴan maza tazo wuya ya ma kasa, sai kawai ta ce, “Dawo ka zauna”..
Bata jira amsawarsa ba ta taso ta kama hannunsa ta maidoshi inda ya tashi. Baya iya bijire umarninta, dan haka ya koma ya zauna kawai kamar yanda ta buƙata. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ita ta fita a ɗakin. Babu jimawa Ma'aruff yay sallama a ƙofar ɗakin cikin rawar murya alamar shima tsoron shigowa yake, dan sun san wanene Dadansu idan yana fushi, ya subahanallah abin babu ƙyau sam. Sum-sum ya shigo kansa a ƙasa kamar munafuki, kaɗan ya saci kallonsa yaga idanunsa a rufe suke, ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke tare da ajiye kayan a kusa da shi kaɗan. Idanunsa cike da hawaye miryarsa na rawa kamar wani ƙaramin yaro, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai tausayin Dada, dan duniya basa ƙaunar abinda zai taɓa musu shi.
“Kayi haƙuri Dada, ga kaya ka canja inji Mammah”.. sanin ya jishi, yasan bazaiyi magana ba kuma yasa shi fita yana share hawayen da suka sakko masa. Wlhy badan Mammah ta hana su ba yau sai sunma Nabeeha dukan mutuwa a gidan nan, kuma da bazata kwanar musu a gida ba. Amma babu yanda suka iya Mammah ta kafa ta tsare. A falo ma sauran ƴan uwansa na zaune jigum-jigum, dan har su Ummi ma sun zo gidan tuni..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 63_
__________________
https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt
https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite
https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt
Assalamu alaikum,
Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝
Kamar
Kayan Yara
Zannuwan Gado
Kayan kitchen
Shoes and bags
Jewellery
Laces, atamfa,shadda
Dadai sauransu.
To nesa tazo kusa,
Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.
Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
..........Washe gari da fitinar Nimrah suka tashi a gidan. Dan tunda ta farka da asuba take ta kuka ƙafarta-ƙafarta. Haka suke zagaye da ita kowa na ƙoƙarin lallashinta. Yayinda Mu'azz ke tayata kukan shima. Sai kusan bakwai Zak-Shadow da bai san abinda ke faruwa ba ya shigo. Dan rashin samun isasshen barci a daren jiya shima yau makara yay ko sallar asuba a gida yayi ta. Dan haka sai yanzu yake fitowa daga sashensa, batare da ya ko kalla hanyar ɗakin Nabeeha ba, hasalima yayi zaton basa gidan, dan tunda suka dawo asibiti jiya baiga kowa ba tsakanin ita da uwar tasu da ƙannen nata, sai Jiddah ce ma da daddare ita da mijinta suka zo duba su tanata kuka da bashi haƙuri akan abinda ƴar uwar tata tayi.
Tun shigowarsa falon yake jin kukan Nimrah. Kai tsaye ɗakin Mammahn ya nufa shima, inda ya tadda duk ƙannensa a ciki. Kowa kuma ƙoƙarin lallashin Nimrah dake kwance jikin Mammah yake yi, amma yarinyar nan taƙi sauraren kowa sai kwarara ihu take yi. Babu wanda yaji sallamarsa sai da ƙamshin turarensa ya shiga hancinansu da gyaran muryar da yayi sannan duk suka juyo, idonsa akan ƙafar Nimrah ya amsa gaisuwarsu, suko hankulansu na'a kan hannunsa shima.
Cikin girmamawa da tsantseni ya gaida Mammah shima, tare da tambayarta jikin Nimrah data ɗan sassauta kukanta.
“Alhamdulillah, sai dai inaga dole mu koma asibiti yanzu dan tunda asuba take kukan ƙafar, inaga tana mata ciwo ne, kaima yaya naka hannun?”.
Hannun nasa ya ɗan kalla, sai kuma ya kalla ƙafar Nimrah ɗin itama. “Ni kam babu wani damuwa Mammah, itama harda rigima dai”.
“Rigima kam ai dole ce, dan tana da hujjar yinta. Wannan ciwon ba ƙarami bane ga babba ma bare ita. Babbar damuwar ma taƙi cin komai ga tea nan har ya huce taƙi sha”.
Hannu ya miƙama Biebah dake riƙe da kofin batare da yace komai ba, ganin haka sai kawai Mammah ta miƙe tana faɗin, “To Biebah tashi ki nema na mutane abincin kari. Mu'azz tashi kaima muje kai shirin makaranta.”
Kamar zai yi kuka ya ce, “Mammah ni bazanje ba, zan zauna tare da Nina”.
Kallon da Zak-Shadow ya watso masa ya sashi sauka a gadon da sauri, sai dai idanunsa cike da ƙwalla. Murmurshi kawai Mammah tayi ta kama hannunsa suka fice. Caraf Nimrah ta ce, “Mammah ni dai ki dawo naki nake so....”
Mammah na ƙoƙarin juyowa Zak-Shadow ya watsama Nimrah harara, sai ta sake taɓe baki zatai kuka.
“Kika bari wannan hawayen suka zubo zaneki zanyi. Maza karɓa kisha. Kin zauna kinama mutane kukan banza amma bakinki baya mutuwa”.
“Ni dai dan ALLAH ka bita a hankali Muhammad, idan bazaka iya ba na dawo na bata”.
Ƙaramin murmushi yayi. “Shike nan Mammah zan bata”.
Suma su Bilal duk murmushin sukayi dan sunji daɗin ganin murmushin nashi. Shima zamansa ya gyara ya fara kai mata kofin bakinta, sai ko ta fara amsa babu musu. Sha kamar uku ta yatsine fuska tana kallonsa, ta ce, “Dada”.
“Uhhhm”.
Ya amsa mata a maƙoshi.
“Kaima ƴar dabar ce ta jimaka ciwo a hannu?”.
Da mamaki ya zuba mata ido, a zuciyarsa yana ayyana (sai shegen surutu). Suko su Ja'afar dariya zancen nata ya basu, jira suke suji amsar da Dadan zai bata amma yayi shiru. Cikin kasa haƙuri Ammar ya ce, “Nimrah ƴar daba kuma?”.
“Eh Uncle Ammar”. Ta faɗa kamar yanda taji Mu'azz na kiran kowansu da Uncle ɗin. Batare da jiran cewar kowa ba ta cigaba da faɗin, “Ummana tace ƴan daba ke riƙe wuƙa da yanka mutane ai. Kaga itama ta riƙe wuƙa ta yankamu ni da Dada, Dada kaima kayi kuka data yanka ka?”.
Ta ƙare maganar tana tsatstsareshi da idanu. Rasama abin cewa yay, sai kawai ya samu kansa da girgiza mata kai. Idanu ta waro masa sosai, sai kuma ta yamutsa fuska alamar motsin da tai taji zafi. Amma bata haƙura ba sake cewa, “Kenan kai baka yi kuka ba? Kuma baya maka zafi kamar nawa?”.
Nan ma kai kawai ya jinjina mata yana kai mata kofin shayin a baki dan ta ƙyaleshi da wannan surutun nata, gashi ta wani tsatstsareshi da idannunta. Kauda kanta tai gefe, dan in surutu nacin Nimrah itafa sai ta fetsar take jin daɗi, dan yanzu ma kai tsaye ta ce, “Dada jira na gama. Kai miyasa baka jin zafin ko kaima ɗan daba ne? Dan Lawwali yace min suna ƴan daba dake yankar mutum idan aka yanke su basa jin zafi kuma basa yin kuka”.
Anya shi kam ya taɓa gamuwa da magananniyar yarinya irin wannan? A zuciyarsa yake ayyanawa, yayinda su Ma'aruff ke ƙunshe dariyar dake cinsu. Dai-dai Nimrah ta kai hannu tana taɓa hannun Zak-Shadow dake kallonta kawai Momyn Nabeeha tai sallama, kafin su amsa ta shigo Nabeeha biye da ita sai su Ismat a ƙarshe, dan ita da kanta ta tattaro su wai su duba Nimrah su bama su Mammah haƙuri. Ai a bazata Nimrah tai wani uban tsalle ta haye jikin Zak-Shadow ta ƙanƙamesa tana fasa ihu da faɗin, “Wayyo Dada ƴar daba ta sake zuwa, ɓoyeni kada ta yankamu. Wayyo Dada wayyo zata ƙara yankamu shike nan ƴar daba mai wuƙa”.
Idan kunji ana sumar tsaye to ita Nabeeha da uwarta sukayi. Dan har tsakiyar kai kalmar (ƴar daba) ɗin nan ta dakesu. Yayinda su Bilal suka kasa haƙuri shi da Ammar suka shiga kwasar dariya. Suko su Amima yanda Nimrah tai uban tsalle ne da firgita ya basu dariya. Ita ko baiwar ALLAH da gaske tsorata tayi, dan tai bala'in shigewa cikin jikinsa, ƙarshe ma rigarsa ta ɗaga ta tura kanta ciki ta duƙunƙune, ALLAH ya sota ma tun a daka tsallen farko ya riƙe ƙafar tata mai ciwo a hannunsa, da ba ƙaramin fami zatayi ba kam, maybe ma ɗinkin ya farke tunda jikin ba wani ƙwari gareshi ba fatar ƙuruciya. Ihun Nimrah ya shigo da Mammah da Biebah, sai Mu'azz da har an masa shirin makaranta.
A tsorace Mammah ta ce, “Wai mike faruwa?”.
Da ƙarfi Nimrah dake cikin rigar Zak-Shadow ta ce, “Ƴar daba ce mai wuƙa Mammah ta dawo zata yankamu ni da Dada, ku yankata Mammah kuma ku yayyankata kamar akuya”.
Duk yanda Yaya Ma'aruff da Yays Ja'afar ke dauriya a wannan gaɓar suma sai da suka dara. Sai Mu'azz ne abinka da yarinta ya hau gadon yana kamo hannunta da faɗin, “Ke Nina bafa ƴar daba bace su Aunty ne fa”.
Cikin kuka Nimrah ta ce, “Ƙarya kakeyi Ƴar daba ce, ranar ita ta yankamu ni da Dada, kuma tace saita kasheni bata sona. Muguwa! Muguwa in ALLAH ya yarda sai kin mutu yau kin haɗu da fatalwar kabari da walakiri mai ƙaton sanda”.
Cikin matsanancin ɓacin rai da kishin ganin yanda Nimrah ta shige rigar Dada, shi kuma ya wani zauna kamar gunki yana riƙe da ƙafarta kawai sai zuciya ta tokare ƙirjin Nabeeha. A zafafe ta ce, “Ubanki ne mugu ɗan daba shegiyar yarinya mayya, Momy ga abinda nake gaya miki nan kinƙi yarda kina wani muzo mu ganta...” tai maganar tana kai hannu zata damƙo ƙafar Nimrah dake hannun Dada. Abinda kuwa bata taɓa zato bane ya faru, dan kuwa caraf aka riƙe hannun nata, tana ƙoƙarin fisgewa cikin rufewar idanu Mammah ta ɗauke fuskarta da mari. Lokaci guda ɗakin yay tsitt, dan bama ita data ɗago a birkice taga Mammah ce mai marin ba hatta Zak-Shadow kansa ya girgiza, dan kowa yasan wacece Mammah akan kawaici....
Katse tunaninsu Mammah tayi, cikin faɗa ta ce, “Shin haka kike dama Nabeeha ko yanzu ne wannan halayyar banzar take neman shigarki? Wane shirme ne wannan kike yi akan yarinya ƙarama ƴar cikin ki, wadda da ALLAH ya baku haihuwa kin haifi wadda ma ta fita......”
Hannun Nabeeha Momynta ta kwace daga wajen Mammah, itama a fusace ta ce, “Haba Hajiya A'isha yada haka da girmanki? Bakiga laifin Haysam shi da ya auri ƴar cikinsa ba sai laifinta, kishiya ko jaririyace ai yin kishinta ba haramun bane balle wannan hatsabibiyar yarinyar mai kama da an haifeta a tsakiyar tasha.....”
“K! Ya isheki haka Malama!!”.
Ma'aruff ya faɗa a zafafe tamkar zai kaima Momy duka. Cikin zazzaro idanu dan shima akwai zuciya kamar Dada ya cigaba da faɗin. “K har kina da bakin cema wata ƴar tasha bayan ga ƴar tasha nan kin haifa mai yankar mutane da wuƙa, ai gaskiya Nimrah ta faɗa ƴar daba kika haifa, sannan Wlhy mahaifiyarmu ta fita cikin idanunki idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki, dan akan Mammah da Dada komai zamu iya yi ciki harda koya muku tarbiyya dan naga tayi ƙaranci anan. Ku mi yasa baku san kawaici bane ba, idan badan Mammah ɗin ba wlhy da tun jiya mun yagalgala ku sai buzinku.”.
“Iyeee!!! Ma'aruff ni zakama rashin kunya?”.
“Anyi miki ɗin, in har zaki taɓa mana uwa duka ma zaki iya ci a hannunmu. Anata muku kawaici amma bakwa ganewa, damma kin samu ana gayawa ƴar taki gaskiya da gyara tarbiyyarta tunda ke kin kasa. Nimrah kuma ta zama matar Dada sai dai duk mai mutuwa ya mutu da baƙin ciki babu canji, wani wasan ma sai nan da shekarun girma.....”
Hannun Ma'aruff Mammah ta riƙo dan yi yake kamar zai kwashe Momyn Nabeeha da mari. “Ya isa haka”. Cewar Mammah tana janye Ma'aruff baya. Kafin ta maida dubanta gasu Nabeeha, babu alamar wasa ko sassauci a tare da ita ta nuna musu hanyar fita, “Ga hanya Hajiya Hasiba, idan kuma kuka kaini bango to zan barku da Muhammad, kun san kuma abin bazaiyi ƙyau ba. Dan na fara gajiya da tausarsa akan wannan