Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   5 / 46

12K to 15K   out of 135.1K words

min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's Win katin ki turo min ta whatsApp.

Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k aramin group kuma (500) kacal,
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y ay an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki=?O?
Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa.
*Tausayi, Sark ak iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, ri?on amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya*

Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala*

Za'ayi tsawon mako Waya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy*

=?O?

Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi ha?uri ba raini bane ko wulak anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, =?O???

*Sayan na gari maida kuWi gida sai kinzo*








By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: =???
*TUBALI*

PAGE 5


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*FREE PAGE NE*

*Littafin TUBALI na kuWine, ki biya 500 in saki a ?aramin group, ko kuma ki biya 1000 in saki Special Group, wanda cikin mako biyu kacal zamu ?are part 1. Ki turo kuWin ta asusuna na GTBank, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan numben whatsApp na 09097853276. Ki saya ki karanta cikin salama ba tare da hakkina a kankiba, in bazaki sayaba ga littatafai nan birjik kamar jompa a Jos sai ki samu na kyauta ki karance salim alin*


Kallo mai cike da tarin takaici ya watsa mata, rikitattun idanunshi cikin nata kwayar idanun kasan cewar suna fuskantar juna.
Wani irin azabebben zogi lips Winshi sukeyi sabida yadda ta bugi gemunshi da goshinta, har hakan yasa lips Win suka haWe da kyawawan ha?orinsa.

Zut-zut haka yakeji suna zogi.
Da raWaWi, wani irin tafasa zuciyarshi takeyi tare da harbawa, files Win campany'nsa da yake da matu?ar mahimmanci da suke watse a ?asa ya zubawa idanu.
Wani irin mugun kallo ya kuma watsa mata duk a cikin abinda baifi 5 second ba.
Idonshi ya kai bisa hannunta dake sha?e da kwalar rigarsa ta gefe.
Hannunshi na dama yasa ya dam?o hannunta da azaban ?arfi, kana ya yarfashi.
Wanda sanadin fizge hannun nata da yayi kuma wayarshi, kirar iphone 12 pro max dake cikin al'jihun rigarsa ya faWo ?asa.

Kana ita kuwa Jannart wani irin masifeffen karkarwa jikinta keyi.
Yayinda kuma gaba Waya hankalinta kecan baya.
Sabida masifar tsoron Yah Junaid da ta tabbatar muddin ya ganta sai ya kusan kasheta.
Haka yasa gaba Waya ma hankalinta baya kanshi, bare taga ta'adin da ta aikata mishi.
Tangal-tangal tayi lokacin daya yarfa hannun nata, da sauri ta dafe ginin gefenta tare da gyara tsayuwarta, cikin rashin sa'a ta sau?e ?afarta ta hagu kan glasss Win fuskar wayar tashi, da tsinin takalminta mai masifar ?arfi.

Saurin yin ?asa da kansa yayi, sakamakon jin ?aran sautin fashewar glass din wayarsa, wanda take dauke da screen mai tsada.
Idonshi ya rumtse da ?arfi.
Yana mai jin tamkar ya sha?e wuyanta sai tayi sanyi.
Sam Ba Waruruwan kudin wayar yake tunawa ba, muhimman abubuwansa dake cikin wayar yake tunawa wanda yasan tabbas zai iya rasa wani abun.

Ita kuwa Jannart da sauri ta sunkuyo jin ta taka wani abu kuma tsantsi ya Webi ?afarta.
Da sauri ta janye ?afar tata cikin wani akasin kuma, ta sau?e tsinin takalmin nata, kan tattausan ?afarsa dake cikin tattausan takalmin fata,
dai-dai kan farcen babbar yatsarshi ta kafa tsinin takalmin tare da sake iya nauyi ta.

"Auchhhhhh!!". Ya sake wani irin sauti tare da rumtse idanunshi da ?arfi, hade kuma da taune lips Win shi na kasa dake ta zogi tun buge shi da tayi.
?ara rumtse idanunshi yayi sabida wani irin,
masifeffen azaba da yaji tun daga tsakiyar kanshi har cikin ?o?on ranshi, kana ya iso kan babbar yatsar tashi.

Da sauri ta kuma janye ?afarta, tare dayin baya kaWan tana mai wai-wayen bayanta, alamun sam hankalinta baya gabanta sai baya.

Wani irin kallo ya zubawa tarin Sarnar da tayi mishi,a lokaci Waya ta lalata mishi abubuwa da yawa, har lfyarshi bai tsiraba
Ta nu?ur?usashi tamkar wanda yayi karo da tirela.

Wani irin nannauyan numfashin ta sau?e ganin Salman ne ke biye da ita a bayan yana ce mata ke Win.
Da sauri Salman ya iso garesu.
Ganin yadda suke tsaye cirko-cirko.

Rayyern ya kalla cikin nitsuwa,
tare da fahimtar karo sukayi, cikin sauri yace.
"Innalillahi karo kukayi, bawan Allah kayi ha?uri."
Ya ?are mgnar yana sunkuyawa files din ya fara tattarewa, yana mai cewa.
"Subahanallahi, wayarka duk ta dare, Jannart garin ya akayi haka".
Ita dai Jannart sai numfashin tsoro take sau?ewa, ta gaza cewa komai sabida ganin wani irin mugun masifeffen kallon da yake watsa mata, sai yanzu idonta ya kai ga ta'adin da tayi mishi.
Da sauri tayi ?asa da kanta dan bata da jarumtar da zata iya jurar kallon nan daga kwayar fitinennun idanunshi.

Yatsun ?afarshi ta tsurawa ido ganin yadda suke tsuma alamun tsananin azaba, ga kuma jini da take tsastsafowa.

Dib-dab-dib-dab haka taji zuciyarta na bugawa a 170.
Salman kuwa cikin yanayin damuwa ya mi?owa Dr Rayyern Mai-nasara Takardun da wayar cikin yanayin jin ba daWi yace.
"Dan Allah da Manzonsa kayi ha?uri bawan Allah".

Idonshi ya rumtse da ?arfi tare da mi?a hannunsa ya amshi takardun da wayar.
Sabida Salman ya gama dashi, tunda yace.
"Dan Allah da Manzonsa yayi ha?uri, to ya zame masa wajibi kuma dole yayi ha?uri sabida wannan shine mafi ?ololuwar al'farmar da mutun zai nema a wurin musulmi yayi mishi, wannan shine kalaman da Abban sa ke cemasa a mafi akasarin lokuta.
Amman badon haka ba yaso ya yarfawa wannan birkitacciyar yarinyar mari Waya rak, taji salon yadda tafin shi yake, so yayi ya yarfa mata mari da hannun hagunshi wanda yasan tabbas sai ta saki fitsari sabida ya lura bata iya bada ha?uri ba, kuma bata da nitsuwa.

Wani irin juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo da fuska a murtu?e,
"Mchewwwww ". Yaja mata wani irin tsaki tare da yin kwaffa kana ya juya yayi gaba ba tare da yayiwa Salman mgn ba.

Cikin kaWuwa Salman yace.
"Jannart ya akayi haka, kinga asarar da kikayi mishi kuwa, nasan tabbas duk yadda akayi kece da laifin karon tunda kin hango mala'ikan Waukan ranki, kina gudu kina rawan jiki kina wai-waye kinzo kin mishi ta'adi.
Kin kuma san kuWin wayar nan da kika fasa mishi sarai amman ko a jikinki.
Sannan kin tsaya kinyi shiru, wannan wanne irin tsorone kijeyiwa Junaid?

Ajiyan zuciya mai nauyi ta sau?e, tare da lumshe idanunta a hankali cikin nutsuwarta da ta fara dawowa tace.

 Allah ya bashi ha?uri, wlh Salman na rasa ta ina zan fara bashi ha?uri ne, kagafa wani irin kallon da yakemin tamkar zai sha?eni ya kasheni, tsoronshi naji.
Sannan kuma duk tsorona kada Yah Junaid ya ganni, wlh in ya ganni a nan kuma bance zanzo nanba bisa aikina sai ya kusan kasheni, duk allurarsa ta sojoji a kaina zai direta."

Cikin takaici Salman yace.
"Shike nan ai mun rasa damar farko, dan yanzu dai da wuya in Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara bai wuceba tun tuni, matsalar ba sanin fuskarsa akayi ba bare ace da mun ganshi zamu ganeshi.
Dama dole bincike zamuyi da numbers din motocinsa, da aka bamu zamu ganeshi mubi bayanshi muga gidansu. Kinga har lau dai tsoron Junaid yana hanaki nasara.
Har nima ta shafeni."

Cikin takaici tace.
"Toh ya zanyi?".

KwaSe fuskarsa yayi tare da juyawa yayi baya.
Itama kuwa juyawa tayi tabi bayanshi.


Riyyam-nsra kuwa, Sat RAYYERN da Usman PA suka Sacewa ganinsa.
Gaba Waya ya gama zagaye wurin babu su ba dalilin su.

Wani irin masifeffen kuka yakeji tun daga can ?asan ma?oshi sa yana taso mishi.
Saboda lokaci daya yaga samu ya kuma ga rashi.
Kana layinshi bazaiyi aiki a nanba bare ya kira Mammy ya sanar mata halin da yake ciki.
Hakan yasa yake jin wani irin ?uncin rai.
Gefe ya koma ya zauna bisa kujera, tare da maida kanshi ya jingine yana mai jin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi.

Da sauri Salman ya nunawa Jannart Riyyam-nsra tare da cewa.

 Ikon Allah Jannart ga mutuminki".

Juyowa sukayi suna kallonshi.
Shidinma kuwa Idanunshi da sukayi ja ya buWe yana kallonsu.

A hankali Jannart tace.
"Kai ba shi bane, sai dai ko ?aninshi".

Da sauri Riyyam-nsra ya mi?e tsaye tare da rataya jakarshi bisa kafaWa.
"Assalamu alaikum".
Yace yana mi?awa Salman hannu.
"Wa alaikassalam".
Yace tare da bashi hannu.
Sukayi musabiha, cikin sanyi Jannart tace.
"Ayyah dan Allah ka cewa yayanka yayi ha?uri, ban sani bane".

Cikin fahimtar cewa. Rayyern suka gani suke cewa yayanshi, ya Wanyi murmushi cikin hikima yace.
"Ta ina kuka haWu ina yake.
Ni ya Sace min ne nasan kuma shima ni yake nema yanzu".
Da sauri Salman yace.
"Ikon Allah ta nan yayi, to amman ba zuwa za'ayi a Waukeku ba".
Da sauri ya nufi inda Salman ya nuna mishi yana mai cewa.
"Dan Allah kuzo ku nuna min inda yayin".
Cikin nitsuwarta tace.
"Wani aiki mukazo yi nan Airport Win kai dai kawai kayi nan Win zaka ganshi."
Salman ne ya Wan harareta irin hararar da har yau bata gano manufarsaba,
Bayan Riyyam-nsra yabi tare da cewa.
"Na nawa kuma aikin yau dai ai mun rasa damar sai dai mubi mataki na gaba, kuma dan Allah fa yace so muje mu nuna mishi."
Dole tabi bayansu.

Gaba Waya harabar wurin Airport parking din babushi babu alamarsa.
Kana sun dudduba gefe-gefen duk bashi, cike da gajiya da son komawa gida Jannart tace.
"Kai to ka tare taxi mana ya kaika gida".
Dafa motarsu yayi tare da kwaSe fuskarsa kana yace.
"Ai ba?one ni, mu ba?ine daga Ethiopia, wani aikine Hamma na yazo yi, shine mukazo tare".

 Toh ka kirashi a waya mana".
Cewar Salman.
Dafe kai yayi tare da cewa.
"Toh ai dole sai na sai layin nan ?asar taku nasa.
Shiru sukayi baki Wayansu,
Can dai Jannart tace.
"Toh yanzu ya zakayi".

Cikin danne tarin damuwarsa yace.
"Ku taimaka ku kaini na sayi layi.
Sannan sai in nemi masau?i".

Haka kuwa akayi Salman ya amince bayan sun kaishi, ya sayi sim card layin Mtn, yayi register.

Tuni lokacin biyar ta gota,
A hankali suka fito bakin shagon.
Cikin kula da alamun kallon akwai inda Salman ya sanshi yace.
"Toh ?anina yanzu ina zakaje ne?".

Jingina kansa yayi da jikin motar kasan cewar, CRV ce tanada tudu.
Idonsa ya lumshe tare da fara wassafo dajar shigar dake jikin Rayyern.
Kama daga Suit Winsa agogon hannunsa takalmansa zoben yatsarsa, uwa uba wayarsa.
Da kuma irin takardun da yaga yana ciccikewa da matsayin inda suka zauna.
Cikin sau?e numfashi ya Wago kansa tare da gamsuwa da tunaninsa yace.
"Ku taimaka ku kaini hotel mai kyau, wanda yake anguwar manyan mutane.
In na isa na samu layi na ya hau zanyi mishi text ta Email Winsa".
Da sauri Jannart tace.

 Toh ni dai Salman ka medani kafin ka kaishi."
Murmushi Salman yayi tare da cewa.
"Toh ai sai mun wuce ta inda yake so Win ba yace unguwar manya ba, mu kaishi hotels Win Nasarawa GRA kawai".
Juyowa tayi ta kalleshi kana tace.

 Uhum kafa san abubuwan wuraren tsada garesu ko, sannan kai kana ma da kuWin ?asar nanne?."
Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.
"Yess ina dasu, nayi canji tun a ?asata, kuma in ma bazasu isaba ai zasu amshi transfer ko?."

Kai ta gyaWa mishi tana kallon tarin kamanninsa da wanda tayi karo dashi.

Bayan sun shiga motar ne.
Baba Ado yaja.
Salman na gaba kusa da Baba Ado shi kuma yana gefenta.
Cikin hausarsa da bata isasshen inganci yace.
"Hotel mai kyaufa".
Gyara zama Salman yayi tare da cewa.
"Kada ka damu. *Nasarawa GRA* itace unguwar da ta tara kaf manyan masu kudi na Kano,babu wani babban mai kudi ko Wan siyasa na Kano da ya isa yake ji da kansa dama sauran jahohi da basu da gida a. Nasarawa GRA hatta Government House ma anan yake.
Sannan a cikin GRA din akwai manyan layuka da sunayensu
*LamiWo Creasend* da kuma *Ahmadu Bello way* da kuma sauran ?ana nan layuka.
Kana akwai manyan Hotel's din da suke Nassara GRA akwai *Tahir Guest Palace*
da kuma *Ni'ima Hotel* da *Green Park* da *Liyafa Hotel* duk wadannan suna cikin Nasarawa GRA ne, kuma manya ne sosai ana ji da su suna da tsada da kuma kyau da inganci, zaka samu duk abinda kakeso a ciki.
Yanzu sai ka zaSi wanne zan kaika, kaga dare ya fara yi mana."

Numfashin ya Wan sauke cikin jin daWi da gamsuwa da bayanin unguwar da suka shigo Win, daga shiga unguwar kasan ta manya ce.
"Muje Taheer Guest palace hotel".
Riyyam-nsra ya faWi yana kallon gefen titin garin.

 To Alhamdulillah gashi ma mun kusa.
 Salman yace yana mai karya kwanan shiga layin da hotel Win yake.

Suna shiga bayan yayi parking, Suka sallameshi suka tafi.
Salman na cewa.
"To sai zuwa gobe zan kiraka in sha Allah inji ko ka gane ya'yan naka. Tunda na amshi number taka ta ?asarmu".
Toh yace tare dayi musu godiya.

Suna fita Suka nufi ma'aikatar su ta Arewa 24. Tafiya ce mai Wan tazara tsakani.
Hakane yasa Baba Ado yake gudu.
Mintuna kaWan suka isa.
Suna isa suka samu su Sunday a tsaye ?i?am to babu salla bare salati sai tsaron Jannart in wata tayi a biyasu makudan kud in, da su kansu har yau basu gano manufar tsaron da ake bata, fiye da shi kanshi Alhaji Idi Sale Dakata'n ba, ko kanshi bai bawa wannan tsaron ba haka babban Wan sa dasu Abdul, to ko dan ita macece shiyasa.

Cikin hikima Baba Ado yayi parking jikin motarsu.
Kana suka fita suka shiga cikin ma'aikatan jim kaWan Jannart ta fito.
Suna ganin ta fito suka mara mata baya.
Tana shiga mota Baba Ado yaja.
Kana yaja suma sauran suka bishi a baya ganin. Yaja Win.

*Dr Rayyern*
Wani Irin karkarwa ?afarsa keyi, sosai yatsar ke fidda jini.

A haka ya tsaida Wan taxi ya shiga, ba tare da yace komaiba, mai taxi Win yaja.
Bayan sun fita Airport Win sun mi?a hanyar cikin gari.
Kanshi ya jingina da jikin kujerar, wani irin masifeffen zafi yakeji zufa na tsastsafo mishi tako ina, sabida zogin da yatsarsa keyi, ga lips Winsa dake raWaWi kana ga zuciyarsa dake tafarfasa.

Sosai mai taxi Win ya dai-dai ta motar tasa bisa titi, a hankali yace.
"Sir ina muka nufa?".
Shiru yayi tamkar bai jishi ba sabida zogin fashewan farcenshi da yatsarsa su suka buwayeshi.
Sai da ya kuma tambaya kana cikin taune lips Winsa yace.
"Nassarawa GRA".
Toh yace kana yaci gaba da driving.

Tabbas da AC cikin motar amman bai gamsar dashi haka yasa yaketa haWa zufa.
Suna shiga cikin tsakiyar anguwar Driver'n ya kuma juyowa ya Wan kalleshi a hankali yace.
"Sir ta ina zamu Sullo?".

A takaice yace.
"Ahmadu Bello way".
To ya Kuma cewa kana sukaci gaba da tafi kan kyakkyawan titin mai faWi da wadatan tsabta.

Tafiya yakeyi a hankali.
Yanayi yana Wan kallon tabka-tabkan gidajen dake shumfud e na gani na faWa tamkar abirnin India.

"Kayi hannun dama". Dr Rayyern Mai-nasara ya faWa mishi a hankali.

To yace tare da ratsa wa damanshi.
Wow yace lokacin da suka fito kan Wan madaidacin titin, da wani irin tamfatsetsen gida mai tsananin kyau na al'farma yake forkon layin.

 Yayi tsaya a nan".
ya kuma tsinkayo muryar Dr.Rayyern.

Juyowa yayi ya kalleshi kana ya juyo ya kalli tamfatsetsen gidan, na al'farmar da in ya kintata nanne gidansu.
Cikin ransa yake tasbihi ga Allah.
Tare da juyowa ya kalli shi kana a mutunce yace.
"Mai gida in shigar da kai ciki mana, naga tun kan ka shiga yatsarka na zubda jini".

Wani irin taSe fuskarsa yayi,a rayuwarsa

5 / 46