NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   9 / 44

24K to 27K   out of 131.7K words

Allah yasa labulen a d'an d'age yake hakan yasashi tsayuwa daga jikin gini yana kallon d'akin.

Zaune take kan gado hannunta da drip an jinginata da pillow tana shan pepper soup da zarah ta aika aka sayo, a hankali take komai cikin natsuwa, ido ya kura mata rigan de safen ne jikinta sede yanzu kanta da hula fuskanta yayi fayau da shi idonta kuwa har yanzu da alamun kuka, ajiyar zuciya me karfi ya sauke, ya jima sossai a wurin yana tsaye yana kallonta kan ya juya ya fice.

Tunani yake yadda za'ayi ta shiga harkanshi, wani malalacin murmushi ya saki da ya tuna da maganan zarah "tana farkawa Kai ta fara tambaya ta zaci kayi class yau" murmushin na fuskanshi ya kira class rep d'insu ringing d'aya ya d'aga ya fara gaidashi cikin ladabi, "Inform all your colleagues I'm having my CA test 2morrow by 8am" dip ya kashe wayan ya jefa sit d'in gefenshi ya ci gaba da tuki cikin nishad'i.

****
Se After 8 Hammad ya dawo asibitin ya ci sa'an samunta ido biyu tana zaune kawai akan gadon, tana ganinshi ta saki murmushi shima murmushin ya sakar mata yaja kujera ya zauna "sannu princess ya jikin?" Tace cikin murya irin ta marasa lafiya "na warke ni kam" yace "Allah ko? Ko zamu gwada 'yar tsere ne yadda zan fahimci kin warke da kyau?" Waro ido tayi tana dariya Tace "rufamin asiri In ba so kake Amin karin jini ba ruwa ba" murmushi yayi yana kallonta ledan hannunshi ya ajiye yana cewa "ba kowa ne?".

Tace "a'a mama tana waje taje d'auraye plate da naci abinci yanzu" yace "Ohk" hira ya ci gaba da mata yana sa ta dariya har mama ta shigo sossai tayi farin cikin ganinshi kamilalle natsatse dashi, gaisawa sukayi a mutunce kan ya mike yace "seda safe mama Allah ya sawaka" Tace "Ameen Ameen mun gode" hannu kawai ya d'agawa noor iman itama ta d'aga mishi, ya juya ya tafi.

Dauriya ce kawai irin nashi amma shi kad'ai ya san damuwan da yake ciki Allah ya gani baze iya fad'awa noor iman abinda mamanshi ta fad'a tana gadon asibiti ba amma lokaci tafiya yake In ya tuna tace nan da sati biyu baba yace, gwara ya fad'a mata tun wuri ta gabatar da wani saurayin nata kan lokaci ya kure, amma ta yaya tana gadon asibiti?.








                        🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
            •Gureenjo6763 on Wattpad•


*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                       *015*

"Yanzu ke dama iman kina da saurayi irin wannan shine kike d'aga hankalinki akan maganan mahaifinki?" Cewar mama tana kallon noor iman, cikin jin kunya noor tace "Ai na fad'a mishi abinda baba yace mama" cikin jin daad'i tace "masha Allah, na san in sunje babanku baze sa bukin da nisa ba kiyi ki warke mu je In fara gyara ki 'yata" murmushi kawai noor tayi tana girgiza kai.

Wayanta ta janyo ta kunna data bata cikin wasu groups dayawa haka bata da contacts dayawa ta tabbatar a whatsapp d'inma In ba hammad na nan bane ba me d'ebe mata kewa d'an gwara zarah, ganin sako a cikin group d'insu na school ne yasa ta shiga ciki don ganin me aka turo, wani irin fad'uwa gabanta yayi "Doctor malabo ze yi test gobe?" Ta furta a fili cike da damuwa.

Toh ya zatayi bari doctor yazo ita kam zata ce a sallameta ta warke In tayi missing test d'innan da matsala, karan shigowan wani sakon ya sata maida hankali kan wayan zarah ce "me mara lafiya ke yi whatsapp a irin wannan time d'in?" 'Bata fuska tayi tare da yin typing "zarah kinga abinda na gani a group? Yayanki fah test ze yi gobe ban san ya zanyi ba".

Zarah tace "haba dae?😳" noor ji tayi idonta ya cika da hawaye se take ganin kaman da gayya yayi hakan zarah tace "kar ki d'aga hankalinki plz besty, yanzu rubuta mishi sako zakiyi na baki da lafiya kan In shiga school d'in se in biyo In kar'ba se In ba class rep ya bashi watakila In kin warke ya miki make up" noor de cikin sanyin jiki tace "Ohk na gode da shawaranki zarah bari yanzu In rubuta".

Kallon mama tayi tace "dan Allah mama Ina son yin rubutu a paper ya za'ayi?" Mama tace "toooh babanki yacemin ze zo kan ya wuce gida bari In ce mishi ya sayo miki foolscap d'in da biro" godiya noor tayi mama ta kirashi da kyar ya yarda ze sayo, bayan ya kawo ta natsu ta rubuta letter d'in cikin kyakyawan handwriting d'inta bayan ta gama ta nad'e ta Adana.

Wata nurse ce ta shigo ta yi mata wasu allurai nan take bacci ya kwashe ta.

*****

"Wato ni zaka nunawa iyakata ko Muhammad? Akan yarinyar da bata da tarbiya da kamun kai kake neman yi min jayayya? Toh yayi kyau, Ina so ka bud'e kunnenka da kyau ka jini har abada kana ji? Har abada ni mahaifiyarka ban amince ka auri yarinyar nan ba ko bayan raina ka aureta ban yafe maka ba, itama yarinyar In asiri ta maka zan je har gidansu in nuna mata kaina ta ganni da kyau wallahi na fi karfin asirinta bade zuri'ata ba".

Hammad ya ce "mom kiyi hakuri plz wallahi zan rabu da ita ba se kinje gidansu ba, abinda yasa har yanzun ma ban rabu da ita ba bata da lafiya ne tana asibiti ba zan iya gayamata cikin situation d'in da take ba, In shaa..." katse shi tayi "na hutace ka zan gayamata da kaina" cikin sanyin murya yace "dan Allah m..." "tashi ka fice ka bani wuri" mikewa yayi jiki a sanyaye ya fice.

Dole ba yadda ya iya yau In ya shiga wurinta ya fad'a mata tayi hakuri ta nemi wani shi kam an mishi iyaka da ita.

*********

Cikin nishad'i yayi test d'inshi ya gama, test d'in da ya basu wahala magana d'aya kayi out, sannan ya kama masu satan amsa dayawa waenda ya yi cancelling test d'in nasu, bayan ya fita ne class rep ya bishi har office ya bashi letter d'in iman akan she is sick bata samu zuwa rubuta test d'in ba, kar'ba kawai yayi ya wuce abinshi.

Kurawa handwriting d'inta ido yayi yana kallo na mintuna kan ya fara karanta lettern, tayi sakon ne cikin hankali ba hayaniya sam wadda hakan ya sashi jin ba daad'in test d'in da yayi da gayya amma shi a ganinshi hakan ne kad'ai hanyar da ze samu don yi mata tambayoyi akan rayuwanta, bud'e briefcase d'inshi yayi ya Adana lettern kan ya hau duba tests d'in da yayin yana cikin dubawa kuma se aka kirashi zasuyi meeting, mikewa yayi ya wuce d'akin taron.

Ya san maganan bata wuce zuwa seminar ba wa ze je, wa baze je ba, shi yana da abinyi wannan karon hakuri zasuyi da sake saken nan ya karasa, Ai ko de maganan seminar ne za'ayi a Lagos kuma shi aka wakilta, tsaki yaja ya so cewa baza shi ba se kuma ya tuna Abba, mtseww ya kuma jan wani yana duba date, kenan gobe ne ze wuce kuma ze yi kwana uku.

Ba tare da yace musu komai ba ya mike ya fice, makarantan ma gabad'aya ya bari ya nufi companyn Abba dukda hafeez ne ke kan komai amma shima yana dubawa, balle kuma shine Director na companyn gabad'aya, office d'inshi na nan ya zauna aka shiga kawo mishi takaddu, dubawa ya fara, ya 'bata lokaci sossai anan kan ya mike ya fice.

Gida yaje ya kwanta hankalinshi na kanta ko ta ji sauki sossai? Ko ta ci abinci? Yana son kiran zarah ya tambayeta ta kai musu abinci kuwa, amma baya so tayi zargin wani abu, ajiyar zuciya ya sauke yana me mikewa, kallon wayanshi da ke ringing yayi hamna ce tun jiya take kiranshi ya ki d'agawa, yau d'inma silent ya sa wayan ya jefa kan gado kan ya fad'a wanka.

**********

Abinda ya faru jiya shine ya faru yau, amma sede yau idanunta biyu akasin jiya da bacci takeyi bata ji komai ba, yau kayan takaici har ummanta da farko ta d'auka ta zo ne don duba jikinta har daad'i ya rufeta amma kuma se jikinta yayi sanyi ganin irin kallon da take jefanta dashi haka su goggo saratu, da inna, maganganu maras daad'in ji suka dinga jifanta dashi na 'batanci wadda ko makiyinka ne baza ka so kaji ana mishi irin wannan cin mutuncin ba.

Dr. Sauban ne ya shigo dukda shigowar tashi be sa sun dena maganganun su ba, da mamaki yake kallonsu ze yi magana inna tayi charab tace "yauwa Allah ya kawoka likita, gwajin ciki nake so kayi mata yau In ciki ne dake na yawon karuwancinki se Hafeezu ya cire ki daga cikin 'ya'yanshi ya kora daji kinji na fad'a miki, baza mu iya ci gaba da zama da d'an shege ba bayan duk hakurin zama dake da mukayi kina kashe aure kina dawowa kina ja mana magana".

Dr sauban yace "hajjiya kuyi hakuri ku tafi plz a condition d'in yarinyar nan ba'a son abinda ze dinga sakata damuwa dubi yadda take kuka dan Allah, ko kuna so zuciyarta ya samu matsala ne?" Bud'an bakin umma se cewa tayi "ya buga ma mu huta, haba yarinya kaman shed'an" wani irin zafine yake ratsa kirjinta, haka lokaci d'aya kanta kaman ana sarawa ranta In yayi dubu to fah ya 'baci kallon umma tayi tace.

"Wai dan Allah umma me na tare miki ne a duniyan nan? Me yasa duk cikin 'ya'yanki ba wadda kika za'bi wulakantawa se ni? Ko kin manta ba uwa bane kad'ai ke da hakki akan 'ya'ya har 'ya'yan ma suna da hakki akan uwa? Yau In na mutu baki nemi yafiyata ba me zaki je ki cewa Allah akan banzantar da ni da kikayi tun daga haihuwana ba tare da na san takamammen laifina ba? Da kuwa ana kiran mutuwa da ana neman shi a samu da ni da kaina zan neme shi ya d'aukeni, na gaji da duniyarnan da tunda aka haifeni ban ta'ba d'and'anan gard'inta ba, na gaji..."

Kuka ne yaci karfinta ta fashe dashi dr sauban cikin tausayawa yake kallonta, ya kuma kalli su inna a hankali yace "hajiya zaku iya tafiya a duk gwaje gwajen da muka mata ba ciki se hawan jini da ciwon zuciyar da yake barazanar kamata" umma da ya lura jikinta yayi sanyi ya kalla tabbas itace asalin mahaifiyar noor iman ko daga kammaninsu da ya 'baci to amma me yasa take cikin masu kuntata mata?.

Fita sukayi yabi bayansu zuwa get ya bawa securities d'in umarni ko sun dawo kada a barsu su shiga, kan ya koma d'akin har yanzu kuka takeyi cikin sanyin murya yace "saudat Ina mama?" Cikin muryan kuka tace "zuwansu yasa taje gida yin wanka da d'auko wasu abubuwan" girgiza kai kawai yayi tare da had'a wasu allurai ya mata, yace "gyara ki kwanta da kyau kiyi hakuri komai na duniya me wucewa ne kuma ki yarda da maganar hausawa da sukace bayan wuya se daad'i In shaa Allahu akwai lokacin da zaki ji daad'i".

Murmushin yake ta mishi tana me share hawayen fuskanta, ba wai don ta aminta da magananshi ba, yana nan tsaye har bacci yayi awon gaba da ita, fita yayi yana juya maganganun mutanen nan, Haka kawai ya za'bi ya kira Malabo ya bashi labari seda wayan ya kusa tsinkewa kan ya d'aga, Bayan sun gaisa se Allah yasa malabon ya fara tambayar shi.

"Ya patient d'inka na jiyan nan?" Sauban yace "to de jikin da sauki kan zuwan wasu marasa imani, mu da muke fata jini ya sauka amma se kara hawa yayi" Da sauri malabo ya mike tsaye yana nufan kofa yace "ganinan zuwa se mu tattauna maganan" sauban yace "Malabo!!" Da sauri malabo yace "dama Ina ta arean asibitin In baka so na shigo kuma shikenan" baya son sauban ya zargi wani abu dukda ya san se ya zarga d'in tunda shi ba mutum bane me shiga shirgin jama'a amma na yarinyar nan ya d'aga mishi hankali.

Kashe wayan yayi ya fice direct asibitin yayiwa tsinke bayan ya zauna ne sauban ya fara bashi labarin abinda ya faru gabad'aya ya kai mintuna 30 yana juya maganganun sauban ya kasa cewa Komai Allah ya sa aka zo aka kira sauban emergency wadda hakan ya bashi damar mikewa ya fara safa da marwa.

Aure Aure! Ciki! Umma!! Sune abubuwan da sukayi matukar d'aure mishi kai, he just can't even imagine his life ba kulawar uwa,  amma ita Haka tayi dauriyar rayuwa ba mahaifiya? Kuma kayan takaici harda mahaifiyarta ake mata zargin ciki ne da ita, naushin iska yayi a fili yace "how on earth did she manage to live her life like this?" Nanma Be ji gabad'aya labarinta ba.

Ficewa yayi zuwa jikin windown d'akin yauma a bud'e yake ya lura yarinyar bata son zafi don jiya yaga bayan fanka ga windown dake d'age tana fifita, kallon fuskanta yakeyi cike da tunanuka kala kala, daga ganin fuskanta ya san baccin ma ba na daad'in rai bane tayi wani iri da ita ta rame se karan hanci da d'an haske da tayi.

Ya jima tsaye anan kan ya juya ya fice gabad'aya daga asibitin duk wani puzzles da ze had'a da kanshi a kan rayuwarta se ya wargaje ya rasa ta Ina ze kama, how could this be possible ace mutum ya d'auki d'a a cikinshi na about 10months yayi nakuda ya haifa kuma ya tsani yaron from that instant?, how on earth za'ace yarinya kaman wannan tana aure aure? And zargin ta fa sukeyi da karuwanci? Innalillahi wainna ilaihi rajiun, be san me ke damunshi ba, be san taya akayi ya fad'a tarkon tausayin yarinyar nan ba, wani irin tausayinta yake ji da be ta'ba ji akan wani bawa ba se ita.

Mace da aka sani da raunin zuciya amma ta iya d'aukan waennan abubuwan ba karamin kokari tayi ba, ze taimaka mata in shaa Allahu even it will cost all what he have in this world ze taimaka mata for sure, amma se yaji labarinta daga bakinta ta hakan ne ze sa ya fara shirya abinda ze yi ya taimaka mata. "I most help her, It's a promise" ya furta yana ajiyar zuciya.







                      🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
       •Gureenjo6763 on Wattpad•


*'yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

   
                             *016*

Dawowan mama ta samu tana bacci so bata d'auka wani abin ya faru ba, se kawai tayi zaman ta kan kujera, har magrib noor iman ta kai tana bacci don har zarah ta kawo musu abinci ta duba jikin nata duk tana bacci, se da aka idar da sallar magrib tukun ta farka a hankali ta mike zaune mama tazo taimakonta Tace "kar ki damu zan iya mama, na gode" ta fad'a har yanzu with bitterness in her tongue, bayi ta shiga tayi abinda zatayi kan tayi alwala ta fito a zaune ta rama sallar la'asar da magrib da ya d'an wuce bata wani jima da idarwa ba aka kira isha ta gabatar kan ta ci gaba da zama.

Mama ce Tace "zarah ta zo kina bacci ta kawo abinci yarinyar 'yar albarka ce tana sonki sossai shiyasa take d'awainiya damu haka, In zubo miki?" 'Dan murmushin yake tayi kan ta gyad'a kai tabbas zarah na sonta zata iya cewa bata ta'ba yin kawa dake sonta irin zarah ba, tsakaninta da Allah take sonta, pepper soup da irish pottage da yaji veggies da mama ta ajiye mata ne ya dawo da ita daga tunanin da ta fad'a, a hankali ta sa spoon ta fara ci kaman me taunan magani.

Tana mamakin me ya hana hammad zuwa yau? Ta duba wayanta kuma ko missed call d'inshi bata gani ba, da wannan tunanin ta gama cin abincin duk da daad'inshi don daga kamshin zaka san yayi daad'i amma bata wani ci sossai ba sbd bakinta d'aci yake mata.

Ta mike kenan don komawa gado tana d'an hira da mama sukaji an bud'e kofa da sallama duk juyawa sukayi suna kallon kofan hammad ne ya shigo, murmushi ta saki ganinshi taji d'an sauki a zuciyarta dukawa yayi ya gaida mama cike da ladabi kan ya d'ago yana mata ya jiki, ta amsa da "da sauki Alhamdulillah" mikewa mama Tayi ta fice.

A tare sukayi parking da hammad kuma a tare suka nufi bangaren amenity ganin ya nufi kofan d'akinta ne ya sashi fara tunanin waye kuma wannan, windown de ya kuma zagayawa ya tsaya yana kallonsu.

Be san ya saki murmushi ba ganin genuine murmushi a fuskanta tunda ta kwanta a asibitin ze iya cewa be ta'ba ganin tayi irin murmushin nan ba se yanzu, ganin mama ta fice daga d'akin yasashi gyara tsayuwa ya kasa kunne don jin me zasu ce, don ma Allah yayishi da kaifin ji.

"Saudat" da sauri ta d'ago ta kalleshi be ta'ba kiranta da sunanta haka ba sbd alkunyar sunan mahaifiyarshi hakan yasa gabanta fad'uwa kallonshi kawai tayi ba tare da ta amsa ba yace "saudat na so ki tsankani da Allah, Ina sonki a yanzu haka kuma na tabbatar har abada bazan dena sonki da kukan rashin mata ta gari ba, na tabbatar abinda zan fad'a will shattered your heart amma ba yadda na iya umarni ne daga wacce bazan ta'ba iya tsallake magananta ba kiyi hakuri, ki rungumi kaddararki Allah ya za'ba miki wadda ya fini".

Kasa kallonta yayi jiki a sanyaye ya fice ko waiwaye babu, wuri guda ta kafawa ido ko motsi ta kasa yi tsabar kad'uwar da take ciki har bata san mama ta shigo ba seda ta ta'ba ta.

Firgigit tayi tana kallonta "Lafiya kuwa iman?" Cikin rawar murya tace "Lafiya klau" Da sauri ta kwanta ta juyawa mama baya, gyara blanket mama tayi akan sallaya tayi kwanciyarta don Allah yayi ta da baccin wuri.

Murmushin takaici ya saki in disbelief yana juya idanu kaman mace, in ya fahimta daidai saurayinta ne yayi breaking up da ita while she's in sick bed with high Bp

9 / 44