Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   7 / 46

18K to 21K   out of 135.1K words

ya buWe kwayar idanunshi sabida,
Jin alamun an rufe marfin jirgin kana jirgin ya fara ?ugin tashi.

Shi kuwa Rayyern har yanzu idonshi na kan kyawawan sawun Riyyam-nsra.
A hankali Riyyam-nsra Win ya juyo ya kalli gefen da Rayyern Win yake.
Da sauri ya Wan sunkuyo da kanshi ganin inda Rayyern ya fuskanta.
Janye sawunshi yayi tare da cewa.
"Salamu alaikum".
Da sauri Rayyern ya juyo sabida muryar yaron sak muryar ?aninsa Ramadan.

Yana juyowa shima Riyyam-nsra yana juyowa ya fuskanceshi.
Wani irin zabura Riyyam-nsra yayi tare da zazzaro idanunshi waje, kana ya yun?uro zai tashi.
Da sauri ma'aikaciyar jirgin dake bayanshi ta nufoshi da sauri tana cewa.
"Hey Are you okay? please sit down!!
Ta ?are mgnar da Wan sauti sabida lokacin jirgin, yake raba tayoyin shi na gaba da ?asa, anfi bu?atar kowa a zaune.

Shi kuwa Riyyam-nsra wani irin masifeffen kaWuwa al'ajabi mmki da tu'jjudine suka rufeshi, gaba Waya jikinshi rawayake.
Cikin buWe baki ya nuna Rayyern da yatsarshi manuniya kana ya nuna kanshi.
Da sauri ma'aikaciyar ta sake cewa.
"Please I say sit down!."
Jin hakanne da kuma ganin yanda yake baya baya.
Yasa ya koma bisa kujerar ya zauna.

Cikin kaWuwa da wani irin fuska mai cike da mmki yace.
"Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, daya haliccemu da kamanni iri Waya."
Shiru Rayyern yayi yana mai kallonshi da gefen ido.
Bai iya shiga sabgar da ba ta saba, a rayuwarsa baya taSa sa kansa a lamarin da bai shafeshi ba.
Da sauri ya juyo jin Riyyam-nsra na cewa.
"Ina ma Mammy na ta ganka.
Allah mai iko.
Inama ace jirgin nan bai tashi ba, da na ro?eka da girman Allah da Manzonsa muje Mammy na taga mai tsananin kama dani."
Sai kuma ya kalli sajen Rayyern cikin tsananin farin ciki, so, ?auna, bege, yace.
"In sha Allah nima daga yau zan fara tara saje irin naka".
Sai kuma ya matso kusa da Rayyern tare da dago wayarshi.
A hankali Rayyern ya Wan juyo kwayar idanunshi kan fuskarshi ganin alamun zai manna kanshi bisa kafaWarsa.
Fuskarshi ya tsuke tare da tsareshi da ido.

Da sauri ya kwaSe fuska tare da karkata kai cikin turo baki yace.
"Na tuba".
Sai ya ganshi lammanim ?aninsa Ramadan sak da yayi haka, dan haka Ramadan kanyi mishi duk sanda ya tsareshi da ido.
Ido ya Wan zubawa lips Win shi yana cewa.
"Please kayi ha?uri hoto zamuyi zan nunawa Mammyna ne, zata so ganinka".
Ya juyo da nufin zaice a a.
Kawai sai yaji Riyyam-nsra ya ron?ofo kanshi da kyau.
Ya manna kansa bisa kafadarsa.
Yana murmushi yayi musu selfie.
Sai ya zama suna kallon juna.
KafaWarshi ya Wan manna da nashi dan jin bugun zuciyarsu ya dai-dai-ta yana harbawa a tare a tare, dib-dib.

Sai kuma ya zuba mishi ido ganin ya taso ya zauna ya juyo ya fuskanceshi da kyau.
Hannunshi ya mi?a mishi tare da sallama.
Dole ya bashi hannu ya kuma amsa sallama tunda horaswar Musulunci ne.

 Sunana Zakariyya amman Riyyam-nsra nakeso a kirani, ni Wan ?asar Ethiopia nanne, ban taSa zuwa Nigeria'n ba sai yau.
Dalilin abokina Nasiru Ahmad zanje.
Kai kuma fa?".

Fuska ya kuma kwaSewa ganin ya janye hannunsa bai kuma ce mishi komai ba.
Cikin yanayin shagwaSa yace.
"Please dan Allah gaya min".
A nitse ya juyo ya kalli yaron da yakeji.
Sonshi da ?aunarshi na ratsa mishi jinin jiki da zuciya, haka nan yaji wani aminci na musamman a kan yaron.
Cikin tattausan muryar da irinta yakewa Ramadan mgn yace.

 Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara".
Ruggumeshi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.
"Nice name. Please Zan iya ce maka Yaya?
Kai ya jujjuya mishi alamun a a.
Da sauri yayi rau-rau da idanunshi tare da cewa.
"Dan Allah fa, to me zan ce maka".
A ta?aice yace.
"Hamma Rayyern".
Wani irin murmushin jin daWi yayi tare da cewa.
"Hamma Rayyern".
Sai kuma ya gyara ri?on da yayiwa wayarsa da tun tuni yake musu video.
Kusan a tare suka sau?e ajiyan zuciya lokaci da jirgin ya gama Wagawa, yayi sama ya rabu da ?asar Ethiopia.
A hankali ya Wan juyar da kanshi kana yaci gaba da aikin da yakeyi.

Da sauri ya kuma kalli Riyyam-nsra da ma'aikaciyar jirgin nan tazo tana ce mishi lfy kuwa, Wazu yake ta rawan jiki ta ?are mgnar cikin yanayin saninsa da son suyi hoto tare.
Murmushi yayi tare da nuna mata Rayyern kana yayi ?asa da murya yace.
"Yayana ne zai zaneni wai na cika surutu".
Murmushi tayi tare da kallon fuskar Rayyern kana tace.
"Ka cika rawar kai, ba kamar yayanka ba."
Sai kuma ta Wan kalli Rayyern tare da cewa.
"Sir a rin?a yi mishi faWa yaron nan baya jin mgn a TIKTOK".
Kai ya gyaWa mata ba tare da ya kalleta ba.

Hoto sukayi da Riyyam-nsra kana tayi gaba.

Usman PA kuwa yana can baya.

A hankali jirginsu yayi ta keta gajumare, yana ratsa sararin samaniya.
Tafiya ta nisa kowa sabgogin gabansa yakeyi.
Amman banda Riyyam-nsra gaba Waya ya shigewa Rayyern shigewa mai tarin yawa.
Ya kuma kasa yakice yaron.
Duk yadda yayi sai yake jin zuciyarsa mai raunice a kan yaron.
Wani irin son yaron yakeji har cikin ?ahon zuciyarshi.
Ga mamakinsa ko yanayin cimar da suka fiso iri Waya ne.
Domin tunda Riyyam-nsra ya shigo bakinsa bai zauna banza ba, sweet da chocolate ya cisu iri daban-daban.
Ya lura yaron bakinsa bai zama shiru.

Hoto kuwa yayi musu sunfi hamsin video kuwa sun kai goma.

Haka sukaci gaba da keta hazo...

A nan gida Nigeria kuwa gidan Alhaji Idi Saleh Dakata.

A hankali Jannart ta fara motsi, alamun farkawa daga baccin da allurar ya sa tayi na tsawon.
Awanni biyu da rabi.
A hankali ta fara motsa fatar idanunta da sukayi mata nauyi.
Dai-dai lokacin kuma Barrister ya turo ?ofar Wakin tare da sallama.
A hankali Mom dake zaune gefenta ta amsa mishi.
"Wa alaikassalam, Barrister ka dawo".
Cikin kula ya gyaWa mata kai tare da ?arasowa bakin gado.

Ido suka zuba mata cikin tausayawa, ganin hawayen dake bin gefen idanunta suna sau?a har cikin kunnenta.

A hankali Mom tasa tafin hannunta ta fara share mata hawayen.
Ba tare kuma da ta buWe kwayar idanun nata ba, ta fara sakin Shesshe?an kuka.

Zama Barrister yayi a bakin gadon, tare da kamo hannunta ya ri?e, cike da tausasawa da kulawa yace.
"Sorry Jannart kiyi ha?uri ki dena, kuka dukkan abinda yayi tsananin zaiyi sau?i".
Jin muryar ?anin mahaifin nata, mafi kulawa a gareta ne.
Yasa ta buWe Idanunta, tare da yun?urawa, zata tashi zaune.
Da sauri Mom ta tallabota, ta zauna tare da jingina bayanta jikin allon gadon.
Gyara zama Barrister yayi tare da kallon Mom yace.
"Mom Abdul a kawo mata wani abu ta Wan ci".
Da sauri Mom ta mi?e tare da cewa. "Toh". Ta nufi hanyar fita cike da kekyawar niya da zuciya.

Shi kuwa Barrister ajiyan zuciya mai nauyi ya sau?e tare da juyowa ya kalli Jannart data gaza tsaida hawayenta.
Murya can ?asan ma?oshi ta fara mgn.

 Abba ?irjina yana ciwo! Kaina yana bugawa, tunani ya hanani samun sau?i, na gaza gano Yah Junaid wanne irin Wan uwane a duniyar nan.
Anya kuwa Abba Yah Junaid yana da cikekken hankali da sanin haramcin babban fasadin da yake son ai katawa gareni."
Sai kuma hawaye shar-shar, suka soma zubo mata ta kasa ?ara sa mgnar.

Shi kuwa Barrister cikin tsananin tashin hankali da kaWuwa da firgici mai birkita tunanin iyaye na gari yace.

 Me kike nufi Jannart wanne irin fasadi kuma?".
Murya na rawa ta kalleshi cikin rauni tace.
"Abba Yah Junaid fa fyaWe yake son yamin, a lokuta ma banbanta, yana ?udirin yi min FyaWe, idan na ?i amince mishi ne, yake yun?urin kasheni.
Abba cewa yakeyi fa zai kasheni in ban amince da shiba.
Ya kuma ce muddin na gayawa wani zai kasheni.
Wlh Abba zai kasheni.
Abba ya zanyi? Ina zan shiga a rayuwata in samu sau?i, ?an Allah Abba ka rabani da gidan nan in ba haka ba Yah Junaid zai kasheni kuma Daddy ba zai hanashi ba".

Ta ?are mgnar cikin tashin hankali.
Da ya ta azzara nitsuwar Barrister Kabir saleh Dakata.
Wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai zafi ta soma tsastsafo mishi.

Cikin tuno abubuwa da dama na rayuwar duniya, ya kamo hannunta tare da fuskantar ta da kyau kana yace.
"Jannart! Jannart!! Jannart!!!".
Ya kirata sau uku duk da amsa mishi da takeyi.
Cikin yin ?asa da murya yace.

 In sha Allah, Junaid bazai kashe kiba, da izinin ubangiji sai kin rayu, rayuwa mai Al'barka domin ke ayace, kuma izinace sannan ta?in shaida mai ?arfi".
Hannunta ya kuma ri?ewa cikin irin sona uba da Wiyarsa yace.

 Jannart zaki rayu cikin aminci.
Domin Ubangijin daya raya Annabi Musa acikin gidan Fir'auna cikin lfy da aminci.
Shiya rayaki a gidan nan cikin lafiya da aminci.
Ya rigada lokacin ya ?urewa Magautan, bazasuyi nasaraba, dan sunyi nasararsu tun shekarun baya sun gama nasara, yanzu nasarar tamu ce.
Gsky zatayi halinta, in sha Allah zanci gaba da zame miki jigo. Kuma zan nema miki GARKUWA, cikin gaggawa kafin su juyo garemu".

Shiru tayi tana jin kalaman ?anin mahaifin nata, sai dai ta kasa sama musu mizanin da zata aunasu ta ajiyesu ta fahimci manufarsu.
Gogewar hausarta batayi surfin ta ?anin mahaifin nataba.
Cikin ruWanin da kalamanshi suka saka mata tace.
"Abba ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ka sake ro?on Daddy ya bakani ko zai yarda, in koma gidanka."

Cikin sau?e nannauyan numfashi yace.
"Jannart sake ro?ar tashi tamkar wasa da rayuwarki ne, kamar dai kusanto da a ...".
Da sauri ya haWiye ragowar mgnar sanin ?wa?walwarta bazata fahimci zancen nasa ba.
Ita kuwa cikin sanyi ta zuba mishi ido.

Dai-dai lokacin kuma Mom ta shigo da tray a hannunta, cup Win tea ne mai kauri, sai soyayyan irish da ?wai.
Cikin nitsuwa tace.
"Abba to..".
Hannu ya Wan Waga mata tare da cewa.
"Ya isa da yamma zan dawo muyi mgn Jannart kada ki kuma yin kuka".

Ya ?are mgnar yana mi?ewa tsaye.
Kai kawai ta gyaWa mishi kana ta bishi da ido har ya fita.

Bayan ya fita Bathroom ta shiga, ruwa ta Wan watsa, bayan tayi brosh kana ta fito.
Ba laifi ta ji sau?in sosai numfashin ta ya dai-dai-ta.

Tea Win kawai ta iya sha.
Kana ta koma ta kwanta dan Alllurar bata ida saketa ba.


Can cikin bacci taji wayarta na suwa.
"Mahmoud".
Tace tare da amsa kiran.
Nan yake shaida mata cewa.
Dr Rayyern Mai-nasara yana hanyar dawowa Nigeria tun safe jirginsu ya taso.
Zuwa azahar zasu sau?a Abuja.
Kuma yau Win zasu shigo Kano cikin alamun bacci tace.

 Toh ya akayi kuma lbrin ya sauya Mahmoud ba sai jibi ba kace?

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Uhumm kin kuwa san waye Dr Rayyern, mutun yana nan tamkar Wahainiya gane shirinsa ko manufarsa fa wuyane dashi.
Ke dai in kin samu dama kiyi ?o?arin zuwa Airport da yamma wata ?il a dace, zan turo miki hotuna Yah Usman PA Yayan Abokina Deen wanda yayisu a bayan motocin Dr Rayyern Win so sai ki Wauki number's Win motocin ta wannan hanyar zaki iya samun damar bibiyarsa".
Cikin sanyi tace.
"Toh Ngd matu?a".

Daga nan sukayi sallama.
Salman ta kira yana Wagawa yace.
"Ya jikin namu?".
Cikin sanyi tace.
"Da sau?i waya gaya maka?".

 A'isha Lawal ce ta gaya min tace Wazu data kira Mom ce ta Waga wai jikinki ya tashi."

Ayyah tace a ta?aice kana ta mishi bayanin da Mahmoud ya mata ta ?ara da cewa.
"Ka shirya da yamma muje Airport Win bari in turoma hotunan".
Toh yace kana sukayi sallama.


?arfe biyu dai-dai jirginsu ya sau?a cikin international Airport Abuja.

Bayan wasu ?an da?i?u, aka fara fitowa.
Mutun kusan 21 suka fito.
Kana Rayyern ya sako ?afarsa ta dama kan matakalan forko.
Wani irin sassanyan numfashi ya sha?a a hankali tare da zu?an iskar ?asarshi abin sonshi da al'faharin shi.

A hankali ya fara takowa yana sau?a cikin haiba.

Da sauri ya ratayo jakarsa a kafaWa tare da biyoshi a baya da gudu.

Usman kuwa shima jakarsu ya ratoyo kana ya biyoshi a baya.
da sauri ya matsoshi.
Juyowa yayi jin an ri?e mishi hannun damanshi.
"Hamma Rayyern daga nan wanne state Win zaka tafi".
Ya rasa gane meyasa zuciyarsa ke bawa yaron amanna ko dan kamar da sukeyi ne.
Sam bai shiryawa amsa mishi ba kawai yaji lips Winshi sun furta.
"Kano".
Wani irin tsalle yayi tare da cewa.
"Yesssss! Nima Kano zan tafi ai".
Cike da mamaki Usman ya nufosu har yana tuntube tare da cewa.
"Sir wannan fa?".
Juyowa yayi ya kalli Usman da salon.
Baya son shisshigi.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri ya dawo kusa da Usman hannu ya bashi tare da cewa.
"Ni ?aninsa ne".
Baki buWe Usman ya bishi da ido.

Daga nan masallacin cikin Airport Win suka wuce, ganin azahar tayi har lokacin yaso zarcewa.

Suna idar da salla Usman ya mi?e da nufin fita ya samo abinci.
Dan yasan ubangidan nasan bazai bu?aci abinci yanzuba.
Juyowa yayi ya Wan kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
"Bishi kuje Restaurant".
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"Bana jin yunwa".
Kai kawai ya gyaWa mishi.
Nan suka zauna har la'asar tayi.
Bayan an idar da sallane kuma, suka koma ciki.

Domin shiga jirgin da zai wuce Kano.

?arfe huWu da rabi dai-dai jirginsu ya tashi daga birnin tarayyar Nigeria zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.


A nan cikin Kano kuwa.

Jannart ce zaune cikin motar, Salman kana shi kuma yana gaba gefe.
Baba Ado dake jansu.
Yayinda sauran garadan dake tsaronta, suke hangame da ba?i a zatonsu tana can cikin ma'aikatar nasu, dan sam basu lura da lokacin da ta fitoba, koda yake Salman ne ya bawa Baba Ado key kana ya jawo motar har zuwa bakin mashigansu ya kawo mishi.
Shiyasa suka fita, basu ganeba.
Kai tsaye filin jirgin sama na malam Aminu Kano suka nufa.

Sosai kuwa Jannart tayi kyau acikin shigar pallazo da kuma tight shirt din dake jikinta, wanda ya bayyana lafaffen cikinta, kasancewar kuma rigar nata na d an bayyana nipples dinta ne, yasa ta daura wata Navy blue fashion top akan shigar ta ta, wanda tsawonsa ya kawo har guiwanta, Yayinda ak afanta take sanye da wani navy blue hill shoe, na company n gucci mai kyau da tsada da uban tsini, akanta kuwa wani had add en medium vail ne wanda ya sauko harkan kirjinta.
Sam akan fuskarta babu wani kwalliya sosai, saidai kuma hakan bai hana zallar kyawun fuskarta bayyana ba, Yayinda small lips dinta suka sha peach lipstick, acikin jikinta kuwa wani sassanyan k amshi ne yake tashi.

Suna shiga cikin Airport Win sukayi paking a Airport parking.
Kana suka wuce suka nufi cikin.

Bayan isarsu da kamar 5 minute, jirginsu Rayyern yayi sau?ar angulu.

Bayan yan da?i?u ne kuma matafinyan suka fara fitowa.
Da sauri Usman ya matso kusa da uban gidan nashi, cikin yin ?asa da murya yace.

 Sir in kira driver?
Shiru yayi ganin ya Wan kaWa mishi yatsarshi manuniya.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sassarfa yake biye da Usman a baya.

A haka har suka fito asalin filin da matafiya kan zauna su jira masu tarbarsu.
Kanshi ya Wan Wago ya kalli taron mutanen, yatsarshi yasa ya Wan gyara zaman farin glass Win dake idonshi.
Gefen lips Winshi na ?asa ya Wan kamo ya Wan tauna a hankali.

Da sauri kuma ya Wan juyo ya kalli bayanshi.
Inda ya hango Riyyam-nsra can baya yana Wan tahowa yana waige waige a alamun shi yake nema.

Gabanshi ya nunawa Usman tare da yin mgna can ?asa.
"?an jarida ne, zanbi nan, in sun tsareka kaji dasu."
Yana faWin haka, ya ratsa yabi yar siririyar hanyar dake gefen damanshi.

Shi kuwa Usman ya nufi hanyar fitan.


Jannart kuwa da sauri cikin tsananin razana ta koma bayan Salman tare da yin ?asa da kanta murya can ?asa tace.
"Innalillahi Salman gacan Hakim abokin Yah Junaid idan ya ganni zai gaya mishi."
Sai kuma ta zaro ido jikin tashin hankali ta dafe kirjinta tare da cewa.
"Na shiga ukuna tare suke da Yah Junaidu ma gashi can bayanshi".
Da sauri Salman ya Wan kalli gabanshi kana ya juyo.
Gaba Waya jikinta rawa yakeyi sabida hango Hakim Da Junaidu sun nufosu gadan-gadan.
Jujjuyawa tayi.
Ganin wata ?ar siririyar hanyar ne gefen hagunta, wacce nan Rayyern yabiyo.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ratsa cikin ?ar hanyar ta Sacewa ganin su.

Nannauyar ajiyar zuciya mai ?arfi ta sau?e, tare da ci gaba da tafiya cikin yar siriyar kusurwar.
Tana tafiya tana wai-waye da juyawa tana kallon bayanta.


Shi kuwa Rayyern, cikin Wan sassarfa yake tafiya.
Saboda so yake kafinma Usman da Riyyam-nsra su fito, ya shiga taxi ya tafi.

Tafiya yake yana dai-dai-ta kan files da takardun da yayi ta aikin rattaSa musu hannu a cikin jirgi.
Haka yasa bai lura da gabansa.

Ita kuwa Jannart tafiya take tana wai-waye shiyasa bata ganin gabanta.

Jin kamar takun wani a bayanta ne kamar ana boyota, kuma yasa ta ?ara saurinta.
Dai-dai lokacin kuwa Rayyern ya iso gab da ita.

Jin ana ce. Ke! Ke!! Yasa ta juya da nufin zata arta da gudu.
Sai kawai ta jita jikin mutum sunyi karo.
Goshinta ya bugi gemunshi da azaban ?arfi.
Take files da Takardun hannunshi suka watse.

Yayinda ita kuma tayi tangal-tangal ta koma baya zata faWi ?asa, da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin sauti mai cike da tsoro, hade kuma dasa hannunta da nufin dafe ginin dake wajen, dan kare kanta daga faWuwa ?asa.
Kawai sai ta kamo kwalan rigarshi ta gefe ta cikin da kuma Suit Win dake saman da ?arfi.
Pet-pet haka boturan jikin rigar duk suka Salle, kab suka watso ?asa, hakan yasa gaba Waya rigunan jikinshi suka buWe.
Cikin wani irin masifeffen takaici yasa hannunshi ya fisge hannunta dake sha?e da gefen kwalar rigarshi.
Ya yarfa hannun tare da zuba mata wani irin masifeffen....!


Kuyi hakuri rashin jina da wuri.

Rayyern da ban Riyyam-nsra da ban ai sunayenma ba iri Waya bako.

Free PAGE ne wannan.




By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: =???
*TUBALI*


PAGE 6
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE ne*


*Littafin TUBALI na kuWine ki biya ki darinki biyar kacal in saki a ?aramin group wanda bonus ne ga dana na, dan in na gama ya zama Complete 1k ne, saukine yanzu ga Masoyana, asalin kuWi nai 1k ne, Special Group kuma su post nasu zaifi yawa. 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276. Kada ki bari garabasar ta wuceki, kice sai an gama, Hajia in kuma kinada zakuwa

7 / 46