NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   4 / 44

9K to 12K   out of 131.7K words

da goggo saratu tsaye suna magana yaransu na nan tsakar gidan suna ta wasa.

Da fargaba ta karasa gaban su inna ta duka har kasa tace “sannu inna barka da rana” tun kan inna ta amsa goggo saratu ta kar’be zancen da cewa “au yau su jawaran ne a gidan innanmu?” Magananta ya dawo da hankalin su goggo hindatu kaina carab goggo kamila tace “jawara ko ashawo, saratu kin san duk abinda yarinyar nan ke aikatawa a bayero kuwa? Hmmm yawo ma batayi se da yaran masu dashi”.

Goggo hindatu tace “Kai kamila wa ya fad’amiki?” Goggo kamila tace “kin san Ai abin duniya bata ‘buya akwai wata makwabciyata da ‘yar ta ke chan ita na sa ta dinga kularmin da wannan Shegiyar wai don zumuncin dake tsakani, in kinji abinda yarinyar take gayamin zaki sha mamaki aji ma bata shiga se malami ya shiga tayi ta karairaya don ya gani ya kyasa a sashi a layi”.

Hawaye ne ya cika min ido tab ga zuciyata dake min zafi kaman ze bar kirjina, in naji irin waennan maganganun a bakin bare ba kasafai ya cika damuna ba kaman yadda nake jin zafin In naji a bakin ‘yan uwana na jini, bud’an bakin inna se cewa tayi “mtseww d’an Allah ku dena damun kanku a kan yarinyar nan, Allah ya gani kunyi iya kokarinku, Allah na gode maka da ka amshi ran maigida be yi tsawon ran ganin wannan abun takaicin a zuriyarshi ba, ni na jima da sallamawa duniya ke saude bakya cikin jikokina wallahi don bazan iya ba.

Haba!! Matsalan yau daman ta gobe daban kullum ke de ke d’in de ce gur’batacciya a cikin zuriyarmu Anya ba chanzawa Aishatu ke akayi a asibiti ba?” Zuwa yanzu kuka Noor iman ke yi bilhakki da hawaye bibbiyu cikin rawan murya tace “inna ba laifina bane, da bawa na da daman za’barwa kanshi yanayin rayuwarshi da Wallahi ban za’bi irin wannan rayuwan ba, aka ce muku nima banda rai ne? Ko kuwa baku san kaddara ba...” buge min baki da goggo saratu tayi yasa ni yin shiru tare da ci gaba da kuka na yayinda inna ta saki salati.

“Eeeeh Lallai yarinyar nan yanzu na yarda da abinda ake cewa d’ari bisa d’ari, zagina kikayi? Nice ban san musulunci ba da har zaki gayamin kaddara, tashi ki bar min gida shegiya gayyar tsiya kika sake tako kafanki gidana se na ci mutuncinki, kuma zan kira ubban naki inji In shi ya d’aure miki gindin yin iskanci” ajiye mata sakon da mama ta bani nayi tare da ficewa Ina hawaye sossai.

Tafiya kawai na dinga yi ba tare da na san inda nake jefa kafana ba har na fita daga layin na ci gaba da takawa ba tare da na nemi abin hawa ba, tafiya yake yana duba abu a sit d’in baya, abu ya manta a office d’inshi har hakan yasashi shiga makarantan ranar lahadi, yanzu ma gidan Sauban ya nufa don bashi wasu takardu shine yake dubawa be hankara ba sitiyarin ya kubce mishi saura kad’an ya bugeta yayi saurin taka birki yana kallonta.

Amma ita bata san anyi ba hankalinta kwata kwata baya jikinta mamaki sossai ya kamashi ita kuwa lafiyanta? Randa ya fara ganinta kuka take yi tana tafiya akan hanya wadda har yayi sanadiyar da yasa ya bugeta, haushin da ta bashi ne ya hanashi fita ya bata hakuri sbd Shi a ganinshi me ze kawo mutum me hankali kan titi gatsal tana tafiya tana hawaye kaman wacce aka sako daga psychiatric.

Toh ga yau ma dukda be kai ga bugeta ba, amma me ya sata kuka bayan yanzu ya ganta lafiyanta kalau? Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa kanshi “Ina ruwana?” A hankali ya ci gaba da tafiya yana kallonta ganin ta nufi babban titi yasa yayi saurin parking ya fita da sauri yaje ya sha gabanta wadda hakan ya sata tsayuwa “hey!! are yhu alright?” kallonshi tayi se kuma ta kalli inda take da sauri ta goge fuskanta tare da kakalo murmushi ta gyad’a kai, ta’be baki yayi kan ya juya ya tari napep.

Empty one, ba tare da ya kalleta ba yace “get in” shiga tayi ya zare dubu sabuwa gal ya mikawa me napep d’in kar’ba yayi, ba tare da ya kara magana ba ya koma motarshi ya ja yayi gaba.



🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
              •Gureenjo6763 on wattpad•


*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this page is dedicated to all my friends (I mean readers of my book) duk wani me son littafin nan wannan page d'in nashi ne, kuyi yadda kuke so, Ina jin daad'in comments d'inku sossai, Allah ya bar zumunci ❤️❤️ big hearts from here*

                            *07*

Seda me napep d'in ya fara tafiya kan yace "hajiya ina muka nufa?" Cikin sanyin murya nace "gandun albasa" Haka kawai na iya furtawa kan na fad'a tunanin me yasa Dr. Abdulraheem taimakana? Ya gane ni ne? Ko kuwa dai taimakone irin ta addini da ya had'amu? Allah masanin gaibu, haka na ci gaba da sake sake ba tare da na ci gaba da kukan ba, gobe monday we are having his class as early as 8 so dole nayi bacci da wuri don na ci alwashin In shaa Allahu bazan sake missing class d'inshi ba.

Ya rab!! Yau ma mutumin nan bakake kaya ya saka, wai ko Lafiyanshi da bakaken kaya kaman wani shaid'an? Bari In kira zarah kwana biyu bamuyi lectures ba so bamu had'u ba, yau ma haka gashi bamuyi waya ba, wayana kirar Tecno M3 na fiddo na danna mata kira ringing biyu ta d'aga "hey besty ya kike?" Nace "Lafiya kalau besty ya gd?" Tace "kalau wallahi, kina raina besty tun d'azu nake shirin kiranki se kika rigani" Ina murmushi nace "ba wani nan kawai don kin ga na riga kira ne".

"Allah ba haka bane ki tambayi ummu kiji se maganan ki nake tun d'azu" ta karasa da shagwa'ba kan nayi magana naji muryan babbar mace cikin kamala tace "Assalamu Alaiki" diriricewa nayi wato seda zarah ta bai wa ummu wayar seda nayi gyaran murya nace "wa'alakumussalam ummu Ina yini?" Tace "Lafiya kalau ya mutan gidan?" Na amsa da "Lafiya kalau ummu" Tace "Toh ma shaa Allah, auta bata fitinarki da surutun ta na tsiyan nan ta hanaki karatu ko?".

Murmushi nayi kan nace "ko d'aya ummu Ai zarah na da daad'in zama" tana murmushi tace "Toh masha Allah, Allah yayi muku albarka a gaida mutanen gida" na amsa mata da zasuji mun gode, kan ta mikawa zarah wayan muka ci gaba da hira ta dinga jaddadamin In zo da wuri gobe In zo da wuri da haka mukayi sallama.

Ina isa gida nacewa umma "umma na dawo" ba tare da jiran amsanta ba na wuce d'akin mama a parlor na taddata itama haka na ce mata ba tare da na jira amsanta ba na fad'a d'aki tare da zubewa kan gado, yau umma ce da girki kuma bata yarda in taimaka mata da komai da kanta take kayanta hakan yasa na kwaso takarduna na fito tsakar gida na fara karatu ina cikin yin karatun su ikhram suka dawo daga islamiya.

Da gudu suka nufo kan taburman suka zauna ko wacce na ban labarin abunda ya faru yau, Ina ta murmushi nace "Kai ikhlas surutunku se ku, kuje ku tu'be uniform nan, baku da assignment na school ne?" Ikhram tace "muna dashi Anty Noor bari inje In kawo ki gani?" Ta mike kenan umma ta fito daga d'aki zare ido tayi kan ta daka musu tsawa "Kai baku da hankali??? Wa yace kuyi mata magana ban hanaku ba?" A tsorace yaran sukayi wurinta ta kuwa kama kunnensu ta murd'e suka saki kuka.

Idona na kanta amma hawaye ne ke zuba "Anya uwata ce" ba tare da ta kalli inda nake ba ta jasu sukayi ciki, karatun da banyi ba kenan na tattare takardun nayi ciki, har yamma ina d'aki ko parlor ban leko ba Ina ji suna ta hayaniya yayinda mama da umma ke hiransu suna dariya Ina ji baba ya dawo ban fita ba, a d'aki nayi magrib da isha kan na fita d'aukan abincina.

A kan taburma na tararda ahalin gidan zaune suna hiransu gwanin sha'awa baba na ta wasa da dariya dasu ikhram wadda hakan ya sani tunawa da yarantata da mahaifina me sona da kauna na, har na d'auko abincin na fito bayan mama ba wadda ya kalli inda nake dukda na musu sannu maman ce kawai ta amsa.

A parlorn na yada zango ina tunanin wani irin iyaye nake dashi da basu yarda da kaddara ba? Kode imaninsu be cika bane ba? Da sauri nace "Astagfirullah, Allah ka ganar dasu" da ba don mama ba na tabbatar da na jima da collapsing, a haka na tuttura abincin ba wai don Ina jin daad'inshi ba sbd kawai kar nayiwa kaina illah da yunwa, Ina gamawa na mike na fita da kwanon na dawo nayi sallahn isha na bi lafiyan gado.

*******

"Oyoyo booo shine kaki zuwa tarana a airport ko?" Ta fad'a a shagwa'be bayan ta zube jikinshi, ba tare da ya mayar da runguman da ta mishi ba yace "da ni na kai ki airport d'in" baki ta turo gaba cikin shagwa'ba tace "Kai Hamma Abdul bakayi missing d'ina ba? I really missed yhu wallahi" ta'be baki kawai yayi, raurau tayi da ido ba 'bata lokaci ta fara hawaye don ta san lagonshi kenan kuka musamman na 'ya mace.

"I know I've wronged yhu da na tafi ba tare da izininka ba plz forgive me bazan kara ba wannan karon ma shagona ne yayi kasa and I need to choose any single thing in there myself amma kuma kaki that's why na gayawa ummu, I'm sorry plz" be kalleta ba ya ci gaba da kallon TV d'in da yake jin kukanta ya fara damunshi ne yasa shi sa hannu ya rungume ta sossai tare da kissing forehead d'inta yace "I missed yhu" murmushin cin nasara tayi.

Abinka da mata da miji tuni sun shirya har yare ya chanza tuni sukayi d'aki don Allah ya gani dauriyace kawai irin nashi, hallitanshi daban ne a cikin maza yana da karfin sha'awa ba kad'an ba shiyasa yaci burin matarshi bazata dinga yin nesa dashi ba sbd kaucewa halaka se ga irin wacce Allah ya had'ashi da ita.

Bayan sun gama samun natsuwa ta tattara ta fice d'akinta yana kallonta be iya ce mata komai ba, to me ze ce? Sau nawa yana gayamata ya fi son jin matarshi a jikinshi ko da ba abinda ze shiga tsakani amma taki yarda sam da su d'inga kwana d'aki d'aya shi ya rasa dalili, sede tazo suyi abinda zasuyi ta tafi girgiza kai kawai yayi tare da mikewa ya shige toilet.

Tana shiga d'akinta ta bud'e bedside drawer ta d'auko wasu pills ta had'iya kan ta fad'a toilet.

Kiran sallahn farko akan kunnenshi wadda yasa shi yin mika tare da sakin salati kaman baze sauka ba chan de ya zuro kafanshi kasa kan lallausan carpet d'inshi ya ajiye fararen kyawawan kafafunshi, nan ma yafi minti biyu zaune kan ya mike gabad'aya ya fad'a bayi, alwala yayi ya fito tare da nufan inda yake ibada wadda aka ware a cikin d'akin aka kawata shi sossai gwanin ban sha'awa d'akin kad'ai se yayi girman wani gidan talakan.

Don gefe parlor ne me d'auke da set d'in kujeru cip da Tv plasma a makale jikin bango, kan inda gadon yake kenan komai a d'akin Ash and black ne ba ta yadda zan iya kwatanta muku had'uwar d'akin nan, ku kiyasta da kanku, nafilfili ya yi tayi kan ya bud'e shelf na littatafan addini dake gabas dashi ya d'auko alqur'ani ya fara karantawa cikin natsuwa da kamala seda yaji kiran sallah kan ya mike ya d'auki chasbi ya fice don tafiya masallaci.

Ba shi ya shigo gidan ba seda gari ya d'an fara haske, direct toilet ya fad'a wow toilet d'inma ya had'u iya had'uwa banda kofan shigowa akwai wani transparent door a tsakiya wadda yaci gabad'aya fad'in toilet d'in filin dake tsakanin first door da second door d'in mirror ne me tsananin kyau black gefenshi daga jikin bango shelf ne me d'auke da towels manya da kanana masu kyau.

Har bathrobe akwai a ciki gefe wasu sets d'in perfumes ne masu tsananin kamshi dake Allah ya halliceshi da son kamshi a rayuwan shi se karamin wardrobe me d'auke da jallabiyoyi kala kala masu kyau da tsada, In ka shiga next transparent door d'in gefe shower ce itama a zagaye take gwanin sha'awa se jacuzzi babba me kyau shima don da gani ba karamin kud'i yaci ba, gefenshi hand shower ne a makale.

Chan kuma daga gefe Hand basin ne shima na yayi, komai na toilet d'in black ne da ratsin fari, wanka yayi cikin natsuwa bayan ya cika sabulan wanka masu kamshi da jacuzzi d'in a cikin bayin ya tsane jikinshi kan ya fito ya zauna gaban madubi ya fara shafe shafe da kalkale kalkale kaman wata mace Allah ya gani yana tattalin fatanshi sossai da kuma gashin kanshi yana basu lokacinsu ne sossai.

Bayan ya gama yayi wanka da turare kan ya nufi real closet dinshi, yana budewa nace 'wow' ciki kayayyaki ne kala kala komai neat gasu a goge a jere reras ba irin kayan mazan da babu ko waenne da bangaren da aka jera su, kuma rabi da kwata bakake ne jefi jefi ne zaka tsinci wata kalar ko fari ko ash shi kuma haka Allah yayishi be son komai colored thing in ba baki ba, fari ko Ash.

Kananan kaya ya zaro riga da wando na companin Armani ya saka rigan se ya mishi kaman body-hug sbd ya d'an matseshi guntun hannu gareshi wadda hakan ya baiwa damtsenshi dake cike a kuma murd'e damar bayyana, a izzance ya wuce wurin takalmanshi ya za'bo normal Aldo sliffers ya saka wow zo kuga yadda ya had'e, briefcase d'inshi kawai ya d'auka ya fito asalin main parlor na saman a kan kujera ya ajiye ya wuce kitchen ya san har yanzu hamna bata tashi ba bare tayi tunanin had'a mishi breakfast ace mutum In ba yawo ba to fah yana bacci?.

Coffee ya had'a ya fito parlor yana sha yana kallon agogo sharp sharp ya gama sha ko damuwa da zafin be yi, ya d'auki briefcase d'inshi yayi waje cikin bakaken motocinshi ya za'bo wata Ford ya shige tare da warming d'inta kan ya ja ya fice daga katuwar tsakar gidan nashi, takwas daidai ya taka kafanshi cikin hall d'in tare da jan kofa a bayanshi.

Cikin tafiyanshi na isa da kasaita ya haura tare da d'aura briefcase d'inshi kan desk d'insu na lecturers, class rep ya kira da hannun ya taso ya zo, bayani ya mishi na abubuwan da ze d'auko a office d'inshi, su projector da microphone kiran wani class rep d'in yayi suka fice don d'aukowa, ta cikin dark space d'inshi yake karewa d'aliban kallo, matan se wani karairaya da iyayi suke.

Ko wacce ta kure adakar kwalliya, kaman masu zuwa wurin party, kaman ance ya kalli wurin ya kuwa hangeta zaune kusa da zarah kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta, fuskanta kad'ai ya kalla ya san tana cikin damuwa gashi minti minti tana share hawaye da alamu kuka take, kan zarah ya maida idonshi se surutu take zuba mata kasa kasa ba tare da ta lura da halin da kawar nata ke ciki ba.

Me matsalan yarinyar nan wai? Me ke damunta haka!! Allah masani ace yarinya karama haka me kananan shekaru kullum tana cikin rud'u da damuwa!! Wayanshi ya fiddo faskekiya da ita ya shiga massage ya rubuta "yhu are very stupid" ya turawa zarah, da sauri ta d'ago ya kuwa banka mata harara don ya cire glass d'in, kus tayi kuwa don class d'in tsit ba ko motsin kirki, sbd wargi ma wuri yake samu, Ina suka ga fuska a nan.

Yana shirin yin magana ne ya ga shigowan class rep, hakan yasashi fasa fad'in abinda yayi niyya, da kanshi ya sauka ya had'a komai kan ya fara lectures cikin kwarewa ga iya jefa tambayoyi kawai se yayi pointing d'inka yayi tambaya, in macece tayi ta karairaya tana amsawa, wacce ta iya fine wacce bata iya ba ya ganar da ita abinda yake nufi, kaman daga sama taga yayi pointing d'inta, zarah ta dafa kirji alamun "me" se ya girgiza d'an yatsan ya nuna Noor, a tsorace a kuma rud'e ta mike ta tsaya.




                      🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
            •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                       *08*

A d'an tsorace ta mike tana kallonshi ita har ga Allah tana class d'inne kawai amma bata san me ake ba, tunaninta na ga irin wulakancin da ta sha a wurin baba yau da safe, har marinta yayi sbd abunda ya faru a gidan inna jiya, hakan yasa kwata kwata duniyar ya fice mata a kai, har tunanin irin matakin da zata d'aukarwa rayuwanta take.

"Yes!! What did I said it's Fungi in hausa?" Ya kuma jefo mata tambayar a karo na biyu, nan ma Shiru tayi hakan ya sa ya tabbatar da cewa gangar jikinta ne kad'ai a class d'in hankali da ruhinta sam basa jikinta.

Tsallaketa yayi ba tare da ya kuma kallonta ba yayi pointing wani ya bashi amsa, be kara bi ta kanta ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi wadda hakan yasa ta zamewa ta zauna kanta a kasa, hannun zarah taji a nata hakan ya sata maida hankali kanta, girgiza mata kai tayi a hankali tace "sorry, karkiyi kuka" murmushi ta sakar mata ita wannan be kai ya sata kuka ba sam.

Aiko cigaba da tunanuka nayi har ya fita ban ma sani ba, hayaniyar da class d'in ya d'auka ne yasa ni dawowa cikin hankalina Ina kallon zarah dake ta kallona ban san dalili ba nace "wai har ya fita?" Hannuna ta

4 / 44