Waye Shi Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   42 / 58

123K to 126K   out of 171.2K words

tashiga ranki abu guda dana sani shine kina sonsa, bari naje na dafawa babanku ruwan shayi dasauri na miƙe.

"Mama bari zan haɗa masa" toh kawai tace nafice zuwa kitchen na haɗa kayan shayin na ɗaura a wuta inajin shigowarsa na juye nakai masa. A palour na sameshi yana zaune nashiga da sallama bayan nayi masa sannu na zuba masa ruwan shyin na miƙa masa. Shi kansa ya lurada yanda jikina yadawo sanyi-sanyi. Daurewa yayi yayimun nasiha sannan yacemin Zanje gidan Hajiyarsa na ƙwana biyu."

"Washe gari Sassafe Natafi gidanta naji daɗin zaman danayi a gidanta danna koyi wasu abubuwa da bansamu na koya a shekarata sha tara ina neman ta ashirin a duniya ba. Kuma hajiya batajin kunya duk wani abunda yakamata ta koyamin tana koyamun shi har wasu daga cikin al'adu na zamantakewa da larabawa wanda bansan a yanda ta koyi hakanba.

Mummy kuwa anata wajen sayyaya kawai takemin tana kashe kuɗi wanda ita kanta batasan yawansu data kashe ba duk wani abunda tasan idan naje can zan buƙata ta siyamin maimakon ƙwana biyu saida nayi 5days a wajan Hajiya sannan nadawo.

Nasamu Baba da maganar Exam ɗita guda ɗaya wacve take kaina tubda dama ya riga yamin register bandai taɓa zuwa ko lactures bane nasiya material da zummar zanyi karatu kawai idan takama za'ayi practical ko wani abun sai naje. baba yace shi yanzu baisan yanda za'ayi ba tunda yasan tafiyarmu wannan satin ce gashi kuma exam ɗin gabaki ɗaya bazata wuce 7 weeks ba kuma baza'a fasa tafiya saboda exam ba abunda za'ayi shine udan naje nayiwa Hammood maganar jarabawar duk da yasan bazai rasa masaniya akanta ba.


A daren ranar jirginsu Hammood ya sauƙa a abuja ƙwana ɗaya yayi a abuja ya iso bauchi. Adaren ranar kuma Yazo gida saida suka gaisa dasu Mama sannan nashiga wajansa. Kallo ɗaya yayimin yasan ina cikin damuwa nikam nakasa kallonsa gabaki ɗaya ma. Hira sai jifa-jifa mukeyi san dama kwana biyu gabaki ɗaya banida walwala tunda nasan ya iso Abuja sai rashin walwalar ta ƙaru bare yanzu danake ganin baifi ƙwana biyi nabar gida ba. Hammood cikin kulawa yakira sunana.

"Zaynab" na ɗago na kalleshi tunda bashiga sai alokacin na kalleshi idanuwanmu suka haɗe waje ɗaya gabana yahau faɗuwa dasauri na kawarda idona. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya jefomin tambaya.

"لا تريد الذهاب معي"
(Bakison tafiya ne dani)?" Dasauri na gyɗa kaina alamun eh. Yayi murmushi yasan za'a rina."



PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."


ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya


Shiru nayi ina sauraron abunda zaice dan ganin yayi murmushi ya ƙaramin ƙarfin guiwa.

"I know bakizo tafiya ba amma yaya za'ayi? You have to kamar yanda na faɗa miki abaya cewa duk ranarda nasaka ƙafata a ƙasarnan bazan tafi batare da keba and yanzu gashi nazo nasan za'ayi haka yasa na ƙara miki morerthan 1month akan lokacin gama school ɗinki yanzu tunda na saka idanuwana akanki bazan iya tafiya ni kaɗai ba, wannan dalilin yasa tunda natafi ban kiraki a waya ba dan ina tunanin da Zarar naji muryarki bazan iya yimiki adadcin ƙarin lokacin dana sanyawa raina zanyi ba, I'm sorry amma wannan karon yazama dole nutafi tare" kukan taɓara na fashe dashi dan dajin kalamansa suna fitowane daga zuciyarsa bazai iya barina na ƙara lokaci tare da ƴan uwana ba. Ya dawo wajanda nake a zaune cikin sanyayyar muryarsa yafara rarrashina yana mamakin yanda kuka bayamin wuya danasaan yanda kukana yake cutar dashi da bazan sake yarda ko drop na hawaye ya ɗiga a idona ba.


"Shhhh is okay Zaynab please لا تبكي (Dont cry) yanzu toh we're not leaving tomorrow sai Jibi" na maƙe kafaɗa nacigaba da kukana. Hannuwansa ya sanya ya kamoni gabaki ɗaya ya shigar dani jikinsa ya rumgume lokaci guda kukan ya tsaya batareda ya furta wata kalma ta rarrashi ba na rumtse idanuwana ina shaƙar ƙamshin jikinsa. Shima ya ɗaura kansa akan gashina yana shaƙar ƙamshin dayake fitowa daga ciki. Dama Mummy ta bada an haɗamin Humra masu masifar ƙamshi kusan kullum saina turara jikina dasu da turaren jiki dana gashi da kulaccam na jiki dana gashi. Mamakin irin ƙamshin dayaji a jikina yakeyi yaji ƙamshi kala-kala a duniya na turaruka brand masu masifar ƙamshi da tsada amma bai taɓa cin karo da makamancin ƙamshin dayakeji a jikina ba bakowani irin ƙamshi bane yake masa daɗi he's picky about turaruka shiyasa turarensa yake na daban amma yayi admitting wannan ƙamshin mai daɗine gashi yana sauƙarda nutsuwa shiru mukayi gabaki ɗayanmu kowanne da abunda yake saƙawa a cikin ransa. A hankali na raba jikina da nasa na sunkuyarda kaina dan banaso mu haɗa idanuwa murmushi yayi ganin kukan ya tsaya. Sai alokacin yasamu ƙarfin lallashi amma lokacin ina kukan rasa abunda zai faɗa wanda zai ƙwantarmin da hankali yayi dan gabaki ɗaya rikicewa yake idan yaga hawayen fuskata sai dai shi rikicewarsa ba'a iya ganeta dan sai dai kawai ya tsaya ya tsura ido batareda yasan abunyi ba.

"I'll إن شا اللله be good to you ki kwantar da hankalinki Ina Sonki sosai bazan cutar dake ba in sha Allah bazaki samu wani tashin hankali a gidana ba zan tsaya miki a komai a matsayina na mijinki and your protcetor bazan yimiki alƙawarin cewa bazakiyi kewar gida ba amma I'll be there na ɗebe miki kewar da kike tare da ita. kuma bazance zan kasance tare dake a kullum ba sai dai ke zaki iya kasancewa tare dani a kullum Idan kinso zaki bini duk yanda zan saka ƙafata muje tare dan banaso ki kasance cikin kaɗaici" nayi shiru ina sauraronsa wato dai barina a gidane bazaiyiba ya rantse sai mun tafi a wannan tafiyar. Baiyi dare sosai kamar yanda ya sababa baifi 1hour ba yatafi saboda akwai abubuwanda yake buƙatar yi kafin yabar ƙasar kai tsaye cikin gida na nufa dukaninsu suna harabar cikin gidan Har mummy dake shashinsu ɗaya da Baba kuma a palourn Baban muke zama shiyasa tafita tabamu waje. Na ƙarasa wajan da suke zaune ana kallona ansan naci kuka.

"Kuka kikaje kikayi masa kenan Marmeeyy? Kina tunanin kukanda zakiyi shi zaisa a fasa tafiyar?" mama ta faɗa cikin ɓacin rai.

"Toh dan tayi kuka shine tayi laifi? Waye baiyi kuka ba lokacin da zai bar gidansu? Kefa a gari ɗaya anguwa babu nisa haka kikayita zabga ihu har aka shigo dake cikin gidannan kina ihu amma bakiyi laifi ba sai ita wacce bama gari ba ƙasar za'a bari ta ita gabaki ɗaya idan tayi kuka tayi laifi?" Mama taja baki tayi shiru jin Mummy na shirin yimata tonon silili a cikin yara. Naje na zauna wajan Mummy na ƙwantar da kaina a kafaɗarta. Cikin muryar kuka nace.


"Mummy kijifa wai jibi zamu tafi dan Allah kiyiwa Baba magana yace masa yabari sai wani sati"

"Au jibi? Kinji tafiyar yanzu tadawo jibi ai Marmeeyy da gobe ne ma tafiyar ta iya yiwuwa yaji tausayinki ne ya ƙara kwana ɗaya akai kuma yanada abunyi ai a cikin satinnan naji Ahamd yana faɗa"

"Mummy toh yatafi mana sai mutafi abayansa ai ba sai lallai muntafi tare ba idan muka isa sai yasaka aje a ɗaukomu"

"Kinga Marmeeyy ni ban is ada wannan zance ba bawan Allahn nan dai yayi ƙoƙari wallh aure yana neman shekara anata jaa masa lokaci saifa da akayi aurenku sannan akayi na Ahamd gashi matar Ahmad yanzu inaga cikinta yakai wata 6 shiyasama bazamuje tare dashi ba ko bikin Aysha yanzu wata 4 yake ciki ina muka isa muce masa yatafi wai sai bayan sati ɗaya? Sati ɗya da jibi ai duk ɗayane wajan ubangiji idan darai da lafiya" na fashe da kuka.

"Wallh Mummy nikam a wajena ba ɗaya bane ko ƙwana ɗayane idan zan ƙara cikin ƴan uwana zanji daɗi"

"Nidai wallh Marmeeyy bansan yaushe kika dawo haka ba gabaki ɗaya kin dawo sakaliya wai akanki aka fara aure da zakiyita fitowa mutane da sababi kala-kala? Ba gashi zaku tafi da Fadeelah da Mummy ba harda Yayanki mafa waya samu irin gatan da kika samu? Kowa shi kaɗai aka kaishi gidan miji amma banda ke wacce gata yayiwa yawa" mummy tayi dariya.

"Toh idan Mummy da fadeelah da Habibu sunanan Mama tana nanne? Ko akwai Baba? Babu anty babu ƙannenta Dan Allah ki saurarawa yarinyar nan taji da abu guda ɗaya." Mama taja baki tayi shiru sukaci gaba da rarrashina harda Anty.

Washe gari sassafe nida Anty fadeela mukaje gidan Aysha har azahar mukakai acan daga nan nawuce gidansu Maryam. Itama tun safe tamin waya akan zatazo nace mata gani gidan Aysha idan nagama zan biyo ta gidan. Kuka sosai mukayi nida Maryam Ummi tana aikin lallashi dama yanda muka shaƙu tasan dole idan akazo rabuwa da aiki. Daga ƙarshe tare muka tafi da ita agidanmu muka ƙwana. Da safe Haka mama tatashi ido jajazir da alamu taci kuka cikin dare amma sai fisfisgewa takeyi dan kar agane. Nima tunda natashi dasafe nake kuka maryam tana tayani mama ganin bazata iya rarrashi ba tabar mana ɗakin gabaki ɗaya. Tun safe nake zuwa ɗakin Baba a kulle gashi wayarsa bata shiga. Dana matsa da zuwa Mummy tacemin ai Baba tunda yafita sallar asubahi bai dawo ba dan dama haka yaƙwana baiyi bacci ba. mummy tace ko runtsawa baiyiba. 12am zamu tafi gashi har 10 Baba bai dawoba nazauna ina kuka ni bazan tafi ba sai naga Baba duk ƙarfin halin Mama saida ta zauna ta rarrasheni. Yaya habibu yafita neman Baba yaduba duk yanda ya kamata amma bai sameshi ba. Hamma ya kawo Aysha muyi sallama saiga Aysha tana kuka riras ganin yanda nake kuka kuma tasan tafiya zamuyi" tsabar kuka jikina har yayi laushi kukan yadaina fita da sauti sai zafin zuciya da nakeji 12 kuwa muka tashi tafiya alokacin danaga tafiya za'ayi nafara tijara babu wanda baiyi kuka ba kaff gidanmu. saida Mukabi gidan Hajiya da Gidan Baba (Alhaji habibu) mukayi masa sallama sukayitamin nasiha sannan muka kama hanyar airport. jirginmu ya sauƙa a abuja amma gidansu Mummy muka wuce sai nazamo kamar wata celebarity kowa son kallona yake ni ɗaki ma nawuce dan haushin mutane nakeji daƙayr mummy tasaka naci abinci ahakanma babu yawa ban fitoba sai bayan la'asar liss nasmau Mummy jibge da kayyayaki agaba da turaruka da abubuwa wanda bansan menene su ba jibgi guda ashe ananma tasa a haɗa mata wasu kayan wancan an rigada an gama dasu dan har sun hau jirgi waɗannan ne zamu tafi dasu. Har kayan sawa da Mummy ta ɗinkamin bansan adadinsu ba gasunan akwati set guda mai 4pcs. Munyi waya da Maryam daga zuwanmu kusan sau 5 kenan a lokacin na faɗa mata saƙonta dana bari awajen Mama. Har wayar Hannunama yanzu ƙarama ce nabar wancan a bata Baba har lokacin wayarsa a kashe take. Kuɗin wancan account ɗin kuwa tunda aka saka ranar tafiya kullum sai nayi tranfer wa Mama iya gejin Tranfer na account ɗin per day.

Bayan magrib jirginmu zai tashi kafin magrib zazzaɓi ya rufeni saboda kukan danasha. Mummy ta haɗamin ruwa nayi wanka tazo tabani magani nasha sai bacci ana kiran sallah naji a kunnena natashi nayi sallah ina zaune har akayi isha'i natashi na gabatar da sallah ban ida ba saiga Mummy tashigo akan nafito. Har lokacin jikina da ɗumi Mummy ta ƙaramin maganin dan bataso jikin yayi tsanani muka tafi airport kai tsaye. Ayanda naga alamun jirgin babu wasu mutane a cikinsa muka shiga aka kaimu wajan zamanmu muka zauna. Bamufi 30minute da zama ba jirgin ya ɗaga dake nasha magani lokaci guda bacci ya ɗaukeni ga zazzaɓi Sa'i-sa'i kawai nake farkawa ina komawa bansan awa nawa muka ɗauka muna tafiya ba dan inajin zazzaɓi sosai hakan yasa baccin yayi nauyi. A hankali nake buɗe idanuwa na Nayi miƙa haɗe dayin addu'a idona har sun kumbura saboda kuka har alokacin hucin zazzaɓi fita yake a jikina.

Idanuwana suka sauƙa akan Hammood wanda yake zauune cike da damuwa da alamu jira yake natashi dasauri na miƙe ina kallon gefe babu mummy da Anty fadeelah ko Yaya habi namiƙe a hankali zan zauna dan jiki a babu ƙwari ya taimakamin na tashi zaune ina kallon gefe yagane wanda nake nema.

"Sun tafi already mun iso you were sleeping akwai zazzaɓi a jikinki naga kaman kinajin daɗin baccin shiyasa nasa suka fara gaba idan kintashi saimu tafi tare" Na kalleshi da mamaki kawai dan ina bacci shine bazai tayar dani ba? ni banmasan cewa tare muke tafe dashi ba dan 2days kenan banji daga fareshi ba ashe shi tun asuba ya wuce abuja yasauƙa a masauƙinsa sannan bayan isha'i yatafi filim jirgi shahsin daya zauna da muƙarrabansa sabanne yasa bamusan yana ciki ba. Ina ƙoƙarin miƙewa yace.

"Idan baki warware ba zaki iya baccin kawai ko kaɗanne ki ƙara na girgiza kai danni yanzu zanfi ganewa na ganni wajan Mummy. Tallafeni yayi a jikinsa muka sauƙo motoci suna jiranmu ya buɗe mota ya shigar dani a hankali sannan shima ya shiga ta wani gate daban mukabi na filin jirgin batraeda mun fito cikin mutane ba da dukkan alamu cincirindom mutane suna jiran sauƙowarsa shikuma bayason hakan hankalinsa gabaki ɗaya yana gareni gani yake duk ƙarancin hayaniya zata takuramin ne. Tafiya mai tsayi ce takaimu gidan da jami'an tsaro a zagaye da ko'ina. Ni dake a kwance nake idona suna lunshe ban lura da mutanen da suke jiran isowarsa ba ciki harda ƴan jaridu muna shiga aka rufe gate babu wanda zai iya hango cikin gidan. Nanma taimakamin yayi muka shiga har ciki yanayin tsaruwar gidan dakuma zazzaɓin dake jikina sai tasa naga kamar mafarki nakeyi. Kai tsaye ɗaki yawuce dani na ƙwanta ya zauna yana kallona nikuma bacci nema yake ƙoƙarin ƙara ɗaukata. Cikin barci naji yana bani hakuri dan yana ganin shine yayimin causing ciwon nan dayasan halinda zan shiga kenan daya danni zuciyarsa ya ƙaramin lokaci.

A lokacin yakira waya yace akawo su Mummy ɗakina dan yasan idan na farka zanji daɗi naganni kusa dasu. Yana ciki riƙe da hannuna suka shigo dake dama sun rigada sun gaisa yayi musu bayanin likita zaizo dubani sannan ya sunkuyarda kansa a gaban Mummy yayimin peck a goshi duk ina bacci bansan abunda yake faruwa ba.

Mummy bata damuwa ba dan tasan al'adarsu ce hakan bazaiji komai ba ko agaban mahaifinsa ko mahaifiyarsa zaiyi hakan. anty fadeela ce ta kalli gefe dan abun yabata kunya.

Bai daɗe da fita ba likita yazo dubani bayan ya dudduba ko magani bai bani ba yace zazzaɓin zai sauƙa saida yabi can yayi masa bayani dan yana cikin damuwa sannan yatafi da zumnar zai shugo nanda 2hours yasake dubawa ko zazzaɓin yasauƙa.


PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."


ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya


Bai kai 2hours da tafiya ba nafarka zazzaɓin ya sauƙa zafin jikinma ba sosai ba mummy ta tashiga toilet ta haɗamin ruwan wanka mai zafi bath-mist tagani kala-kala cikin toile ɗin duk na mata da kayan wanka kala-kala wanda ga dukkan alamu dan wacce zatayi amfani da ɗakin aka haɗasu tayi amfani da bathmist data gani a cikin toilet ɗin wajan haɗa ruwan wankan dake nata wanda ta haɗomun daga can ba'a buɗe kayanba tukunna. Nan da nan banɗakin ya ɗauki ƙamshi bayan ta haɗa tafito tace nashiga nayi wanka. Namiƙe jikina babu ƙwari na nufi toilet ɗin tunda nashiga ƙamshin ya daki hancina irin ƙamshin turarensa ne sakk sai dai wnnan ƙamshin yafi wancan sanyi ma'ana wancan yayi ƙarfi sosai ba kamar wannan ba da dukkan alamu wanda yake amfani dashi anyishi ne dan maza wannan kuma na mata. ƙare toilet ɗin nake da kallo Nakeyi da badan Mummyn ba bansan yaya za'ayi na iya amfani da abubuwan cikin toilet ɗinba. Gabaki ɗaya na cire kayan jikina na shiga cikin ruwan na ƙwanta lumshe idanuwa na nayi dan naji daɗin ruwan sosai na daɗe ahaka a ciki amma zafin ruwan bai sauƙa ba ga dukkan alamu ta saita ruwan a dai-dai temperature ɗinne bazaiyi ƙasa ba kuma bazaiyi sama ba. Daɗin ruwan ya lulani tunanin dangina ina tunaninsu hawaye yanabin fuskata saida Mummy tayi knocking ganin na daɗe sannan natashi nayi amfani da Showergel dake wajan nayi wanka towel na ɗauka cikin jerinsu na ɗaura sannan nafito Sai alokacin na ƙarewa ɗakin kallo komai na ɗakin farine sall hatta da funitures babu sirkin kala ya tsaru sosai Gaban dressing mirror kuwa mayuka ne da turaruka acike rinkiss kala-kala amma gabaki ɗaya brand ɗinsu ɗaya. Mummy tace na ƙarasa na shafa mai babu nusu na ƙarasa wajan danni kaina wajan ya burgeni inataso na ƙarasa nazauna narasa wanne man zan shafa daƙyar na iya cankan wani na shafa sannan na taso Babu kayanda zan saka a ɗakin gabaki ɗaya kayanmu har yanzu ba'a buɗe suba bamusanma yanda yake ba

42 / 58