Author : Billyn Abdul Category : Adventure
nishaɗi, yayinda wasu suka fara kiɗa da ƙarfen gado wasu cokula da plate da aka raba musu.
Dariya suka bama Sojojin da ke kula da su, dan haka suka tsaya suna kallon suna murmushi kawai. Dan basu da zaɓin daya wuce su bar su suyi farin cikin farko kafin a fara horo na gaskiya, a wannan gaɓar idan ma ance suyi wannan nanayen bazasu yin ba. Duk wannan abin da ake Haysam na zaune ne kawai a gefe bakin wani gado yana kallonsu, bai yi waka ba balle rawa, amma murmushin da ke gefen fuskarsa ya tabbatar da shima yana jin irin farin cikin da suke ji. Kai da ka kalla idanunsa kasan akwai tsananin buri amma a zuciyarsa akwai tambayoyi da yawa. Sai faman ayyanawa yake a zuciyarsa (Zan iya jure wannan sabuwar rayuwar kuwa? Yanzu ko mi Mammah take yi da su Ja'afar. Ƙilama Ammar da Mimi sunyi kukan rashin ganin yau bani zan kaisu makarantar allo ba, bani zan musu wankan dare ba, bazamu ci abinci tare ba. Ƙilama suna can sunama Mammah rigimar kuka). Haka dai ya zurfafa a tunani shaƙiyancin ƴan uwansa ɗalibai na yin nesa da kunensa.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 27_
__________________
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara
Saloon
Kunshi na salatap Dana zane
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari
Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
........A wannan dare na farko Haysam bai iya bacci ba saboda tunanin gida. Ga hayaniyar sabbin abokai, ko gajiya basayi sukam duk sun cika hall ɗin da ɗumi, kaida ka gansu kasan ƙuruciya da farin cikin samun cikar buri ya baibaiye rayuwarsu gaba ɗaya. A hankali Haysam dake kallonsu kawai ya lumshe idanunsa, zuciyarsa na ayyana masa, “Rayuwa ta ta fara daga yau. Farin ciki a Bauchi tare da Abiy, Umma da Mammah, rayuwar ƙunci da kukan rasa Abiy da Umma. Fuskantar ainahin rayuwa da fara gwagwarmaya a Kano tare da Mammah da Inna, kukan rasa Inna, samun cikar burin ɗakko hanyar zama soja a yau. Ko mi gobe zata zo da shi idan da rayuwa? Wane sakamako zamu kalla a jibinmu ta duniya da lahira. Ya ALLAH kasa inyi nasara, nasara mai albarka ta duniya da lahira”.
Ganin dai barci yaƙi zuwa masa sai kawai ya tashi ya fita tare da ɗaukar sallaya a cikin jakarsa. Alwala yayo ya dawo barandar hall ɗin ya shimfiɗa abin sallar ya kabbara salla. Wannan horo ne da Abiy yay masa tun bai kai haka ba, bayan rasuwarsa kuma Mammah ta ɗora daga inda ya tsaya, shiyyasa sallar dare ta zamar masa jiki sosai, idan ma baiyi ba har jinsa yake kamar mara lafiya. Sai gab da asuba yaji barci na ɗibarsa, sannan ya tattara ya koma ciki, zuwa yanzu hall ɗin ya koma shiru, duk sunyi barci, sai tashin minshari kawai kake ji. A gadon da ya ajiye jakarsa yaje ya kwanta, baima kammala addu'a ba barci yay awon gaba da shi....
_________★
Asubar fari wani ƙarar whistle mai kaifi ya karaɗe kunnuwansu. A firgice suka shiga tashi, kafin su gama nutsuwa aka shiga faɗin, “Get up! Move it, move it, move it!”
A hankali Haysam ya shiga buɗe idanunsa ba kamar yanda sauran ke kwaramniyar tashi ba, a nutsensa ya tashi zaune yana mai karanta addu'ar tashi a barci. Wannan safiya ce ta farko bayan shigar su NDA, daga kuma yanzu sun sake tabbatar da kowane motsin rayuwarsu zai koma ne akan tsari.
Sauran ƴan uwansa ya fara bi da kallo, yanda wasu ke tashi da sauri, wasu suna neman takalminsu, wasu kuma suna a yanayin na tsoro sai abin ya bashi dariya, murmushi ya ɗanyi yana kauda kansa, dai-dai nan yaji muryar na kusa da gadonsa yana faɗin, “Dan ALLAH ko kaga takalmi na?”.
Karon farko ya kalli gefen damar tasa inda yaron yake, ba shi da girman jiki sosai, dan a cikar jiki da tsayi ya fishi, yana neman takalmin ne da hawaye cike da idonsa. Hakan ya bayyana rauninsa sosai. Tausayi ya bama Haysam, dan sai yaga kamar Ma'aruff ko Ja'afar ne a gabansa, duƙawa yay yana ƙoƙarin tayashi nema, sai ko gashi ya ɗauko masa takalmin a ƙarƙashin bunk ɗinsa daya shige, miƙa masa yayi.
“Ka kwantar da hankalinka gashi nan, saka muje kafin su dawo su same mu anan kaga kowa yana ƙoƙarin fita”
Karɓa yaron yayi yana murmurshi, sai kuma cikin ƴar rawar muryar tsoratar da har yay bata barshi ba ya ce, “Na gode ɗan uwa, sunana Imran... Imran Abbas, kai fa miye sunanka?”.
Haysam dake miƙewa ya ɗan murmusa cikin kasaita, yana miƙa masa hannu dan ya taimaka masa ya tashi. Fahimtar hakan yasa Imran miƙa masa nashi hannun shima ya miƙe. Sai da suka je kusa da hanyar fita a hall ɗin gaba ɗaya sannan ya bashi amsa da, “Haysam Abdul-rasheed Shehu”.
Imran ya kalle shi fuska cike da murmushi ya ce, “Woow sunanka mai daɗi”.
“Kaima naka yana da daɗi ai”.
Cewar Haysam yana masa ƙaramin murmushi, dan haka kawai yaji son Imran ɗin ya shige masa rai.
Imran ya ce, “Naka yafi nawa daɗi, dan kamar sunan larabawa”.
Kafin Haysam ya ce komai ƙarar whistle ta sake cika kunnuwansu da karfi.
“OUTSIDE NOW! FORM UP!”.
Aka faɗa cikin bada umarni ga na ciki da suka rage. Ai da gudu suka shiga rige-rigen fita, gadajen su na girgiza, ƙasan hall ɗin na ƙarar takalman boots ɗin ƙafafunsu. Koda Haysam ya duba gefensa tuni Imran yabi ayarin masu fita da gudu, sai ya girgiza kansa kawai shima ya fice. A ransa kuwa yana raya, “Yanzu wannan matsoracin a haka zai zama sojan?”. Bashi da mai bashi amsa, dan haka ya shiga cikin sauran ƴan uwansa.
Fili ne fetal, ga ɗan karan sanyin asuba dake ratsasu na cikin watan sha biyu, sai da sojojin dake zagaye da su suka gama ƙare musu kallo sannan aka bada umarni ga masu yin salla suje suyi. Dama abinda ke tsunkulin zuciyar Haysam kenan. Ai shine gaba-gaba a masu barin wajen, suna idar da sallar asuba cikin jam'i aka sake kaɗosu cikin sauran ƴan uwansu. Babu wani ɓata lokaci aka shiga koyar da su discipline, bin layi cikin tsari, da bin umarni. Suna tsaye a wannan fili har rana ta fara haskakawa, iska mai sanyi ta safiya na cigaba da busa su tako ina, masu rawar sanyi tun sunayi har sun dake. Wani instructor ya ɗauki megaphone ya fara magana cikin rashin wasa.
“This is NDA, not your father’s house! You eat when I say you eat! You sleep when I say you sleep!”
Da yawansu hanjin cikinsu sai kaɗawa suke, sai ƙalilan masu taurin zuciya irinsu Haysam. Imran kuwa yana gefensa yana ƙoƙarin tsayawa dai-dai amma jikinsa yana karkarwa. Haysam ya kalle shi ta gefen ido kaɗan, sai yaji tausayinsa ya kama shi, dan haka ya matsa kusa da shi a hankali, kafadarsa ya ɗan taɓa da tashi kafaɗar dan ya samu daidaiton tsayawa a layi kamar kowa. Kallonsa Imran ɗin yayi shima, dan baisan ma shine a kusa da shi ba. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, tare da yimasa kallon godiya cikin yanayin lumshe ido. Sai kuma ya shiga haɗiye hawayen da suka cika masa idon.
Murmushi kaɗan Haysam yay masa ya ɗauke kansa ya maida ga mai musu jawabi, sai dai a zuciyarsa yana ayyana “Tabbas na yarda da maganar Abiy dake cewa (Ba kowa ne ake haifa da ƙarfi ba… amma akwai wasu da zuciyarsu ta fi ƙarfinsu. Karaya ba ita ce rashin jarumta ba, amma tana bayyana rauni ga namiji. A komai ka tsaida zuciyarka, ka yarda UBANGIJI shike sarrafa al'amura sai ka samu jarumta irin ta MAZAJEN FAMA da suka gabata). Ɓoyayyar ajiyar zuciya yayi yana mai jinjina kai da ayyana “Hakane Abiy, maganarka nakan gaskiya. Dan haka daga yau na ɗauki alkawari zan kula da Imran har sai wannan runduna ta san cewa ƙarfi ba daga tsokar jiki kawai yake ba, ƙarfi na asali da gaskiya daga zuciya yake.”
Tsawar da aka sake daka musu ta dawo da Haysam a zahirinsa ya saki batun tunani ya sake nutsuwa kamar saura yana sauraren abinda ake faɗa kamar kowa.
“When I say go, you move! When I say stop, you freeze! You understand me?!”
“Yes, Sir!!!”.
Suka amsa da ƙarfi, a tare.
“Good! Today, we start your Morning PT, that’s your first test! You will run two kilometers around this field!”
Shiru kake ji gurin ya sake nutsuwa, sai zukatansu dake bugawa da sauri-sauri a ƙirazansu.
“Go! Move it! Move it! Faster!”
A tare suka motsa kowa ya ara cikin ta kare, jikake tiff!! Tiff! Tifff!! ƙafafunsu suna ta dukan ƙasa, ƙarar takalma na bada sauti kamar saukar ruwan sama. Imran yana gefen Haysam, yana ƙoƙarin yin sauri kamar kowa amma numfashinsa yana sarkewa. Kamar mai shirin faɗuwa, sai faman danne ƙirjinsa yake, yana shakar iska da ƙyar.
“Haysam ba zan iya ba...”
Ya faɗa cikin shashsheka
“Imran! Kada ka tsaya, ka karfafa kanka, Abiy na yana cemin (Namiji baya zama rago garkuwa ne), dan haka kada ka tsaya kaji!” Haysam ya faɗa yana riƙe masa hannu. Sai ko Instructor ɗaya ya hango su daga nesa, cikin ihu da tsawa ya ce, “Keep moving, you two! No one stops! You stop, you fail!”.
Sakin hannun Imran Haysam yayi ya matsa yana ɗan tura shi gaba, cikin son kwantar masa da hankali ya ce, “Ka tsaya ta gabana. Idan ka faɗi, nima zan tsaya. Amma ba za mu faɗi ba in sha ALLAHU”.
Idon Imran cike da hawaye, cikin son ƙarfafa kansa kamar yanda Haysam ya faɗa ya jinjina masa kai. A haka suka ci gaba da gudu, duk da cewa jikinsu ya fara gajiya, zufa kam ta jiƙe goshinsu dama illahirin jikinsu tamkar ba safiya ba. Lokacin da suka iso ƙarshen filin, sauran ɗalibai suna ta rige-rigen samun abin dafawa, wasu suna tsaya suna tari, wasu suna hawaye. Haysam ya riƙe hannun Imran har suka ketare layin ƙarshen gudun sannan ya jinginashi da jikinsa suna sauke numfashi a tare.
Instructor ɗin da yake biye da su ya tsaya yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ba tare da yayi magana ba, sai kawai ya murmusa yana mai girgiza kansa.
“Discipline. Determination. Teamwork.”
Ya furta kalmomin cikin karsashi kamar yana jin daɗin yanayin daya gansun.
Zubewa Imran yay ƙasa yana shakar iska da ƙarfi, jikinsa na dan rawa ga zufa tai masa sharaf. Durƙusawa Haysam yay kusa da shi shima, yana share masa gumi da hula. “Na faɗa maka, idan ka tsaya, nima zan tsaya. Kuma ba zan bari ka faɗi ba, kada ka sare Imran, domin ba'a fara komai ba, dan yanda Abiy na ya gaya min wanene soja a labari wannan matsayin sharar fage muka fara”
Imran ya ɗaga ido cikin hawaye, amma wannan karon hawaye ne na tsoro, da rauni mai tafiya da godiya da jin ƙarfin gwiwa daga sabon aboki a sabuwar duniya. “Na gode Haysam, kai ne jarumi na farko da ya tsaya saboda ni, tabbas kai ZAKI na ne, kuma inuwa ta ne. My Zak-Shadow”.
Kai Haysam ya girgiza ya ɗan yi murmushi mai sanyi, yana duban rana wacce ke fara fito da haske ɗumi. Sai kuma ya kalla Imran ɗin daya miƙe tsaye akan ƙafafunsa, shima miƙewar yay yana kallonsa. “Imran kaima Zaki ne ai, domin anan babu wanda yake shi kaɗai. Saboda Soja ba ya tafiya shi ɗaya sai da runduna.”
“Ni ai kaine tawa rundunar kuma inuwa ta Zak-Shadow”.
Kai kawai Haysam ya sake girgizawa, hakan yayi dai dai da busawar iska mai daɗi dake tafe da ƙarar murya daga nesa, “Fall in! Line up, cadets! Next exercise, push up!”
Imran ya kalli Haysam cikin murmushi, shima Haysam ya murmusa, zuciyarsa na ayyana masa abu ɗaya cike da tabbaci. Rayuwarsa ta soji ta fara a yau, amma abota ta gaskiya ta riga ta samun tushe da mafari a zukata guda biyu.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 28_
__________________
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara
Saloon
Kunshi na salatap Dana zane
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari
Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Rana ta biyu ta kasance da sabon sauyi ga su Haysam duk da dai zamu kira sauyin bamai yawa da tsanani ba ne. Domin kuwa daga gudu, sai tsalle-tsalle, da kiran Yes, Sir! da karfin murya, kowanne cadet ya fara jin cewa jikinsa na canzawa, kamar yanda rayuwa take canjawa daga barin ƙuruciya zuwa sabon ƙalubale mai banbanta kai da sauran jama'ar gari. Ba su da lokacin tunani na zahiri, amma kowannensu ya fara fahimtar cewa a cikin NDA duk suna amsa sunan masu daraja ɗaya ne da fuskantar ƙalulabe ɗaya a ƙarƙashin ɗoki, zumuɗi da burin zama soja...
>>>>>>>>•<<<<<<<<
Yau kwanakin mako cif da shigowar su Haysam NDA, a satin gaba ɗaya rayuwa mai sauƙi ce da cigaba da morar ƙuruciya da ƙarasa zazzage sauran wautar data rage a gaɓɓan jiki irin ta masu shekarunsu. Domin kuwa satin gaba ɗaya babu wani abin kuzo mu gani dake nuna musu ma an fara wasan, shiyasa wasu a cikinsu suka fara shagala da maida hankali a nishaɗi da ƙulla abota kawai a tsakani.
Saɓanin Haysam yaro mara kwaramniya da yawan magana. Ba ruwansa da kowa sai Imran, komai nasa a nutse, akoda yaushe yana gefe nesa da hayaniya da nishaɗin sauran. Sai dai a duk inda yake Imran sabon aboki sabon ɗan uwa na manne da shi. Da yake shima Imran ɗin baida hayaniya sosai sai abotar tasu tai dai-dai. Sai dai shi yanada surutu, dan a kwanakin kaf har ya kammala bama Haysam labarin ƴan gidansu A to Z. Yayin da shi kuma Haysam bai iya gaya masa komai ba bayan sunansa da garinsu Bauchi da Kano da suke a yanzun.
Kamar yanzu ma suna can daga bayan hall ɗin kwanan nasu ne suna hira ko nace Imran na zuba masa surutu kiran da akema su sabbin ɗalibai ya riskesu. A tare suka miƙe suka zagayo ta gaba, batare da neman ba'asi ba suka bi ayarin saura