Waye Shi Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   19 / 58

54K to 57K   out of 171.2K words

"Yayi ƙarfi kam amma kuma yanada daɗi na maza ne" Nayi saurin na ɗebi kayan nabar wajan. Maryam kuwa ta faɗi hakanne dan ta fahimci turaren Hamma ne tun a napep taji ƙamshinsa amma ganin halinda nake ciki yasa hankalinta bai kawo mata wani abunba sai yanzu dataji Mama tayi tambaya sannan ta fahimci wani abin yasa tayi saurin shiga ta kareta.

A ɗakin Mamana zuba kayan nakoma ɗakinmu na zauna nayi tagumi abun duniya yataru yayimin yawa kawai sai naji hawaye sunabin kumatuna.
Meyasa Hamma zaiyimin haka?" Mai yasa zaiso shiga gonarda bata riga tazama mallakinsa ba? Meyasa zai lulluɓe soyayyarda nakeyi masa da haushinsa? Tabbas yau Hamma ya bani haushi kuma ya ɓata mun rai dan ban taɓa tsammanin haka daga gareshi ba. Toko dama Hamma basona yakeyi bane?" idan yana sonta bazai taɓa aikata mun wannan abunba. Nafaɗa tunani mai zurfi zuciyata ganata kawomin abubuwa kala-kala kawai saina fashe da kuka. Ana haka maryam tashigo ganin ina kuka ta nemi waje ta zauna cikeda tausayina jikinta yamutu takasa rarrashina. Nayi kuka yakai na tsawon 30minute Har yadawo shassheƙa. Sai asannan maryam ta tattaro ƙwarin guiwarta tace.

"Babe please. Dan Allah kiyi haƙuri haba mana. Tundaga kallon yanayinda kika shiga nasan Hamma ya ɓata miki sosai amma yaya zakiyi? Zaki kashe kanki akan namijine? Bayan shi yanacan zaune may be ma harya manta da abunda yafaru. Koma me yafaru nasan Hamma nasonki sosai tnda mece first-love nasa kamar yanda yake a wajanki everything wil be alright okay' just take it easy. Hamma nasonki sosai koma meya faru may be saiya fiki dana sani banajin zai yarda ya saɓa miki dason ransa"

"Na ɗago idanuwana wanda harsun canja kala sunkuma dawowa fararensu nace dagaske kike yana sona?" amma yanzu kika gama cewa may be ma yanacan yama manta da abunda yafaru"

"Uhum yana sonki sosai wancan na faɗane kawai"

"Bakya kallon wani abun bayan soyayya a idonsa" ta jijjiga kai tace.

"absolutely nothing babe" nasauke ajiyar zuciya. Nazuba tagumi ta zauna kawai tana kallona" sai bayan nasamu sauƙin abunda nakeji sannan nashige toilet nayi wanka nafito. Duk yanda naso mu haɗuda Yaya Ahmad bansamu wannan damar ba dan ko palour bansake leƙawa ba har dare yayi. Maimakon nayi karatu dai kuma na lula tunani. Gashi ko message Hamma baiyi minba abunda ya sake ɓatamin rai kenan bare ajega kira ya kirabi yabani haƙuri. Na buɗe littafin amma bana gane komai aciki daga baya kanma zazzaɓine ya rufeni. Haka na ƙwana a daren zazzaɓin bai sakeni ba sai asubahi bayan ya sakeni kuma sai bacci haka na daure nayi sallar asubahi gashi da sassafe mukeda exam bansamu na goma bacci ba haka na tsaya na dudduba littafi ga rashin bacci ga rashin ƙarfin jiki dakuma raunananniyar zuciya"

6 da wasu abubuwan nayi wanka kafin nagama shiri 7 yayi nafito nayi ɗakin Mama maryam itama ta shirya na gaisheda Mama. Ta kalleni jin muryata sai taga fuskata ta kumbura.

"Marmeeyy badai karatun kika kwana kinayi ba idonki yayi haka?" nayi yaƙe kawai tace.

"Aikuwa dai da kinyi baccinki kinga yanda fuskarki ta kumbura? Ana kallonki ansan baki samu bacci ba ana ƙare exam ɗinnan kidawo ki ƙwanfa" toh nace sannan canja zancen da faɗin.

"Babe muje Maryam tataso cikeda tausayinta dan ita tasan abunda yafaru muka yiwa Mama sallama muka fita" kamar yanda nayi tsammani babu motar Hamma a ƙofar gida. Maryam ma tasha mamaki muka wuce muka tafi abunmu"

Kusan nice ƙarshen fita a hall ɗin exam ɗinnan dan abubuwanda nasani basuda yawa bana tunanin sun isheni naci jarabawarnan gashi wani irin bacci nakeji ina zaune har saida lokacin fita yacika likacin 11:00am ina fita nawuce yanda nasan zan samu Maryam. Tana kallona tamiƙe kawai ta isoni muka kama hanyar fita.

"Babe ya exam ɗin dai ta tambaya dan tasan anfafata saboda yanda taganni wujiga-wujiga"

"Hmm kibari kawai sai dai mu nemi taimakon Allah"

"Jiya baki samu bacci ba babe ga dukkann alamu karatunma bakiyishi ba. Babe you have to be strong fa Hmmm tun ba'aje ko'ina ba kina irin haka? Idan iyayenmu suka faɗa miki baƙin cikin maza da suke shanyewa su zauna kamar komai bai faruba zakisha mamaki. Bayin Allahan nan sun shanye abubuwa dayawa sai dai Allah yasaka musu da alkhairi"


Inajinta kawai amma ban tankata ba har muka shiga fita gate muka tsari napep takaimu har gida. Ɗakinmu nawuce ina shiga na canja kayana na ƙwanta sai alokacin nasamu bacci har azahar ban tashiba ina tashi nayi wanka saboda yanyin zafi da ake agarin na shirya nafita palour anan nasamesu duka da zannuwan dana ɗebo jiya nashigo dashi. A gefn Mama. Ina fita palour Mama tace.

"kinga da kika ɗan samu hutun fuskarki harta ɗan saɓe" na zauna muka fara hira sai alokacin nasamu sauƙin abunda nakeji akayita raha sannan Mama ta miƙo mana atamphopin dasuke gefenta kowa ɗaɗɗaya nida Maryam Anty fadeelah da Aysha. Sannan tafara bayani.

"Yayanku yazo dasu Jiya guda shida ankon bikinsane amma bana tunanin zaku samu ɗinki ana yanzu idan kuka bayar sai dai ko can abujan" nace.

"Ni tareda Ya Ahmad zamu tafi dannasan bazai wuce ƙwana biyu ba zai koma"

"Har indai muka kaiwa tailor na zamu samu kafin mutafi cewa maryam" mama tace.

"toh saiku shirya kukai masa" Anty fadeelah da Aysha sy bazasu kaiba dan sunce bazasu jeba. nashiga ɗaki dan ɗaukan mayafina idona yakai kan wayoyina da suke haske suna sanar dani inada missed called ko ajiyayyen saƙo."


ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.



Na ɗauki wayar gabana yana faɗuwa  wayarda Hamma ke kirana da ita nafara ɗauka. saƙonsa ne kamar yanda nayi zato saƙo ne yana mai bani haƙuri haɗeda nuna yayi bai dai-dai ba ya sanar dani cewa kunyar abunda ya aikatamin ya hanashi nemana kuma yahanashi zuwa wajena. Ban amsa saƙon ba na rufeta na ajiye na ɗauki ɗayar wayan saƙon wancan mutumin ne ita Kuma yanamum murna da kammala jarabawata. Na taɓe baki sannan na zuba wayoyin acikin jakata. na ɗauki veil ɗina na fito. Nasamu Maryam harta shirya kai tsaye muka kai ɗinkin muka dawo batareda ɓata lokaci ba dan banason zama ma a wajan. Ya shaida mana nan da 2days zamu samu dan haka mun bashi kuɗin ɗinkin kawai munjuyo. Idan yagama zamuje mu ƙarɓa kokuma yakawo mana har gida.

Mun samu Ya Ahmad a wajan Mama. Mama tana kallonmu tace.

"Har kunkai kenan?" muka amsa mata da.

"eh" tace aikuwa kunyi sauri dama yanzu Yayanku ke tambayar wajanki" saida na zauna sannan nace.

"Ina wuni Yaya" lafiya Marmeeyy yafaɗa alokacinda yake ɗago idanuwansa ya dibeni Maryam ma tace ina wuni ya amsa mata yana kallona sai naga kuma ya haɗe rai yace.

"marmeyy wannan ƙaramin gyalen fa? Ahaka kika fita?" na dubi veil ɗin jikina na turo baki nace Ya Ahmad me yayi?" Mama tayimin danƙwalo tace.


"ƙaniyarki yayi marmeeyy" Maryam tana jin haka tayi wuff tashige ɗaki. Ya Ahmad yacigaba da faɗin.

"Mama kar abatta tasake fita ahaka Baba yasan kinfita? Da izininsa kika fita zan gaya masa ya hanaki bazaki sake fitaba" mama tace.

"Toh shikenan in sha Allahu bazata sake fita ba. Kayi haƙuri" Nace.

"Yaya ni bazanma sake fita ba sai ranar da zamu tafi"

"Thou yayi jibi zamu tafi kushirya dawuri fitar sassafe zamuyi inaso kusamu event da za'ayi" Harna fara murna saina tuno ɗinkinmu nace.

"yaya akwai ɗinkinmu wajan tela fa kuma yace zai kai jibin"

"Kubani lambarsa idanna fita zan kirashi na ƙara masa kuɗi yayi zuwa goben"

"Yaya amma fa da Maryam zamu tafi"

"agidansu za'a barta ne" ya tambaya.

"Ai yanzu anan gidan takeda zama Umminta da abbanta sunyi tafiya kaga idanna tafi nabarta bazataji daɗin zama ba"

"Toh " kawai ya amsa dashi sannan ya miƙe yace.

"Itama sai akarɓa mata ashoben koh?" Mama tace.

"Nabata nawa ma shine yanzu suka kai ɗinkinsa"

"thou Bari naje Baba yana jirana" yafaɗa haɗeda ficewa.
A palour yasamu Baba amma kamar fitowarsa kenan danko zama baiyiba. Yashiga da Sallama Baba ya amsa a lokacinda yake ƙarasa zaunawa. Bayan sun gaisa Baba yace.

"Kunyi magana da Mummynku akan zamanka anan?" saida ya sunkuyarda kai sannan yace.

"Bamuyi magana da itaba amma munyi magana da yarinyar da iyayenta kuma sun amince sun nuna jin daɗinsu akan hakan. Mummy ko bayan biki zan gaya mata tunda dama ba daga biki bane za'a kawota ba sai bayan wani ɗan lokaci"

"okay toh amma kasamu gidan kuwa?"

"Eh shine yanxu nazo na ɗaukeka muje mu gani idan yayi sai ayi maganarsa"

"Toh ma sha Allah hakan yayi sai muje kawai koh?"
Miƙewa Baba yayi yafara tafiya sannan Ya Ahmad ya bishi a baya suna zuwa jikin mota ya buɗewa Baba ƙofar motan yashiga yarufe sannan yaje ya buɗe gate sannan yadawo yazagaya shima yashiga ta mazaunin driver. Saida yafita agidan sannan yafita yarufe gate ɗin yakoma yaja suka tafi saida sukayi nisa sannan yadubi Baba yace.

"Baba mai yasa ake barin Marmeeyy tana fita anyhow? Kasanfa bai kamata kabarta taringa fitaba idan bawai school ba duba da abunda yafaru. yazama dole asanya ido akanta sosai kar azo ana danasane kar a cutarda ita" baba ya yi ƴar gyaran murya sannan yace.

"Hakane yanzu bari suje bikinka su dawo tukunna sai muga abunda za'ayi" Sunje sunga gida yayi kyau sosai dama saida suka biya suka ɗau dillalin gidaje daganan suke wuce wajan mai gidan a lokacin akayi magana aka kafa shaida aka siya tunda dama ba yanzu aka fara maganar ba tun wancan zuwan Hamma aka fara maganar. Bayan sun dawo yanemi mai ɗinkinmu ya ƙara masa kuɗi sanann sukayi yarjejeniya akan gobe zamu samu.


Murna da ɗaukin tafiyarda zanyi ta cikamin cikina ya kawar minda baƙin cikin danake ciki. Aranar kusam saƙo 5 Hamma yayimin ko guda ɗaya banyi masa reply ba banmasan me zance masaba ayayinda zanyi reply ɗin dan haka kawai na sharesu. Amma zuciyata ta rigada ta sauƙo tayi rauni ayanda naga yanata bani haƙuri yana faɗin wallh bada niyya yayi bai baitaɓa tunanin aikata hakan agareni ba. Shi tunda yake a rayuwarsa ma bai taɓa attempting ɗin gwada hakan bama. Ko jiyanma akasi kawai aka samu baiyi niyyar hakanba. Ƙamshin turarenda yake jikina ya tada masa hankali daya kasa jurewa amma dukda hakanma yasan hakan bawai Hujja bace da zaisa ya aikatamin haka ba kuma bawai yana faɗan hakan bane dan kare kansa ba sai dan ya samawa zuciyata nutsuwa. Na tabbata da Yayi nadamar abunda ya aikata domin kuwa kalmansa sun nuna hakan. Ni yanzu har tausayi ma yake bani. Har dare nasamu messages ɗinsa sosai har washe gari na tashi na tarasda message ɗinsa.

Washe gari muka fara shirye-shirye nikam harna haɗe kayana waje ɗaya.

Maryam ma ta haɗe nata su Aysha da anty fadeelah kam dagaske suke bazasu je ɗinba dan babu alamun hakan.

Da Yamma tela yakira Ya Ahmad yace yagama ɗinkin. Ya kawo masa har gida muna zaune ya Ahmad yasghigo dashi yabamu" yadubi anty fadeela yace.

"Ke fadeelah angama muku nakune"

"mu wai? Ai bamu kai ɗinkin ba" tabashi amsa.


"me zakuyi amfani dashi kenan" ya tambaya. Caraf na amshe nace.

"Ai sunce bazasu jeba" da mamaki yace.

"Bikinnawa ne bazaku jeba?" taɓata rai sosai tace.

"Kafa san halin Mummy bazata bari mudawo ba har indai mukaje" tsaki kawai yaja yabar ɗakin yayi wajan Baba. Bayan Baba yafito sallar magrib yatsaya wajan Mama yace takira masa yaran. Muna ciki mama tashigo wai muzo inji Baba. Muka fice dukanmu yacewa su Aysha.

"Yayanku yacemin wai bazaku je bikinsa ba?" Aysha tace.

"Baba gara kar muje kasan halin mmmy bazata bari mudawo ba" Baba yace.

"Kuje babu abunda zai faru zaku dawo rana ɗayama zaku dawo dasu Marmeeyy bazan bari ku ƙara ko ƙwana ɗaya agarinba" da haka suka amince zasuje amma har lokaci zuciyarsu tana musu ɗar-ɗar kafin yafita yace nahaɗa masa shayi kafin yadawo.

ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.


Kafin yadawo na haɗa masa shayinsa Na rage wuta yana heating a hankali na zauna Ina jiran dawowarsa muna zaune naji shigowarsa na juye a mug nakai masa. Da casbi na sameshi a hannu yana jaa nashiga nayi masa sannu na jawo glass table dake gefen kujera har gabansa na zuba masa shayin a ƴan ƙananun kofi na ajiye gefe yaɗan huce saina zauna akan carfet yana yimin sannu nayi murmushi. Yace.

"Gobe zaku tafi koh?"

"Eh" nabashi amsa.

"akula sosai kinji koh" sannan ga wannan ya ciro bandir ƴan 200 20k kenan ya bani yace.

"Idan zakiyi amfani dashi" dasauri na girgiza kai nace.

"A'a Baba kabarshi kawai babu abunda zamu buƙata koma mun buƙata Yaa Ahmad zai bamu" Ya ajiye Kuɗin agefena yace.

"Wannan kuma ni Babanku nabaku kuyi amfani dashi" nayi ƙasa da kaina nakasa jurewa nace Baba ina kasamu kuɗi?" dannasan Baba baida kuɗi wata rana 2k ma dayaya yake samunta? Haka kawai zaiyimin kyautar 20k bayan nasan ba lallai idan shi yanada hakan a ajiye ba. A kullum shi yanaso ya takura kansa wajan faranta mana. Saida yayi murmushi sannan yace.


"Yakamata Baba yazo yakama sana'a tunda gashi ƴarsama tasan bayayi tana tambayarsa yanda yasamu kuɗi" na girgiza kaina nace.

"bahaka nake nufi ba Baba banaso ka tukura kanka ne kasan komai mukeso za'ayi mana acan"

"Yayanki Ahmad yabani dubu ɗari biyu aciki nabaku ni ban takura kaina ba kuma duk wani abinda zanyi muku ba takura kai bane" na jijjiga kai na amsho kuɗin ina godiya. nace.

"Baba kai sai yaushe zakazo? Yayi shiru Sannan yace.

"Yakamata naje ne?" na jijjiga masa kai sannan nace.

"Sosai ma Baba idan bakajeba Ya Ahmad bazaiji daɗiba koda ba zai iya fitowa ya nuna maka ba. Idan kuma kaje zaiji daɗinda bazai kasa nuna maka ba" Shiru yayi baice komai ba Nakai kusan 9 aɗakinsa har Anty tashigo dake itace a ɗakin ina ganinta namiƙe nayi musu Sallama na fita.

Ɗakin mama nawuce kai tsaye nasake fitowa duk wasu Abubuwanda nasan zan buƙata mama tasake shiryaminsu saida tayimin faɗa itama. sosai akan tafiyarda zamuyi. Nakai wajan 10:00pm wajanta kafin natashi natafi.

dana shiga ɗaki naga missed call na Hamma banbi takaiba dan kona kira bansan abunda zance masa ba. Mun ƙwanta Da wuri saboda tashin wuri.

Washe gari tunda mukayi sallar asubahi bamu koma bacci ba. da sassafe muka shirya tafiya har Baba ya rakomu har mota da Mama anty kam bata fitoba dan ita wajanda Ya Ahmad yake bata zama dan bayajin tsoron disgracing ɗinta gaban kowa. harda Yaya habibu a tafiyar. Mu bamusanma dashi za'a tafi ba sai ganinsa mukayi ya shirya ya fito. Muka shiga motar dukanmu muna baya sai Yaya habibu yana zaune agaba.
Addu'a Baba yasanya mukayi sannan yayi mana sallama nan da nan naji idanuwana sun fara cikowa da hawaye dan tunda nake bantaɓa tafiya nabarsu ba koda sau ɗaya ne kullum inanan ina naniƙe da iyayena. Idona taciko taff na runtsesu inajin wani iri acikin zuciyata kamar wacce zantafi nabardu gabaki ɗaya. Har muka ɗauki hanya addu'a nakeyi acikin raina idona suna lumshe ban buɗesu ba. Ina jiyosu har suka fara hira. ban buɗe idanuwana na ba har saida naji ƙarar wayata ina dubawa naga Hamma batareda na amsa ba najira ta katse na sanyata a silent na maida jaka. Anata hira bansaka baki ba sai can yaa Ahmad yace.

"Wai ina marmeeyy ce ko bacci tayine?"

"Ganinnan" nabashi amsa.

"Naji bakinne ya mutu muɗus. Kardai duk san tafiyar abakine?"

"A'a Yaya kasan nifa bantaɓa tafiya ba"

"Tooh kar amin amai amota" yafaɗa hankalinsa yana kan tuƙinsa. Tunda muka fara nisa ya lura da wata mota a gabanmu ɓaka siɗik wanda taɗan bamu tazara kaɗan. Bayan kusan 30minute ya gano wata a bayanmu motocin ba iri ɗaya bane amma jikinsa yabashi tafiyarsu ɗaya kokuma yace tafiyarmu ɗaya atakaice. Ta bayanmu bata zo ta wuce ba dukda bawani gudu muke ba, ƴat tazara tabada a tsakaninmu. ta saita speed ɗinta dai-dai da namu namu yanda tazarar bazatayi yawa ba sannan kuma kusancin bazaiyi yawa ba. Ta gabanmu kuma batayi nisa damu sosai ba. sunyi abun atsari yanda baza'a fahimci komai ba amma Yaa Ahmad dake yasan komai dole zai fahimci wani abun.
Murmushi kawai yayi dan ya tabba wannan motar tare muke tafiya dasu. Yayi tsammanin hakan sai yaji abun ya matuƙar birgeshi dan koshine a matsayin Hammood zai bawa abunda yakeso tsaro na mamaki wanda idanba ikon Allah
ba babu wani abunda zai iya tunkarar abunda yakeso. Hankalinsa ƙwance yake tuƙinsa har muka kusa isa Abuja."

__________


Ƙarfe uku na dare jirginsu ya sauƙa a Abuja cikin sirri dan babu wanda yasanda hakan. Ko ma'aikatan filin jirgin manyan kawai sukasan da sauƙar kuma angargaɗesu da kar kowa yasani dan haka bbau wani yasani daga ƙofar filin jirgin motaci sukazo taryansu aka wuce dasu masauƙinsu.

Yariga mahaifinsa sauƙa danshi sai awajan asubahi ya sauƙa dama shi yake jira tafiyarsu da bambanci.shi daga Abu dhabi yazo mahaifinsa daga kuwait kuma lokacin tashinsu ba ɗaya ba so dole aka samu bambamcin lokaci dama shi isowar mahaifinsa yake jira so yana isowa jirginsu yatashi zuwa bauchi Acan sukayi sallar Asubahi.

Abhie yana sanardashi cewa Nawrah ta matsa sai yazo da ita. Baizo da itaba saboda bai fahimci amfanin zuwannta a yanzu ba yayi mata alƙawarin next zuwa da ita zaizo amma yanzuma yasan halinta da taurin kai ba lallai idan ya amince ta zauna ɗinba. Murmushi kawai moood yayi sanin cewa sassafe Marmeeyy zatabar garin koda tayi gigin zuwa bazata haɗuda itaba dan yasan damuwarta ta ganta ne kawai, shikuma ba yanzu yayi niyyar nunawa duniya itaba yasan wacece Nawrah da zarar da santa ta kowa ya santa. Yasan yanda rayuwarsa take akan idon mutane ko kaya yasaka sai an faɗi kuɗinsa har turarenda yake shafawa mutane sunsan kuɗinsa. Amma wannan karon lamarin ysha bambam. Ya barwa mutane abunda yaga damar su sani amma banda wannan

19 / 58