NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   33 / 44

96K to 99K   out of 131.7K words

amsa Don neman tsokana irin nata ta fara wata wakar.

"Anyi sake ga d'an zaki ya girma... wa za ya jaa da ikon Allah.... mu bamu nufin cuta ga d'an uwa... kowa ya cuce mu mu barshi da Allah......." "Saudah" ya kira sunanta ta waigo gabanta na fad'uwa Don duk sadda ya kirata da asalin sunanta se taji tsikar jikinta na tashi "na'am" ta amsa tana dawowa baya dama har ta wucesu "Kun gaisa da umma?" Tace "eh mun gaisa" wani kallo suka watsa mata, tayi musu murmushi ta wuce room d'inta.

Murmushi yayi yana girgiza kai, su kuwa dining suka nufa suka zuba abinci ko waccensu ta fara ci yana nan tsaye ta fito da katuwar gyalenta lullu'be a kanta da jakanta da kuma wayanta a hannu, kallon yadda kwana biyun nan ta kara kyau da kyalli se shining fatan jikinta ke yi kawai yake, fararen hakoranta gabad'aya ta bud'e mishi tana murmushi, yace "je ki side-bed akwai phones d'ina da car key ki d'aukomin" d'akinshi tayi bayan tayi nodding, da sauri ta d'auko suka fito ba tare da ta kallesu ba tace "mun fita" .

A mota yake tambayarta waye Muhammad, dukda de taji maganar bazata amma haka ta danne ta bashi labarin muhammad kaman yadda shi ya fad'a mata da dalilin da ya sa ya rabu da ita, Shiru yayi bayan gama ji yana tunani kenan In zarah ta aureshi zata iya fuskantan tsanar uwar miji kaman yadda ita Iman ke fuskanta, Allah ze iya nunawa ummu iyakarta akan erta da sauri yayi auziyya ya kau da zancen daga zuciyarshi, a wani babban store yayi parking ya fice mintuna kusan ashirin ya dawo ya bud'e boot aka zuba mishi wasu manyan ledoji, shiga again yayi yaja bata lura da inda suke zuwa ba seda yayi parking d'ago kan da zatayi ta ganta kofar gidansu dukda ta san ba wani tarba zata samu ba amma farin ciki sossai ya nuna akan fuskanta, se kallonta yake cikin tausayawa cikin rawar murya tace "na gode Hamma kaman ka san nayi missing su ikhram sossai" yace "zan wuce zuwa azahar zan turo driver ya d'aukeki se ya kaiki gidan ummu se bayan isha zan taho In d'aukeki" Tace "to ba matsala na gode kwarai" hararanta yayi tayi murmushi yace "keep smiling don't cry ohk?" Kai ta gyad'a ta bud'e ta fice tana cewa "Allah ya kiyaye ya tsare" da Amin ya amsa bayan shiganta gidan ya kira yara ya basu ledojin da kud'i suka shigar mata.  "Adda oyoyo Adda oyoyo" da gudu suka zo suka rungumeta itama cikin murnan ganinsu ta rungumesu a jikinta.

Hafsy ce ta fito daga d'akin umma itama da gudu tazo ta rungumeta se ta fashe da kuka tayi kewar yayartata mijinta ya saka numbern iman d'in black list kuma ya rantse muddin taje gidan Iman a bakin aurenta ta san da ya san zata zo yau da be barta zuwan ba, baba ne ya fito daga d'akinshi yana cewa "menene haka hafsat? Se kace wasu yara?" Saketa Iman tayi ta tsuguna "baba Ina kwana?" Yace "Lafiya kalau mamana ya kika baro gida?" Tace "Alhamdulillah baba" yace  "masha Allah tashi a kasan nan ga key d'in d'akin mamanku ku bud'e ku shiga" kar'ba tayi tana murmushi yaran da suka shigo da ledojin ta kalla tana murmushi gaskiya mijinta ya cika jarumi kuma wacce ko wacce mace ke burin samu ji seda ya had'ota da sha tara na arziki da ita ko tunanin hakan ma be fad'o mata ba d'akin Mama ta bud'e suka ajiye kayan tsakiyar d'akin.

Suka fice bayan sun nuna mata sabbin Hamsin hamsin d'in da ya ba kowannensu ta tabbatar yanzu zasu kaiwa iyayensu labari su kuma su shigo ganin gulma girgiza kai tayi, da sallama ta d'aga labulen umma zaune take kan kujera hannunta rike da chasbi tana ja hijab sanye jikinta da alamu walaha ta idar kasa Iman ta zauna tace "sannu umma mun sameku lafiya?" Sau d'aya ta kalleta ta kau da kai cikin kasan makoshi tace "lafiya" hawaye ne ya cikawa Iman idanu ta mike ta fito da kallo umman ta bi bayanta hawayenta na zuba akan kuncinta da sauri ta goge tana me ci gaba da tasbahanta.

Damuwanta ta kawar ganin yadda en uwanta ke murnan ganinta baba da kanshi ya fita ya sayo mata drinks masu sanyi da ruwa, ita da hafsy suka sharewa Mama d'akinta da yayi kura suka goge suna hiransu, bayan sun gama suka baje ledojin kayan kwalama ne a ciki jibgi se frozen chickens guda biyar da wasu turaruka masu kamshi da manyan  turamen atampha super wax guda hud'u.

Da yadin maza gezner wadda se jikin shi Malabon kawai take gani kala uku ta tabbatar na su baba ne hakan ya sa ta ba Hafsat yaduddukan da turare guda biyu ta kai mai godiya ya hau yi da zuba mata adu'o'i, har d'akin maman ya zo ya sanya mata albarka seda tayi hawaye, turamen zannuwan duk uku da turare d'aya ta ba hafsy ta kaiwa umma, ko kallon kayan batayi ba hafsy de ta ajiye mata ta juya.

Ita hafsyn ta ba d'ayan da turaren da ta ware guda d'aya, ta cewa su ikhram zata d'inko musu nasu tsalle suka dingayi chocolates da sweets din ta hau rabiya duk makwabtansu da ta san suna da yara seda ta d'ibar musu ko Ina aka kai musu su ikhram ke kaiwa bayan sun gama ta had'asu da nasu se ga mata sun fara shigowa wai sun zo godiya alhali gulma ce ta kawosu, aiko nan suka hau kus kus idan ta wuce kusa dasu sassanyar kamshinta ya bule su har lumshe ido suke suna jinjina kai tsabar gulma.

Azahar na yi tayi sallah bata jira abincin umma ba ta shirya, d'akin baba ta koma suka fara hiran jikin mama da yadda tafiyarsun ze kasance, har kasan ranta girma da darajar mijinta suka ninku mata, suna hiransu me daad'i da babanta suka jiyo sallama akan drivern da ze d'auketa ne.

Sallama tayi musu ba yadda baba be yi da ita ta jira taci abinci kan ta tafi ba tace ita kam a koshe take har mota su ikhram suka rakata kaman zasuyi kuka, haka suka rabu. Har cikin gidan Abba ya ajiyeta tayi godiya ta fito, direct parlorn gidan ta nufa gabanta na fad'uwa.

Da sallama ta shiga har ummu ta fara amsawa amma ganin wacece yasa ta karasa amsawar ciki ciki a kasa ta zauna ta gaida ta ko kallonta batayi ba, zahra dake zaune kan kujera ta mike zaune tana kallonta itama ita take kallo se sukaji duk hawaye ya zo musu ga su ga junansu amma ba halin magana gashi seda suka ga juna tukun kewar da suke binnewa na kwanaki ya bayyana.

Ganin zata iya fashewa da kuka yasa ta tashi ta haura sama, nan Iman ta ci gaba da zama tana tsoron tambayar Ina Abba ummu ta masife ta, gajiya tayi da zaman ta dinga muskutawa, tsaki ummu tayi ta mike ta hau sama anan ta ci gaba da zama har la'asar ga yunwa da ya fara nukurkusanta a zuciyarta da na sanin kin tayin baba na kamata sede hausawa sunce da na sani keyace.

Jin har an idar da sallah ya sa ta mike ta nufi waje daga gefe ta d'an bayan ginin gidan taga pampo da dashi ake bawa flowers ruwa, da tayi niyyar tafiya se kuma ta fasa anan tayi alwala ta matsa chan gefe inda interlocks ne shimfid'e a wurin daga inda take tana hangar boys quarters da kuma gidan babban injinsu.

'Dan kwalinta ta zame ta shimfid'a ta gyara gyalenta ta tada sallah, bayan ta idar tayi zamanta nan, ta danna waya ta gaji tayi game ta gaji ga yunwa da ta fara tunanin ze mata illa don ulcer d'inta taji ya fara nukurkusanta a kirji. Baiwar Allah har magrib tana zaune a wurin anan tayi magrib se ta zame ta kwanta idanunta na fidda hawaye, me ta tarewa ummu ne bata sani ba tana matukar son ganin ummu ta d'auketa 'ya kaman yadda Abba ya d'auketa tana burin ganin ranar da zata zo ummu na nan nan da ita cike da so da kulawa amma batayi tunanin mafarkinta ze iya zama gaskiya ba tunda har yau ummanta ma bata chanza ba.

Zarah dake tsaye tun d'azu a sama tana kallonta tana hawaye ne ta fito ta gangara zuwa kitchen kallon me aikinsu tayi tace "akwai bakuwa a backyard ki kai mata abinci" da "to" ta amsa kan ta had'a abincin ta fito ummu da ta kasa ta tsare ne tace "ke laure Ina zaki da abincin nan?" Laure tace "hajiya zarah ce tace akwai bakuwa a waje In kai mata" wata uwar harara ummu ta sakar mata daga ita har zarah dake zaune saman one seater hannu a kan kumatu tace "wuce ki mayar min da abinci kan In sa'bamiki daga ke har wacce ta aike kin" tana kallon zarah tace "wawiya kawai marar zuciya ki ci gaba da shiga harkar wanchan karuwar watarana se na sa'bamiki" mikewa zarah tayi ta haura tana kuka wayanta ta d'auka ta kira Abdul yana d'auka tace cikin kuka "hamma pls ka zo ka d'auki Iman hakanan" a rud'e yace "me ya faru? Me ya sameta?" Tace "Kai de dan Allah kayi sauri" kashe wayan yayi ya mike daga zaunen da yake a company ya fito da sauri ya d'auki mota ya fito.

Gudu ya dingayi yana tunane tunane me ummu zata iya yi wa Iman, kaman an wulloshi haka ya shigo gidan hasken motarshi da kuma hasken lantarkin da ya haske gidan suka had'u suka haske mishi figure d'inta wani irin bugawa zuciyarshi yayi.

Da sauri ya fita ko kashe motan be yi ba yayi kanta d'agota yayi a hankali ta bud'e idanunta kanshi ta kakalo murmushi fuskanta yake shafawa yana duba inda take kwance a cikin gidan ubanshi amma wai matarshi ke kwance kasa kaman wata almajira rawa bakinshi ya dingayi yana ta son yin magana ya kasa se shafa fuskanta yake yana duba jikinta, jikinshi ta shiga cikin rawan murya tace "I'm fine" d'aukarta yayi chak zuwa mota ba tare da ya kara kallon ko cikin gidan ba ya ja a d'ari suka fice tuki yake zuciyarshi na mishi tukuki da turirin zafi wani irin wulakanci ne wannan, wani restaurant ya tsaya ya yi mata takeaway seda hawaye ya cika idanunshi ganin yadda take ci da sauri sauri alamun taji yunwa watakila tun breakfast da sukayi shima ya lura ba wani cin kirki tayi ba.

Jiki a sanyaye ya ci gaba da jan motan zuwa gidansu be iya ce mata kanzil ba ya sauka itama ta fito suka haura sama kowa ya shige d'akinshi wanka tayi kan ta fito tayi isha anan ta kwanta bacci ya kwasheta, ya jira shigowarta ganin har dare yayi sossai bata shigo ba yasashi shiga d'akin nata hangota yayi kwance kan sallaya ta dukunkune tana bacci d'aukanta yayi bayan ya zare mata hijab ya haura da ita kan gadon ya sanyata jikinshi tare da lumshe ido wani irin haushin duk mutanen da suke cikin gidansu na ratsashi har zarah me yasa bata kirashi tun farko ba? Kai har shi karan kanshi haushin kanshi yake ji da ya sa aka kaita bayan ya san halin ummu, Allah Allah gobe yayi yake ya kaita wurin baba fufore ta samu warakan matsalanta In ya sa kafa suka bar kasar ze ga me binta ya mata wulaknci chan, da haka bacci ya d'auke shi.

Washegari kaman yadda jiya ya kasance musu haka yau ma dayake ya fad'amata jirgin 11 zasu bi a tsanake ta shirya musu kayayyakinsu kan tayi wanka bayan gaisuwa ba wadda ya iya yiwa wani magana a cikinsu kuma sun jima tare tana gyara d'akin yayi wanka ya fito yana shiryawa tana shirya mishi akwatinshi bayan sun gama suka je suka ci abinci karfe 10:30 nayi suka fito driver ya d'aukesu se airport anan suka ga ummu ita bata ma gansu ba kau da kai yayi tace "ga fa ummu chan" yace "na ganta" Tace "baza mu je mu gaisheta ba? Gashi har Hamma Hafeez da ya kawota ya tafi" Shiru ya mata tace "kaji" tsawa ya daka mata "wai ke kam baki da zuciya ne? Bazaki nuna fushinki a fili ba?" Baya ta matsa Allah ya sa ba mutane ta inda suke hawaye ta taro a cikin idanunta tana kallonshi kanshi ya dafe duk haushin jiyan nan ne de be bar ranshi ba, hannunshi ta kama cikin sanyin murya Tace "kar de kacemin kana fushi da ummu Hamma? An ta'ba fushi da iyaye? Kana so Allah ya hukuntamu? Kayi hakuri dan Allah ni ne tayiwa Abu kuma wallahi na yafe duniya da lahira ban riketa ba sbd uwa take a gareni mu ci gaba da adu'a in Shaa Allahu zata chanza ko ba haka kake cewa ba?" Shiru yayi haka ta dinga lalla'bashi da kyar ya sauko seda suka hau jirgin yaje ya gaisheta ta amsa tana mishi kallo mamaki ganin Iman ya sa bata d'aura da abinda take son fad'a ba Haka kuma bata amsa gaisuwanta ba hannun ta ya kama suka koma seat d'insu da kanshi ya sanya mata belt ya kuma rike hannunta ita kuwa ta kwantar da kanta kafad'anshi tare da lumshe ido har jirgin ya daidaita a sama.




                    🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*044*

Mintuna Arba'in ya kaisu yola daga kano ba wani delay dogarawa da securities da kuyangi suka zo taransu da motoci na alfarma, ba tare da ya jira wani bushe bushen algaitarsu ba ya kar'bi key a hannun sarkin dogaran ignoring looks da ummu ke jefa mishi ya bud'e mata front sit ta shiga ya zagaya ya shiga seda ya jira aka sanya musu kayansu boot kan ya ja motar da wata matsiyaciyar gudu ya fice daga airport d'in, Haka kawai yake jin wani irin zafi da kunci a ranshi da ya rasa dalili, yana d'aukan kwaltar da ze d'auke shi har cikin yola ranshi na kara turara da zafi wata irin wawan birki ya taka a tsakiyar hanya da ya sa duk ababen hawan kan hanyar police barrack suka tsaya da tafiya kan kace me wuri ya kacame da masifa sbd ya tsayarda kowa dake 'barin da suke.

Da mamaki take kallonshi yayinda shima ita yake kallo wasu irin bad thoughts ne kawai ke yawo a ranshi da ya rasa menene musabbabinshi da kyar ya iya fighting mood d'in ya juya ga titi ya ja motar bata ce mishi komai ba shima be ce mata ba ya ci gaba da tafiya abin mamaki shi fa yana ganin gudu yakeyi amma sam kaman a hankali yake tafiya inda ya kamata ace sun wuce tuni se kuma ya gansu wurin.

Seda suka kusa hour daga jimeta kan suka fara shiga cikin yola abin tafiyan mintuna goma zuwa sha biyar, kallonta yayi ta kwantar da kanta ta lumshe ido, tsayar da motan yayi gefen titi ya lumshe idanunshi tabbas akwai abinda ke faruwa sede shi karan kanshi ya rasa menene, wannan kam kan su isa fuforen se yaushe kenan shi abinda ya isheshi gashi fa yana gani gudu yake cikin speed amma kuma...... dafe kai yayi yana ambatar 'Innalillahi' hannunshi ya sa ya kunna qira'a cikin muryan sheikh Abdulrahman sudais yayi bismillah ya kuma tada motar amma still same thing ke faruwa.

Da kyar ya samu suka iso ABC se kuma motar ta mutu gangarawa yayi gefen titi ya tsaya tare da bud'ewa ya fito bayan ya bud'e gaban motan, duddubawa yayi komai lafiya ba abinda beda lafiya gaban motan dawowa yayi ya tayar mota tace tasheni muga, hannunta ya kama se yaji hannun sanyi kaman an sa cikin kankara sunanta ya kira "Saudah! Saudah!! Saudah!!!" Amma shiru ko motsi batayi ba, jijjigata yayi nan ma fa Shiru kake ji.

Tsorata yayi da hanzari ya sa hannunshi kasan hancinta da kan kirjinta na hagu komai normal to me ya faru wani irin bacci ne wannan in ma baccin take? Sunanta yaci gaba da kira yana girgizata ko alamun taji babu, sarkin dogarai ya kira yana d'agawa yace "A kawo mini mota Ina wuraren ABC" ya kashe wayan se ya hau neman layin baba fufore da kyar ya samu layin ya shiga "Assalamu Alaikum" baba ya amsa da "wa'alaikassalam warahmatullah Abdulraheem" yace "na'am baba barka da rana" baba fufore yace "yauwa ya hanya kun samu baro fadar?" Abdul yace "a'a baba wani abin al'ajabine yake faruwa shiyasa nake so inji daga gareka, mun baro Airport tun awa d'aya da ya wuce amma ka ganmu har yanzu a yola, wani irin 'bacin rai nakeji da dana sanin tun farko meyasa na fara aurenta, baba In Ina kallonta wani tsanarta ke ruruwa a raina.. kaga tayi bacci ne ko menene amma nayi ta kiran sunanta taki tashi... meke faruwa baba?".

Wasu adu'o'i baba yayi ya kai aya tare da salati yace "Abdulraheem ka zama kanka ka maida hankalinka akan kanka karka yarda wani abu ya shiga tunaninka kana ji na? Sannan ka dinga maimaita A'uzubikalimatillahi tammati min sharri ma khalaka da la'ilahaillah anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen ka rufe da ayatulkurseeyu zaku iso lafiya in shaa Allah".

Gyad'a kai Abdul ya dingayi, yana kashe wayan ana Parker wata motar bayanshi fita kawai yayi ya zagaya ya d'auketa a hannunshi bakinshi na fara adu'o'in da baba ya fad'a mishi da sauri dogarin da ya janyo motan ya bud'e mishi motan ya sanyata baya ya kwantar da ita keyn kawai ya kar'ba ya zagaya ya shiga driver sit be iya yiwa wanchan dogarin magana ba ya ja yana kuma kunna qira'a a motar bakinshi na maimaita adu'o'in da aka sanyashi.

Tunda ya bar ABC ya fara d'aukan hanyar fufore yake ganin abubuwa kala kala amma be tsaya ba kuma be dena adu'a ba,

33 / 44