Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   32 / 46

93K to 96K   out of 135.1K words

yasa suke fita wasu k asashwn suje su fara aiki Acan, ko kuma kowannensu saiya zaga gefe yaje ya bud e asibitin kanshi, saboda baisamu yanda yake so a gwamnati ba, wannan dalilin yasa ayanzu asibitocin gwamnati suka lalace suka zama kara zube,, Domin anriga da ancire Tubalin abunda aka gina asibitin akai haka yasa duk mai ?arfi da yar wadata bazaibi ta kan asibitin gwamnatin ba, wanda kuma da al'ummar ?asa aka ginasu.
Sannan yana da matukar muhimmanci ga iyayen yara suke kula da tsabtar jikin raya da muhalli da abinda zasuci domin shine babban rigakafi.
Ya k are maganan yana me gyara zaman necktie din dake wuyansa.
Sosai yayi masifar kyau yadda yake dan jujjuya fararen yatsunshi

Inda Jannart kuwa ta ci gaba da cewa.

 To Doctor yaya za ayi agyara matsalar Government Hospitals din domin in ?antasu ta yadda al'ummar ?asa zasuje garesu da kekkyawan ya?ini!?.

Dan muskutawa yayi still kuma cikin rashin tsoro ko fargaba cikin ya?inin da Kekkyawar manufa yace.

 To Da farko dai asibitotin gwamnati abunda zai gyarasu abu maisauki ne!? .
Da sauri ta Wan fuskanceshi tare da cewa.
 Duk da lalacewar da sukayi gyaran mai sau?in ne? Ta yaya ko kuma ta ina gyaran zai fito da sauki!? .
Cameras din ya Wan kalla kana ya gyara zamanshi tare Waura kafa Waya bisa Waya cikin masakaicin amo yace.
 Idan har gyara akeso ta yadda zasu in ?anta tofa dole daga kan, Shugaban k asa, Governors, Ministers, senator's har zuwa kan ciyamomin kana kama daga Sarki, Waziri, Galadima, Wambai, Chiroma, Durbi, Garkuwa, ?an buram, Majidadi, Ma'aji, dama duk wasu masu fad a aji, na siyasa da masarautun gargajiya. suyi kokarin daina zuwa asibitotin kudi, ko fita kasashen waje Dan duba lafiyarsu, su tsaya su ingata asibitotin Gwamnati, ta hanyar dasu kansu asibitotin zasuna basu Kekkyawar kulawa,
Ya zama asibitin da Sarki zaije.
To shi fadawan sarki zasuje.
Kana asibitin da shugaban kasa zaije ya zama shine na talakawa, ta hakane zai sa shugabanni su san halin da asibitocinsu suke ciki, da in?ancin likitocin da kayan aikin.
Haka zai sa a kula da in ?ancin asibitocin.
Domin duk wani asibitin gwamnati matukar akwai ingantattun Doctor s da kayan aiki da watar tsabtacewa.
Toh dai-dai yake da duk wani asibitin kudi, hakanne kuma zaisa asibitotin kudin su dakushe, su durkushe.
saboda yawnacinsu bawai anginasu Dan taimakon al umma bane, anginasu ne kawai saboda neman kudi irin na yaki haram yaki halal, tayanda talaka bazai tab a amfana dasu ba sai dai su cika aljihunsu.
Da sauri Jannart ta juyo ta kalleshi.
Ido cikin ido sukayi da juna,
Bakinshi ya taSe tare da yimata wani irin munafukin harara, hakane yasa tayi saurin yin ?asa da kanta
Kai ta jinjina, cike kuma da gamsuwa da kalaman nasa tace.

 Tabbas maganarka tatafi Kan hanya mai kyau, sai-dai kuma amma baka ganin yin hakan zai dakushe mutane da dama, musamman ga masu privet hospital kamar yanda ka fad a!!!.

Kansa ya d an girgiza, sannan kuma akaro na farko da tun zamansa awajen ya dago kansa da nufin ya kalleta da kyau dan tambayar da tayi masa.
Saidai ko secan daya bai dauka yana kallontan ba yakau da kansa gefe.

In don t care manner yace.

 Hakan ba wata matsala bace ai, Domin bani da yakinin cewa yin hakan zai tauye musu hakkinsu .
Da sauri ta kuma cewa.
 Toh kuma kake bada shawara a rushe asibitocin? .
Wani irin kallo ya Wan watsa mata.
Sabida ta mishi tambayar cikin gajin ha?uri irin nasu na ?an jaridu.
Dan bata tsaya taji ya dasa Ayaba.
Koda yake haka suke.
Yan jaridun suna jin daWin jefowa mutun tambaya kamar sau?awar aradu ko kuma titsiye.

Cikin tsare fuska yace.  Dama meyake sawa su bude nasu asibitotin? .
Ya mata tayarma tare da tsareta da ido.
Yar-yar haka taji tsikar jikinta na tashi.
Haka yasa da sauri ta kauda kanta gefe.
Shi kuwa kai ya jin jina tare da cewa.
 Baki sani bako?
To bari in gaya miki...
Ya kare mgnar yana mata hararan ?asan ido kana yaci gaba da cewa.
 Dama rashin samun isasshen abunda zasu rufawa kawunansu asirine, saboda sometimes acikin asibitotin Gwamnatin, gwamnati bata biyansu al'bashi akan kari, baya ga haka kuma bata basu isassun al'bashin da zasu dauki nauyin iyalansu sabida gwamnatin tayiwa malaman jinya dana makarantu ri?on sakainar kashi Alhamdulillah gwarama wannan gwamnati da muke ciki.
Duk da haka ana bu?atar ?ari.
Domin duk lokacin da Gwamnati ta fara biyansu isassun al'bashi, To ba wani abu da zaisa suje su bude privet Hospital toh ko sunje sun buWewama wa zai je musu in dai asibitocin gwamnatin nada inkanci , Domin ak asarnan ba yawan asibiti muke da bukata ba, ingancinsu kawai shine abun buk atar mu, tayanda talaka da maikudi da fulanin daji zasu samu gamsashshiyar kulawa, batare da nuna wani banbanci ba!!!.

Ajiyar zuciya Jannart ta sauk e, kana kuma cikin yanayin nutsuwa tace.

 Mungode sosai Dr. inafatan kuma Gwamnati zataji shawarar daka bada kuma tayi aiki dashi, yanzu kuma zamu shiga babi na biyu. wanda ya shafi b angaren kasuwanci kafin mu dawo nan a likitance.

Yah Salam shine abinda ya faWa a ransa.
Sabida ya lura yau bakinshi sai yayi tsami sabida magantuwa da wannan fitinenneyar yarinyar take sashi.
Kamar a tsakiyar kanshi yaji ta kuma cillo mushi tambaya.
 Shin Dakta wacce irin shawara zaka bayar, agame da yanda sha anin saye da sayarwa ya zama acikin k asarnan, misali ta yanda ayanzu kayan abinci yayi tsada sosai, akullum wasu daga cikin yan kasuwa k ara farashin kayansu suke, rayuwa tayiwa talaka tsada, manyan y an kasuwa da kamfanoni sun had e kai da baki waje daya, Koda yaushe farashin kaya hauhawa yake, tayaya ne za a samawa al umma sauk i, musamman manoma, wanda sune ma suke noma abincin amma kuma Idan ya shigo kasuwa sai yazo yafi karfinsu, shin wacce shawara zaka iya bawa manoma?.

Numfashi ya dan fesar ta bakinsa, saboda yanda yaji labbansa sun soma gajiya da yawan motsasu da yake.

Hakanne kuma yasa batare daya dago ya kalli ko cameran ba, saidai atausashe yace.

 Shawarar da zan iya bawa Manoma itace, duk wani manomi Idan har ya noma abunda zaici, To kada yayi gangancin saidawa, har sai ya tabbatar daya ware ishashshen abincin da zai isheshi, har na tsawon wata shekarar da zai sake noma wani abincin, kafun nan sai yazo ya saida wanda zai sayar, saboda gudun kada ayi gaban mai ha?ar rijiya. kai ka noma ka gama shan wahala, sannan kuma ka tattara ka sai dashi lokacin da yake araha, bayan y an wasu watanni sai yayi tsada, ga kuma wanda kake dashi ya riga ya k are ga damuna ta sako sama ruwa ?asa ruwa, fita nemowar ma wata rana sai ya gagara, kaga kenan nakan daka saida shi zaka sake zuwa ka saya, akan farashi mai masifar tsada, kenan Kai Manomi kaine ka wahala a banza.
Sannan kuma ya kamata manyan kamfanoni su dinga tausayawa talakawa, su daina yi musu irin wannan hawan k awaran, zuwa su sai abincin manoma tun yana gona basu shigo dashi gari ba su kuma manoma ku farga da wannan sagegeduwar da akeyi muku.
Sannan kuma su manoman kansu, su daina sayarwa masu manyan kamfanoni abincinsu tun yana gona, saboda wasu tun abunda suka noma yana yabanya suke saida shi, atunaninsu ko da ace abun da suka noma din baiyi kyau ba ko sanadin fari ko tsuntsaye ko kwari ko tsutsa, su dai sun samu kudi, da yawan mutane basu san al'barkar dake cikin kayan gonansu ba, saboda haka yana da kyau, ka dinga girbe abunka kana gyarawa da kanka, ka kididdige abinda ka samu ka ware na bu?atunka kafun ka mik ashi ga wasu, sannan kuma duk wani manomi yayi kokarin saida abincin daya noma, akan farashi mai kyau, saboda ko yaya guminsa ya keci.
Domin shi kadai yasan wahalar daya sha wajen noma ta, sannan yanzu Idan akayi dubi, gaba daya manoma da talakawa su suke shan wahala, musamman Idan aka shiga cikin damuna, haka komin ruwa da iska zasu tsaya neman abunda zasu rufawa kansu asiri suyi noma dan ciyar da al'umma duk kudinka fa, in manomi baiyi noma koda kuWin ka bazaka samu abincin ba, shin zakaci kuWin naka ne!!!?. Sannan ku kuma y an kasuwa da kamfanoni masu karawa kayan abincinsu kudi, ba komai kuke ciba face *RIBA* haramtacciya, wanda kuma kowa yasan hakan ba abubane mai kyau bane, ga wanda suke sayan abinci su b oye sai yayi tsada su fito dashi, suma duk Allah naganinku, kuma Allah da kansa baya tausayawa wanda baya tausayin na kasa dashi.

Kai gaba daya mutanen dake boye abayan cameras din suka jinjina, hatta MD da kansa shima ya samu cikakkiyar gamsuwa da bayanan da suka fito daga bakin Dr. Rayyern din.

Ba kuma a iya cikin tv station din ba, har acikin gaba daya k asar tamu, mutane da yawa dake Kallon Live Program din sun samu cikakkiyar gamsuwa, Yayinda kalaman Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din ya ratsa zuk atansu, ciki kuwa harda mafiya yawan manoma da suke kallon shirin, sabida Tashar Arewa 24 TV tayi zarran birni da ?aune suna kallonta maza da mata manya da yara.

Adai-dai lokacin kuma Abba Kabir zaune yake agaban tv yana Kallon shirin, shi kansa ya gamsu da kalaman Dr. Rayyern din, saidai kuma sosai zuciyarsa ta cika da tsananin mamakin, ganin da wanda Jannart din ke hira yau.

Acan babban falon gidansu Jannart din kuwa, Alhaji Idi Sale Dakata, Dr. Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa ne, zaune sun zubawa babban TV plasma din dake cikin falon idanu.

Wanda kuma yanzun akayi musu kira na musamman, akan su kunna tashar Arewa24 Dan Ganin hirar da akeyi da Dr.Rayyern din.
Hakance kuma ta kasan a wurare da dama yadda wasu ke kiran wasu manyan ?asar suna shaida musu su kunna tv tashar Arewa 24 TV suga program Win da akeyi da Dr Rayyern Mai-nasara.

Jin abubuwan da Rayyern din ya fad ane kuma, yasa Alhaji Abdu Tababa yin k wafa, kana cikin takaici yace.

 Amma dai wannan yaron anyi d an iska, mai tsaurin ido, kujifa abunda yake fad a, wai gwamnati ta rushe asibotin kudi ta inganta nata, Lallai yaron nan bashi da tsoro.

 To shi nashi asibitin na uban meyene, shegen yaro mai jajayen kunnuwa.

Cewar Dr. Lukman da yakejin kansa kamar ya kurma ihu yayi fiffige yaje ya sha?o wannan yaron.

Yayinda Alhaji Idi Sale Dakata kuwa ya rumste idanunsa, saboda shi ayanzu ko son Ganin yaron bayayi, hasalima gaba daya tunaninsa ya tafi ne akan yanda zai ga bayan Rayyern din, saboda al'?awari ne da yayiwa kansa cewar saiya b atar da yaron daga Doron k asa.

Acan cikin tashar ta Arewa24 kuwa, Jannart ce ta sake gyara zamanta, batare kuma da ita ma ta d ago kanta ta kalli Dr. Rayyern MAI-NASARA dinba tace.

 Toh Doctor mu dan koma baya.
Kaba da shawara akan cewar aduk ar da asibitotin kudi, a tada na Gwamnati, ta hanyar zuba ingantattun likitoti da kuma kayan aiki, To irinku fa masu asibitotin kudi yaya zakuyi kaida ire-iren ka masu privet Hospital's, kodai kuma zaku dawo aiki a asibitotin Gwamnati ne! Ku watsar da naku asibitocin!!?.
Cikin gamsuwa da yarda da kai yace.
 Kwarai kuwa, saboda ai hakan bawai gazawa bace, Indai muka had e hannu da Gwamnati dan musamar da ingantaccen kulawa ga al umma, To mu hakan kamar alkhairi ne agaremu, ba kuma najin hakan zai tauyemu ko ya ragemu da wani abu.

Ya fad a atak aice saboda ya fara gajiya da amsa tambayoyin yarinyar mai shegen baki cai-cai surutu tuni yawun bakinsa sun kafe.
Hannunshi yasa ya Wan shafa sajenshi har zuwa kan lips Winshi sabida ji yayi kamar bakinshin yayi tsawo ne da surutu.

Jannart kuwa, again cikin sanin makamar aikinta tace.

 Amma kamar baka goyon bayan duk wani privet hospital, in na fahimceka.
Kuma naga kaima kana da naka hospital din, wanda kuma bana gwamnati bane, ya akayi to hakan ta kasance? meyasa baka had a hannu da Gwamnatinba!? kun ingata Koda asibiti daya ne!!!? .

Wannan Tambayar ta saka duk magautan
Dr. Rayyern Mai-nasara dake Kallon tv suka saki Murmushin mugunta, saboda atunaninsu yarinyar ta kawosa makura inda bazai iya amsa tambayoyin nata ba Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.
Saida yaji tamkar ya shiga TV ya goya Wiyar tasa Jannart, sai yakeji kamar dan su tayi mishi wanna tambayar dan ta kure musushi.
Dr Lukman kuwa hannunshi ya dun?ule tare da jinjinawa Jannart harda yimata alamar kiss dan masifar daWi.

Ita kuwa Jannart batama san sunayi ba, kuma bada wata manufa tayi tambayarba sai dan dacewar hakan tunda tasan yanada asibitin.

Shikuwa Rayyern ko ajikinsa baiji wani abu ajikinsa dangane da tambayar da Jannart din tayi masa ba, hasalima Dan gyara zamansa yayi, cikin kuma kwarin guiwan da ako yaushe yake tare dashi yace.
 Banyi karatun likita Dan yin aiki akarkashin wani ba, asali Tubalin karatuna shine Idan na kammala na raya asibitin, dake gine tun kan zuwata duniya.
saboda amfanar al umma, bawai iya mai kudi ba kawai harda talakawa, saboda babu wani wanda, asibitin Mai-nasara Hospital yafi karfin zuwansa, koda kuwa bashi da karfi, Mai-nasara Hospital muna da foundation na taimakawa marassa karfi dashi mukeyin dukkan taimakon daya dace, sannan kuma Mai-nasara Hospital bawai irin asibitotin nan ne da kowa ya sani ba, Ina da confidence akan Hospital dina, ako ina kuma zan fada batare dajin na fadi ba daidai ba!!!.

Kai Jannart ta jinjina, saboda ayanzu kam amatsayinta na y ar jarida ta gamsu da duk kalaman mutumin, musamman da ta fahimci with full confidence yake magana, ba irin na wasu mutanen ba, da mafi yawancin maganansu Kame kame da kuma k aryane.
Domin sometimes ma suna fad an karyane Dan su kare kawunansu daga titsen yan jarida.

Daga can gefe kuwa, Asiya ce dake tsaye take ta aikin bankawa Jannart d in Harara.
Yayinda takejin wani irin kuna da radadi acikin zuciyarta, Lallai Tabbas taso ace itace ta samu wannan damar, taso ace yau itace akan stage din tare da mutumin da kyau, nutsuwa da kuma haibarsa suka matuk ar tafiya da hankalin ta, kana kuma mutumin da take ganin cewa, samun daman magana dashi ma wani matakin nasara ne.

Kamar kuwa yanda Asiya ke jin tukukin bakinciki acikin zuciyarta, haka ma Dr Lukman, yakejin kamar ya shiga cikin tv n ya shak o wuyar Dr Rayyern.
Abunda yasan bazai taba samun daman aikatashi ba a gaske kenan.

Kallonsa ya mayar gasu Alhaji Idi Sale Dakata, cikin takaici yace.

 Lallai wannan Dr Rayyern din shege ne, ko ta Ina so yake ya tauyeni, bakinsa baya tab a mutuwa, kowacce tambaya akwai amsarta acikin kansa.

Murmushin daya fi kuka ciwo Alhaji Idi Sale Dakata n yayi, cikin takaicin daya lullub e zuciyarsa yace.

 Nan kusa wannan bakin nasa bazai sake motsawa ba, wannan alk awari ne na daukawa kaina.

Murmushin Jin dadi Dr Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa sukayi, saboda sanin hali irin na Alhaji Idi Sale Dakata da sukayi, Domin sunsan duk abunda yace zai aikata saiya aikata Tabbas.

Ab angaren Gidansu Rayyern kuwa, Abba Mamy, Ramadan da kuma Riyyam-nsra ne zaune afalo suna kallon shirin, gaba daya sun bada hankalinsu akan shirin, musamman ma Abba, da tunaninsa ya rabu izuwa wani waje na daban.
Kallon Rayyern da kuma yarinyar da takeyiwa Rayyern din tambayoyi yake baya ko k yaftawa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin abu na daban.

Su Ramadan kuwa Hamman nasu suka tsurawa ido,suna mai jinjina kawunansu saboda irin amsoshin da Hamman nasu ke bayarwa, yana matukar ratsa zuciyarsu, acikin zuciyarsu kuwa babu wanda bai yaba da irin kyawun yarinyar da takeyiwa Rayyern din tambayoyi ba.

Jannart kuwa, akaro na barkatai ta d ago ta kalli camera s din dake haska su, mike din dake gefenta ta gyara, tare da cewa.

 Kamar dai yanda kuka sani, ayanzu zamu bud e layukan wayoyinmu saboda, masu kira.
Dan fadar ra ayoyinsu da tambaya, ga numbar layin namu kamar haka...
Tana gama fad an numbers dinne kuma ta kunna wata waya mai kaman telephone dake aje agabansu, kan wani had add en table.

Aikuwa kaman jira ake sukunna layin saiga kiraye-kiraye suna shigowa.
Wanda manyan mutane-ne suke kiran.

Numfashi ta Wan fesar tare da gyara zamanta.
Kana ta Wan kalli wayar da wani kiran ya kuma shigowa tun kan ta ajiyeta.
Picking call din Jannart tayi, tare kuma da latsawa tasa wayar a hands free.


Cikin zazzakar muryarta tace.

 Assalamu Alaekum.

Daga can b angaren aka amsa mata, da murya irin ta manyan mutane.

Jin hakanne kuma yasa ta cewa.

 Barka da shigowa filin bakon mako.

 Yauwa Barka dai .
Aka faWa daga daya sashin cikin girma.
Ita kuwa Jannart lumshe idonta tayi tare da cewa.
 Ko zamu iya sanin waye akan layi?.

 Sunana Alhaji Abubakar Ginsau S.A protocol na gwamna, nakira ne kuma Domin na jinjinawa babban Bak o DR. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, agame da maganganu masu amfani daya fad a, Insha Allahu kuma maganan zata isa ga kunnen way anda ya kamata suji, sannan muna godiya k warai matuk a, da irin shawarwarin daya bayar.

Kai Jannart ta jinjina, tare da dan satan Kallon Dr Rayyern din, wanda ya kauda kansa gefe, kamar baiji ana yabonsa ba.

 Girman kai rawanin tsiya.
Tafad a acikin zuciyarta, Yayinda afili kuwa cewa tayi.

 To S.A protocol muma godiya muke sosai, sannan bakon mu Dakta shima yana godiya.

Daga haka kuwa kiran S.A din ya katse, wani kiran kuma ya sake shigowa.

Cikin tashin hankali Dr Lukman ya mik e tsaye, tare dasa hannunsa ya dafe kansa, zuciyarsa cike da takaici yace.

 Lallai wannan yaron ya shallake duk wani tunani na, ba a banza ba ake kiransa da Mai-nasara ba, tunda gashi yayi sara akan gab a, daga maganansa har S.A da kansa ya kira, ya kuma shaida cewa maganar zata tafi har wajen governor, wannan wanne irin Dan iskan yaro ne? Mai sa'a .
Cikin tsananin takaici tsana Alhaji Idi Saleh Dakata ya fesar da numfashi tare da cewa.
 Ai yamafi Dan iska wannan yaron da kake gani Dr

32 / 46