Tubali Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Khaleesat Haidar Category :  Love

Chapter   30 / 46

87K to 90K   out of 135.1K words

ke cikin zuciyarsa da alamun umarni yace.

* Jannart Aurenki ya kusa fa zanyi miki Aure! *

Ya fadi mgnar cikin serious

Wanda hakan yasa Jannart cikin wani irin yanayi mai rauni.
Da harbawar zuciya cikin sauri Jannart din ta D.......




By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: D'ago kanta ta kalleshi, da Idanunta wanda lokaci daya yanayin cikinsu ya sauya, musamman yadda maganar da taji ya fito daga bakin Abban ya daki zuciyarta matuka gaya.

Abba Kabir kuwa ganin ta d'ago kanta ne yasa shima?ya zuba mata ido, fuskarsa sam babu alaman wasa.

Hakannne kuma yasa ta maida kanta k'asa, tare da d'an lumshe Idanunta, a hankali ta soma wasa da y'an yatsun hannunta.

Yayinda takejin zuciyarta na dan bugawa.

Dai-dai lokacinne kuma Aunty Dijat ta bud'e kofar d'akin ta shigo.

Yanayin yanda tagansuda dinne kuma ya sakata sakin murmushi, tare da karasowa ta zauna? akusa da Jannart din.

Kallon Jannart din Aunty Dijat tayi, tare kuma da bud e bakinta da niyar yin magana.

Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir saurin d aga mata hannu alamun dakatarwa.

Kallonsa Aunty Dijat din tayi, lokaci guda kuma itama ta sauke kanta k asa.

Hakanne kuma yasa gaba ki d aya d akin ya dauki shiru, babu abunda ke tashi sai sautin fitan numfashi, da kuma ajiyar zuciya da suke ta saukewa dukansu akai akai.

Almost 10mn kafun Abba Kabir din ya sake d ago Kai ya kalli Jannart, cikin tausayawa da kuma danne abundake cikin zuciyarsa yace.

 Jannart kinji abunda nace, Ina fatan bazaki bijirewa umarnina ba kamar yadda kika al'? warta min.

Kai Jannart din ta d ago Ahankali ta kalli Abban nata.
Domin sai takejin maganganun nasa tamkar wani abu na daban, wanda bata tab aji ko sanin akwai shiba.
Ita dai tasan kalmar Aure, amma batasan haka kalmar kan zuwarwa mace cikin zuciyarta ba, batasan ya rayuwar cikinsa yake ba.
Saidai koma meye ta sani bazata tab a bijerewa umarnin Abban nata ba.

Idanunta tasake mayarwa k asa, kana kuma Cikin sanyi ta jinjina masa Kai, alaman  Eh.

Ajiyar zuciya mai k arfi Abba Kabir din ya sauk e, cikin kuma son sake tabbatarwa kansa amincewarta yace.

 Jannart duk da cewar bani nahaifeki ba, amma matsayin uba nake awajenki, haka kuma Kallon y ata ta cikina nake miki, wannan yasa bazan tab a yi miki dole ba, shin kin amince da hukuncin dana yanke akanki?

Kanta ta sake jinjina masa, tare da bud e Labb an bakinta da takejin sun danyi mata nauyi a hankali tace.

 Eh Na amince Abba, duk hukuncin daka yanke akaina dai-dai ne.

Numfashi Abba Kabir din ya fesar, tare da sake gyara zamansa.

Kana yace.
 Alhamdulillah naji dadi kwarai, Insha Allahu kuma yanzu akwai shirye shiryen da zamu fara, Domin banason lokaci ya ja da yawa.

Kanta ta d an langwabar gefe, kana cikin yanayin sanyi tace.

 To Abba, amma akwai abunda nake shiryawa, saboda ranan alhamis dinnan, zanyi wani program, Dan Allah Abba kabani dama, nasamu nayi shirin nan, Idan yaso daga baya komai ma sai ayi.

D an murmushi Abba Kabir din yayi, tare da cewa.

 Karki damu Jannart, shirin da nakeyi akannaki ma zaikai har bayan alhamis din, saboda haka kina da ishashshen dama na y an wasu kwanaki.

Ajiyar zuciya ta sauk e, tare da d an sakin murmushi, saboda yanzu ta danji sanyi acikin ranta, Yayinda ta kuma k ara samun hope akan cewar Lallai lailai bazata rasa aikinta ba.

Aunty Dijat kuwa Kallon Jannart din tayi, Yayinda takejin tasananin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarta.

Lallai Tabbas tasan cewa, Jannart din bata san komai ba, aharkar auratayya sai abunda ta karanta a musulunce, wanda hakan yasa dole tana buk atar mai taimaka mata.
Sanin wasu abun a zahiriyar rayuwar duniya more Especially aure.
Tasan Jannart cikekkiyar janitalauce, sabida kan haka aka reneta aka bata tarbiya, bin umarnin na gaba da ita, ya zama komai na rayuwarta bata da zabin kanta ko ra'ayinta sai abinda manyan ta suka faWa, shiyasa suke sarrafa ?wa?walwarta sun hanata yancinta sun dakufeta bata da wani abu sai amsar umarni daga garesu.
Shiyasa ta kasance mai sau?in kai da rauni kana ga tarin ha?uri.
Wanda suke tasirin hanata tsayuwa kan ra'ayinta.


Hannunta Aunty Dijat din ta rik o, kana cikin tausasawa tace.

 Naji dadi da kika amincewa maganan auren nan Jannart, Domin kuwa aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, acikin aure akwai abubuwa da yawa, farinciki da kuma akasin haka, amma ni naji ajikina cewar auren da zakiyi shine zai zame miki Tubalin farin cikin ki, Rayuwa zata sauya miki Jannart, zaki zamanto Mace mai y anci, k uncinki zai gushe, Yayinda haske zai bayyana acikin rayuwarki Insha Allah, sannan kuma ako da yaushe kiyi riko da addu a, Domin abubuwa sukanyiwa bawa tsanani ne Idan yana wasa da addu a, Addu a makamin mumini ne Jannart, musamman gake, da ace bakya sakaci da addu o i da ko Junaid da yake yawan musgana miki, bazai tab a samun daman fuskantar ki ba, saboda Allah zaina baki kariyarsa akoda yaushe.

Kai Jannart din ta jinjina, cike da gamsuwa da maganganun Aunty Dijat din kuma tace.

 Insha Allah zanna rik o da addu o i, Nagode sosai Aunty Dijat.

Murmushi Aunty Dijat din tayi, tare kuma da cewa.

 Ba komai Jannart, Allah Ubangiji ya kawo mana saukin damuwarmu.

Da Ameen suka amsa dukansu, Yayinda Jannart din kuwa ta d an kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, ganin lokaci yaja sosai ne kuma yasata, d an mikewa tsaye.

Tare da Kallon Abban nata tace.

 Abba zan tafi wajen aiki kada nayi latti.

Kai Abba Kabir din ya jinjina, had e kuma da mik ewa tsaye yace.

 Allah ya kiyaye hanya Jannart ya kuma Kareki aduk inda kike.

Da Ameen ta amsa, tare kuma da daukar jakarta, ta juya ta fice daga cikin dakin.

Sam bata damu da maganan auren da Abban yace zaiyi mata ba, saboda batasan menene zata tsinta acikinsa ba, wannan yasa ko tambayan wanda sa a aura mata din da kuma sunansa batayi ba, Ita dai ahar kullum tamkar rak umi da akala take, duk inda aka jata zuwa zatayi.
Saidai kuma tana da tabbaci cewa Abban nata bazai yi abunda zai cutar da ita ba.

Koda ta fito compound din gidan, kaitsaye wajen motarta ta nufa.

Tana shiga cikin motar kuwa Drivern yaja suka tafi, Yayinda kattin guard dinta suka rufa musu baya.

Kaitsaye hanyar tashar tasu ta Arewa24 suka nufa.

Jin yanda suka mik i titi ne kuma yasa ta, jingina bayanta da jikin kujerar motar, tare da lumshe Idanunta.

Ahankali ta sauk e wani irin ajiyar zuciya, Yayinda kalaman Aunty Dijat kuwa suka shiga dawowa cikin kanta filla filla.

 Aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, Aure shi zai zame miki tubalin ginuwar farincikin ki.

Abunda kwakwalwarta ke maimaita mata kenan, wanda kuma har yanzu ta kasa warware kalaman.

Meyasa Aunty Dijat din tace aure zai zame mata tubalin farin ciki? Menene acikinsa? Wacce kalan rayuwa ce zatayi, har kuma ta samu farinciki bayan zata zaune akarkashin wani ne wanda bata saniba bai santaba.
Ya yake irin Yah Junaid da Daddy ne ne ko irin Yah Azeez da Abba? Wai shin menene ma manufar auren nata da Abba bai gaya mataba?

Tayiwa kanta duka way annan tambayoyin da ko kusa bata da amsarsu, ba kuma ta da mai amsa mata su yanzu.

Batasan komai akan hakan ba, ba ta kuma tab a tunanin hakan acikin kwakwalwarta ba, shiyasa takejin duk wata kalma da ta shafi aure, amatsayin bak on abu.

D an numfasawa tayi, tare da watsar da duk wani tunani dake cikin ranta, dai-dai lokacin kuwa suka iso babban parking space dake cikin tv station din.

Bayan Baba Ado ya gama dai-dai-ta parking din motar ne kuma ta fito, kaitsaye ta nufi cikin gidan tv nasu.

Ahankali take taka k afafunta, Yayinda kowanni taku da zatayi yake dauke da jan hankalin mai Kallon ta.

Azahirin gaskiya kuma awajenta tafiya takeyi normal, Yayinda duk wani mai Kallon ta kuwa, ke ganin tafiyar tata tamkar tafiyar hawainiya, saboda komai nata na dabanne, tana da wani irin tsarin halitta mai matukar burgewa, wanda kuma ko ita kanta batasan cewar tana dashi ba.

Tura kofar babban office dinnasu tayi ta shiga bakinta dauke da sallama.

Jin Sauti da amon zazzakar muryar nata ne kuma yasa, duk mutanen dake cikin office din juyowa suka kalleta.

Wani dogon tsaki Asiya taja tare da kauda kanta daga kallonta.

Ita kuwa Jannart Sam hankalinta ba a kanta yake ba, duk da irin Kallon da taga tanayi mata kuwa Amma bata damu ba.

Fuskarta d auke da murmushi ta k arasa wajen, Aysha Lawal da kuma Salman wanda suke zaune awaje daya suna duba wasu takardu.

Murmushi Aisha Lawal din ta sakar mata, tare da cewa.

 Jannart Idi Saleh Dakata yau kinyi lattin zuwa wajen aiki, saboda haka sai munciki tara.

Murmushi mai kama da dariya Jannart din tayi, har saida fararen hak waranta suka bayyana, hakan kuwa shiyasa dimples dinta duk suka lotsa.

Kafad an Aysha n ta d an buga, kana cikin muryata da babu hayaniya sosai tace.

 Kai Aysha kwata-kwata fa mintuna 10, na kara akan yanda nake zuwa kullum.

 Eh duk da haka dai.

Ayshan ta fad a tana murmushi.

Jannart kuwa zama ta d anyi agefe dasu, tare da dawo da Kallon ta ga Salman Wanda ya saki idanu da baki yana Kallon ta.

Had a idanu da sukayi ne kuma yasa shi saurin janye idanunsa daga kanta.

Itakuwa Jannart batare da ta fahimci komai na daga Kallon da Salman din keyi mata ba tace.

 Good morning colleague.

Gashin kansa ya d an Sosa kana awayance yace.

 Morning Colleague, fatan kin tashi lafiya ya jikin naki.

 Da sauki sosai, Domin nama warke yanzu babu wani abu dake damuna.

Jannart din ta fad a tana me ajiye Jakarta,
Adai-dai lokacinne kuma Hajia Rabi'ah da Aunty Fauziya D Sulaiman suka shigo, cikin sashin su Jannart din.

Ganin Jannart din da sukayi acikin office dinne kuma yasa, Aunty Fauziya D Sulaiman sakin murmushi, kana cikin jin dadi da kamala da mutuntaka tace.

 Masha Allah gaskiya Jannart ansamu lafiya, tunda har an fara fitowa office.

Murmushi Jannart din tayi, cikin kuma jin dadin kulawan da yan office din nasu ke bata tace.

 Alhamdulillah my Aunty Fauziya naji sauki, kuma Ina saka rai da fatan cewa Insha Allah Gobe ma zan gudanar da program dina.

Kai Aunty Fauziyan ta jinjina, tare kuma da matsowa kusa da Jannart din sosai.

Cikin yin k asa da murya irin ta maganan sirri tace.

 Masha Allah, amma Jannart kinaga kuwa Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din zaizo.

Kanta tad an langwabar tare kuma da juyawa, ta kalli Salman wanda shidinma kuma Kallon ta yake.

Kai Salman din ya jinjina mata, cike dason bata karfin guiwa yace.

 Karku damu Insha Allah Zaizo.

Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, tare da daura hannayenta akan kafad an Jannart din.
Murya atausashe tace.

 Karki damu Jannart, ko da ma ace bai samu zuwa goben ba, ai kina da sauran chance harna tsawon one week, Insha Allah kuma muna saka ran dacewa.

Kai kawai Jannart din tad an jinjina, tare da komawa ma zauninta ta zauna, lokaci daya kuma duk jikinta yayi sanyi, domin tasan gobenne kawai last hope dinta, kasancewar bata da tabbacin cewa, wani satin zata kasance available, musamman ayanzu da Abba Kabir yake kokarin fara shirye shiryen b oyeta.

 Yah Allah Kabani sa a.

Tafad a k asa-k asa, tare da maida idanunta ta lumshe, saboda gaba daya yanzun ta karaya da komai.

Salman kuwa daya karanci tarin damuwa akan fuskar Jannart din, ji yayi komai na Office din baya yi mishi dadi, duk yanda yaso ya daure zuciyarsa akanta kuwa baya tab a iyawa.

Haka yake d agowa time to time yana satan Kallon ta.

Itakuwa Jannart samma batasan yanayi ba.

Aysha Lawal ce kawai take lure dashi, fahimtar abunda ke ran Salman din agame da Jannart dinne kuma ya sakata sakin murmushi.
Batare kuma da tace komai ba taci gaba da ayyukanta.

Haka dai Jannart ta kare gaba d aya wuninta a office din, duk yanda kuma taso kawar da fargaban dake ranta ta kasa.

K arfe 5 dai-dai tayiwa su Salman da Aysha Sallama,kaitsaye ta wuce gida.

Koda suka iso gidan nasu, haka ta fito daga cikin mota gaba daya duk jikinta asanyaye.
Direct falonsu ta nufa, inda tana shiga cikin falon kuma wayarta dake rik e a hannunta ta soma kara.

Kallon ta ta mayar kan screen din wayar.
Lokaci daya kuma murmushi ya bayyana akan fuskarta, saboda sunan Yah Azeez da ta gani.

Picking call din tayi, tare da kara wayar akan kunnenta.

Sallaman da tayi dinne kuma yasa Daga can b angaren Yah Azeez ya amsa mata, tare da cewa.

 My y ar k anwa Jannatuwa, bari na fara bada hakuri kafun ki shigo da korafin rashin kiranki da wuri da banyi ba.

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan shagwab e fuska, tamkar Yah Azeez din yana ganinta. Tace.

 ai saura kad an nayi maka fushi Yah Azeez, kuma da baka kirani yau ba ko hmmm, ko kakira bazanji rarrashi ba.

Murmushi Yah Azeez din yayi, cikin tsananin so da Kaunar yar uwartasa yace.

 I m sorry Jannart wallahi aikine yayimin yawa kuma na kira sau biyu Mom ke Wagawa tace kina bacci, yanzu ya jikin naki, Ina fata kinji sauki sosai.

Kanta ta jinjina had e da cewa.

 Naji sauki sosai Yah Aziz, Domin yau har wajen aiki naje, yanzu shigowa ta ma gida.

 Masha Allah Lallai jiki yayi kyau, To Allah ya kara afuwa, sannan kuma ki kara hakuri kinji Jannart, Insha Allah watarana sai labari, komai da Junaid keyi miki zaizo ya wuce, kuma Allah zai saka miki akan duk wani cutarwa da Junaid keyi miki, shima kuma zai ga sakamakon abunda ya aikata.

Idanunta ta d an lumshe, saboda har acikin zuciyara taji sanyi da dadin kalaman Yayan nata, inama da ace shine akusa da ita ba Junaid ba, Lallai da taji dadin duniya, Domin ko ayanzu da baya kasar, yana iyaka kokarinsa wajen bata kulawa, da nuna tausayawansa agareta.

Numfashi ta d an fesar kana Asanyaye tace.

 Nagode Sosai Yah Azeez, kuma Insha Allah zan kara hakuri akan wanda nakeyi.

Murmushin Jin dadi Yaya Azeez din yayi, Domin dama yasan tuncan k anwartasu mai biyayyace, akan duk wani abu daka umurceta.

Still cikin nuna kulawa yace.
 Yauwa y ar k anwata, yanzu fad Amin akwai wani abun da kike buk ata ne, ko kud i sai na tura miki ta account, ki saya duk wani abu da kikeso.

Murmushi tayi, hadi da cewa.
 A a Yah Azeez bana buk atar komai.
Domin last week Abba Kabir yayimin shopping, sannan kasan akwai kudi da yawa a account dina, ko salary na Idan anturomin bana sayan komai dasu.

Ajiyar zuciya Yah Azeez din dake kan wayan ya sauk e.
Nandai suka d an tab a hira kafun daga bisani sukayi sallama.

Bayan ta kashe wayar nata ne kuma ta lek a kitchine ko zata ga Momy, saboda tunda ta shigo babu motsin kowa agidan.

Ganin kitchine din bakowane kuma yasa kaitsaye ta wuce bedroom dinta, saboda tanason yin wanka Tsarkin data samu.
Akwai kuma wasu bayanai da zata had a acikin system dinta.

Acan B angaren Dr. Rayyern Muhammad Mai-nasara kuwa zaune yake akan wata had add iyar royal chair, Yayinda yake sanye da wani had add en suit mai kalan ruwan k wai ajikinsa.

Daga gefe guda kuwa drinks da kuma Chocolate d insa ne, sai kuma sabuwar wayarsa Iphone daya k ara saya, dake rik e ahannunsa.

Inda kaitsaye ya shiga cikin contact d insa, yana neman wani numbern tsohon abokinsa, Salisu, saboda yanason yiwa Salisu din ta aziyya kasancewar yaji labarin rasuwar Baban shi.

Yana cikin tsaka da duba contact dinne kuma, idanunsa suka sauk a akan numbern Salman.

Numbern da Idan bazai manta ba, sune wanda suke son ganinsa, ya kuma yi musu alk awari zuwa.

Saurin sanya hannunsa yayi ya dafe kansa, saboda sai ayanzu ne ma abun ya fad o masa, gaba daya kwata kwata ya manta ma dasu.

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk e, tare da dan cije Labb an bakinsa.

Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

 Allah Nagode ma daka tunatar dani, Allah kada ka bani ikon daukan al'k awarin da bazan iya cika shi ba.

Jawo wayarsa yayi ya duba date da kuma rana.

 Today is Wednesday, gobe ne al'k awarin dana d auka kenan zai cika, Insha Allah zanyi kokari naje, kodan yaronnan ya tsira da aikinsa, ya kuma samu abunda zai ciyar da iyalansa.
Tabbas zanyi cancelling duk wani schedule dina na Gobe, har sai na samu naje tv station dinnan, bazan tab a zama mai karya alk awari ba Insha Allah bazan zama sanadin rasa aikinsa ba.

Ya fad i hakan, yana me mik ewa tsaye, tare kuma da d aukan laptop d insa.

Kaitsaye ya koma wajen zamansa da yake na musamman, acikin katafaren office din da yake new company n sa.


Tahir Quest Palace.

Riyyam nsra ne kwance akan makeken gadon dake dakin hotel din, wanda kuma yanzun gama wayarsa da Mammy da kuma Zaiton.

Idanunsa ya d an lumshe tare kuma da juyowa ya kalli, matashiyar budurwar dake kwance agefensa.

Almost 1hour kenan yanzu da zuwan ta wajensa, wanda kuma itama sun had u ne da ita anan Tiktok, Yayinda itama take cikakkiyar celebrity ce a Tiktok din, sannan kuma yar asalin Nigeria ce cikin Kano tayi shuhura a iya ti?a rawa da bin wa?a, ga iya sa fitinennun suturu masu bayyana tsiraici hakan yasa kasuwarta ke ci.

Idanu Riyyam din ya zuba mata, Domin kuwa Wannan shine Karonsa na farko daya fara mu amala da wata mace y ar Nigeria.

Yarinyar dake kwance agefen nasa, kuwa ganin irin Kallon daya ke mata ne, yasa ta kashe masa Ido, tare da turo masa kirjinta gaba, wanda ko kaya babu ajikinta.

Hakan ya faru ne kuma saboda sheke ayarsu da sukayi ita da

30 / 46