Author : Billyn Abdul Category : Romance
yasa tadawo ta zauna ba'ason ranta ba. Mummy Tajira Baba yazauna sannan tafara karanto masa ƙorafinta. Saida tagama sannan yace.
"Bantari nunfashinki ba Mummy amma akwai babban dalili dayasa akayi hakan wanda yin hakan kawai shine mafita. Banyi hakan dan banason Marmeeyy ko inason fifita Aysha ba.
Aysha da Mummy dukansu Ƴaƴanane kowacce inason farin cikinta babu wacce zan tauye acikinsu dan ƴar uwarta taji daɗi"
"Mummy kibar zancennnan kawai har indai Marmeeyy ce ta fahinci kowa da komai bata ɗauki abun da zafi fa kawai dai ranta baya mata daɗi ne kuma bata fushi da hukuncin" Mama tana gama faɗin haka ta miƙe tana tace"
"Bari naje zamu kasuwa da Aysha akwai kayan kitchen da bamu gama sayayyya ba yanzu zamu shiga mu sayo" har takai bakin ƙofa Baba yakira sunanta. Ta tsaya cakk dan Baba ya kwana biyu bai kirata dasunanta ba bata juyo ba Har saida yacigaba da Magana.
"Ko sau ɗaya bazaki tambayeni dalilin dayasa najuya auren Marmeeyy kan Aysha ba? Da zaki tambayeni da zan zauna nayi miki bayanin komai tun daga farko yanda zaki fahinci lamarin. Baba (Alhaji Habibu) shine ya hanani faɗa miki komai amma har indai zakici gaba da shareni banaji zan iya bin umarninsa zan zauna nayi miki bayani ki fahimta anyi abunne batareda son zuciya ba" sai alokacin ta juyo tayi murmushi.
"Tunda Har Baba ya hana ka gayamin toh sanina baida amfani dan yasan dalilin dayasa yace kada ka gayamin ina bayan hukuncinsa. Sannan niba shareka nakeyi ba kawai yanayin da Marmeeyy ke shiga ke jefani wani yanayi da banajin daɗinsa amma da zarar angama biki nasan komai zai dawo dai-dai" Bata sake magana ba tafice Baba ya sauke ajiyar zuciya yabita da kallo yanajin babu daɗi acikin ransa."
Dake wannan semetern bawani tsayi zatayi ba har munci rabi abubuwa sun fara zafi exam baifi saura 1month ba hakan yasa sam bana zama agidan kuma naji daɗin hakan dan nasamu damar kaucewa abunda banason gani.
ƴan uwan Mummy suka haɗa event Mummy bataso hakaba dan itama auren ya fice mata arai. Mamakin yanda Aysha take rawar kai takeyi tana ganin wautarta zata auri mijinda baya sonta take wannan abun wanda takasa gane dalili yin hakan son saurayin dama takeyi ko tanayine danta ƙuntatawa ƴar uwarta kamar yanda fadeelah tafaɗa mata.
Nadawo daga makaranta nawuce ɗakinmu kai tsaya dukda yanzu bancika zama a ciki sosai ba nafi zama ɗakin Mama dan banason zama waje ɗaya da Aysha. Ɗakin nasamu acike da ƴan mata ƴan uwansu Aysha waɗannan masu masifar jida kansu. Ina ganinsu najuya dasauri zanbar ɗakin dan danasan suna ciki bazan shigaba bansan da isowarsu ba.
"Ina kuma zakije? dawo nan ko kiyi abunda zakiyi ki sake fa Marmeeyy baza'a hanaki sakewa awani gida azo gidan mahaifinki a hanaki ba" Cewar Anty fadeela.
"Bansan da mutane aɗakin bane zanje ɗakin Mama na faɗa ina ƙoƙarin fita" no babu yanda zakije zoki canja kayanki anan. Banason musu da ita dan haka na ƙarasa shigowa. Nafara cire kayan dake da Vest aciki.
"Baku mata jaje ba" cewar Aysha. Dariya su duka suka saka sannan wasu daga ciki suka fara faɗin.
"Allah sarki Allah yamaida alkhairi" ban kulasu ba. Ina jiyo ɗaya acikinsu tana faɗin.
"Aysha bakida Dama haka kikayi wuff da Bawan Allahn nan yanzu wasa gaske saura kwanaki yazama naki ke kaɗai kuma fa yahaɗu wallh ki ganshi fa lallai kinyi gamda katar. Mamaki nakeyi a'ina Aysha tasamu photonsa? Banason jin wani abun dan haka dasauri na ƙarasa cire kayan zan fice.
"Bakiji ba" Aysha tafaɗa ban kulata ba. Kinga please ki sakamin No Hamma anan sorry to ask inba wajanki ba bansan yanda zan samu ba ba cin fuska bane yanayi ne" taƙarasa tana miƙamin wayarta.
"Anya aysha kinada hankali kuwa? Nikam lamarinki na bani mamaki. Wallh Marmeeyy karki kuskura kibata taje yanda zata nema tasamu ƴar iska" ko kallo anty fadeela da tayi magana bata isheta ba.
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin
Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba
Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔
Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo
Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍
Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝
------
Bansan lokacin da murmushi ya suɓucemin ba wanda ni kaina bansan na menene ba amma tunanina yafi bani na jin daɗine tunda na fahimci ko lambarsa ma bata dashi hakan yana nufin ko kiranta bai taɓa yiba kenan. Sai Alokacin naji inada buƙatar na maida mata amsa tunda nasamu damar yin hakan.
"Anya Aysha kinada hankali kuwa? Zumuɗin auren mutuminda baisan dakeba ko kamanninki bana tunanin ya sani bare ace ya kiraki a waya haka zakiyi zaman aure shine kiketa ɗauki. Wane irin zama kike tunanin zakiyi da namijinda zuciyarsa ta karkata wani waje? Ki zauna kiyi tunani sosai ba Zumuɗi da rawar kai yakamata kiyi ba yakamata ki zauna kiyita addu'a kina roƙon Allah yacire masa son wacce yake fama da ita a zuciyarsa ya sanya masa ƙaunarki. Wannan shawarace a matsayina na ƴar uwarki" Cikin ƙuluwa tace.
"Duk namijinda zai soki Marmeeyy ina tunanin idan ya ganni zai soni fiye da ke dan saiya ninkamin sonda yake miki ai ido ba mudu bane amma yasan kima"
"Okay all the best" shine abubda nafaɗa nabar ɗakin. bayan shigata ɗakin Mama na zauna a gado haɗeda sauƙe ajiyar zuciya Naji sanyi da daɗi sosai a raina banyi tunanin zan samu sauƙi alokaci ɗaya hakaba. Gabana yayi mummunan faɗuwa. Danayi tunanin abunda ya sakani jin daɗin. Anya kuwa nayiwa kaina adalci? Murna nakeyi da rashin kiran da Hamma ke yiwa Aysha? Hakan yana nufin naji daɗin nuna halin kk inkula da yayi da ƴar uwata kenan?" na jijjiga kai da sauri dan banason ya kasance haka. Na tabbata samun damar mayar mata da martanin maganar da take jefamin yasamamin nutsuwa naja dogon numfashi na zube akan gado.
Washe gari zasuyi event ɗinsu dan haka tunda na tafi makaranta ban dawo ba sai har 6:00pm ina cikin makaranta harda maryam itama taƙi komawa gida. Babu yanda banyi da itaba tatafi wajan event ɗin taki. Dana matsa tacemin.
" ke idan naje hakan yana nuni ina farin ciki da bikin kenan? Toh banayi garama ki barni" haka nagaji nabarta ban bar makaranta ba saida na tabbatar kowa yagama tafiya wajan event ina shiga gida ana kiran magrib Kia tsaye ɗakin Mama na wuce ban fito ba sai washe gari ko kalan kayanda Amarya da ƙawayenta suka saka bandaniba. Bansan ango yaje ko baijeba. Mummy ma ban gantaba sai da zan tafi makaranta nabi muka gaisa. Zan fito inaji wasu suna zancen ango baijeba na taɓe baki nawuce abuna. Yau ma irinta jiya nayi sai magrib nadawo. Dake a harabar gida suke event ɗin na taras dasu amma ko kallon yanda suke banyiba nawuce ciki. Anty fadeelah ma ashe bata halarci event ɗin ko guda ɗaya ba bansaniba saida nashiga na tarasda Mama tanayi Mata faɗa nima na saka baki muna tausarta amma cewa take har indai bazan jeba toh itama bazata jeba. Na nuna mata saboda school yasa bansamu event ba takasa fahimta dan haka kawai na yanke shawarar zanje event har indai za'ayi a ƙarshe. Tausayin Aysha ya kamani ganin yanda ake event ba ango bare ƴan uwansa. A paper na rubuta numbern Hamma nakai mata ɗakinda take na ajiye. Tagani batace komai ba nima bance ba dan banama buƙatar tace ɗin bana tunanin yanzu zan iya bari ta faɗamin maganarda ranta yakeso batareda na rama ba.
Ina fita taɗauki numbern dake babu kowa a ɗakin tayi dialing numbern bata daɗe tana ringing ba aka ɗauka ta gaisheeshi ya amsa murya babu yabo ba fallasa. Yayi shiru dan bai gane wacece ba. Tafara in ina.
"Uhmm Uhmm Aysha ce" har cikin ransa tsakani da Allah bai gane wace Aysha dan haka yace.
"Aysha! Aysha! Banganeba. Tarasa me zatace masa yagane sai tace.
"Uhmm dama marmeeyy ce ta bani lambarka shine nace barina kira naji ko zaka halarci diner da za'ayi on Saturday ranar ɗaurin aure. Idan bazaka samu damar zuwa ba sai kawai asoke event ɗin"
"Marmeeyy tabaki Number na? Yayi exclaiming. Da sauri tace.
"eh" a yanda yake zaune yazama statue yakasa koda motsi bayan yayi confirming abunda kunnuwansa sukaji masa. Menene hakan yake nufi kenan? Marmeeyy ce da kanta tabata Numbernsa? Marmeeyy ta yafeshi ta manta dashi ta daina sonsa
kenan? Haka actions nata suka gwada amma baiyi tunanin zata iya daukan numbernsa tabada sisternta ba bayan tasan ita kaɗai yakeso. Yaji ɗaci aransa dakƴar ya iya buɗe bakinsa yace zan kiraki. Yana faɗin haka ya datse kiran."
Lallai marmeeyy tawuce iyakarta kuma tasaka shi yaji zafi yaji babu daɗi. Amma dole zai rama zaije event ɗinda za'ayi kodan shima yasamu ya ƙuntata mata gwargwadon yanda tayi masa. Kai amma anya zuciyarsa zata iya jurar ganin ya ƙuntatawa Marmeeyy kuwa domin yana sonta idanya ƙuntata mata ya tabbata saiya fita shiga damuwa.
Nikuma anawa wajan ba ƙaramin dauriya nayiba dana iya ɗaukan number na bata dan saida nayi hawaye amma yaya zanyi? Tunda inada hanyarda zan taimaka mata kawai gwara na taimaka matan dam bazan barmu dukanmu cikin ƙunci ba."
Har washe gari bai kirata ya sanarda ita akan zai halarci event ɗinba shi asaninsa grooms ke shirya diner idan suna buƙata baisan wane karbani yakaita shirya diner bayan bata shawarceshi ba.
Dakyar wasu daga cikin abokanansa da sukasan yanda lamarin yake suka tausheshi akan yaje. Daya tsaida zuciyarsa akan zuwan kawai saiya tura mata text message akan zai halarta. Amma shi dai har yanzu Marmeeyy yakeso kuma yana addu'a akan Allah yayi ikonsa ya canja lamarin.
Aranar akayi walima itama ban halarta ba ina makaranta har aka tashi.
Washe gari daya kasance ɗaurin aure da zazzaɓi na tashi dan abun ya dokenk sosai gani nakeyi kamar almara wai Hammana zai auri ƴar uwata. Aysha inajin kamar zan iya haƙuri bayan auren amma sakda ranar tazo naji haƙurina gabaki ɗaya ya ƙare. Toilet nashiga nayi kuka na godewa Allah nafito ban fitoba dan nasan idanna fito kowa saiya fahimci halinda nake ciki.
Dagani har Hamma munkasa yarda cewa yau rana tazo da zata saka katanga a tsakaninmu zamu zama ba mallakin juna ba ina tuna hakan sai inji hawaye yana zirara akumatuna.
ƙarfe sha ɗaya da rabi 11:30am aka ɗaura auren Hamma da Aysha Bikin yayi mutane dukda bawani gayyata akayi ba shi Hamma abokanansa idanba na jiki bama bai sanar musu ba. Amma haka abokanan wannan ya sanarwa wannan har suka samu halarta. Hamma kawai yana tafiya ne amma jiri ɗebansa yakeyi ɗakyar yasamu ya sulale yabar cikin mutane dan jiri ɗebansa yakeyi akowani lokaci zai iya faɗuwa."
ZAYNAB BAWA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin
Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba
Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔
Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo
Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍
Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝
------
Tun da aka ɗauki azumi akayi sallah gabaki ɗaya hankalinsa ya karkarata yayi wajanta babu wani abu dayake muradi da burin gani daya wuceta. Yana mararin sanyata a idanuwansa yayi kewarta samada yanda baki zai iya faɗa. Ga abubuwa sunyi masa yawa kuma a wannan lokacin yana tunanin dole ya bayyana mata kansa a yayinda zaije gareta yagaji da ɓoye kansa wannan karon yana buƙatar shima tasanda zamansa matsayinsa na mijintabamma yaya zaiyi da alƙawarin da ya ɗaukawa Baba? Yazama dole yacigaba da ɓoye kansa har lokacin da Baba zai bashi izinin bayyana mata kansa. Wannan dalili ya tsareshi daga zuwa ganinta ya taushi kansa yabawa zuciyarsa haƙuri amma yaga zuciyarsa a wannan karon tana neman fin ƙarfinsa kodan ba wannan karon bane ta saba yimasa haka. Alokacinda ya fara sanin Marmeeeyy yaso ya danneta amma ta gwada masa bazata dannuba saboda taga abunda takeso haka taci galaba akansa ya biye mata wannan karonma hakan takeso tayi masa. Ziciyarsa ta azabtu da son ganinta ko jin muryarta. Ɗaya daga cikin wayarsa ya ɗauko. Yanata tunani yayi ko kar yayi bazai iya hana kansa ba A wannan lokacin abisa tilastawan da ziciyarsa tayi masa yayi dialing numbern marmeeyy.
Ina zaune abun duniya ya taru yayimin zafi narasa yanda zan saka kaina tunda naji labarin an ɗaura auren nakejin jiri-jiri harda zazzaɓi dan zuciyata sai tashi takeyi nakasa cin komai. Tun banaso kowa yagane har Mama tazo ga sameni a cikin wannan yanayin tashiga tashin hankali matuƙa zama tayi tanamin nasiha da kalamai masu ƙwantarda hankali da sanyaya zuciya.
"Marmeeyy kina jina? Ki ƙwantarda hankalinki kisan cewa kowani irin lamari rubutacce ne wajan ubangiji dama can Allah ya rubuta Hamman ba mijinki bane. Kuma bamu isa muja da hukuncin Allah ba. Alkhairi kawai muka roƙa a wajansa kuma inada yaƙinin alkhairin zai bamu. Karkiji komai karki riƙe komai a zuciyarki ki tashi ki fita cikin ƴan uwanki ko zakiji sanyi. Idanma bazaki iya hakanba ki zauna anan ki ɗauki ƙur'ani ki kiranta zakiji sanyi. Tayi tamun nasiha sosai ina jinta har tagama kuma Alhamdulillhi nasamu sauƙi. Na lumshe idona kamar mai bacci ganin haka yasa tafita. Ina zaune ƙwance wayata tafara ruri a hankali na jawota. Ina ganin lambar saida gabana yafaɗi amma na dake. Baitaɓa kirana ba tsawon shekara biyu anshiga da uku kullum saƙonnk kawai yake aikon dasu. Bansan dalilin kiranba yasa bazan iya ignoring ba amma kafin na ɗauka nayi saƙa da warwara sunfi goma. Ina pjcking na kara a kunnena nayi shiru. Ba'ace komai ba daga wayar nima bance ba. Na maida idanuwana na lumshe wayar tanakan kumatuna saitin kunnena a hankali nake sauƙe numfashi. Bansan me yasaba sai nakeji kamar mai kiran yana saurarona daga numfashin danake fitarwa.
Daga yanayin yanda numfashina yake sauƙa yagane cewa ina cikin damuwa gabaki ɗaya sai yajishi babu daɗi Marmeeyyn da yasani mak surutuce da fara'a amma yajita shiru gashi tana jan bumfashi tana sauƙar dashi cikeda damuwa bazai iya sauraran hakanba dan haka ya datse kiran. 15minute bayan datsewar kiran naji sallamar Yaya Ahmad. Har yanzu wayar nakan kumatuna yanda take ban sauƙetaba koda naji datsewa wayar. Sallama yayi nabashi izinin shigowa dan bazan iya tashi jafita palournba sam banason haɗuwa da mutane. Tubda Ya Ahmad yake inbanda yarinta bai taɓa shiga ɗakin mama ba sai yau. Yashigo yazauna akan comfy bedroom chair dake gefen gadon Mama. Na gaisheshi batareda na tashi ba.
"Marmeeyy tashi ki zauna zamuyi magana" batareda na amsa ba na nemi mike zaune.
"Kina sonsa da yawane har haka?" nayi ƙasa da kaina ya fahimci abinda nake nufi zuciyarsa tayi wani iri yakasa cewa komai. Bayan wasu mintuna kafin yacigaba da magana.
"Marmeeyy kisan cewa kuma na yarda cewa Allah bazai ƙwace wani abu atare dake batareda ya canja miki da ninkinsa sau babu adadi ba. Mijinda nake mikk buri da fata shine wanda zai soki ya ƙaunaceki ya riritaki yaga kimarki da darajarki ya zame miki gata kamar yanda kika zamewa gabaki ɗaya ahlinki gata. Ina miki fatan mijinda zai soki aduk yanda kike mijinda zai fahimci kina cikin damuwa daga zallan numfashinda kika sauƙar basai laɓɓanki sun furta ba wanda zai fahimci damuwa acikin ƙwayar idanuwanki batareda taimakon kalaman bakinki ba. Na tabbata bazaki daɗe cikin wannan damuwar ba dan ayau na tabbata cewa Allah ya amshi addu'armu.
Yanzu kitashi kiyi wanka idan kingama ki kirani zan fita dake may be zakiji sanyi aranki daganan zan wuce nasamu Baba zamuyi magana akwai wani suprise da zan miki amma sai kinmin alƙawarin sakin ranki nayi murmushi sannan nace.
"Ya Ahmad karka damu kanka da saika farantamin kar kaje ka takura kanka kaga ranar haka kacire maƙudan kuɗi ka siyamin wayarda tafi ƙarfina idan kanaso na saki raina zan saka kasan kawai zanji babu daɗine amma yanzu zan tashi nayi wanka ma" murmushi kawai yayi ya fice natashi daƙyar nashiga nayi wanka.
A ɗakin Baba Ya Ahmad ya shaidawa Baba abunda yake faruwa badan ya ɗaga masa hankali ba sai dan yanaso yaɗaga maganarsa akan cewa ba yanzu zai nunawa Marmeeyy akwai auren Hammood akanta ba shi aganinsa tunda marmeeyy nason Hammood koda da son bana aure bane bazatai masa uwar shawo kaiba. Sannan yana ganin Hammood kaɗai zai iya cireta a wannan damuwar da take cikk ya ƙwantar matada hankali. Bai bar ɗakin ba har saida ya sanya Baba ya amince da zai Kira Hammood da kansa dan yazo ya bayyanawa Marmeeyy kansa."
Bayan na fito a wanka wadrope na buɗe anan idanuwan suka sauƙa akan kayanda nasaka ranar diner ya Ahmad na cirosu ƙamshinsu yana dukan hancina har lokacin kayan ƙamshin turaren wannan mutumin sukeyi dukda sun ƙwana biyu a ajiye tun ranar dinner bansake sakasu ba bansan dalili ba amma naji daɗin ƙamshin danya sanyamun nutsuwa kuma dama tun abaya ƙamshine mai saka nutsuwa. Daga yanda nasaka kayan na gane naɗan faɗa ban shafa komaiba na ɗaura ɗanƙwali na yafe gyale tunanin Ya Ahmad zaiyi magana yasa na canja zuwa hijabi wanda zai shiga da kayan na saka plat shoe na fito a plaourn mama naga matar Ya Ahamd ni banmasan shigowarta