Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   13 / 46

36K to 39K   out of 135.1K words

baccin ya daukesa.

Acan sashin Riyyam-nsra kuwa, koda ya shiga dakinsa na hotel din, haka ya tarar da komai nead.

Wanka yayi tare da zuwa ya fada kan gado, hade da jawo wayarsa ya runguma, bayan ya kunna data ne kuma ya shiga whatsapp sama sama yayi chatting acikin whatsapp din, kana daga bisani kuma ya dawo ta inda yafi karfi Wato Tiktok.

Atakaice dai saida yakai kusan 2am yana sheke ayarsa kafun bacci barawo ya daukesa, haka kuwa yayi baccin yabar data d insa akunne.


Washegari.

Kamar koda yaushe yauma 7:30 am ya gama shirya kansa tsab, cikin royal high quality black suit, tare da white long sleeve wacce tayi masa kyau sosai.

Kasancewarsa mai kyau ne kuma shiyasa komai ya saka saiyayi masa kyau.

Ahankali yake saukowa daga kan steps din falon, Yayinda briefcase d insa ke rike ahannunsa na dama.

Mamy dake tsaye tana shirya dining table ne ta dago ta kalleshi.

?an guntun Murmushin gefen baki yayi, wanda ya Wan bayyana fararen ha?oransa, kana cikin nitsuwa yace.

 Good morning Mamyna.

Murmushi itama Mamyn tayi, cike kuma da soyayyarsa tace.

 Morning My beautiful son, kafito a dai-dai maza zokayi breakfast dinka.

Karyar da wuyansa gefe yayi, tare kuma da duban agogon hannunsa.
Muryarsa adan sanyaye yace.

 I m sorry Mamyna yau sauri nakeyi, amma idan Ramadan yazo fita ki hada masa breakfast dinnawa a basket ya kaimin office.

Murmushi Mamy tayi tare da cewa.
 To ba matsala adawo lafiya Allah ya tsare ya kuma bada sa a.

Da  Ameen. Ya amsa kana cikin jin dadi ya Sakai ya fice daga cikin falon.

Dai-dai fitowarsa compound din gidanne kuma, Riyyam da Ramadan suka shigo atare.

Cikin sauri Riyyam ya karaso, tare Da dan rungume Rayyern din, fuskarsa dauke da Murmushi yace.

 Good Morning Hamma Rayyern!

Idanu Rayyern din yadan lumshe tare dasa hannu ya shafa kan Riyyam din, cikin kuma yanayinsa na rashin sabo dayin magana yace.

 Morning Riyyam, Ina fata kunyi waya da Naseer yau, ya jikin Malam din?

Kai Riyyam din ya jinjina tare da fadin.

 Eh munyi waya dashi, ya kuma tabbatarmin cewa jikin Malam din da sauki.

Kai Rayyern din ya jinjina tare da cewa.

 Okay bani numbern Naseer din.

Yafada yana me mikawa Riyyam wayarsa dan yasa masa numbern Naseer.

Ramadan kuwa kai ya jinjina cike da gamsuwar lallai Hamman nasa ya dauki lamarin malam da matu?ar mahimmanci.

Hakan kuwa akayi domin cikin abunda bai wuce 1mn ba Riyyam ya sakawa Rayyern din numbern.

Ramadan kuwa dake tsaye fuskarsa dauke da dan mamaki yace.

 Hamma Rayyern me zakayi da numbern Naseer kuma?.

 Zanje na duba Malam Mai-nasara ne, tunda har Abba ya a mince dana dubasa din, tofa Tabbas saina duba sa, zan kira Naseer din idan basa hospital har gidansa zanje na dubasa.

Rayyern din ya fada in full confidence.

Ramadan kuwa Kai ya jinjina cike da gamsuwa, sai kuma suka hada baki atare shida Riyyam wajen cewa suma zasuje gidan Malam Mai-nasara din.

Kansa kawai ya kad a, adai-dai kuma lokacin da yake shiga cikin motarsa yace.

 Okay nidai yanzu hospital zan wuce, sai Idan na tashi ne zan biya can gidan nasa, amma idan kuna da chance zaku iya zuwa maybe mu hadu acan .

Yana gama fadan hakan yaja murfin motar ya rufe, batare kuma daya saurari mai zasu sake cewa ba, yasa Hadi driver yaja motar suka bar wajen.

Su kuwa Ramadan da Riyyam kaitsaye cikin gidan suka wuce.

Koda suka karasa cikin falon Riyyam aladabce ya gaishe da Mamy da kuma Abba wanda yake yanzu fitowarsa daga daki.

Cikin farincikin ganinsa Mamy ta amsa, Yayinda Abba ma ya amsa masa fuska asake.

Anan kan dining table sukayi breakfast.
Bayan kuma sun kammala ne Riyyam da kansa ya gyara wajen, tare da kai plates din da suka bata kitchine ya wanke.

Mamy kam cike da mamaki take kallonsa, domin kuwa duk da ta hanashi saida yayi, inda yake bata labarin cewa ai yanayiwa Mammynsa ma, saidai watarana dagangan sai yakiyi dole Zaytoon ce zatayi.

Mamy dai itakam dariya kawai takeyi, saboda daga jiya zuwa yau din kawai, zama da yaron ya zame mata sabo.
Abba kuwa ido ya zuba musu da inda yake zaune can tsakiyar falon yana nazartar ?arfin halin Riyyam-nsra da shisshiginsa garesu anya kuwa!?.
Ya Wiga ayar tambaya a kan yaron.

Acan hospital kuwa Rayyern bayan yadan duba wasu daga cikin patients dinsa ne, ya d auki waya ya kira Naseer.

Bayan sungaisa ne kuma yake tambayar Naseer din, jikin Malam Mai-nasara.

Tofa ananne Naseer din yake fada masa cewar.

 Ajiyan ankai Malam din Zanna Hospital, amma kuma an sallamosu Yanzu dai Malam din yana gida, kuma babu laifi jikin da d an sauki. 

Kai Rayyern din ya jinjina, tare da cewa Naseer din ya turo masa adireshin gidan Malam din zaizo anjima.

 To. Naseer din ya fada cikin minti kadan kuwa ya turowa Dr Rayyern din, da text message na address din gidan Malam Mai-nasara.

12: am dai-dai Rayyern ya kammala duk wani abu abunda yakeyi acikin hospital din.

Haka ya fito daga cikin office dinnasa yana taku cikin nitsuwa da kuma zarransa dake kara bayyana kwarjininsa da haiba na cikakken da na miji.

Kaitsaye compound din asibitin ya nufa, yana zuwa kuwa ya shige cikin motarsa batare da bata lokaci ba, driver yaja motar suka fice daga cikin asibitin gaba daya.

Bayan sun hau titi ne kuma drivern ya juyo yadan kallasa, kana aladabce yace.

 Ranka ya dad e Ina muka nufa?.

 Hausawa sabon titi. Ya fada atakaice.
Tare da sanya hannu ya zare glass din dake manne a idanunsa.

A dai-dai wannan lokacin kuwa Ramadan Riyyam da kuma Naseer ne, acikin motar Ramadan din kirar Range rover velar 2019, inda suma kaitsaye suka nufi Unguwar ta Hausawa sabon Titi, wanda suna tafiyar ne kuma bisa jagoran Naseer.


After some 20mn suka iso gaban wani gate din makeken gida mai tsananin kyau da girma.

Wanda kuma yake nanne gidan Malam Mai-nasara.

Horn Ramadan dake driving ya danna.

Jin karan horn dinnasa ne kuma yasa maigadi, Dan lekowa ganin dalleliyar motar da yayi ne da kuma Naseer a gaba ne yasashi karasawa da hanzari ya wangale babban farin gate din.

Wanda hakan ya bawa Ramadan daman tura kan motar tasa ciki.

Wanda shigansu cikin gidan kuwa. yayi dai dai da wani irin masifeffen bugawar zuciyoyin Riyyam-nsra da Ramadan.

Kokarin maida gate din maigadin yasomayi saidai kuma ganin wata dakekkiyar motar again BMW ta faso kaine, yasashi wangale gate din.

Inda matukin motar ya tura hancin motar ciki.

Wanda saukan tayoyin motar acikin gidan, yayi dai-dai wani irin azabebben harbawa da zuciyar Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara yayi.

Cikin wani irin matsanancin faduwar gaban da yakeji, da kuma dukan da zuciyarsa keyi ya bud e idanunsa inda ya saukesu A...!




Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki=?i? >??? da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci=??iya kudinka iya shagalinka=???kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari=?
? munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai >???da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm>?????
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: =???
*TUBALI*

PAGE 10
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*FREE PAGE ne*

*Na kuWine littafin Special Group 1k ?aramin group 500 ne kacal, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sai katin MTN ki copy number's Win katin ki turo min ta whatsApp*


Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki=?i? >??? da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci=??iya kudinka iya shagalinka=???kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari=?
? munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai >???da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm>?????

Akan motar su Ramadan, wanda tuni Naseer ya fito daga cikinta, Yayinda Ramadan da Riyyam ke kokarin fitowa suma.

Tsumammun eyes d insa masu dauke da wasu sinadarai na musamman ya lumshe, tare da sanya hannu ya dafe dai-dai saitin zuciyarsa.

 Yah Allah kabani nutsuwa, k arfi da kuma k warin guiwa ako da yaushe! .
Yafad i hakan acan k asar zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri.
Kwata-kwata baisan meyasa agaba d aya y an kwanakin nan, zuciyarsa ke yawan harbawa da k arfi ba.
Saidai kuma koma meye yana fatan ya zame masa alkhairi.

Bud e murfin motar yayi ahankali tare da zuro kyakyawan k afafunsa waje.

Dai-dai lokacin da ya gama fitowa acikin motar kuwa, su Ramadan da Riyyam suka k araso.

Riyyam-nsra kuwa da murmushi ya kasa buya akan fuskarsa ne yace.

 Laa Hamma Rayyern kaima ka iso?

Kai Rayyern din ya jinjina masa alaman.
 Eh.
Naseer kuwa dake tsaye agefe, wayarsa ya zaro tare da dannawa lambar Uncle Mustapha (Kawunsa, yayan mamansa) kira.
Bugu daya kacal kuwa Uncle Mustapha ya d aga wayar.

Jin an d aga wayanne kuma yasa Naseer cewa.

 Uncle Mustapha gamu nan cikin compound tare da Dr. Rayyern din dana gaya maka cewa zaizo ya duba jikin Malam.

Uncle Mustapha dake zaune acikin falo, kuwa saurin mikewa tsaye yayi, batare kuma daya katse wayan ba yace.

 Masha Allah to Naseer ka shigo dashi mana, ku shigo ku shigo.

Yanayin yanda yayi maganar yana me nufar hanyan fita daga cikin falonne kuma, yasa sauran yan uwansa dake zaune acikin falon suka dan kalleshi.

Daga waje kuwa Naseer ne ya kalli Rayyern din, hade da cewa.

 Hamma Rayyern mu shiga..

Bai gama rufe bakinsa ma baiyi ba, saiga Uncle Mustapha d in ya fito, fuskarsa dauke da yalwatacciyar murmushi ya soma takowa inda su Rayyern din suke.

Idanu Rayyern da kuma Ramadan suka Wan zuba mishi.

Kamar kuwa yanda suka zuba mishi idanu, haka shima ya zuba musu nashi idon, musamman akan Rayyern da kuma Riyyam, wani irin kallo yake musu mai dauke da mamaki, da kuma yanayi mai bayyana alhini., ciki kuwa harda fuskar Ramadan da yakewa kallon ya taSa sanin mai irin fuskar farin sani.

Isowar Kawu Mustapha n kusa da sune kuma yasa, duk tunanin da suke suka tsaya cak.
Hannu Rayyern ya mik awa kawu Mustaphan, wanda shima ya mik o masa nasa hannun fuska asake, sukayi musabaha.
Bayan sun gaisa da Rayyern dinne kuma, Kawu Mustapha n ya bawa su Ramadan da Riyyam-nsra hannu suka gaggaisa.

Cikin kuma yanayin dake bayyana zallar farinciki da mutum tawa, Uncle Mustapha n ya dubi Rayyern, kana atausashe yace.

 Masha Allah Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara barkanka da isowa.
Cikin ikon Allah Jiya iwarhaka munata fama da neman damar yanda za ayi muganka, sai gashi kuma yau kaida kanka ka tako k afarka izuwa inda muke, kai Masha Allah sannunku ku iso mu shiga daga ciki.

Murmushi Rayyern yayi kana anutse yabi bayan, mutumin da ayanzu kawai ya shaida da karamcinsa.

Su Ramadan ma rufa musu baya sukayi, Yayinda Riyyam ke tafiya yana k arewa katafaren gidan kakan abokin nasa kallo, wanda aka matuk ar k awatasa, kasancewar kuma gidan nada part-part da yawa ne, shiyasa ya zama kamar wani mention, Yayinda Kota ina dake cikin gidan, aka cikasa da shuke shuken korayen trees.

Isowarsu bakin kofar da zai sadaka da babban falon dake cikin gidanne, yasa Rayyern d an lumshe idanunsa, saboda hakan yaji harbawar da zuciyarsa keyi na sauk a, Yayinda zuciyar tasa kuma keyi sanyi.

Haka kuma yakejin wani irin abu na ratsa cikin tafukan hannaye da k afafunsa.

Kasancewar kuma shike bayan Uncle Mustapha dinne, yasa shiyayi na biyun shiga cikin falon, da girmansa yayi a had a manya manyan faluka guda biyu awaje daya.

Taka k afarsa ta dama da yayi acikin falon kuwa, shiya sanya shi jin wani irin sanyi na game duk jikinsa.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali, wanda yayi dai-dai da sauk e ajiyar zuciyar Ramadan da kuma Riyyam-nsra suma duk alokaci daya.
Kamar kuma yanda Rayyern din yaji azuciyarsa, haka suma sukaji.

Shigowarsu cikin falonne kuma, yasa gaba d aya ahalin Mai-nasara da y ay a da kuma jikokinsa dake kewaye dashi, duk suka d ago kai suna kallonsu.

Atake kuwa tsananin mamaki da tu ajjudi ya bayyana akan fuskar wasu manya daga cikin mazauna falon.
Inda suka kafe su Rayyern din da ido, basa ko k yaftawa, hakan yafaru ne kuma saboda wani tsananin kama da suka hango.

Kawu Mustapha ne yadanyi murmushi saboda Kallon da yaga y an uwannasa nayiwa su Rayyern, wanda kuma shima yasan dalilin da yasa y an uwannasa ke kallonsu haka.

D an juyowa yayi ya fuskanci y an uwannasa cikin kuma bayyana farin cikinsa yace.

 Manyan bak i mukayi, domin babban Doctor din da ya shahara, ya kuma yi kaurin sunane da kansa yazo dan duba Malam, Wannan shine Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.

Yakai karshen maganan yana meyi musu nuni da Rayyern dake tsaye.

Ajiyar zuciya suka sauke gabaki d ayansu tare kuma da had a baki wajen yiwa su Rayyern din iso.

Karasa shigowa cikin falon su Rayyern din sukayi, kana kuma cikin girma da mutumtawa Rayyern ya shiga bawa, manyan mazan dake zaune acikin falon hannu suka soma gaiggaisawa.
Kowannensu fuskarsa dauke da murmushi.
Bayan kuma sun gama gaisawa da Rayyern dinne, su Ramadan suma suka matso suka gaggaisa dasu.

Yayinda Rayyern kuwa ahankali ya sauk e idanunsa akan fari kuma kyakkyawan Dattijon dake kwance, wanda ayanzu ya soma d an yunkurin tashi, musamman saboda jin shigowar su Rayyern din.
Dattijo ne mai matuk ar kamala, mutumci da kuma haiba, haka kuma duk da yana da yawan shekaru da y ay a, amma hakan baisa tsufansa ya yawaita ba sabida hasken Addini da ri?o da ibada.

Idanu Rayyern yadan lumshe tare kuma da budesu alokaci guda, yana me ambaton sunan Allah da ya sauk ar masa da wata iriyar nutsuwa, acikin y an mintunonin da basu wuce 5 ba.

Su Uncle Mustapha kuwa ganin Malam Mai-nasara dake kishingid e akan lallausa kuma tattausan sofa, na kokarin tashi zaune ne, yasa cikin tsananin kulawa da kuma kauna suka taimaka masa ya tashi zaune.

Idanu Malam Mai-nasara din ya zubawa kyakkyawan matashin saurayin dake dan nesa dashi wato Rayyern.
Wanda kuma shima Rayyern din kallonsa yakeyi.
Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin sanyi, da kuma rauni mai tsananin gaske.
Ga kuma wani abu da yakeji na game dukkan mashigan ramin iska dake jikinsa.
Yanaji ajikinsa tamkar wata duniya ce sabuwa ya shigo.
Yayinda Ramadan da Riyyam dake bayansa suma sukejin thesame irin abunda Hamma Rayyern dinnasu yake ji.

Wanda kuma bawai iya sukad aine sukejin hakan ba, harda shi kansa Malam Mai-nasara, domin kuwa har izuwa yanzu ya kasa dauke idanunsa daga kan Rayyern.
Sannu ahankali kuma ya d aga hannunsa tare dayin alama akan Rayyern d in yazo kusa dashi.

Aikuwa Rayyern din kamar jira yake, cikin nutsuwar da ya zame masa jiki, ya matso kusa da Malam din sosai, hakanne kuwa ya bawa Malam din daman kamo hannun Rayyern d in ya rik e acikin nasa.

Nannauyar ajiyar zuciya mai sauti suka sau?e atare shida Rayyern d in, saboda had ewar hannayensu waje d aya shiya haifar da daidaiton bugun zuciyoyinsu.

Kai Dr. Rayyern ya d an rank wafar cikin kuma muryarsa mai tsananin taushi, dake bayyana nitsuwa da mutumtawarsa ga Dattijon mai tsananin karama a idanunsa yace.

 Malam barka da rana, ya ?arfin jikin naka?

Idanu Malam Mai-nasara ya lumshe tare dajin wani irin sanyi acikin zuciyarsa, wanda lokaci guda ta d auki soyayyar Rayyern din ta ajiye awani waje na musamman.
Tabbas fuskar Rayyern din ta ratsa shi, Yayinda ta kuma so tono masa wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya masu yawa.

Sake rik e hannun Rayyern din da kyau yayi, tare da cewa.

 Alhamdulillahi jikina da sauki, kaine Dr. Rayyern Basheer Muhammad Mai-nasara ko?

Kai Rayyern ya jinjina masa, tare kuma da cewa.
 Eh Malam ni ne Dr. Rayyern Basheer Muhammad

13 / 46