NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   40 / 44

117K to 120K   out of 131.7K words

chan yace "zazzabine ya kamata da asubar nan" Anty rahama da kalthum murmushi suka sake suna fahimtar inda maganan ya dosa sede suna kuma mamakin ya za'ayi tayi ciwo biyan ba buduruwa bace? Oho Allah masani.

Umma tace "ba yadda zamuyi hakanan zaka biya muku flight in yaso mu mu tafi da umman taku a mota, ban yarda da cewa asiri Hajiya umma zata mana ba watakila ita ma asirin aka mata ba cikin hankalinta take ba, Allah sarki er uwata" Abba yace "bazamu tafi da ita a mota ba baze yiwu ba, tabi mota ita kad'ai ko ku had'ata da d'iyarta bazata cika burinta na kashe min ku ba" ummu zatayi magana ya d'aga mata hannu yace "this is my final decision so bana son wani objection, Abdul je kula da Lafiyar matarka, hafeez tafi Airport muga ko za'a samu flight, rahama, kalthum kuje gida ku shiryo ku kuma tambayi izinin mazajenku zan kirasu waya"

Yana kai nan yayi sama zuwa part d'inshi, duk mikewa sukayi suka tafi cika umarni, shi Abdul har ga Allah be yi niyyar sake komawa yola ba gashi sati biyun da aka ba mama a hospital jibi ze cika, tunanin kiran international office yake, kaman kuwa yana ransu se ga kiransu d'agawa yayi suka gaisa cikin harshen turanci suka fad'a mishi visa d'insu iman da baba da kuma mama are ready zasu iya tafiya any moment.

Godiya yayi ya kashe wayan ya kira hospital ya tabbatar musu ayi arranging mishi komai zuwa farkon next week ze fita da ita, sallama sukayi ya shiga motanshi ya tayar zuwa gidanshi yana isa Abba na kiranshi ya tabbatar mishi ya cewa Hamna ta shirya maza ta je gidan yanzu da trolley d'inta, yana kuwa shiga d'akinta ya fara shiga tsaye take tana taka rawa ta Kure Home theater, duk tunaninta komai ya kammalu ne jin bata ji motsin iman ba tun da garin Allah ya waye.

"Ki shirya zaku wuce yola yanzu da umma" kallon mamaki ta mishi tace "yola?? Sbd mene?" Yace "when you reach Abba's house you ask him this stupid question, he's there waiting for you" yana kai nan ya juya ya fita, d'akin Iman ya shiga bata kan gado se karan ruwa da yaji a bayi kenan wanka take, without second thought ya fad'a toilet d'in ihu ta kwala tana juye juyen neman towel a rud'e.







                      🖤Gureenjo🖤


               🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
     *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                             *052*

Da hanzari ya d'auke towel d'in cikin sigan neman tsokana ya d'age hannu sama me makon ta nemi wani abin se ta fara neman kwace towel d'in hadda tsallenta wadda hakan ya bashi muguwar dariya aiko be rike ba ya fara yana kuma d'age towel d'in sama yayin da ya kankance idanunshi yana morewa kallonta hakan, ganin dariyarshi da kuma kallon da yake mata na kara karfi ne yasa ta hankalta da abinda take aikatawa da azama ta shige bayanshi ta rungumeshi tare da 'boye fuskanta a cikin bayanshi tasa hannu biyu ta zagayo cikin shi.

Murmushi ne ya subuce mata jin har yanzu dariyarshi yake, rana na farko kenan da taga ya jima yana asalin dariya ba murmushi da ya saba ba wadda hakan itama ya sata jin sanyi har cikin ranta, muryan shi ta tsinta yana cewa "oh hayatee come on zo ki kwace kayanki mana ko kin hakura..." da wani irin murya yake maganan, cikin shagwa'ba da bubbuga kafa kasa tace "uhm uhm zaujii bana so" murmushi yayi yace "Toh zo kici gaba da wankanki" Tace "uhm uhm se ka fita plssss" yace "Toh sakeni In fita" nan ma ta kuma cewa "uhm uhm sede fa ka juya mu tafi a haka kana fita In rufo kofa" siririyar dariya ya saki yana cewa "Lallai ma hayatee toh me zaki 'boye min me ban gani ba? Ko se na siffanta miki yadda duk wani hallita na jikin ki ya....." katse shi tayi da wata shagwa'ba me kashe zuciya "uhm uhm ni Allah bana so zaujii ko kayi shiru ko Inyi kuka" Murmushi ya saki yana kama baki yace "errrh Abdulraheem kama bakinka kan Sarauniyarka ta fara rigima Don bazaka ji da daad'i ba".

Dariya tayi da ita d'in makale bayanshi ya juya suka fara tafiya dariya abinda ta sa sun ya ke bashi, in ba gulma ba bayan ta gama tsalle yanzu a gabanshi kuma ta koma bayanshi wai bata so ya ganta, suna isa kofa maimakon ya fita se yayi wuff ya juyo ta wadda hakan ya sata tsala mishi kara ta kuma shigewa jikinshi dariya ya kuma saki, ya rungume ta tare da kissing kumatunta yace "can't love you less hayatee, My drama queen" sakinta yayi zata kuma makaleshi yace "kinga idanuna rufe suke ba ganinki nake ba" kallon idanun tayi aiko rufe suke a ganinta fa kenan amma shi fess yake ganinta, murgud'a mishi baki tayi tana d'an hararanshi seda ya fita ta rufo kofa tukun yace "I see that!!! Kuma se kin gayamin da wa kike Allah ya fito dake" baki ta kama tana zare idanu tana jinshi yana waka har ya fice.

Murmushi tayi tana sauke ajiyar zuciya kan ta koma ta karasa wankanta ta fito mai ta shafa tayi feshe feshen turarukanta masu bala'in kamshi da sanyi atampha ta d'auko zata saka se kuma ta fasa ta d'auko less riga da zani wadda d'inkin rigan ya had'u karshe leshin ma kana gani zaka san ba karamin kud'i ke gareshi ba, gashi purple and pink ba karamin amsanta yayi ba, haka nan ta tsinci kanta da shafa powder ta saka kwalli tare da shafa pink wet lipstick a saman lips d'inta a hakan ba karamin kyau tayi ba tayi wani fresh da ita kamshinta na amare ya bule ko Ina ya had'u da na turaren da ta saka bayan ta gyara d'akin kan shiganta wanka, d'aurinta ta kafa kan ta mike ta fito parlorn saman ba kowa se tvn dake kara.

Kitchen ta nufa Don wani irin yunwa ta tashi dashi don ma ta sha tea cikin dare had'e da magani, freezer ta bud'e ta fiddo kaza ta ajiye tana kokarin fiddo kayan miya ne taji an rungumeta ko bata juyo ba ta san waye daga kamshin sassanyar turarenshi da take bala'in so, juyowa tayi tana murmushi ta sakala hannayenta bisa bayan wuyanshi tare da karya kai tace "zaujiiii" ta wani ja sunan har cikin ranshi yake jin amsa kuwwan muryanta me matukar kashe mishi jiki da bud'e mishi duk wata kofa ta tsikar jikinshi In ta kirashi da zaujiin nan.

Wani irin mahaukacin kaunanta ke kara ninkuwa cikin rai da zuciyarshi, kasa amsa mata yayi se gira da ya d'age mata yana me kallonta musamman pink lips d'inta, motsa su tayi tana cewa "yunwa..... bari In girka mana abinda zamu ci" seda ya tsotse lips d'innan da suka tsone mishi ido kan yace "ummu says karkiyi girki ki shirya muje gidanta, and am sorry zan sake baki wahala Abba yace mu shirya zamu tafi yola gabad'aya".

Kallonshi take cikin fara'a da sakin fuska tace "lafiya dae ce ko?" Yace "toh dae da sauki, je ki shiryo kar yunwa ya illatamin ke In shiga uku" cikin murmushi ta zame ta koma room d'inta lafaya ta d'auko purple yaji stones ta d'aura kan less d'in ta d'auki wayanta a hannu ta fito, hannunsu cikin na juna har mota daga ka gansu zaka san ba karamin soyayya suke wa juna ba gashi sunyi mugun matching dukda ita chocolate color ce shi kuma asalin fari ke gareshi.

Shi har ya ma manta da wani matsalan umma hiransu suke cikin nishad'i har cikin parlorn ummu inda suka tarar da en gidan zazzaune ummu de ta buga tagumi yayinda zahra ke danna waya hafeez ma na kan doguwar kujera kwance ya lumshe ido, ummu na ganinta ta mike tana cewa "daughter sannu ashe bakiji daad'i ba?" Zubewa kasa Iman tayi tace "mun tashi lafiya ummu?" Ummu tace "Lafiya kalau ya jikin?" Tace "naji sauki ummu Alhamdulillah" kallon zahra da ko d'ago kai batayi ba bare ta kalleta tayi, Abdul na zama gefen ummu ya d'auki trow pillow ya wulla mata a zabure ta mike tana zare ido se kuma tayi ihu cikin jin daad'i ta fad'a kan Iman wadda har seda Abdul ya furta "hasbunallahu wani'imal wakeel" shi da ba shi aka fad'a kanshi ba amma shine da jin zafin.

Cikin fad'a yace "zahra d'agata wani irin sakarci ne wannan? Bakiji nace bata da lafiya ba?" Turo baki zahra tayi tare da sake Iman d'in da se murmushi kawai take dukda taji d'an zafi sbd yadda duk jikinta har lokacin be bar ciwo ba, ummu tace "Ai rashin hankalin zarah!! Allah ya shirya dae kawai azo ayi bukinkin ma ko zan huta In ba Iskanci ba tun yaushe nake miki magana akan rashin lafiyar ummanku da yadda babanku ya tsara tafiyan ba daad'i, kikayi kunnen uwar shegu dani ashe AirPods kika saka kika maida ni mahaukaciya, ya miki kyau".

Mugun kallo Abdul ya mata se idanun ya sauka cikin nata, cikin wani irin sigar tafiyar da hankali ta karkad'a mishi idanun, taune lips yayi yana jin sakonta har kwakwalwan kanshi, ajiyar zuciya ya sauke yace "ummu kiyi hakuri kin san har yanzu yaranta ke cike kanta, wayyo ummu am hungry, yunwa ze kasheni" kallon hafeez da ya mike zaune yana kallonsu tayi ta banka mishi harara, kan ta dawo kan Abdul tace "bana son gulma yaushe kuma ka fara kukan yunwa rayuwarka?" Bata jira amsanshi ba ta d'aura da "bari inyiwa Abbanku magana ko don daughter" ta mike ta Haura, ajiyar zuciya duk suka sauke hafeez yace "nide na shigesu kunga wani hararan da ummu ke zuba min minti bayan minti?" Zarah tace "nide ko fa me zatayi sede tayi hakuri na riga na tsani matar" Abdul ya wani 'bata fuska shima yace "geez hate her tooo" dariya duk sukayi ganin yadda yayi kaman an ajiye mishi kashi gefenshi.

Shiru sukayi ganin ummu na saukowa batayiwa kowa magana ba se iman tace "daughter tashi muje kici abinci kar muyi tafiya da yunwa" mikewa tayi tana tafiya a hankali sbd kar kowa ya fuskanci halin da take ciki gangarowan Abba ne yasa hafeeez da Zahra kwasa har suna rige rigan hawa dining sbd yanzu ummu bata isa ta korasu ba, Abdul da Abba sukayi murmushi yayinda Suka samu harara daga ummu sede batace komai ba.  A natse sukaci abinci suka gama.

Abba yace "Toh kun san late flight muka samu Allah ma ya sa ba'a cika ba ku tashi muyi harama" gangan Iman ya koma kasa kasa yace "ba abinda zaki d'auka?" Tace "eh na bar wasu kayana chan dawowarmun nan" yace "baby kin tabbatar kin koshi? Ko In rike miki takeaway?" Da sauri ta girgiza kai yace "you sure??" Ta gyad'a kai yace "ya jikin kuma naga har yanzu kaman baki tafiya daidai" baki ta zumburo kallon su Abba yayi ya girgiza kai kawai yana cewa "yarinya kinci sa'an su Abba zamu had'e ne" gwalo ta mishi ya kuma gyad'a kai yana taune lips.

Zarah dake gefe se dariya take dukda ba jinsu take ba amma soyayyarsu na kasheta, basu wani 'bata lokaci ba suka wuce Airport duk cikinsu ba wadda ya d'auki komai se cards d'insu sbd duk suna da kaya chan kuma ba Lallai ne ma su jima ba, a Airport suka had'u da su Anty rahama kowacce mijinta ya kawo ta, nan da nan suka d'aga cikin mintuna suka isa yola motocin fada ne suka zo suka tare su da dogarai da kuyangai, cikin convoy na burgewa suka isa fada sun samu baba fufore ya zo suna tattaunawa da kannenshi a tsaitsaye suka mika gaisuwa kowa yayi part d'inshi akan da yamma za'a zauna family meeting.

Suna shiga d'aki ya d'agata sama zuwa kan gado tare da fad'awa jikinta ba ta yadda zata ji zafi ba yace "baby naga kin warke I need you" waro ido tayi tuna azabar wuyan da tasha da sauri ta nemi mikewa ya kuma danneta ya sa hannu ya zare lafayan jikinta kan ya  samu fatan cikinta ya fara mata jakulkuli yana cewa "me ma kikamin d'azu???? Yanzu wa na kama" ihu ta fara da dariya tana "wayyo wayyo ka bari dan Allah, na tuba" be bari ba seda yaga tana dariya har da hawaye shima murmushi cike a fuskanshi cikin wani irin salo me wahalar fassaruwa ya fara yawo da hannun nashi a hankali zuwa lungu da sakon jikinta kan kace kobo zance ya chanza.

Bayan kammaluwan komai ya d'auketa suka shiga wanka tare, duk se murmushi suke zubawa Don har ga Allah itama fah taji daad'i kasancewa dashi wani irin so da kulawa ya nuna mata wadda bata tunanin wata mace ta san salon nashi bayan ita, a wankan ma neman tsokana da ta'be ta'ben da ba'a aikeshi ba kawai yake suna fitowa suka shirya shi ya wuce massallaci don sallar azahar da aka kira ita kuma tayi a d'aki bayan ya dawo suka d'an kwanta bacci se la'asar suka tashi inda suka samu abinci kala kala da aka shirya musu a kan dining sallah kawai sukayi suka fito suka ci abincin.

Sunayi yana duba time sharp sharp sukayi suka fice babban parlorn me martaba, duk family an taru waenda duk suke cikin gidan Kwai da kwarkwata sune kusan karshe shiga, nenne Petel ce tsugune gefe tana aikin kuka yayinda kallon fuskan baba galadima ze sa ka gane shima yana cikin alhini, umma ce d'aure a gefe se shure shure take na se ta fice daga gidan tunda aka shigo da ita mijinta wato baban Hamna na zaune yana karkad'a kafa gyaran murya me martaba yayi kowa ya natsu, yayi umarni baba modibbo ya bud'e taro da adu'a nan ya zuba musu adu'o'i kan aka shafa.

Ya fara da introducing abinda ya kawosu na Ciwon hajja umma, Hamna ta zama abin tausayi tayi tsuru tsuru a zabure take sbd saura kiris umma tayi ajalinta sau ba adadi ana tsayuwa taimakonta duk ta firgice, sunanta mai martaba ya kira ta amsa a tsorace yace "na san bazaku rasa aikata aikin sirri da mahaifiyarki ba kinga dae abinda yake samunta bamu da tsimi bamu da dabara se abinda Allah yayi se kuma abinda zaki fad'a mana na me kike tunani ya jawo hakan, sbd idan ba'a san musabbabbin Ciwon ba ba ta yadda za'a taimaka mata".

Shiru tayi se kuka tsawa aka daka mata "natsu ki kula ki San wadda ke miki magana" kukan ta karawa karfi tana zazzare idanu, kaman an mitsini umma ta wani ihu kan ta fara fad'an abubuwan da ta aikata da irin tsanan da tayiwa ummu da irin tuggun da ya dinga sakata da iyalanta da wuraren bokayen da tayi ta zuwa haka ta dinga zuba kaman rediyo lalattacce.

Mamaki, Al'ajabi da tausayi had'e da damuwa ya had'ewa waennan familyn musamman manyan da suke ganin gazawansu ta wani 'bangaren ne yaja hakan yayinda take fad'an abubuwan da ta aikata kamanninta na sauyawa daga fara zuwa baka idanunta suna wani iri marar kyaun gani, mijinta ne ya katse shirun ta hanyar mikewa ya kalleta yace "hmmm karshen alewa kasa, hajjiya umma kenan ashe lokacin girban abinda aka shuka yayi kenan? Baki ta'ba kyautatamin ba a rayuwar mu na aure shekara da shekaru kin maidani tamkar masa a tanda se yadda kika juyani zanyi kin zalunci zaman aure zan iya yin rantsuwa da alqur'ani wannan yarinyar taki ba 'yata bace ba sbd rabon da ki yarda in kwanta dake a matsayin matata ta sunnah tun daren farkonmu, shekaru talatin kenan itakuma erki na shekara ashirin da, Allah ya gani kuma shi ba azzalumin bawansa bane ko na yafe miki ubangiji baze ta'ba yafiya a gareki ba sbd baki daraja umarninshi ba, hajjiya umma kije da halinki na sakeki saki uku, na barku lafiya" ya juya ya fice nan fah parlorn yayi tsit cikin jimami yayinda Hamna ta sandara ihu tayi kan maman nata tana jijjigata "waye ubana umma? Umma ki fad'amin da wani bakin kazamin kikayi zina kika haifeni, wayyo ni" tana kuka umma na dariya.

Kukan da Iman ke yi ne ya isheshi wai ita sarkin tausayi dama ga ranshi na mugun tafasa abubuwan da sukayi mishi tsakaninshi da ummunshi na dawo mishi Sannan abubuwan da sukayi ta bashi na kazantan boka na sakashi jin wani mugun amai na taso mishi, ga abinda tayi niyyan yiwa iman da Safen nan da hakan ya faru bata kira sunan umma ba da shikenan yanzu yana nan hankalinshi In yayi dubu ya tashi, mikewa yayi ya kama hannunta ta mike itama kallon hamna da ta tsaya kallonshi yayi yace "na sauwake miki...." nenne tace "Abdulraheem" be kalleta ba ya karasa "igiyoyin aurena dake kanki guda biyu" ihu ta kurma tayi kanshi kan ta karasa ya daka mata tsawa azuciye "na rantse da sarkin dake busan numfashi yatsanki d'aya ya ta'ba jikin rigata se nayi miki muguwar illaar da har abada bazaki manta dashi ba, Sannan had'ani da mahaifiyata da kuka tayi a baya ban yafe ba Allah ya sakamin da mafi azabar sakayya" ya fisge hannun iman sukayi waje ana kiranshi Ina yaki tsayuwa se part d'insu.

Abubuwanshi kawai ya d'auka ya kuma janyo hannunta a parlorn ta tubure tare da cewa "wai lafiyanka hamma? In fah rai ya 'baci hankali baya gushewa iyayenmu ne chan suke kiranka....." katseta yayi da cewa "wuce mu tafi Saudah karki kara 'bata min rai" Tace "amma..." tsawa ya daka mata "shut up!!!! In kema bazaki bini ba fine se inyi tafiyata dama yanzu mata sun fara bani tsoro" ya juya ya fara tafiya a sanyaye tabi bayanshi hawaye na zubo mata, mota ya shiga itama tazo ta shiga tunda suka fara tafiya yake wayoyi kala kala duk cikin harshen turanci kuma a hanzarce har suka isa Airport bazasu samu jirgin kano ba se na lagos ji yake In ya kwana yola mutuwa ze yi haka ya biya musu suka wuce.







                   🖤Gureenjo🖤


       

40 / 44