Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
cireka ba bazan so kaki jin maganar mahaifiyarka sbd mace ba, na fahimceka yanzu, na gode".
Mikewa tayi tace "zan tafi se anjima" da kallo ya bita har ta shiga mota yau ita ke ja bata taho da driver ba dama chan ta iya rigima ne irin nata ta matsawa Abba ya sama mata driver wai driving na gajiyar da ita, Muhammad ya jima sossai zaune anan kan ya mike ya fice zuciyarshi cike fal da tausayin iman Adu'a yayi alkawarin sata har ta samu kwanciyar hankali a rayuwanta ze cigaba da adu'a Allah ya bawa Abdul daman taimakonta, sannan ya barta da mutane irin su zarah da mama, ya karkato hankalin iyayenta kanta ba se sadda ta musu nisa ba.
******
Bayan isha baba na zaune kan taburma a tsakiyar gida yana jin rediyonshi yaji yaro yayi sallama ya shigo yace "wai ana sallama da malam hafeez inji wani a waje" yace "to to waye kuma yake sallama dani?" Yaron yace "wani ne ban sanshi ba" mikewa baba yayi ya zura silifas yabi bayan yaron, Abba ne tsaye daga shi se riga da wando na wani yadi wadda a cikin kayanshi gabad'aya ze iya cewa shine me karamin kud'i dukda ya kai 20k amma In ba ka san kan yadudduka ba baza ka ta'ba ganewa ba sannan be d'aura babban rigan ba hannunshi ba agogo takalmin kafanshi kuwa lufas ne na wankan shi.
Musabaha sukayi da baba kan yace "Lafiya kuwa malam kake nemana?" Abba yace "Lafiya klau se alkhairi, wato malam d'ana ne yaga 'yar wajenka Saudah yace min alambaran duniya ba wacce yake so se ita, kuma baya son auren ya d'au lokaci sannan gaskiya bazan 'boye maka ba yana d'an ta'ba shaye shaye" ya karasa yana furta "Astagfirullah" a zuciyarshi baba yace "to masha Allahu fad'uwa yazo daidai da zama dama chan miji nake nema mata ido rufe Ai Don yana shaye shaye ba wani abu bane ze dena ne, ni de a matsayina na mahaifinta na bashi ita duniya da lahira in da hali ma yazo juma'an nan a d'aura musu aure".
*Allah ka rabamu da uba irin wannan*
*dukda nayi niyyar yin pages biyu ban samu dama ba amma ga wannan long chapter d'in ya ninka kowanne tsawo a kafta, and plz don't forget to comment*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*dedicated to MUKARU DA JUNA group thank yhu so very much🥰🥰*
*019*
Da tsananin mamaki Abba ke kallon baba, wani irin uba ne wannan? Wani irin ubane ze so 'yarshi ta auri mashayi bayan ya san outcomes na zaman aurenta? Ya yarda ze bada 'yarshi ba bincike ba komai? Yanzu kai be ma san me ze iya cewa akan baba ba, Da kyar ya iya had'a "Toh Toh zamu duba In zamu iya had'a komai kan juma'an" baba yace "a'a ba se kun had'a komai ba ma na hutace ku har sadaki ni zan biya mishi" Abba yayi saurin cewa "A'a wannan kam ze biya amma sauran abubuwan se a hankali ze mata ka san yanayin rayuwan", godiya baba ya d'inga yi kaman wadda aka ce an baiwa kujerar Makkah alhalin jin daad'in ya rabu da kaya yake yi kuma yayi alkawarin wannan karon ta kashe auren wallahi se ta bar mishi gida.
Cike da tausayin iman Abba ya tafi, se yaji wani sonta a matsayin 'ya ya shige shi kai koda ace rabuwa sukayi da Abdul, ba fata yake yi ba baze ta'ba barinta ta dawo gidan nan ba ze ci gaba da riketa har Allah yasa ta samu wani mijin kuma.
******
Tun 8pm suka fara presentation d'in amma sam hankalinshi kwata kwata baya kan abinda akeyi tunani kawai yake ko me Abba yake tattaunawa da baba? Ko ya yarda ya bada auren? "Dr. Abdulraheem Ahmad Malabo do yhu have anything to say?" Da sauri ya mike yana cewa "yes sure" kan ya tattari abinda ze yi presenting ya fita ya farayi cikin had'add'iyar turancinshi.
******
Tunda ta farka daga alluran take kwance kawai ita kad'ai ta san abinda take sakawa a zuciyarta, Allah ya gani tayi iya hakurin da zata iya yi, ta gaji hakanan, so ta yanke shawaran ana sallamanta daga asibitin nan bazata jira wani auren tozarcin da baba ze mata ba, zata tafi chan inda ba wanda ya santa tayi irin rayuwar da zata ji daad'i, ta'ba kafanta da akayi ne yasata maida hankali kan wadda ya ta'ban.
Murmushi tayi kan ta d'auke idanunta tana mikewa zaune tace "zarah kin dawo?" Zarah tace "yes sarkin tunani na dawo, meyasa kike son takura kanki da tunani ne? Ko kin manta duk abinda ya faru da bawa Allah ya riga ya rubuta tun kan a hallice shi? Ki d'auki matsalanki a matsayin ba komai ba zakiga ya wuce". Iman tace "kayyah zarah kowa haka yake cemin ze wuce ze wuce amma banga alamu ba".
Zarah tace "chuppp ze wuce in shaa Allahu" zama tayi ta d'iba mata abincin da ta kawo a plate tare da gyara zama da kyau tace "haa open your mouth" dariya iman ta saka tana cewa "ke me haka se kace wata baby? Come on bani zan iya ci da kaina" zarah tace bata san zancen ba ai bata da lafiya se ta bata cokali take ta kokarin sawa a bakinta yayin da ita kuma take ta kawar da kai tana sa hannu cikin dariya suke tayi seda zarah taga iman tayi dariya sossai kan ta mikamata chokalin tana murmushi.
Kar'ba tayi ta fara ci zarah na ta bata labarin ban dariya, yawanci duk akan 'yan gidansu da yadda take musu rigima da fad'an ummu In an ta'bo Anty hamna da fad'an Abdul da hamna, da yadda suke kawo kara kullum musamman hamna se dariya iman keyi musamman yadda zarahn ke yi da fuska duk irin labarin da zatayi se tayi expiration d'in so childish.
A haka iman ta cinye abincin plate d'in tas ba tare da ta lura ba, dafa kafad'an zarah tayi tace "thank yhu zarah, kin ragemin damuwana sossai, In Ina tare dake har mantawa nake da wani damuwa" zarah tana murmushi tace "you are welcome dear, bari inzo In tafi yau nayi dare a waje" Iman tace "Eyyah de karki tafi plz ki kwana dani yau" zarah tace "Da ummu zata yarda da nafi kowa farin ciki amma bata yarda in kwana a ko Ina".
Har zarah ta mike iman ta tsinci kanta da cewa "Hamna matar Dr. Malabo ce?" Zarah ta juyo tana 'bata fuska tace "yes matar yaya Abdul ce, and cousin sister d'inmu baki ga ba yadda take rayuwar aure kaman wata jahila shide yaya Abdul be yi sa'ar mata ba gashi ummu kwata kwata bata son laifinta kwanaki fah har pills yaya ya kamata tana sha amma da yayi magana ummu ta goyi bayanta, duk da ta san irin son haihuwan yaya, auren fa is getting to five years amma taki yarda har yanzu ta haihu, yucks I hate her".
Iman da ta bud'e baki tana kallon zarah, tayi wani murmushi tace "Kai zarah tamabaya fa d'aya na miki, ke dama zubaida aka sa miki ba fatima ba" dariya zarah tayi kan tace "ni na tafi se da safe" iman tace "jira in rakaki mota samun In taka kafafuna na gaji da zaman wuri d'ayan nan" fita sukayi tare zarah na ci gaba da mata surutu, iman tace "ai ni ba gane hiran kin nan nake yi ba sbd sunayen da kike kiran ban sansu ba" zarah tace "duk zaki sansu ne bari gobe zan baki labarinmu gabad'aya yadda In Ina hira zaki fahimceni".
Har mota iman ta rakata kan ta juyo tayo d'akinta zuciyarta wasai gaskiya zama da zarah akwai daad'i, ba kad'an ba, tana zama a mota ta fiddo wayanta ta kira hammanta seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga a daidai lokacin ta tada mota tana reverse "Assalamu alaikum hamma barka da dare" Yace "wa'alaikissalam yauwa barkanki dae, me kike yi har yanzu a waje zarah?" Tace "wallahi na d'an tsaya da iman ne kad'aicin kar ya mata yawa" yace "hakan yayi kyau" Tace "Hamma plz ka samo mana shawara?" Yace "yes na samu" Tace cikin farin ciki "Alhamdulillah menene gobe in je mata da albishir na san zatayi farin ciki sossai" seda ya d'an murmusa kan yace "Abba ya nema min aurenta" waro ido tayi in disbelief tace "dan Allah dae yaya da gaske kake?" Yace "dama mun saba wasa irin haka dake?".
Wani irin ihu ta sake da seda ya matsar da wayan daga kan kunnenshi se kuma tayi d'an Shiru yace "menene kuma?" Hawaye ne ya gangaro mata tace "ashe iman da gaske takeyi yaya? Ashe baza ta ta'ba samun farin ciki me d'aurewa ba? Ashe bazatayi auren soyayya kaman yadda take buri ba?" Cikin kasa da murya yace "wa ya gaya miki?" Tace "gashinan yaya zaka aureta ne out of sympathy, na so mata farin ciki a rayuwa" yace "kina tunanin bazan iya bata farin ciki ba" zarah tace "yaya ba haka bane amma a sanin da na maka baza ka ta'ba d'aukanta da muhimmanci ba tunda ba sonta kake ba, and na tabbatar se ta fuskan ci kalubale sossai wurin Anty hamna da ummu".
Shiru ya mata tace "ya akayi Abba ya yarda ya nema maka aurenta?" Ya d'an yi Shiru ta gane ya fara gajiya da surutun ne, ta san sbd ita ce ma ya sa ya jima da su Anty Rahma ne da ya jima da kashe wayanshi "I told him everything single thing about her, and believe me yanzu inaga Abba yafi sonta akaina da ke ma" murmushi zarah ta sake har tana had'awa da dariya tace "bade ka fara kishinta ba?" Tsaki yayi, tana dariya tace "Ohk yaushe zaka dawo Hamma?" Yace "tomorrow evening" Tace "and yaushe ne baban yasaka auren?" Yace "hey I'm pissed off da surutun kin nan, Friday za'a d'aura after juma'at prayer, and mind you karki fad'awa kowa maganan auren nan kin san what ummu is up to In aka zo maganan hamna, har ita karki fad'amata".
Tace "Ohk tohm, yhu know am good at keeping secrets" yace "look who's talking" tana parking a harabar gidansu tace "yauwa Hamma ka sayomin chocolates dayawa plz" tsaki yaja kan ya kashe wayan, murmushi kawai tayi ta karasa cikin gida, Alhamdulillah tayiwa Iman murnan samun miji irin hammanta a zamanin nan samun irinshi se an tona, haka shima ta mishi murnan samun mace irin iman amma tsoronta d'aya irin zaman da zasuyi kan su fahimci juna don shi mutum ne me murd'ad'en hali.
Gashi ba sonta yake yi ba bare tace abin ze d'an daidaitu amma ba matsala zata yi iya kokarinta wurin ganin ta fahimtar da Iman waye Abdul tunda duk duniya zata iya cewa tafi saninshi akan kowa bayan ummu, tunanin ummu kad'ai ya sa gabanta fad'uwa what if ummu ta tsani Iman? Yadda ummu ke son hamnan nan ta san definitely bazata bada goyon baya akan auren nan ba, Allah sarki iman bazan so ki shiga wani tashin hankalin uwar miji ba kuma amma ya zamuyi?.
Ummu da ta fito daga kitchen tuntuni tana ma zarahn magana bata ma jita ba seda ta ta'ba ta kan tayi firgigit tace "ummu" ummu tace "tunanin me kikeyi haka da kankantar shekarun Kin nan?" Shagwa'be fuska tayi kan tace "haba ummu kema kya tambaya bayan kin san besty na na asibiti?" Girgiza kai kawai ummu tayi ba don ta yarda ba tace "Toh tashi ki hau kiyi wanka ki huta yau tun safe kike asibiti har warin asibiti kikeyi" zata fara rigima ummu Tace "chupp bance ki min shagwa'ba ba ni bazanyi magana da me warin asibiti ba" baki zarah ta turo gaba tana mikewa tace "ni bana warin asibiti Allah" nufan ummun tayi da iya gaskiyarta take son ta shunshunata taji ko tanayi, ummu se ta matsa baya tana dariya, hannunta na toshe da hancinta.
Hafeez da shigowarshi kenan yayi saurin sa hannu a hanci yace "uhm uhm uhm ummu me kika samu me wari a parlorn nan haka" Da hannu ta nuna mishi zarah tace "gata nan" a zuciya zarah ta haura sama tana bubbuga kafa su kuma suka sa dariya.
********
Washegari da safe sauban ya sallami iman dayake sunyi waya da Malabo a jiyan yace ze iya sallamanta In har ta warke ya sauya plan, sauban be tambayeshi komai ba sbd ya san tunda yace ze fad'a mishi ze fad'a d'inne, Ai ko iman sossai taji daad'in sallaman da ya mata, ya juya ze fita kenan tace "Dr." yace "yes" Tace "plz ko zaka iya had'ani da wadda ya biyamin gabad'aya kud'in jinya na In mishi godiya?" Yace "a'a shi wadda ya Biyan yace ba se na bayyanashi ba don Allah yayi ba don ki gode mishi ba, in short ko sunanshi be yarda in furta miki ba" juya kai gefe tayi kan tace "shikenan kayi mishi godiya, Allah ya biya shi da gidan Aljannah" yace "Ameen" kan ya juya ya fice, ba 'bata lokaci suka had'a 'yan kayyayyakinsu kan su gama ma zarah ta zo so da motanta suka nufi gida.
Da sallama ta shiga gidan dayake itace a gaba, baba dake zaune akan taburma yana karyawa be ko amsa sallaman ba yace "jibi zan d'aura miki aure, ban bukatar jin komai daga bakinki, for ur information ba taron da za'ayi a gidana, sbd kud'ad'en da na kashe a aurenki na baya sun ishe ni kayan d'akinki de tun na aurenki na farko shi za'a kaimiki don d'a me tarbiya da biyayyya ne ake yiwa kayan d'aki me ma'ana da kyau, and Ina so ki sani wallahi na rantse da girman Allah kika kashe aurenki kika dawo gidan nan ko gidan wani d'an uwa nawa Allah ya isa ban yafe ba kai ko Ziyara ban yarda ki kawo ba se sadda na nemeki kinji na gayamiki".
Be jira cewarta ba ya shige d'akin umma, kukan ma yau kam kin zuwa mata yayi don haka se taci gaba da tafiyanta a hankali zarah ce ta dafa kafad'anta tare da bubbugawa alamun de rarrashi, Mama ma ta dafa d'ayar se kawai ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai mutane biyun nan sun isheta soyayyarsu gareta ma ni'ima ce Alhamdulillah.
Bayan tayi wanka ta shirya suka karya da zarah da mama shima de abincin zarah ce ta kawo amma umma bata kawo musu wani abinci wai don sun yi dawowar sassafe ba, kuma a lokacin ta gama breakfast, don har ikhram da ikhlas sun tafi school, Bayan sun gama Mama ta mike ta fice zarah ta gyara zama akan gadon Mama tace "are yhu ready?" Iman tace "ready for what?" Zarah tace "au kin manta nace zan baki labarinmu yau?" Iman tace "oh oh na tuna am all ears" gyaran murya zarah tayi kan ta fara......
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*020*
Mai Martaba sarkin Adamawa na goma sha hud'u Alhj. Muhammad barkind'o Aliyu Mustapha (lamid'o) shine wadda ya Haifi Abbanmu 'yan asalin kauyen Malabo ne dake kasan fufore local government, Adamawa state. tun farkon sarautar Adamawa a hannun familynsu yake har kawo yanzu, matanshi guda biyu hajiya nenne da Hajiya mama, nenne itace uwargida kuma itace mahaifiyar Abbanmu 'ya'ya goma Allah ya bata bakwai maza biyu mata, Uncle Aliyu, Uncle mustapha, Abbanmu, Uncle hamza, Uncle Mukhtar, Uncle Sadisu se uncle sabi'u, matan kuma Anty Saliha da Anty Murja sune kuma kanana.
Yayinda hajiya Mama ke da hud'u duk mata Aunty Maimuna, Aunty zulfa'u, Anty fatima se Anty maryama, akwai kishi me tsanani tsakanin hajiya nenne da hajiya mama dukda akalar kishin gabad'aya akan hajiya Mama ne da asalin sunanta ya kasance hauwa, hajiya nenne wadda asalin sunanta saudah macece me tsananin hakuri da kawaici, sarauta a jininta yake kasancewarta 'yar sarkin gombe yanzu haka yayanta ke mulkan gombe, shi yasa ta kasance me miskilanci kan ta d'aga kai ta kalli mutum ma aiki ne a gareta sa'banin hajiya mama da badaga gidan sarauta aka aurota ba.
Dukda yadda lamid'o ya so 'ya'yanshi su zamanto masu had'in kai amma inaa hakan be faru ba sbd hajiya Mama ta hurewa yaranta kunne basu son 'ya'yan hajiya nenne ko na miskala zarratin, gaba me tsanani sukeyi dasu, a ta 'baganren nenne yaranta basu damu da hakan ko kad'an ba kasancewarsu maza kuma ba yara kanana ba har gwara ma matan.
Lamid'o yana da kani guda d'aya Abdulraheem wadda ya kasance galadiman Adamawa, a hannun nenne ya karasa girmanshi kasancewar iyayensu da suka rasu tun kan yayi wayau, yana matukar son nenne da yaranta sbd itama tana mishi so ne na tsakani da Allah, be yi aure ba seda aka haifi Abbanmu da shekara biyu ya auri 'yar wazeerin Adamawa Salma aurensu da shekaru biyu ta haifi Ummun mu wacce asalin sunanta Rashida.
Ganin bayan ummu kaman basu da rabon samun wani d'an yasa suka d'auki son duniya suka d'aurawa ummu kowa rashida har cikin sashin nenne yaranta sossai suke son ummu musamman Abba, ba wadda ya isa ta'bata a kafatanin masarautar be rama mata ba har yayyunshi kuwa, sede In iyaye, hakan yasa Baba galadima da nenne petel wato 'nenne karama' yi mishi alkawarin bashi ummu In ta isa aure.
seda ummu ta shekara bakwai kan aka haifi Hajiya umma (hafsat) wato mahaifiyar hamna, so Kin san de son da za'a nuna mata baze kai na ummu ba, ba wai itama ba'a sonta ba a'a, gashi Allah ya yita da tsananin rashin kunya da iyayi da gadara se kace lamid'on ne karan kanshi ya haifeta, tunda ta mallaki hankalinta taga Abba suna soyayya da ummu hankalinta yayi mummunan tashi sbd ita a duniya ba wadda ta gani tana so se shi sede kash bata ma gama JSS class ba akayi aurensu da ummu.
Yaran me martaba mazan duk ba wadda yake aiki a yola se Uncle Aliyu wadda shine yarima