Waye Shi Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   17 / 58

48K to 51K   out of 171.2K words

zanje ba zan dawo gidan mahaifina bayan bikin yayana zan dawo gidanmu kinga ai bazata ƙi karɓan baƙin da sukaje mata biki ba nikuma gayyar Yaa ahmad nema ba nata ba. Kudai da kukejin bazakuje ba saboda kunajin tsoro ku zauna idan mundawo zamu baku labarin yanda bikin ya kasance"

  "Uhmm" Kawai tafaɗa tana mamakin ƙarfin hali irinna marmeey. Amma tasan al'amura bazasu tafi dai-dai da Mummy ba."


Ɗaukan littafina nayi nafara karatu ban daɗe dafara karatu ba kiran Hamma yashigo na ajiye littafin gefe muka hau waya bamu mukayi sallama ba sai da 12:00am tayi muna sallama na ƙwanta bacci.


    ---------

Sun buga wasan ƙwallo sun dawo cikeda tarin nasarori dama bayan dawowarsa ya shirya zuwa wajan mahaifinsa.

Ƙwana biyu kawai ya ƙara ayanda ya tsara suka shirya tareda nawrah suka nufi wajan mahaifinsu a ƙasar Kuwait.

   Dake tafiyar jirgi bawani nisa bane tsakanin Abu dhabi da kuwait ba tafiyar 2hours takaisu har cikin gidan mahaifinsu.

Gidane mai girman gaske yafi ƙarfin akirashi da anguwa guda wanda mutanenda suke rayuwa a cikinsa su kansu basusan kansu ba gidane wanda yake ƙunshe duk wani abunda ɗan adam zai buƙata akwaishi acikin wannan gida hatta da asibiti da filin jirginda helicopter ɗinsu yake tashi. Su Hammood kuwa koda isarsu a main airport suka sauƙa lokacin ɗan ƙaramin jirgi na mahaifinsu yana jiransu suna sauƙa suka tashi izuwa gidansu. Duk wannan gida mallakin mutum ɗaya ne amma shi kansa baisan yawan mutanenda suke rayuwa a wannan gida ba.

  Suna sauƙa wajanda jirgin ke sauƙa akwai motocinda suke jiransu da zasu kaisu cikin gidan" saida sukayi tafiya 15minute acikin gidan kafinnan ta kaisu zuwa ainihin kan gidan tako'ina suka ratsa sojojine suke tsaran gidan tun daga farkonsa har ƙarshensa. Suna isa aka buɗe musu ƙofa suka shiga ciki babbar  ƙofarda zata kaika cikin gidan mai masifar tsayice tafi tsayin mutum biyu daga nan sai wani tangamememen palour wanda aƙalla kujerun ciki sun kai 5set kowanne ɓari da nata. Wani balarabe kyakkyawa wanda bazai wuce 55years ba yake sauƙowa daga faffaɗan matakalarda take yalli kamar wanda aka yita sa diamon komai na gidan tangamemene komai an yankeshi da girma. Suna haɗa idanuwa da wannan mutumin ya sakar masa murmushi shima murmushin ya sakar masa yana ƙarasowa ya buɗe masa hannu. Ya ƙarasa yayi hugging mahaifinsa. Cikeda ƙauna da ɗumbin soyayya mahaifin yayi masa peck a gefen kumatu shima ya mayar masa sannan yace.

"مرحبا بك في البيت حمود حبيبي "
(welcome Home Hammod).

شكرن يا أبي
(thank you father) Nawrah dake gefe tacika tayi Famm mahaifin baima lurada ita a wajanba har saida yaji takun tafiyarta tana shirin barin wajen.
Saida yayi dariya dan yasan rikicinta sannan yace.

أنا آسف ياحبيبتي تعال وعانقني
( I'm sorry my dear come hug me)
Ta kaɗa kai tayi wani gefen batareda ta jiyo ba ya furzarda iska haɗeda girgiza kai yana dariya yasan halinta sarai mugun zafin kaine da ita. A kujerunda sukafi kowannen kyau da tsaruwa a cikin falon suka zauna. Mahaifin yace.

"Kacika alƙawarinka Hammood naji daɗin ganinka sosai" Shima yace.

"Naji daɗin ganinka nima" Suna zaune a wajan suna tattaunawa har aka kira magrib Dagannan suka tashi sukayi sallah basu shigoba har bayan isha'i. Mahaifin yasa a sanarda gabaki ɗaya iyalansa akan tare zasuyi dinner. da Hammood dan haka 8:30pm tayiwa kowannensu wajan cin abinci. Hakan kuw akayi kafin 8:30pm dukansu sun hallara Har Nawrah da Hammood. Sai mahaifinsu da wasu mata guda biyu ga dukkan alamu matansa ne sai yara mata guda uku da namiji guda ɗaya. namijin shine yashigo a ƙarshe bazai wuce 13years ba gabaki ɗayansa. Dukansu ƙannen Hammood ne amma iyayensu daban waɗannan mata da suke zaune a wajan sune suka haifesu kowacce yaranta biyu. Suka fara dinner cikin ƙwanciyar hankali amma affan ya damu Hammood sosai yayi murna da ganinsa dan haka zuba kawai yakeyi ko a kujera ata kusa dashi ya zauna ƙanwarsa ta zauna akai ya tasheta ya zauna kafin sugama yayi musu selfie yafi sau goma. Mahaifin dariya kawai yakeyi shiyasa yakeson Hammood yazo gida basa samun damar zama haka da iyalansa sai idan Hammood yana nan, saboda kowa na ɗaukin zama da cin abinci dashi. In bayanan kuwa ya tabbata wasu daga cikin iyalansa sukan iya months ko hanya bata haɗasu ba."


ZAYNAB ALABURA

*BIBIYATA YAKEYI*
        *(WAYE SHI)*





       Har matan mahaifinsa ma kowacce burinta ace da jituwa a tsakaninsu saboda yanda mahaifinsa kejin maganarsa. Bayan sun gama  dinner sai aka zauna palour aka taɓa hira alokacin affan yashima yayi video yasake wani haka yakeyi dama koda yaushe Hammod yake gari aikinsa kenan.

  A hankali da ɗai-ɗai dukaninsu suka fara watsewa har suka watse duka saura Affan shi kaɗai. Dawayo mahaifin ya koreshi yace.

"Habibi  اترك اخاك حمود ليستريح  (Leave your brother alone to rest)" yatashi badan ransa yasoba yayi musu sallama yafita. Suka tashi suka tafi can waje wajan wani shaƙatawa lamuben a wajan sai ruwa da akayi mishi wani design da dutsina wajan yayi kamada beach. Suka zauna idanuwansu nakan ruwanda yake zubowa. Yanayin wajanma kawai zai sauƙarda nutsuwa da kwanciyar hankali.

"Yaya ka sameta?" Shine tambayarda mahaifin nasa ya jefo masa.

"Tana lafiya" yabashi amsa.

"I need more explanation" mahaifin ya faɗi.

"Dafarko dai ina kallonta sai naji na ƙara sonta" mahaifin saida yayi dariya sannan yace"

"You got my approval" dan dama yace yaje ya ganta har indai bayan yaje yaji ani abun nata baiyi masa ba ko yaji bata ƙwanta masa araiba toh bazai amince da auren ba. Hammoda ya ɗaura da faɗin.

"Inason komai tattare da ita ina shagaltuwa da kallonta alokacinda take magana sannan alokacinda nafara ɗaura idanuwa na akanta nasamu nutsuwarda bantaɓa samun makamanciyarta ba. Bantaɓa jin irin wannan soyayyar ko alabari ba sai akaina. Babu wani sabo da mukayi da ita batama san ina sonta ba amma dana tafi nabarta na tsinci kaina cikin kaɗaicin da bantaɓa tsintar kaina aciki ba. I get used to living  alone but not anymore. Moreover i see my world in her eyes" Saida Abbie ya nisa sannan yace.

" i am hapy for you yarona ya samu abunda yakeso nayi maka alƙawarin mallaka maka ita kota wani irin hali" ya girgiza kai haɗeda yin dariya yace.

"Abbie barni nazama namiji na tinkareta na samu soyayya kamar yanda ordinary people suke samu"

"Hammood Habibi you're not ordinary person. Kayi amfani da damarka alokacinda Allah yabaka. Dama yabaka ne danka moreta" Dariya kawai yayi batareda yabawa mahaifinsa amsa ba. Mahaifin yace.

"Your mum sai yaushe zaka rarrasheta harta amince?"

"Just leave her kasan Mum bazata taɓa amincewa ba. She's not the type to give up easily"

"ka rarrasheta she's still your mum"

"bayan yarinyar tazo gidan saina rarrasheta ta amince. Amma banda yanzu zata iya ruguza komai kasan hakan tunda kafi kowa sanin halinta" Baban ya jijjiga kai yace.

"Hakan yayi amma yazama dole bayan lokacin kayi mata biyayya ka sanya ta amince"

"Toh" shine abunda yafaɗa kawai. Danshima ya ƙudirta hakan amma sai bayan aure.

"Yaushe zaka koma ganinta?"

"Nan sa 1month ko three month i guess. I missed her" Abbie yayi murmushi kawai yanajin daɗin zama da sukayi da ɗansa yana masa expressing feelings dake cikin zuciyarsa yana faɗa masa cikinsa wanda abaya sam baya iyawa. Yawanci zaman kurame sukeyi sai dai mahaifin yayita hirarsa yana amsawa sama-sama. Shikam dai zaice yaji daɗin wannan tatayyar Hammood da wannan yarinya ko babu komai ya samu kusanci sosai da ɗansa gashinan yanzu a 2months ya ganshi har sau biyu idan abaya ne saisu doshi shekara basu haɗuba yakance aiki yayi masa yawa sai dai shi yatashi yaje ganinsa amma yanzu gashi yana cewa yazo ya amince kuma yazo ɗin har suna zaune suna hira cikeda sabo.

Suna zaune nawrah tafito ta samesu dayaks tasan nanne wajan zaman mahaifin nasu da dare kai tsaye nan za'a ganshi. Zama tayi a cikinsu sukaci gaba da hira. Abbie yacewa Hammood.

"Wannan zuwanne nawa ko sai wani?"
"duk yanda kayi" yabashi amsa.

"okay idan kaje saina biyoka a baya kona baro saika dawo duk yanda ta yiwu dai" Nawrah dake sauraronsu tace.

  "Ina zakuje"

"Ganin surikar gidannan" abbie yabata amsa. Tayi insisting akan lallai itama sai anje da ita zataje ta ganta. Hammood yace.

"La nawrah habibty not know kibari saita amince dani tukunna sai kije mata matsayin ƴar uwa" da rashin fahimta Nawrah tace.

"What? Banganeba har yanzu bata amince dakai ba me take ɗaukan kanta?" abbie yayi dariya yasam zafin kan nawrah sannan yafara lallashinta.

اهدأ النورة حبيبتي"
"(Calm down Nawrah Habibty) Yayanki fa na miji ne karki duba matsayinsa dole saiya jajirce har indai yana son zama da mace ya ajiye matsayinsa agefe ya saka aramsa shi ba kowa bane sannan mace za ƙwantar da kanta tayi masa biyayya iya iyawarta ta sama masa farin ciki. Alokacinda ya ajiye rawanin sarautarsa alokacin zata naɗa masa rawanin a fadarta. Ke macece nasan kinsan hakan so ki barshi ya nemo soyayyarsa ta hanyarda zai iya" taɓe baki tayi dan maganar bata zauna mata akai ba kuma tasan halin abbiensu Hammood ko batunda yazo masa bamai kama kai bane bazaiyi wani tunani ba saiya amince. Bata daɗeba tayi musu salmama ta koma ciki. Tana shiga jikinta har ɓari yakeyi takira layin Mum ɗinsu bayan ta ɗauka ta shaida mata abunda yake faruwa cikeda ɓacin rai. Mum tace.

"Hakan yayi kyau sosai tunda yarinyar bata karɓeshi ba tukunna komai zaizo mana da sauƙi naji daɗin wannan labarin yanzu haka ki sanya ido kiga abunda zanyi amma sai kinmin abu ɗaya duk yanda za'ayi kiyi kutafi tare sam karki barshi yatafi shi ɗaya yayi kyakkyawan tsaro akan yarinyar nan ta tsohe duk wata kafa da zamusan yanda take wanann karon mu nuna masa muma munada wayo. Babu yanda za'ayi yana sananne a duniya ya auri wacce zamuji kunyar munata yanzu haka da zuwa gobe kisan yanda zakiyi ki shawo kansa yayarda kutafi tare idan bai amince ba cikin guards ɗinsa dole zamu samu wanda zai mana aiki" cikeda jin daɗin mahaifiyarta ta nema musu mafita sukayi sallama.


Hammood basu tashi a wajanba saida dare ya taba Sannan ya koma shashinsa an gyara ko'ina an canja komai according to his taste. Wanka yashiha yafara yi sannan yadawo ya zauna alokacin  yaji wata irin kewarta a duk lokacinda yayi maganarta aranar haka zai tsunduma cikin kewarta.

"Wayarsa ya ɗauko ya tura saƙo".


-------------

   Ina zaune saƙo yashigo wayata saida gabana yayi mummunan faɗuwa saboda nasan daga yanda saƙon yataho."



    ZAYNAB ALABURA

*BIBIYATA YAKEYI*
(WAYE SHI?)




Lokacin munagama waya da Hamma kenan dan kusan raba dare mukayi muna waya saboda washe gari zaiyi tafiya kuma zai zama busy ba lallai musamu lokacinda zamuyi waya ba. Ina shirin ƙwanciya saƙon yashigo wayata saida nasamu mummunan faɗuwar gaba sanin ta yanda saƙon ya fito. Kamar bazan duba saƙonba sai kuma na janyo wayar dan zuciyata bata iya jure share saƙon nashiga cikin message ɗin sai naga saƙo kamar haka. (Did you missed missed me?) dasauri na ajiye wayar gaban yanata bugawa nace wannan bawan Allahn duk wata hanya da zaibi yabawa mutum mamaki ya santa. Tayaya akayi yasan nayi tunaninsa? Na saka wayar a silent na ajiyeta gefe na ƙwanta bacci maimakon bacci ya ɗaukeni sai kuma nashiga tunani. Yazama dole da zarar nagama wannan exam ɗin nan nabawa Hamma damar fitowa da kowa zai sanshi iyaye su shiga magana. Idanba  hakaba wannan mutumin da batasan waye shi ba zai iya fitomin ta hanyarda banyi zato ba. Da wannan tunanin araina nayi bacci."

  Tun daga wannan  lokacin ban ƙara samun saƙo daga gareshi ba kuma hakan ya samamin nutsuwa sosai danna tabbatarda lafiya qalau. Na kauda hankalina gabaki ɗaya yakoma kan Hamma dakuma exam dayake ƙaratowa Maryam bata sake tunamin tanason zama gidanmu ba nima ban sanarda ita yanda mukayi da Baba ba ganin Baba bai bani wani feed back ba may be koya manta kokuma mahaifinta bai amince ba. Hakan yasa bansake tuna masa zancen ba."


Yau yarage saura 3week bikin Ya Ahmad mukuma saura saura 1week mufara exam. Yanzu bama shiga school sosai saboda kowani lacture yayi covering ko Hamma bamucika samun haɗuwa dashi ba ko waya baya kirana da dare sosai sai yace nayi karatu.

Karati nayishi harna gashi dan haka nataso nafito palour yanda najiyo muryarsu Mama, anty, Anty fadeelah da Aysha. Daga lokacin dawowarmu ɗakin mama zuwa yanzu ba ƙaramin shaƙuwa bane tashiga tatsakanin su Mama dasu Aysha ba. Kulawarda suke samu wajanta ko wajan Mummynsu basu sami kamarta ba, ko abu Mama zata saya idan batada kuɗinda zata saya mana gabaki ɗaya toh takan haƙura ne. Anty ma yanzu suna gaisheta kuma tana masawa sannan Ana zaunawa ayi hira gabaki ɗaya. Ina fitowa Mama tace.

"Marmeeyy angama karatunne?"
Na zauna kan carfet nace..

" bangama ba Mama kawai na gajine shine nafito nahuta karatun duk babu daɗi"

"Gara kina hutawa ai ƙwaƙwalwar saita samu huta idanba hakaba idan stress na karatun yayi yawa sai kiga kinayi yana zubewa ana tufka da warwara"

"Ainagani dan saina gama idanna dawo baya sai naji kamar bansan komai ba dan haka ban sake ɗaukan littafi sai gobe" Aysha tace.

"Da'Allah ba'ace kizaƙe dayawa ba meye laifin da daddare? Yarinya da a Atbu kime dakin gane kurenki" harararta nayi nace.

"Keda kike Atbun ai naga kin gane kurenki" dama kusada ita nake zaune ta sanya Hannu ta dungure kaina tana faɗin.

"Kekam dai kinjiwa rashin kunya daɗi" mama tace.

"Make bakin zaki ringa yi zata shiga hankalinta ai maras kunya. Idan ta'isa tayiwa Yayanta Mana (Habibu)" Aysha tace.

"Aishi zansa yamata duka yanda bazata sakemin rashin kunya ba"

"Idan kunyi haƙuri ma ana gama Exam zan kama hanyata nabi Yaa Ahmad bazan dawo ba sai kunnemeni" na faɗa na dake. Anty fadeela wacce sai lokacin tasaka baki tace.

"Aikuwa zakije ki haɗu da dai-dai dake dan Mummy Aya ce ingaya miki" mama ta danƙwaleta da hannu ta rufa bakinta tana dariya itama Aysha dariyar tasaka harda ƴar ƙwafarta.

Muna zaune saiga Yaya Habibu yashigo da sallama haɗe da Ƙatuwar trolly a hannunsa saida yakaitta ƙofar shiga ɗakin Mama sannan ya ajiye muduka muna binsa da kallo bamu kaiga tambaya ba saiga Maryam nan tashigo da sallamarta Hannunta ɗauke da ƴar ƙaramar trolley sai jakan Hannunta. Dasauri natashi da murnata nayi kanta ina ihu zanyi hugging ɗinta ta tureni gefe tana faɗin.

"da Allah matsa ko meye ruwanki dani? Keda bakyaso nazo?" wanda sukeso naso ai gashinan sunyi magana nazo" ban kaiga tanka mata ba mukaji muryar Umminsu tana faɗin.

"Nima matsamin a hanya kona tureki kema" nayi gefe ina faɗin.

" sannu da zuwa Ummi"

"Yawwa sannu Marmeeyy " maryam tayi ciki mama tana faɗin.

"Marmeeyy bazaki karɓi kayan hannun Maryam ɗinba?"

"Batta tashigo da kayanta nafaɗa ina zaunawa Ummi ƙaraso ciki Mama tanayi mata barka da zuwa. Ta zauna suka gaggaisa. Dama tun ranar walimar sauƙarmu da suka haɗu basu sake haɗuwa ba.
Ummi tace.

"Ga maryam nan sai haƙuri min haɗaku da aiki"
Mama tace.

"Ko menene abin aiki?" aida Marmeeyy da Maryam Duk ɗaya suke" Ummi tayita godiya. A haife ta girmi Mama sosai amma dayake macece mai gyara bazaka taɓa cewa takai shekarunta ba. Ummi tace.

"Abbansu yana mota wai yanaso su gaisa da Babansu daga nan Abuja zamu wuce anan zamu tashi" Mama tace"

"Toh bari ayi masa magana kishigo dashi. Dukansu suka miƙe Mama taje ta sanarwa Baba sannan aka buɗe masa ƙofa suka shigo shida Hamma da Ƙofar Babban falonsa"

" Sun daɗe aciki suna hira ashe sunsan juna tun suna samari amma dai bawani sanayya can ba sai gashi kuma zumunci ya ƙullu yanzu. kusan 1hour Abba yana wajan Baba har Hamma yakoma mota yabarsu dan shi zai kaisu. Ummi ma na wajan Mama amma batayi zaton Abba zai jima haka wajan Baba ba.

"Kinga dai ta dalilin yara zumunci ya ƙullu" cewar Ummi. Mama tace.

"Gashinan sai dai muyi fatan Allah ya rayasu zumunci yacigaba ko bayan ranmu. Duka suka amsa da Amin.

Bayan Abba yafito muka rakasu har waje danyi musu Sallama sai alokacin naga Hamma. A kunyace na gaisheshi na fisge. Yanata kallona nikuma Allah. Allah nakeyi kar wani ya lurada irin kallonda yake yimin dan duk rashin fahimtar mutum idan yaga kallonda yake yimin saiya fahimci wani abun. Kamar baisanda mutane a wajanba yaketa aikamin da kallo daga ƙarshe na ɓuya a bayan Maryam har aka gama sallama akayi addu'a suka tada mota a zatona babu wanda ya lurada kallonda yake yimin Ashe bansaniba duk abunda yakeyi akan idon Abbansu. Muna kallonsu har motarsu tatashi ta kaucewa ganin idonmu sannan muka koma ciki."



ZAYNAB ALABURA

Wannan littafin na kuɗine kibiya  ₦300 ta asusun  bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

    A ɗakin Mama Maryam tasauƙa dan kayanta ma anan aka zubasu. Shikenan mukabar karatu muka shiga sharholiya. Maimakon musamu karatu kamar yanda muke tunani sai kuma wasa saida Mama taci ƙaniyarmu kafinnan muka Cigaba da karatu.

  
Koda yaushe da  rana muna palour ko cikin gida kokuma ɗakinmu na daa da dare muke rabuwa ita tashige ɗakin Mama mukuma mushiga ɗakinmu. Ƙwana biyu Hamma yayi acan yadawo. Amma bayan 3days yasake komawa.


sai ana gobe za'a fara exam kafin  nasake samun saƙo daga wancan numbern anamin addu'ar farawa a sa'a.  Tun daga ranar kusan kullum ne ƙwana duniya sai nasamu saƙon addu'a daga wannan number dake gabaki ɗaya ma yanzu wayar ba damuna tayi ba yasanya nafita harkarta tunda ko data bana buɗewa.

Wancan wayarne take kullum atare dani dannasan Hammana yakan kirani idan yasamu sarari a aikin daya jeyi.

Maryam kuwa wata shaƙuwace na lura tashiga tsakaninsu da Yaya Habib abun har mamaki yake bani shiba mai zaman gida bane amma musamman yake zuwa yimata hira.

Ban Fahimci abunda yake faruwa ba saida ranar muka fito daga exam lokacin mun rubuta Exam na biyu kenan. ita tafara fitowa sai tazauna tajirani. Da nafito maimakon mutafi sai na bita muka zauna muna ɗan hutawa kafin mutashi muwuce gida tace.

"Babe duk gidanku Yaya Habib yafiku kyai shine yayi kamada Baba sakk" Na harareta nace.


"

17 / 58