Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   3 / 46

6K to 9K   out of 135.1K words

gwatsaleta yace babu ruwanta sunfi kusa.

Wannan ne ya ?ara tsananta zubda hawayen ta.
A haka ta fara tattara mishi falon da gaba Waya ya birkitashi.

Shigowa yayi ya zauna yana mai Binta da ido, duk inda tayi.
Wani irin abu yakeji a kanta.
A hankali ya mi?e yabi bayanta lokacin da ta shiga Bedroom.
Da sauri ta juyo jin shigowarsa.
Gefenta ya matso fuska a murtuke hakan ne yasa bugun zuciyarta ya ?ara tsananta.
Har kana iya ganin yadda numfashin ta ke fita da yanayin tsoro.
Fuska ya kuma murtukewa.
Kana yace.
"Munafuka, sai kace da gaske haka kike tsoron maza, ji yadda kike tafiya ba bra kina wani karkakaWa ?irji irin ke gaki ?ar iska mai son maza ko?."

Idanunta ta rumtse da k arfi cikin kuma ?unan ran ?azafin da Yah Junaid ke jifarta dashi murya na rawa tace.
"A'a".
Cikin haWe fuska ya daka mata tsawa tare da cewa.
"Toh meya hanaki sa bra?".
Murya na rawa tace.
"Dr. Lukman ne yace in daina sa bra, sabida matsalar numfashin da Athsman Wina ke jamin. In nasa ya matse min ?irji sai numfashina yayi ta sha?ewa".

Wani irin dogon tsaki yaja tare da cewa.
"Ubanki zanci in baki dena raina min hankali ba, matse ?irjin da ?atti keyi bai sha?e numfashin ba sai saka bra ne zai cushe miki numfashin."
Fice min da gani!!". Ya k are maganar a tsawace.

Jin hakanne kuma yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye na zubo mata sabida raWaWin marin daya yarfa mata da zafin kalaman zargi da yake binta dasu.

A falo ta samu Mom da sauri ta faWa jikinta.
Cikin sakin sassayan kuka tace.
"Mom ki gaya musu wlh ni ba yar iska bace, Meyasa Mom Meyasa Ya Junaid ke jifana da mugayen maganganu, shifa yaya nane..

Jawo hannunta Mom tayi suka zauna bisa kujera, a hankali tasa tafin hannunta tana share mata hawaye cikin yin ?asa da murya tace.
"Na sani Jannart kuma Allah ya sani, ke ba ?ar iska bace. Yaushe ma kika samu sakewar rayuwar duniya kullum kina cikin takunkumi.
Ko ina zakije da masu gadinki.
Na rasa wannan masifar tsaron na menene kina girma ana ?ara killaceki kamar abun rashin gsky."
Cikin shesshe?an kuka tace.

 Mom shi Yah Junaid gani yake, su masu tsaron nawa dasu nake iskanci.
Daddy Kuma gani yake in ya cire masu tsaron da wasu zanyi iskanci.
Wlh na sani Mom bawai dan tsaron lfyata bane yasa Daddy ware min masu tsaro.
Shima zargina yakeyi ko Mom?".
Jin yadda numfashin ta ke fitane yasa mom gyara zamanta kana ta fuskanceta da kyau.
Allah ya sani tana son Jannart tamkar ?ar cikinta.
Amman duk yadda zatayi bata burge Alhaji Idi da Junaid, gani suke kamar so take Jannart ta lalace ne don ba ita ta haifeta ba.
Cikin kula da tausasawa u?ubar da suke shayar da ita tace.
"A'a Jannart Daddynku baya zarginki, shi ya bada masu tsaronkine sabida larurar ciwonki, kina bu?atar makusanci a koda yaushe, tunda abu kaWan ke tada miki athsman Win wanda kinga tun da yana nimoniya, kina girma yana canzawa ya ri?a har ya zama asman shiyasa yake tsananta kulawa a kanki.
Sabida abu kaWan ke tada miki shi.
Kuma Yah Junaid Winki yana sonki.
?an uwa, uwa Waya uba Waya ya wuce wasa.
Sun haWa da son da Mamanki zatayi mikine da tana raye".
Cikin zubda hawaye tace.
"Mom kin bani son da ya kamata uwa ta bawa ?arta, ni banyi maraicin kyakkyawan tarbiyar uwa ta gari ba.
Kawai dai basa so nane".
Cikin kafeta da ido Mom tace.
"Jannart ki yarda dani, tashi muje kici abinci".
Cikin nitsuwa tasa hannunta ta share hawayenta kana ta mi?e.
Dinning area suka nufa.
Suna zama Daddy ya fito da hakama Junaid da Abdul.
Nan suka zauna sukayi breakfast.

A hankali ta sauke numfashi ganin Junaid ya mi?e ya bar wurin.

Sai kuma ta Wan kalli Alhaji Idi Saleh Dakata.
Cikin takatsantsan da girmamawa tace.
"Daddy Ina son zanje gidan Aunty Rabi'ah akwai wani aikin da zamuyi a can".
Ido ya Wan zuba mata.
Ita kuwa da sauri tayi ?asa da kanta.
Tana tasbihi cikin ranta, da addu'ar Allah ya Waurata a kanshi.
Juyawa yayi ya fara sau?a kan steps Win tare da cewa.
"Kada ki daWe.
Kuma ?afarki ?afarsu Sunday."
Cikin sabo da hakan tace.
"Toh".
Kana ta mi?e ta nufi Wakinta. Mom kuma ta fara tattara kan table Win.

Wanka tayi cikin nitsuwa da kuma sauri-sauri.
Tana fitowa, ta zauna ta tsane jikinta kana ta busar da tattausan suman kanta.
Ta shafa mishi mayuka, sannan ta tubkeshi.
Mai ta Wan shafa kana ta Murja farar hoda, tare dasa man baki.
Sosai tayi kyau duk da bata cika kwalliya a fuskarta ba.
Wasu tattausan riga da wondo pallazo farare ?al ta zaro,
Sai wata doguwar riga budaddiya mai igiya a tsakiya.
pantie tasa, kana ta zira dogon wondon daya kasance yayi tightin fatar jikinta.
Dole sa bra baya cikin jadawalin rayuwarta sabida larurar ciwonta.
Sai dai takan sa rigunan su Wan matseta.
Rigar ta zura irin mai wuyanan nane wato, high neck, naWe wuyan tayi ta gyarashi.
Cib-cib rigar tayi mata a jikinta gwanin burgewa ?irjinta yayi cas a tsaye babu alamun ron?ofowa bare zubewa.
Lafaffen cikinta ya taimaka kwarai wurin bayyana tsayeyyun breast Winta.

Doguwar rigar kimono blue color mai Wigon fari-fari'n ta Waura saman riga da wondon, cib kuwa kimonon yayi mata ajikinta, inda kuma har ?asa yazo mata.
Igiyoyin dake sar?afe tsakiyan rigar ta kama ta Waure.
Hakan ya bawa tsakiyar rigar haWewa, sama can kan ?irirjin ta kuma gefe da gefen ya rufu har ya samu damar rufe nimples Win ta.
Sai kuma tsakiyan bai ida rufuwa ba.
Sai kuma can ?asa ta nan zaka gane riga da wondone a ?asan doguwar rigar farin mayafi rigar ta dauko tayi Rolling kanta fuskarta ta fito a ciki kamar sifili (0) a ciki.
Sosai shigar tayi masifar mata kyau.
Wanda kuma sune suturunta na yau da kullum wanda tafi so da jin daWin sawa, kasan cewar rigunan cikin masu taushine suna buWuwa dai-dai jikinta.

Turare mai sau?in ?amshi ta fesa, sanin sa mai tsananin ?amshin yana da illa ga baliga in zata fita da kuma lfyarta.
Wasu fararen takalma sau ciki masu taushi tasa.
Kana ta zari babbar wayarta kiran iphone11promax ta fito.

A bakin ?ofar shigowa falon tayi kiciSis da Mom cikin.
Yanayin sakin fuska Mom tace.
"Kai masha Allah Wiyata kinyi kyau".
Cikin yanayin jin daWi tace.
"Ngd Mom bari inje da wuri in samu in dawo da wuri".
"Toh hamzarta Wiyata, sai kin dawo".
Toh tace kana ta fita ta tafi.

Tana fitowa harabar gidan
Wadannan garadan marasa kan gado suka mi?e baki Wayansu.

A hankali ta matso kusa da Driver'n'.
Cikin kula yace.
"Jannart yau kuma ina zamu je, naga yau ba ranar aiki bane?".
Cikin jin daWin yadda dattijon ke mata mgn ta mutuntaka tace.
"Baba Ado, gidan Hajia Rabi'ah zamuje".
Marfin motar ya kama da nufin buWe mata, da sauri tace.
"Baba Ado ka bari zan buWe".
Murmushi yayi kana ya bude mata, ta shiga.
Suma sauran suka shiga sauran motocin suka tafi.

Suna isa gidan Hajia Rabi'ah.
Bayan sunyi parking ta nufi cikin gida su kuma suka zauna a waje.

Da sallama a bakinta ta tura ?ofar.
Da sauri taja da baya ganin Asiya dake fitowa.
Sai kuma ta shigo ganin taja gefe tana hararanta.
Da sauri tayi ciki jin Hajia Rabi'ah na cewa.
"A a Jannart kin iso ko.
Maza shigo daga ciki".

Cikin jin daWi ta shigo.
Ta zauna inda Hajia Rabi'ah ke nuna mata.
Cikin girmamawa tace.
"My Aunty Ina kwana".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah ya ?an tsaron ki".
Cikin yin gajeren murmushi tace.
"Gasu can a tsaye a bakin gate tamkar dogaran sarki".
Dariya ta Wanyi kana ta kalli wani Wan matashi dake zaune can bisa kujarar Dinning area tace.
"Toh Mahmoud ga Jannart Win ta iso.
Tunda ka?i bawa Asiya amsa ko Waya".
Da sauri ta juyo ta kalli inda aka kira Mahmoud.
Shi kuwa tasowa yayi ya nufo cikin falon yana mai cewa.
"Aunty naga kamar hasadace ke cinta, kuma ma bada ita nai wayaba.
Ita kuma wanna sai saiSi.
Kin san tun safe ina nan kin ajiyeni kamar mara aikin yi".
Cikin nitsuwarta tace.
"I'm so sorry. Ina kwana".
Gefe ya zauna kana yace.
"Wuni dai tunda 12 tayi".

Nan suka gaisa kana Jannart ta fuskanceshu da kyau.
Cikin sani makamar aiki tace.
"Yaushe jirgin Ethiopia zai diro Nigeria a wanne gari Waya Abuja ko Lagos ne?".
Murmushi Mahmoud yayi tare da cewa.
"Wato zaki nuna min ke yar jaridace, tuni kin fara tambaya da wayo.
Jirgi zaki tambaya ko shi?".
KwaSe fuska tayi tare da kallon Hajia Rabi'ah kana a hankali tace.
"My Aunty menene ma sunan nashi?".
Cikin zuba mata ido Hajia Rabi'ah tace.
"Iyeh wato ma har kin mance sunan nashi. Kin manta cewa sunan nashi ne kawai makaminki."
Cewar Hajia Rabi'ah.

Ita kuma Jannart takwara kanta tayi bisa kafaWa kana tace.
"Please my Aunty gaya min zan ri?e".

"Rayyern". Ta bata amsa a takaice.
Ita kuwa ido ta lumshe tare da fesar da numfashi can cikin zuciyarta tace.
*"RAYYERN! RAYYERN!! RAYYERN!!!* Ta maimaita sunan sau uku kana ta juyo ta kalli Mahmoud cikin nitsuwa tace.
"Mahmoud ranar yaushe zai dawo? Da wanne lokacin jirginsu zai iso daga Abuja ko Lagos zuwa Kano?".
Gyara zamanshi yayi kana yace.
"J....!


free PAGE .


=???
*TUBALI*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk i Biya 500 k aramin farashin na k aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna.

ACCOUNT NO 0661110170.

BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA

BANK GTBank

sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276.

*PLS TAKE NOTE BAND VTU*
kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's Win katin ki turo min ta whatsApp.

Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k aramin group kuma (500) kacal,
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y ay an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki=?O?
Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa.
*Tausayi, Sark ak iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, ri?on amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya*

Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala*

Za'ayi tsawon mako Waya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy*

=?O?

Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi ha?uri ba raini bane ko wulak anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, =?O???

*Sayan na gari maida kuWi gida sai kinzo*









By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: *TUBALI*

PAGE 3

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*FREE PAGE*
*?AN?ANO*
*NMETTARI enji men nfulSe*


"Jibi". Ya bata amsa a ta?aice yana mai kallon Kyakkyawar fuskarta.

Ita kuwa gyara zamanta tayi tare dasa hannu ta amshi cup Win ruwan sanyin, da Hajia Rabi'ah ke mi?a mata-ta ajiye shi bisa Stoll din ba?in glass dake gabanta.
"Nagode". Ta faWi cikin nitsuwa, sannan ta kalli Mahmoud dake bin fuskarta da ido.
Cikin yanayinta na nutsuwa da kuma bayyana zallan ajinta na y a Mace tace.
 Akwai tabbacin jibi zai dawo? Sannan ta Abuja ko Lagos zasu sau?a?".

Wayarshi ya zaro a al'jihun rigarsa yana mai lallatsata kana yace.

 In sha Allah jibi zasu dawo.
Dan last night muna tare da Deen ?anin Usman PA'nshi.
Yayi magana da yayan nashi kan jikin mamansu ya tashi, yaushe zasu dawo.
Toh nan Usman Win ke cewa jibi zasu dawo.
Iya abinda na sani kenan, sauran bayani kuma sai dai in tuntuSi Deen Win".
Ya ?are maganar yana sa wayar a amsakuwa yadda duk zasuji.

 Hello Deen ya Gida".
Cewar Mahmoud.
Deen dake zaune gaban mamansu wanda yanzu ya gama magana da Usman ne yace.
"Lfy lau Alhamdulillah Mahmoud".

"Yah jikin Mama".

"Alhamdulillah jiki da sau?i".
Ya bashi amsa yana mi?a mata maganin.

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Yah Usman Win yana dawowa ko?".
?an gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Eh to, zasu dawo, amman sai jibi fa kuma nan ma wata ?il in sun iso su kwana a Abuja wata ?il suda nan sai ranar jumma'a".
ya ?are mgnar da sanyi.

"Ayyah ba komai ai in dai jikin da sau?i, jumma'a kamar yaune Allah dai ya dawo dashi lfy. Ka gaida min Mama da jiki Allah ?ara ?arfin jiki".

 Amin Amin". yace kana sukayi sallama.

Katse kiran yayi tare da juyowa ya kalleta.
Numfashi suka sau?e ita da Hajia Rabi'ah.
Sai kuma tace.
"Alhamdulillah, toh Mahmoud ko zaka bani number Deen".
Da sauri yace.
"A a in fa yasan me kike bincika bazai saurareki ba".
Hajia Rabi'ah ne ta amshi zancen da cewa.
"Kada ki damu Jannart in sha Allah komai zai tafi dai-dai.
Shi Mahmoud Win shi zai rin?a samo mana bayani.
Tunda kuna da number n juna zaike miki bayani, ba sai kin fito kinzo nan ba, tunda fitar naki aikine mai zaman kanshi."
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"Toh shike nan My Aunty, Ngd Matu?a Allah ya saka da al'khairi".

 Amin Amin. tace
Tana mai gudun kada aikin ya bar hannun yarinyar tunda kowa ya ganta dai yasan bawai tana yin aikin dan neman kuWi ko suna bane, tana yine dan ra'ayin tane gashi du-du watanni huWu tayi da fara aikin kuma suna jin daWin mu'amala da ita, so dama sanyin da shirin yayi shiyasa aka canza wanda ke yinsa a baya.
Kuma da alamun tana matu?ar jin daWin aikin.

Kiran Salman ne ya shigo wayarta.
Da sauri ta amsa tare da karawa a kunne.
"Assalamu alaikum".
Tace cikin sassayan sautin ta.

Daga b angarensa kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Wa alaikissalam, Jannart kinbi diddigin Rayyern d in? Kuma wane lbri kika samo mana a kanshi? "

Cikin yarda da kai tace.
"Duk motsinshi na cikin tafin hannuna!".
Dariya mai sauti Salman yayi.
Hakama Hajia Rabi'ah da Mahmoud.
"Karsashi nki da ?arfin guiwarki akan aiki yana burgeni Jannart .
Cewar Salman.
Cikin sau?e numfashi tace.
"Toh ba doleba Salman, tunda naji ana shirin korata, ai sai inda ?arfina da hikimata suka ?are".

Cikin wasa yace.
"Ke har wani ?arfi a garreki da dai kin tsaya a hikimar na yarda".

Murmushin daya sanya beauty point Win ta lotsawa tayi.
Haka dai suka Wan tattauna batun bayan ta mishi bayanin abinda ta ji kan dawowarshi.

Saida tayi sallan azahar ne kuma ta fito suka nufi gida.

A kan hanyarsu ta komawa ne, Baba Ado driver'nta ya Wan juyo ya kalleta cikin kulawa yace.
"Jannart yanzu dai ciwonki da sau?i ko?".
Numfashin ta Wan fidda kana a hankali tace.
"Alhamdulillah da sau?i dai zance, amman yana yawan motsa min a kwanan nan kamar yana son tashi."
Cikin tausayawa yace.
"Toh amman har yanzu babu wani maganin da ake baki sai allurar da akeyi duk watan ne?".
Kai ta gyaWa mishi tare da cewa.
"Eh".
Numfashi ya Wan fesar kana yace.
"Allah ya sau?a?a yasa zakkan jikine al'farmar Annabi da al'?ur'ani".
Cikin jin daWi tace.

 Amin Baba Ado nagode!".

A can Ethiopia birnin Addis Ababa, kuwa.
Riyyam-nsra ne tsaye gaban wayarsa daya tsaida.
Rawa yakeyi da murmushi a fuskarsa.
Sai kuma ya kalli gefensa.
Wata kyakkyawar budurwa wacce a ?alla suyi sa'anni.
Murmushi yakeyi cikin harshen Hausa yake cewa.
"Jibi iwar haka ina hanyar Nigeria, su Zayton kuma sai dai ayi ta aikin zumbura baki.
Fan's ku gani, wai kishi takeyi dani".
Da sauri ta kai mushi bugu tare da matso

3 / 46