Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   4 / 46

9K to 12K   out of 135.1K words

?wallar idanunta, tana faWin
"Mammy! Mammy!!".
Wata kyakkyawar matace mai Kekkyawar sura da jiki da shiga ta kamala, wacce kyan surarta ya iya boye ainihin shekarunta, ta fito daga cikin wata ?ofar da fuskantar inda ya kafa wayar tashi.
?an gudu-gudu da tsalle-tsalle yake yana zagaya parlon Zayton na biye dashi a baya.
Da sauri yayi tsalle tare da Wan sakin ?ara yace.
"Ohh Mommy".
Jin ta Wan sa hannu ta bugi ?eyarshi.
Tura baki yayi tare dasa hannunshi ya shafa ?eyar yana mai zazzarewa Zayton ido.
Abin gwanin ban dariya da ka gani kasan akwai Kekkyawar sha?uwa, ?auna, tausayi, da son juna.
?auke wayar tashi yayi ya sake video a shafinsa na TIKTOK.
Kun san matsalar su kenan ?an TIKTOK duk abinda zasuyi ko sukeyi sai sun nunawa duniya, More Especially irin Riyyam-nsra da yayi shuhura yayi zarra da dubban dubatan masoya mabiya, musamman a cikin kwanakin nan da yai mgn da Hausa ya janye mana hankalin matasan Nigeria, domin kuwa ayanzu followers d insa harsun d arawa two million.
Gane abin da yayi dinne kuma yasa. Mammy matsoshi da kyau ta kama kunnenshi ta Wan matse.
?ara ya kuma Wan saki, wanda yasa Zayton tuntsirewa da dariyar jin daWi tana Waga mishi gira.
Ita kuma Mammy cikin Wan faWa tace.

 Wato kai Riyyam baza ka taSa canzawa bako, duk motsinmu sai ka bazamu a duniya? Kai kam inaga kana gab da nuna duniya yadda kake kashi ma ko".
Hannunshi yake Wan yayyarfawa tare da cewa.
"Afwan Yaah Mammy na tuba, wayyo Hamma Mammy zata tsinke min kunne".
Dariya Zayton tayi tare da cewa.
"Zai aikata fiye da hakama Mammy ja kunnen da kyau".
Hannunshi ya kai ya bugi hannunta tare da cewa.
"Yarinyar nan ki shiga hankalinki fa".
Fuska ta haWe tare da cewa.
"Waye yarinyar yaro in ka manta in tuna maka nice babba 15 minute nake baka, kaga kuwa dole ace da mijin iya baba, dan 15 minute ba 15 second bane".
Sosai Mammy ta saki murmushi suna matu?ar sata nishaWi da Webe mata kewa, da danne mata duk wani ?uncin rayuwa, Especially in suna faWa kan girma.
Zayton son girma kamar gyambo, 15 minute da take bashin nan ji takeyi kamar shekaru goma sha biyar take bashi.
Gefe ta zauna kana suka zo suka sata a tsakiya.
Cikin sakin fuska ta shafa kan Riyyam-nsra tare da cewa.
"Zoh nan autana".
Gwalo yayiwa Zayton tare da Waura kanshi bisa cinyarta tuni kuma ya sake haWa video.
Murmushi yakeyi yana yiwa Zaiton signal tare da cewa.
"Mammy asamin al'barka".
Da sauri itama ta sako kanta tare da cewa.
"Mammy ai nice mace, dan haka ya ri?e girman ya matsa ni in kwanta".
Cikin yin ?asa da murya Mammy tace.
"Ya isa haka ku bari, Dida na bacci kada ku tada min ita".
Toh sukace dan yadda tayi mgnar ba wasa.
Bayan ya saki wannan video Win ne kuma.
Ya gyara zamanshi ya fuskanci Mammy da kyau jin tana cewa.

 Riyyam sam hankali na. baya kwanciya da wannan rawan kan naka! Ina jin tsoron kayi nesa dani, gaba Waya ka juye ka zama Wan nanaye, ka zama tamkar mazari duk inda kake sai rawa, sai wa?a, sai haWa comedy duk inda kake waya na hannu, kai kaWai a ganka kana dariya ko kana kuka ko kana haWa fuska ko layi, kai gasu nan dai barkatai, ka zama Wan Film a fili ka rubuta lbri ka tsara ka bawa kanka umarni kayi shirin.
Ga Wan karen yawo yau kace zaka tafi waccar ?asar, gobe kace zakaje waccar gashi ka zama babu sirri duk inda kake an sani, shiyasa nake jin tsoron zuwanka Nigeria duk inda kaga mata sai ka bisu da ido".

Da sauri ya gyara zamanshi cikin nitsuwa kamar ba shiba yace.
"Mammy babu komai sai al'khairi, ki yarda dani bana wani mugun abu, in ke bakya gani na ai Ubangijin talikai daya busan numfashin yana ganina".

Uhum tsakanin uwa da Wa kenan ya gane cewa tana zargin shi ne ko tana tsoron taSarSarewar tarbiyarshi.
Cikin sau?e nannauyan numfashin tace.
"Wlh badon dole ba, bazaka jeba, amman ba komai Allah ya kaika lfy ya dawo da kai lfy.
Sai dai dole ka nitsu ka dena wannan rawan kan".

Hannunshi yasa ya kame kanshi kana yace.
"Toh Mammy na dena".
Murmushi tayi hakama zaitun.

Washe gari ranar Laraba, Kano Nigeria.

Cikin bacci taji numfashin ta, na fita a cushe, kana tana sha?an zazzafan ?amshin turaren sa mai masifar ?arfi da tafiya da numfashin ta.
Idonta ta buWe cikin wahalar numfashi.
Da sauri ta ida buWe su duka tare da fisgo numfashin ta a wahalce.
Sabida ganin Yah Junaid da tayi sunkuye a kanta hannunshi na kan ?irjinta.
Wani irin tsuma da karkarwa jikinta ya farayi, da azaban ?arfi.
Cikin tsananin tsoro da razanin ta yun?uro zata tashi, tare da furta "innalillahi wa innalillahi raji'un."
Wani irin azabebben tsoro firgita kaWuwa da gigitane suka dirar mata lokacin Waya jin yadda yasa hannunshi ya matse ta tare da murtu?e fuskarshi.
Cikin tsananin rawan jiki take zaro ido murya da baki na rawa tace.
"Innalillahi Wa inna Ilaihirraju un Y... Ya... Yah... Juna..Junaid, me haka!!

Wani irin masifeffen kallo ya watsa mata, tare da kai hannunshi duka biyu kan breast Winta, yayi musu wani irin masifeffen kamu wanda yasa ta saki wani irin gigitaccen ?ara, lokaci Waya kuma numfashin ta ya fara off and Dawn, ciwonta na gab da tashi.
Shi kuwa Junaid wani irin sanyi yakeji a ransa tare da rumtse tafin hannunsa.
Mom kuwa dake Wakinta, ita da Abdul cikin razanin jin sautin muryar Jannart ta mi?e tsaye jiki na rawa, ta fito falo.
Dai-dai lokacin kuma Jannart Win ta fara wani irin fiffizgewa sabida numfashin ta dake shirin barin gangan jikinta.
Wata iriyar fitinenneyar zufa mai cike da zafi, ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.

 Hahhhh! Uhhhhhhhh!! Fuhhhhhhhheeeeyyyy!!! M...Mom!"
Ta fuzgo maganar da ?arfi lokaci daya kuma numfashin ta ya dena shiga sai fifita.
Jiki na rawa Mom ta kutsa kanta cikin Wakin nata.
Shi kuwa Junaid wani irin fitinenne abu yakeji yana tsirgar masa.
Hannunshi ya kirjinta. Tare da yiwa breast Win ta wani azabebben ri?on da saida yaji.
Gamsuwa shaiWan cinsa.
Kana ya juya ya nufi ?ofar fita.
A bakin ?ofar sukayi kiciSis da Mom.

Wani irin mugun kallo ya watsa mata.
Ita kuwa Mom wani irin kallon tuhuma take binshi dashi.
"Mchewww".
Taja wani dogon tsaki ganin bazai bata hanya bane yasa ta matsa gefe.
Wucewa yayi tare da cewa.
"Sai kiyi ai".
Ita dai bata bi ta kanshi ba, ta wuce cikin Wakin.

A gigice ta nufi kan gadon tana kiran ta.
"Jannart! Jannart!! Jannart!!!".
Ta ?arisa kiran sunanta a gigice tare da hawa kan gadon ta jawota jikinta tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Abdul! Abdul kazo".
Da gudu Abdul ya nufi Wakin sabida dama yana falo Juinad ne ya hanashi shiga.
Cikin ruWani tace.
"Abdul kira min Daddynku. Ka gaya mishi jikin Jannart ya tashi".
Da sauri yace.
"Toh Mom amman bari in fara kiran Dr Lukman".
Ya ?are mgnar yana kara wayarshi a kunne.
Ita kuwa Mom sai jijjiga Jannart daketa kokuma da numfashin ta takeyi.
Cikin rauni Abdul yace.
"Assalamu alaikum. Daddy".
"Na'am Abdul ya akayi ne?".
Alhaji idi sele Dakata dake zaune a Office nashi Barrister Kabir Saleh Dakata na zaune a gabanshi.
Ya amsawa Abdul da kulawa.

 Daddy jikin Jannart ne ya tashi, na kira Dr Lukman kuma baya Wagawa".
Da sauri yace.

 Innalillahi Bari in kirashi yanzu-yanzu".
Ya ?are mgnar da katse kiran.
Cikin kula Barrister Kabir Dakata yace.
"Yaya lfy kuwa? Jikin Jannart ko?".
Cikin damuwa yace.
"Eh".
Mi?ewa tsaye yayi tare da cewa.
Bari inje mu tafi asibiti".

Tuni kafin yayi wata magana ma ?anin nashi ya fita.
Abdul ya kuma kira tare da cewa.

 Ga Abbanku na zuwa da likita".
Toh yace kana ya katse kiran.
Shiru yayi yana nazartar irin son da ?anin nashi keyiwa yaranshi, Especially ma Jannart yana mata wani irin so na musamman.
So na da ban a cikin yaranshi.
Ajiyan zuciya ya sau?e tare da meda kai ya jingina da kujera.
A hankali yake jujjuyawa, yana mai ?o?arin kauda tunanin da zuciyarsa ke kawo mishi.

Shi kuwa Barrister Kabir yana fita kai tsaye.
Asibitin Hamda
Ya wuce. Yana mai kiran babban Dr.
Yana tafe cikin gudu kamar maiyin doguwar tafiya.

Yana isa kai tsaye Office Win Dr Sajo ya wuce.
Yana ganinshi ya mi?e tsaye tare da cewa.
"A a ?anina! Ka iso, ko ina mara lafiyar?".
Cikin girmamawa da alamun tsohuwar amintaka yace.
"Barka dai Yaya Sajo, dan Allah kayi ha?uri mara lafiyar tana gida.
Ni kuma daga Campany n Yays Dakata nake, so kafin in koma gida in Waukota komai zai iya faruwa, kasan matsalar cutar athsman shiyasa nace bari in biya mu tafi tare. Dan Allah kayi ha?uri".

Murmushi Dr. Sajo yayi tare da fara tattara abin bu?atarsa yana mai tuno amintaka da mutuntakar da ke tsakaninsa dasu a baya.
Cikin kuma kula da amintaka yace.
"Ba komai ?anina muje, dama na gama yau bani da aiki".
Cikin jin daWi ya juya ya fita, shi kuwa yana biye dashi a baya.

Motarshi suka shiga, shiyasa yake taka motar da kyau.
Tsoro yakeji yasan yadda ciwon ke wahalar da ita.

A can gida kuwa, gaba Waya Mom da Abdul sun rikice.
Ita kuwa Jannart tuni ta gama gigicewa ta fita haiyacinta, fuskarta nan tayi jazir.
Sai fuzgo numfashin takeyi da ?arfi.

Wayar Abdul ne tai ringing yana Wagawa yace.
"Abba jikin fa ya tsananta".
"Subahanallahi Abdul gani nan zuwa yanzu".
Toh yace kana ya katse kiran.

Suna isa kai tsaye cikin gidan sukayi.

Abban na gaba Dr Sajo na biye dashi a baya.
Suna shiga Dr. Sajo ya fara aikinsa, allura yayi mata dan samun dai-dai-ta numfashin ta.
Allah cikin ikonsa kuma a take ta fara sau?e ajiyan zuciya, lokaci Waya jikinta ya fara sakewa.
Sai ga wani irin bacci mai nauyi ya kwasheta...

Kusan a tare suka sau?e ajiyar zuciya baki Wayansu.
Cikin kuma sau?e numfashi Abba yace.
"Alhamdulillah".
Hakama Mom.
Abdul kuwa shiru yayi yana mai jin tausayin yar uwar tasa.

Dr. Sajo kuwa, harhaWa kayan aikinshi yayi, kana ya kalli Barrister Kabir, gyaran murya yayi tare da cewa.

 Ciwonta yayi zurfi a jikinta, kuma bata bin doka da ?aidar maganin yadda ya kamata".
Da sauri Mom tace.
"Ai ba'a bata magani Allura kawai akeyi mata duk wata".
Cikin mamaki yace.
"Allura kuma? Toh wacce iriyar Allura ce duk wata kuma!?."
Cikin sanyi Abdul yace.
"Gaskiya bamu san wacce iriyar Allura bace".
Da sauri Dr Sajo ya kalli Barrister tare da cewa.
"Wanne Dr ne yake duba ta?".
Numfashi mai nauyi Barrister ya sau?e kana a hankali yace.
"Dr. Lukman ne".

Wani irin shiru Dr Sajo yayi tare da alamun nisan nazari.
Kana yace.
"Ok muje ko Barrister".
Toh yace kana suka nufi hanyar fita.
Sai kuma ya Wan juyo ya kalli Mom dake gyarawa Jannart din kwanciyarta, cikin nitsuwa yace.

 Kada ki damu, zata samu lfy in sha Allah, sannan zamu canza mata Dr da zai na kulawa da ita da kyau".
Kai ta gyaWa tare da cewa.
"Mun gode".

A hankali Dr. Sajo ya juyo ya kalli Barrister Kabir dake jan mota, dan medashi asibitin sa.

 ?anina akwai buk atar a canzawa Jannart likitan da zaina dubata.

Cikin nitsuwa Barrister Kabir ya Wan juyo ya kalleshi tare da cewa.
"Yaya Sajo meyasa!?".
KafaWarshi ya Wan Waga tare da cewa.
"Noh ba komai, kawai dai ciwonta yanada bu?atar gamayyar likitocin zamani bawai a tsaya kan Waya ba, a samo wani shima ya gwada kwarewar sa".
Uhum Dr.Sajo bai tuna cewa da babban Lawyer yake mgna ba.
Cikin fahimtar wani abun Barrister Kabir yace.
"Toh ba matsala in sha Allah za'ayi haka. Amman ina zamu samu likitan?".
Da sauri yace.
"A wannan mai sau?ine, akwai wani Babban Doctor yarone matashi mai ?uruciya da sanaiyar ilimin likitanci na juya da yau, kana harna gobe yana bincika yasan aikinsa, mun gamsu dashi, Dr Rayyern Mai-nasara."
Da sauri Barrister yace.

 Zakayi mana hanyar ganinshi kenan? Dan ance yana da wuyar gani".
Ya ?are maganar yana yin parking.
Kai ya Wan juyo ya fuskanceshi tare da cewa.
"Eh to Gaskiya yana da wuyar samu, saboda yawan aiyuka, kuma a wani sashin bashi da wuyar gani, in har kaje Mai-nasara Hospital Winsa, muddin dai yana ?asar, toh zaka ganshi sai dai ko in baya ?asar, in kuma bakayi sa'a ba, sai a turaka wurin wani Dr ?aninsa da kuma amininsa Win ba shiba, tunda yanzu aikin Company's dinsa sun tasoshi gaba, dole ya samo wasu likitocin bayan shi.
SaSanin da da shi kaWai ke jan ragamar asibitin.
Amman idan nasa hannu na baku takarda zuwa gareshi kuna zuwa shi Win zaku gani".

Cikin gamsuwa Barrister yace.

 Alhamdulillah nagode matu?a Yayana".
"Haba ba komai Kabir yiwa kaine. Yauwa sai kuma batun allurar da akeyi matan nan, abar yi matashi akwai bu?atar in santa, sannan ina son sanin sunan allurar".
Ya ?are zancen yana fita daga cikin motar.
Cikin gamsuwa Barrister yace to.
Kana sukayi sallama.

Ganin lokacin sallan azahar yayine kuma yasa ya nufi masallaci.
Koda aka idar da sal???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?lah kuwa.
Gidan yayan nashi ya koma.


Ethiopia.
Dr Rayyern Mai-nasara ne. Tsaye cikin wasu tattausan Suit masu masifar kyau da taushi tare da she?i.
Inda Riga da wondon suit din suka kasance pink color masu dauke da zane-zanen fari, sai kuma neck tie Win shi daya kasance fari, yayinda long sleeve dinsa ma ta kasance white, takalmin dake kafansa kuwa pink color ne mai dauke da harafin R-M.
Sai kuma Diamond watch din dake hannunsa mai Wan karen she?i da tsada.

Wayarshi kirar iphone 12pro max ne sa?ale a kafaWarshi yayinda ya mannata a kunne yana magana.
Kana kuma hannunshi Waya na ri?e da System Win shi. Daya hannunshi kuma na lallatsashi.
Bisa alamu aiki mai muhimmanci yakeyi.

Ga kuma wani irin masifeffen ?amshi mai Wan karen daWin sha?a da yake fitarwa.
Lallausan Sajenshi nan ya kwanta lib, yayiwa kyakkyawar fuskarsa kawanya sai she?i yakeyi.
Haka kuma ?an madaidaicin bakinsa mai jajayen lips na motsawa a hankali.

Yayinda siraran idanunshi suka fito ras, cikin Wan siririn glass mai ruwan garai-garai, irin na Doctor's daya li?ashi cas bisa karan hancinsa.

A hankali ya juyo ya kalli Usman daya shigo cikin alamun shiri.
"Sir gani". Usaman ya fada anutse.

Da idanunshi yayi masa nuni da jakarsa, yana maici gaba da maganar da yakeyi a wayar.
"Uhumm". Yace tare da lumshe idonshi.

A can Waya sashin kuwa ba tare da damuwa ba Sulaiman yaci gaba da magana.
Sabida sanin haka Allah ya halicce Rayyern mafi akasarin lokuta maganar Uhumm, ne ko eh ko hmm koko a'a
Bai cika yawan surutu ba, da fari gani suke miskilanci ne, sai daga baya suka fahimci abin da gaskene. Dan muddin za'ayi ta surutu ko hayaniya ko magana da ?arfi a kanshi ko kukan yaro ko babba, a take idanunshi ke kaWawa suyi jazir, lokaci Waya ciwon kai ke rufeshi larurarsa.
Ido ya Wan juyo yana kallon Usman dake tsaye gefenshi.
Yayinda kuma yake jin Sulaiman na cewa.
"Wallahi Rayyern ni kamanninku ya daina bani mamaki yanzu sai dai tsoro, Allah ko da yayi magana da hausa ko muryarshi iri Waya da Ramadan kuma".
A hankali yace.
"Hmmm Sulaiman social media ka biyewa ko?".
Da sauri yace.
"Dan Allah tsaya kaji, yaushe zaku dawo?".
A ta?aice yace.
"Jibi!".
Cikin fidda numfashi Sulaiman yace.

 Toh gashi kuma shi yaron yau zai taho Nigeria, ni nai zaton yau nema zaku dawo ince Allah yasa ku haWu a jirgi kaga zahiri, abu kamar an dama kunu an raba har Wan makolloto yake dashi irin naka fa".

?an gajeren numfashi mai d auke da gajiya Rayyern ya fesar tare da cewa.
"Uhmm, it s Okay a gaida Baby".
Yana faWin haka ya katse kiran.
Sai kuma ga wani kiran ya shigo.
Da sauri ya zauna bisa kujerar bayanshi kana ya amsa kiran.
Cikin tsananin girmamawa hade da ladabi da biyayya da kuma tarin mutuntaka yace.
"Assalamu alaikum".
A can Waya sashin kuwa, wani kyakkyawan mutum ne mai cikar haiba kamala ne, zaune.
Alhaji Bashir Muhammad Mai-nasara kenan, sai Mami mai Wakinshi dake gefenshi.
Kana Wan matashin ?aramin Wansu Dr Ramadan Mai-nasara na zaune gaban Abba'n nasu.

Cikin tarin so kula bege da kuma ?auna,
Alhaji Bashir ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Wa alaikassalam".

Cikin jin daWin jin muryar mahaifin nashi yace.
"Abba Barka da safiya".

"Barka dai Rayyanu".

Ido ya lumshe cike da son mahaifin nashi yace.
"Abba kuna lafiya?".

"Lafiya lau Alhamdulillah, ga Mamynku da Ramadan wai in tambaya musu yaushe zaka dawo, suna kewarka".

Murmushin gefen baki daya bayyana fararen kyawawan ha?oransa yayi, cikin kuma sau?e numfashi yace.
"Nima ina kewarku Abba in Sha Allah yau ina hanya amman Abba kai kaWai fa".
Murmushi yayi fahimtar cewa.
"Shi kaWai yasan yau zai dawo kenan."
Ramadan kuwa murmushi yayi sabida jin abinda Hamman nashi ya faWa.

Mamy kuwa Kekkyawar mace mai cikar haiba, murya ta Wan Waga tare da cewa.
"Toh me zan dafa maka".

Idonshi ya lumshe fahimtar sun jishi kenan.
Cikin sanyi yace.
"Mamy'na komai ma".
Amsar wayar tayi tare da cewa.
"Cin za?i zai Barka kaci abinda zan dafa maka ko?".
Cikin fuskar annuri yace.
"Yesssss! Mamy".
"Toh shike nan Babana Allah ya kawo min kai lfy".
"Amin Amin Mamy".
Yace cikin lumshe ido
Daga nan sukayi sallama.
Kana ya juyo ya kalli Usman kana a ta?aice yace.
"Mu je".
Da sauri Usman yace.
"Sir ina muka nufa?".
Cike da mamaki Usman ya Wago kanshi da sauri ya zuba mishi ido cikin al'ajabin jin yana cewa.
"Nigeria".
Ya buWe baki zaiyi magana ya Waga mishi hannu tare da nuna mishi ?ofar fita.

Haka yasa ya gimtse maganar kana ya Wauki kayyakin nasu
Suka fita.


Boke International Airport Addis Ababa Ethiopian.Suka nufa kai tsaye

Still Kai tsaye Airport parking suka nufa.
Bayan Driver'n'shi yayi parking.
Da sauri Usman ya fito ya buWe mishi, marfin motar.
Cikin nitsuwa ya zuro ?afarsa ta dama waje , tare da sau?eta ?asa ahankali, Saidai kuma da sauri ya rumtse idanunshi tare da dafe ?ahon zuciyarshi saboda wani irin m...!





=???
*TUBALI*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk i Biya 500 k aramin farashin na k aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna.

ACCOUNT NO 0661110170.

BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA

BANK GTBank

sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276.

*PLS TAKE NOTE BAND VTU*
kada kiyi

4 / 46