KIDA A RUWA BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure

Chapter   48 / 49

141K to 144K   out of 146.5K words

nafi son abu kai tsaye, maida gaba baya a zance nakan kallesa kamar aikin mata ne. Dan ALLAH cikin girmamawa kawai muyi abinda ya dace”.
         Cikin taushi yayi magana, amma ga mai tsatsar zuciya zasu kalli kalamansa a masu zafi. Kamar jami'an gwamnatin dake wajen da wasu a membobin zaman. Sai dai shi Brigadier General yasan Haysam sani na amana da gaskiya, shiyyasa ko kaɗan bai ɗauki kalaman nasa a komai ba face na mazan fama. Sai kawai ya murmusa idanunsa akan Zak-Shadow ɗin.
        Shi ko Lt. Col Peter Okon cikin jin zafin kalaman Zak-Shadow ɗin ya ce, “Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu. An samu wasu video clips daga ayyukanka da suka gabata, musamman wanda ya faru a yankin Bankaura, wannan video clips kuma a cikin kayan Ojo amintacen yaronka aka same su kamar yanda kaji tun farko. Gasu za'a kunna maka ka gani”.
      Ko kallon inda yake Zak-Shadow baiyi ba, bai kuma amsa masa ba. Koda aka kunna tvn ma yaja wasu sakanni kafin ya kai idonsa kansa. Zuciyar sa ta ɗan buga musamman a wajen harbin Umman Nimrah da mahaifinta, amma bai nuna ba. Sai dai har videon ya kai ƙarshe bai ɗauke idonsa akan tvn ba, sai da ma Brig. G. Ya ɗan buga table ɗin sannan.
      Su duka ya kalla cikin idanu ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ya ɗan yi murmurshin da su kuma ya daki zukatansu. Kai tsaye ya ce cikin murya mai ƙarfi, “Sir! Ai ban san a aikin namu harda masu ɗaukar aikin videos ba ma sai yanzu, ba zan tsaya ina kare kaina da magana kawai ba, sannan ban damu da sanin dalilin daya saka a ɗaukemu videos ɗin ba. Sai dai ko bayan na ɓata kamar yanda masu ɗaukar ko ogannin da suka saka a ɗauka ɗin ke buƙata ina so a bincika comm log ɗin mu da footage ɗin asali dan wannan edited video ne. Sannan akan Ojo ban yarda da fallasa abokin aiki ba tare da hujja ba. Mun fi son tabbatar da gaskiya kafin mu kai rahoto.”
Tabbas buɗaɗɗun kalaman Zak-Shadow ba ƙaramin tasiri sukai a zukatan su Brig. G. Ba, dan haka hall ɗin yay shiru na wani lokaci, kafin Col. Haydar ya nisa cikin jimami da nauyin furuci ya ce, “Lt. Col. Haysam ka fahimci cewa wannan kwamiti ba yana tuhumar ka da laifi bane bisa son kai ko wata manufa, amma muna bukatar gaskiya. Wannan al’amari ya wuce duk abinda muke tunani. Musamman daya kasance mun samu tabbacin Ojo na hannunka kai da Major Imran”.
“Sir, na san aikin soja, kuma na san kima ta fi darajar rayuwata......”
“Kana nufin an shirya maka ƙarya kenan Lt. Col?”. Lt Col. Peter Akon yay maganar cikin katse Zak-Shadow yana tsatstsare shi da ƙananun idanunsa. Shima cikin ido ɗin Zak-Shadow ke kallonsa dole sai Lt. Col. Akon ɗin ya fara janye nashi, dan wani abu mai zafi ya gani a cikin idanun Zak ɗin. Amma sai ya wayance da faɗin, “Muna saurarenka Lt. Col. Haysam.”
Wani shegen murmushi Zak-Shadow ya ɗan saki kaɗan, tare da janye idanun nasa ya maida kan Brig. G. Maimakon wanda yay tambayar dan tsabar yarfi. “Sir idan hakan ba shiri bane, to miye ake son ni Haysam na kira shi? Mun san akwai leak tun lokacin da muka gano Ojo yana aiki da wasu a waje. Mun tabbatar yana aika bayanai ga wani bangare a ɓoye. Mun fara bincike a kansa tare da Major Imran a yanda ya dace, gashi kuma abin na neman canja salo mai ban mamaki. Ko akwai kuskure akan abinda muka yi?”.
Bring. G. Ya nisa yana gyara zama, “Tabbas kuna kan dai-dai Lt Col. Haysam, sai dai miya sa baku kai rahoto kai tsaye ba? Sannan office ya kamata Ku ajiye shi ba wani waje ba.”
“Sir hakan ta faru ne because muna so mu tabbatar da gaskiya kafin mu gurfanar da shi, muna son mu kama shi da hujja mai tabbatar da gaskiya, kuma laifina ne ni kaɗai babu Major Imran a ciki”.
Shiru ne ya ratsa ɗakin. Sai Brigadier General ya ɗan jingina kai ya ce cikin sanyi, Lt. Colonel Haysam, gaskiyarka zata bayyana. Amma dole ka san wannan al’amari ya kai matakin da ya wuce mu. Za a tura tattaunawar mu kai tsaye ga Chief of Defence Staff da kuma Office of the Minister of Defence. Muna so ka tsaya kan gaskiyarka, but until further notice, you are under administrative watch”. Ya ɗan yi shiru, sannan cikin murya mai nauyi ya ƙara da cewa, “Har zuwa lokacin da za mu kammala bincike, an dakatar da kai daga duk wani aiki na soja. Za ka zauna nan Abuja, kuma ba za ka iya fita daga FCT ba tare da izini daga ofishin Defence ba.”
Ko kaɗan babu wani alamar damuwa a fuskar Zak-Shadow ya miƙe, ya yi salute cike da girmamawa, tare da faɗin, Yes, sir. I have nothing to hide. Na amsa. Na sadaukar da raina ga wannan ƙasa, ba zan fara gujewa gaskiya yanzu ba saboda hana maƙiya nasara, zan basu ƙafa fiye da yanda suke tunanin samu, amma a sanar da su koda ace zan ɓuya, wata rana gaskiya zata dawo dani ko ta kawo wani wanda ya fini”. Daga haka ya juya abinsa ya fita.
Yana fitowa idonsa ya sauka kan Major Imran dake tsaye jikin motarsa alamar shi yake jira. Idanu suka zubama juna na wasu sakanni, kafin Zak-Shadow ɗin ya cigaba da takowa a hankali har inda Imran yake. Murmushi Imran yayi shi kuma Zak-Shadow ɗin ya hararesa.
Sake murmusawa yay, cike da rashin damuwa ya furta, “Gaskiya zata fito, amma sai lokaci ya kai da yarjewar UBANGIJI”.....

((★))

A ɓangaren su Brig. G. Ƙofar na gama rufewa bayan fitar Zak-Shadow ɗaya daga cikin mambobin kwamitin Col. Haydar ya juyo yana kallon Chairman ɗin Kwamiti Brig. G.
“Sir, idan har ya kasance gaskiya ne wannan makirci ne to mun shiga cikin irin abin da ba a taɓa ganin irinsa ba. Kuma hakan na nuna akwai wani bigger hand a cikin wannan abun, kuma gaskiyarka ba Lt. Col. Haysam kawai aka hara ba gidan soja ne gaba ɗaya”.
Kasa ma bama Col. Haydar amsa Brig G yayi, dan shi kansa ya ɗauki zafi musamman da kalaman Haysam na ƙarshe a yanzu. Miƙewa yay cikin bada umarni yace a ɗakko masa Ojo daga inda Major Imran yace sun ɓoyeshi, daga haka ya fice, dole kowama ya miƙe har jami'an gwamnatin dake tare da su.........✍🏼


_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 69_

__________________

https://chat.whatsapp.com/DMVSa4G3a9sDd8Jjgm0mzs?mode=ems_copy_t

Kin Dade kina Neman group din dazaki tallata kayanki kyauta Baki samuba to ki hanzarta shiga free advert group na EASHAS BITES AND BEAUTY domin tallata Kayanki kuyi saving number dinta domin samun shiga group dinnan akwai members Sama da 500+ aciki💃💃💃💃👇👇👇👇

wa.me/ 2348064705686

__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Motar shiru Zak-Shadow na murza siyarin a hankali tamkar baya so, a gefensa Imran ne zaune cikin alamu na tunani mai zurfi. A gabansu motar sojoji ce haka ma bayansu. Sai dai sukai tafiyar fin mintuna goma tsakaninsu da inda suka baro a karo na farko Zak-Shadow yay magana idanunsa akan titi.
      “Ina son su Ma'aruff su dawo kusa da Mammah”.
     Kallonsa Imran yayi na sakanni, kafin cikin damuwa ya ce, “Saboda mi?”.
         “Saboda bazai yiwu mu duka muyi nesa da ita ba.”
     “Wace irin magana ce wannan? Kai ina zaka da har zakai mata nisa?”.
   Murmushi mai yalwa Zak-Shadow yayi yana sake juya sitiyarin cike da ƙwarewa, sai kuma ya ɗan kalla Imran fisha ya maida idanunsa kan titin. Kamar bazai ce komai ba dan har Imran ya fidda rai da samun amsa, kafin ya ɗan furzar da iska. Cikin komawa serious ya ce, “Imran nasan ka san abinda nake hange, kuma bana jin akwai abinda zai hanashi faruwa sai wani ikon ALLAH. Mutanen nan sun gama shirya komai kafin su tunkaremu, kuma zaka tabbatar da hakan yanzu babu jimawa. Dan haka ina son a tsaida aikin gidansu ai musu gini anan cikin gidan tunda akwai fili ta baya. Idan zai yiwu kuma a canja tsarin gidan gaba ɗaya ma har Bilal da Ammar su samu nasu kowa ya zauna a ciki. Ka fara zama da su Ja'afar ɗin kasan abinda muke da shi a ƙasa, dan naso yin hakan dama sai dai nasan lokaci ya ƙure......”
     Cikin ɓacin rai Imran ya katseshi da faɗin, “Wai miye kake faɗa haka. Na gaya maka ka daina min irin wannan wasan.”
       “Humm! Imran ba wasa nake ba”.
   “To ka sani kuwa duk inda kake muna tare”.
“Bazai yiwu ba. Dan ina son a lokaci dana ɓuya kai ka cigaba da aiki. Na ajiye maka saƙo a ɗaki na..”
     Dai-dai nan suke isowa ƙofar gidan Imran inda aka ajiye Ojo. Tuni sojojin da suke tare duk sun dirga daga motocin da suke, dan haka Zak-Shadow bai kula kallon da Imran ke masa ba ya buɗe motar shima ya fita. Sai da ya ga Imran bashi da niyyar fitowa sannan ya leƙasa da faɗin, “Malam fito ka bada key mana”.
     Shiru Imran ya kasa motsawa, dole Zak-Shadow ya zagaya ta inda yaken ya buɗe masa da kansa. Tamkar wanda juwa ke neman zubarwa haka Imran ya fito, yasan wanene Haysam, sani irin na ciki dabai ɗin nan. Tunda har ya ambata batun zai ɓuya akwai abinda ya gama shiryawa, wanda shi Imran yake gudu da son yaƙa. Ganin duk sojojin sunyi tsaye alamar shi suke jira da ƙyar ya iya ciro waya a aljihunsa ya shiga ƙoƙarin kiran mai kula da gidan, sai dai har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba. Ya sake na biyu ma haka, zai sake na uku Zak-Shadow yay ɗan murmurshi. Sai kawai ya dubi sojojin yace su ɓalle ƙofar.
      Hakan kuwa akai, sun tafi da nufin ɓalle ƙofa suka sameta a buɗe. Tun a anan aka tsaya kallon kallo, sai dai basu ce komai ba suka tura gate ɗin suka shiga. A tsakar gida suka tadda mai kula da gidan a yashe, ga wayarsa da Imran ke faman kira a gefe. Tattaɓashi ɗaya daga cikin sojojin yayi, cikin sauri ya ɗago ya ce, “Baya numfashi”.
         Cikin tashin hankali Imran ya iso wajen, shima ya tattaɓashi amma da gaske baya numfashi. Suna ɗagoshi sukaga alamar an dakeshi ne ta ƙeya da wani abun. A take shugaban tawagar ya basu umarnin shiga gidan, shiko Imran sai jijjiga yaron yake yana ambaton sunansa amma babu alamar rai tare da shi. Zak-Shadow na gefe tsaye kawai ya zubama Imran ido...

     Cikin abinda bai fi mintuna goma ba su Zak-Shadow suka fahimci babu Ojo a gidan an fita da shi. Dan a cikin gidan a ɗakin da Imran ya tabbatar ya ajiye Ojo duk ya aɓaci da jini har ta kan stairscase da falon. Dama gidan babu komai a cikinsa. Amma duk da haka sai da sojoji suka bincike ko wane lungu da saƙo nashi. Iyakar tashin hankali Imran ya shiga, amma abin mamaki Zak-Shadow ya dake a zahiri, koda akwai wata damuwa a tare da shi ya barma ransa.
     Tuni sojojin dake tare da su har sun isar da saƙo zuwa Headquarter. Ba'ai wani dogon lokaci ba aka zagaye anguwar da sojoji. Maƙwaftan dake jikin gidan duk an sakasu sun fito duk da ma sabuwar anguwa ce. Su akai taima tambayoyi suna bada amsar komai dalla-dalla. Sun tabbatar da wasu mutane ne suka zo gidan, hakan na nufin sune suka ɗauke Ojo kusan awani uku da suka shuɗe kenan, dan wasu sunga motar data shigo anguwar har cikin gidan, sannan duk sunji sanda mai kula da gidan keta ihun neman ɗauki amma tsoro ya hana su fita kasancewar su mata, ga shi kuma sunyi harbin bindiga har sau biyu.
       Cikin sa'a wani saurayin yaro ya bada siffar motar kaf da lambar jikinta, daga haka suka baro gidan shi kuma yaron Zak-Shadow da Imran ɗin suka wuce da shi asibiti. Sai dai me, suna isa asibitin sai ga sojoji an saka sun biyo bayansu wai kulawar yaron zata koma ƙarƙashin ikonsu. Tun daga nan Zak-Shadow ya fahimci anzo dai-dai wajen.....

<<%>><<%>><<%>>

          Ɓatan Ojo ya sake hargitsa komai ta kowane ɓangare, dan hatta a cikin su jami'an sojin dake jin Zak-Shadow bazai iya aikata abinda ake zarginsa a kai ba zukatansu sun fara rawa da wasi-wasi. Sai dai a gefen zukatan nasu basa fata hakan ta kasance.
       Sai dai mizai faru kuma, ana kukan targaɗe kan batun Ojo sai kuma ga na karaya ya faru, dan kuwa misalin ƙarfe biyar na yammar wani mummunan labarin ya sake isowa hukumar sojoji. Wai an harbi jirgi mai saukar angulu na sojoji dake ɗauke da su Dagger a hanyar kawosu nan Abuja. Sabon zance kenan. Cikin gaggawa aka aika jami'ai inda abin ya faru. Kuma a cikin wani ƙauye abin ya faru, har an samu mutuwar fararen hula shida wasu sun jikata. Hakama sojojin dake tare da jirgin mutum biyu a cikinsu sun rasu, sauran sun raunana. Su Dagger su goma sha uku ne, an samu gawar biyar a cikinsu, sauran takwas ba'aga ko mutum ɗaya ba, hakan na nufin an ɗaukesu kenan.
     Duk da zancen bai gama bayyana ko a Headquarter ɗin ba, a yanayin nan duk wani masoyin Zak-Shadow dole ya kasance cikin jimami da fargabar abinda zai iya biyo baya, domin kuwa case ɗin su Dagger shine tushen case ɗin Ojo da ayanzu kai tsaye ake tuhumar Zak-Shadow akai.

    _____________★

        A Defence Headquarters kuwa, batun ɓacewar Ojo da batun su Dagger ya kai ga har gidan gwamnati. Abin mamaki, cikin ƙanƙanin lokaci aka kira taron gaggawa. (Emergency Security Council Meeting). Ba a ɓata lokaci ba, tuni manyan jami’an tsaro suka hallara cikin ɗakin taron, kowanne da fuska mai ɗauke da damuwa da jimamami, dan rashin su Dagger da Ojo kai tsaye na nuna tabbacin zargin da akema Zak-Shadow ne, duk masu bashi kariya basu da wani sauran abin faɗa. Bayan ƴan mintuna kaɗan da tattaunawa, an fito da hukunci mai nauyi. COAS ya samu umarni daga sama kai tsaye na kama Zak-Shadow. An kuma tabbatar masa a daren yau dan ba'a buƙatar wata hayaniya.
    Wannan shine saƙon umarni da COAS ya samu a dai-dai wannan lokaci da agogo ke neman buga ƙarfe shida na yammaci a ofishin ministan tsaro bayan fitowarsu daga meeting room.
     Shiru General Yusuf yana kallon ministan tsaro dake bada umarnin bai iya cewa komai ba na ƴan dakiku. Ya kasa ma kallon sauran takardar da ke gabansa. Sai da Ministan ya sake maimaita umarnin da baki cikin ɓacin rai, yana jaddada cewa umarnin daga shugaban ƙasa ne, sannan Janar ya furta,
    “Yes, sir”.
   Ya faɗa yana sauke numfashi mai nauyi tare da miƙewa ya fito. Da sauri aka buɗe masa mota ya shiga, tunda suka baro ofishin minista ya faɗa duniyar tunani. A zuciyarsa kalmomin Minista ne kawai ke maimaituwa a kwalwarsa kamar amsawa kuwwa ne a cikin kunensa. Haysam Abdul-rasheed... to be apprehended.
Hankalinsa a tashe yake matuƙa, zuciyarsa na masa zafi. Duk da cewa aikin soja ya koya masa ya bi umarni ba tare da tambaya ba, wannan karon zuciyarsa ta ƙi yarda. Amma ba shi da zaɓi.
      Suna isowa office shima yay kiran Director of Military Intelligence dake ƙoƙarin barin office. Amma dole shima ya yanke nasa hanzarin ya amsa kira. Tunda ya shigo office ɗin ya fahimci akwai matsala sosai, dan fuskar COAS ta nuna kai tsaye. Yayi gaisuwa cikin girmamawa. Amma COAS bai iya ya amsa da baki ba hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan sakanni biyu ya fara magana muryarsa cike da raɗaɗi, “Issue the arrest directive Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu quietly. No noise.”
        Shima ba ƙaramin faɗuwa gabanshi yayi ba, ya ɗan zaro idanu waje zuciyarsa na girgiza. Sai dai kafin ma yace komai COAS ya miƙe abinsa alamar baya buƙatar wani zance. Rai a dagule ya fice daga ofis ɗin ba tare da ya tsaya da kowa ba ya bar Headquarters ɗin gaba ɗaya zuwa gidansa, kamar wanda yake guje wa wani abu da zuciyarsa ta kasa jurewa.

       Bayan mintuna talatin, takardar Arrest Directive ta fita da cikakken sa hannun doka. An tura ƙungiyar jami’ai shida daga Military police da zasu kama Zak-Shadow bisa umarni, tare da amsar dukan abinda ya shafi matsayinsa.

        (((*)))(((*)))

     A ɓangaren Zak-Shadow da Imran sam basu sam mike faruwa ba, dan yanzu ma suke isowa gida daga asibiti bayan jam'an sojan nan sun tabbatar musu da komawar kulawar yaron a ƙarƙashinsu bisa umarni daga Headquarter kai tsaye gida suka nufa.. Sun yi ƙoƙarin kauda hankalinsu daga tashin hankali, kowa da tunanin da yake ƙoƙarin ɓoyewa, duk da shi Imran yaso su cigaba da tattauna maganar da suka fara ɗazun da Zak-Shadow ɗin, amma shi kuma yanata kaucewa sai kawai

48 / 49