Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
wani cika ni da surutu" dariya tayi tace "Toh Ina ji ummanah me ya faru?" Umma tace "ni kam ko kun ta'ba waya da babanku tunda suka tafi? In na kira layinshi baya shiga" da mamaki tace "Ina suka tafi?" Umma tace "ee bakuyi maganan da maigidanki bane? Na zata ya fad'amiki yasa bamuyi maganan ba ai tun randa akayi rasuwan nan suka wuce da safe zuwa ganin likita da mamanku".
Shiru tayi tana mamaki a hankali tace "bamuyi maganan ba, In ya dawo In Shaa Allahu zan mishi magana watakila suna waya" Umma tace "Toh shikenan, maman Abulkhairi sun tafi kauyen su mijinta daga baucin ya d'an kwana biyu sbd rashin lafiyar surukarta, su ikhram suna gaida ke" Tace "Ina amsawa ummahna itakuma surukarta Allah ya bata lafiya, se da safe ummah" sukayi sallama ta kashe wayan.
Ta jima zaune tana tunani Allah sarki duk wani ups tackles na rayuwanshi baya mantawa da ita da family d'inta wani irin sonshi take ji wadda ya wuce misali se yanzu take gane ashe tun kallon farko da ta mishi ne sonshi ya mata mummunan kamu, wani irin bukatan mijinta take abinda yayi mugun bata mamaki, a haka ta lalla'ba tayi isha kan ta kwanta nan kan sallayan ta takure, ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba gashi ta kashe wuta, ta jima sossai kwance d'akin har bata san iya adadin lokutan da ta d'auka ba se jin motsin kofa tayi alamun za'a shigo bata damu ba sanin ba me shigowa se shi tana nan kwance bata motsa ba har aka shigo cikin d'akin tana de kallon inuwan mutum tsaye yana dube dube, murmushi tayi taki magana kaman kuwa ya san itace nan yayi wurin sallayan sede tun daga tafiyan ta fara kokonton anya wannan shine? Don tafiyanshi ba haka yake ba, bata gama tunani ba taji ana shafata kamshin ba namijinta bane da hanzari ta mike tana buge hannun tace "wayene?" Muryanta na rawa.
Danneta yayi niyyan yi se tayi saurin mikewa tsaye tana lalu'ban inda hasken d'akin yake amma kan taji har ta kunna ya kama hannayenta ya matse ihu ta kwala cikin neman agaji tayi karfin halin saka duk karfinta ta bangaje shi tayi kofa da gudu kan ta isa ya sa mata kafa cikin mugunta se gata a kasa tayi mummunan buguwa ihu tayi tana ambaton sunan Allah cikin rauni Don ta bugu da tiles d'in sossai.
Danneta yazo yayi a wurin yana shirin shiga gonan da ba nashi ba, da karfi tayi ihu tana kwala kiran sunanshi "Abdulraheeeeem" kaman kuwa walkiya bulb d'in d'akin ya kunnu haske ya gauraye d'akin da hanzari ta d'ago Ai kuwa ta Ganshi tsaye ya kura musu ido yana kallo idanunshi sun wani rine sunyi ja jijiyoyin jikinshi babu wadda be tashi ba.
Wani irin karfi ne yazo mata lokaci d'aya ta bangajeshi ta mike da gudu tayi wurin mijinta hijab d'in jikinta da ya rabe biyu ya fad'i kasa daga ita se bakar doguwar riganta me dogon hannu, hannunshi ya bud'e mata ta fad'a tare da kankameshi kaman irin jariri ya firgita sossai da sosssi d'innan ta fashe da wani irin kuka a razane.
Lumshe idanunshi yayi yana jin tafasar zuciyarshi na karuwa sbd sautin kukanta, jajayen idanunshi ya bud'e akan wadda ya shigo mishi kan mata yayi, gayen na duke a kasa yana aikin zazzare ido yana neman ta inda ze gudu sede babu tunda tsakiyar kofan Abdulraheem ke tsaye kallon da yake aika mishi ma kad'ai ya isa ya kasheshi, da gangan ya matsa gefe Don yaga irin livern da yaron ke dashi aiko ya taso da gudu ze fice, wani muguwar tad'iya da Abdulraheem yayi mishi seda yayi tumble sau biyu kan ya fad'a da kai kan tile se ga jini, sakinta yayi yayi kan yaron ya hau duka kaman an aikoshi seda Iman taga ze yi kisa kan ta dafa kafad'anshi cikin kuka tace "hamma please ya isa haka" lumshe idanunshi yayi kan yace cikin wani irin murya "sanya hijab kizo" da sauri ta d'auko wani khimar d'in ta sanya ta biyoshi wani irin rikon mugunta yayiwa hannun yaron kan ya fara janshi duk jikinsu jini yaron ya jikkata ainun.
Tana biye dasu a baya suka d'inga ratsa mutane da bayi da dogarai har cikin parlorn mai martaba yana janye dashi, wani irin wurgi da yayi dashi zuwa jikin gini seda manyan wurin suka mike banda me martaba, modibbo ne ya fara cewa "Lafiya Abdulraheem me ke faruwa?" Se wani irin huci yake yana jin ko kwatan 'bacin ranshi be sauka ba sbd d'an wannan dukan, baba yarima ne ya kuma cewa "Abdulraheem lafiya me ya maka haka?" Nan ma Shiru yayi se huci kaman wani kumurcin maciji ran maza ya 'baci.
Abbanshi ne yace "wai ba magana ake maka ba?" Yana kallon me martaba yace "shigarwa matata yayi a cikin masarautar nan ba waje ba" salati duk en wurin suka d'auka harda me martaba a cikin gidanshi? Matar jikanshi? Tabb Lallai wadda ya aikoshi dashi kanshi basu nemi zaman lafiya ba, kallon yaron yayi kan ya kalli sarkin dogarai da mutanenshi dake tsaye, sun san abinda yake nufi dukda be yi magana ba, bulala suka fara zafga mishi suna tambayar "wa ya aiko ka??" Basa jira yayi ko kyakyawan numfashi zasu kara lafta mishi seda ya kuma yin tilis kan ya bud'i baki da kyar yace "sarauniya Mama" Shiru parlorn yayi ran Abdulraheem na kara 'baci ji yake kaman yayi tsuntsu ya ganshi gaban mama yaji dalilin da yasa ta nemi tozarta mishi iyali.
Bada umarni me martaba yayi kan a kira meeting d'in gaggawa duk wani jininsu dake cikin fadan su hallaro, nan take aka fara shela da buga kararrawa cikin mintuna kad'an aka fara shigowa a tsaye yake duk wadda ya shigo sede ya zagayeshi ya wuce yayinda ita kuma iman ta tsuguna gaba kad'an dashi kanta kasa seda parlorn ya cika makil har umma kan me martaba yayi gyaran murya yace "Hauwa kin gane wanchan? Kin san bana son karya da me yinta" kallon saurayin tayi tana zaro ido tace "a'ah ranka shi dade, shi yace ya sanni ne?" 'Diyarta karama fatima wacce batayi aure ba har yanzu amma zata girmi Iman tayi saurin cewa "Abba na sanshi kuma na san itama ta sanshi Abba sunanshi Ishaq hayanshi tayi yayi blackmailing Matar Abdulraheem samun ya saketa kaman yadda ya saki hamna se ta chusa mishi Aina'un Anty zulfa'u" kallon mahaifiyarta tayi tace "dama na gayamiki bazan rufa miki asiri ba muddin akan cutar da wani d'an uwana ne" zuru zuru tayi ta rasa abin fad'a abin ya zo mata bazata bata ta'ba tunanin fatima zata tona mata asiri ba, dukda tsanan bakin halinta da tayi.
Shiru parlorn yayi modibbo ne ya katse shirun da cewa "yanzu fisabilillahi abinda ya faru da hajja umma be isheki ishara ba? Abinda ya faru be sa kin tuba kin zubar da makaman yakinki kan ahalin nenne ba?" Wato nenne manga, mai martaba yace "kyaleta modibbo tunda bazata shiryu Don Allah ba zata shiryu Don wuya, sarkin dogarai na bada umarnin d'aure yaron nan da giyar kud'i kad'an ya d'ibeshi har yayi gigin aikata 'barna d'aurin rai da rai da azaba me tsanani, Sannan na yankewa duk wani jinin Hauwa'u gadon wannan kujeran mulkin nawa ko da ita da 'ya'yanta ne suka saura daga jinina, hakanan na cireta daga cikin jerin sarauniya na wannan karnin ta koma kaman kowa a fadan nan, zata koma karshen ginin masarauta da tafi tsana akan komai a cikin gidan nan da rayuwa ita kad'ai ba baiwa bare kuyanga hakanan fatima zata koma zama da d'aya mahaifiyarta"
Kau da kai yayi daga kallon da nenne ke mishi na neman afuwa ta kallo kawai ya gane ya kau da kai ne sbd ya san bazata iya magana nan ba sbd sanin girman sarauta da izzar basarake da kuma jinin su dake yawo jikinta, nan take aka aiwatar da abinda yace Mama na kuka na komai aka tusa ta gaba, yace "nayi hakan ne don ya zama ishara akan duk me shirin cutar da d'an uwanshi yanzu da shi Abdulraheem be gane ba ze iya sawwakewa matarshi cikin fushi Daga nan duk wani matsala zata iya faruwa, Sannan nayi hakan sbd na gaji da halin da hauwa ke nunawa sauran 'ya'yan wannan masarauta tun kan su mallaki hankalin kansu kawo yanzu, kowa ze iya tafiya" mikewa ummu tayi ta kama hannun iman suka fice bata kai ga kaiwa kofa ba malabo ya rike hannunta yace.
"Ummu kiyimin aikin gafara bazan iya kara kwana cikin masarautan nan ba kiyi mini izinin tafiya don Allah" kallonshi tayi zatayi magana suka had'a idanu da Abba ya girgiza mata kai se ta sake mishi hannun mata tace "shikenan Allah ya kareku a duk inda zakuje se munyi magana" mai martaba yace "ba de zuciya akayi da masarautarmu ba ko?" Modibbo yace "aiko dae kar ace baza'a kara shigowa ba don naga alamun hakan wannan da kishi kaman mazan larabawa" dariya akayi da kyar ya iya yin murmushi yace "haba na isa?? Ban isa ba ai mai martaba In Shaa Allahu muna dirowa Nigeria nan zamu fara sauka" ya kalli modibbo yace "malam ai a wurinka muka gado cikin wannan tauhidin da ka saba koya mana dolen dole" dariya duk akayi ya juya ya fice.
Part d'insu suka fara yi wannan akwatin da ya saya musu a lagos wadda ko bud'ewa basu kara yi ba tun barowansu ya d'auka da wasu important abubuwanshi ya d'auka mata wayanta suka fito driver ya d'auka aka kaisu Greenland hotel suka kama room suka shiga ya rungumeta ya sauke ajiyar zuciya itama rungumeshi tayi cikin sanyin murya tace "thank you" yace "for??" Tace "na zuwa kan lokaci a sadda na bukace ka" kuma rumgumeta yayi yace "I'm sorry" Tace "for?" Yace "for leaving you all alone bayan na san kema kina bukatata" Tace "I love you zaujii, I truly do, I was really afraid that shikenan rabuwanmu tazo da Allah ya bashi sa'ar shiga gonanka" yace "I love you too hayatii, god forbid da ko mazan duniya ne suka shiga gonata matukar bada son ranki bane babu abinda ze sa In rabu dake" had'e bakinsu tayi yayin da ya d'agata chak zuwa kan gado ya mata runfa da faffad'ar kirjinshi.
A daren ya musu booking flight washegari da safe bayan sun karya sunyi wanka ta saka waenchan kayan da ya saya mata tayi matukar kyau da shigan shima se yabawa yake ta lura yana matukar son d'abi'ar turawa inba haka ba Ina ita Ina saka wani coat da jean se d'an scarf da gashin kanta kawai ya rufe, drivern masarauta ya kira aka kaisu Airport ba 'bata lokaci jirginsu ya d'aga se Miami.
Suna sauka wannan yaron nashi da ya turo Patrick ya zo ya d'aukesu zuwa suit da ya kama musu inda suke sama da Baba seda suka kuma hutawa kan suka fito zuwa asibitin nan suka samu Baba sossai Iman tayi murnan ganinshi haka shima ya kuma yi mishi gaisuwa Don suna waya kullum da wayan Patrick ya san da rasuwan, shiga wurin doctor dake in-charge yayi Don jin me suka binciko kan Mama, kai tsaye ya fad'a mishi abinda ke damunta wato.............
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*
*`Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*055*
“Tumors as you can see here” ya mika mishi wani X-ray “tumors are masses of abnormal cells in the brain it can be on spinal cord, that have grown out of control, it can be between benign (non-cancerous) or maligent tumors (cancer) the main concern about it is:- 1- how fast they grow
2- how readily they spread through the rest of the brain
3- where they are located
4- if they can be removed or destroy and not come back”
Katseshi Iman tayi da cewa “hope hers is non-cancerous” a rud’e cikin taradaddin amsan da baturen likitan ze bata, murmushi ya mata kan yace “yes hers can be easily destroy, ur mom will gonna be fine soon don’t worry” kallon Abdul yayi kan yace “she has small amount of diabetics that’s hyperglycemia, the diabetics met with the tumors and all are dangerous diseases that lead to coma that’s why it would be difficult to many doctors to figure out the exact problem” ajiyar zuciya ya sauke yana kallon iman da ta dafe kanta kallon doctorn ya kuma yi yace “please do anything that can make her better from those diseases especially the brain tumor” Kai doctorn ya gyad’a cike da gamsuwa yayi en rubuce rubucenshi ya mika musu wasu papers ganin akwai sa hannu ya mikawa baba da yaji dukkan bayanan da akayi hannu ya saka aka ba doctorn ya kuma basu wani abubuwan da zasu bukata daga pharmacy bills d’in na kasa, ba tare da Malabo ya yarda bappa ya gani ba ya mike yana mikawa doctorn hannu suka fice.
Duk yadda baba ya so ya biya ko kad’an daga cikin abubuwan da yake kashewa ne malabo yaki, haka ya biya komai da komai ba ‘bata lokaci aka fara treating mama, satinsu biyu a miami seda ya tabbatar an gama komai saura jiran farkawan Mama tukun suka fara shirin wucewa, a sati biyun nan ba wurin shakatawan da basuje ba na cikin garin miami, Florida state of united state, daga kan Miami Beach, Art deco historic district, south beach, vizcaya museum and gardens, Everglades national park.
Yininsu chur a bayside market place in da ya kasance large outdoor style mall dake cikin ruwa with more than 150 shops and restaurants sunyi sayayya har na hauka duk wani shiga na turawa wadda baze bayyana jiki ba seda ya saya mata da mahaukatan nighties a sati biyun nan wani irin mahaukacin soyayya sukayi da ya zauna daram a cikin zukatansu so, shakuwa, kulawa, zallar ruwan kauna shi suka nunawa junansu.
Restaurant yafi kala goma suka je daban daban a areas daban daban wasu a cikin ruwa kai sune har night club a cikin boat sukayi tasha mamaki taga ikon Allah bata ta’ba zaton akwai irin wuraren nan a duniya ba, sune har bay-front park suka ga su light tower da dare, karshen inda suka je shine zoo Miami inda ya ke d’auke da over 3,000 wild animals itade ba dabban ubangiji da bata gani ba, har getto area d’insu da yake d’auke da wynwood walls street art suka zaga inda taga mutane masu ban mamaki mata da maza kowa da zane daga kai har kafa na tattoo.
Anan ta samo wani saffron grills inda suke Gasa duk wani abun ruwa wayyo Ai kullum se sunyi ordern wani abin na ruwa taci, dukda sauran abincinsu ma duk ba laifi taci a heshi and sushi Asian cuisine, santorini, havana vieja, numfashinta seda ya kusa d’aukewa ganinta a freedom tower gashi cikin dare wayyo bazata iya fasalta yadda wurin nan yake ba se wadda yaje, Tabbas ta yarda da inkiyoyin miami da ake ce mishi “magic city”, “gateway to the Americans”, and “capital of Latin American” Don har d’an yaren Latin d’in ta koya.
Ya jata har cikin university d’insu inda yayi visiting wani friend d’inshi, in takaice muku Noor Iman kam ta zama wata baturiya cikin sati biyun nan tayi fresh ta kara kyau da murjewa wasu wuraren suna d’an zuwa da baba kaman day trip key west with boat sunje dashi wasu wuraren kuwa kud’i kawai yake bayarwa d’an gidanshin nan su fice da baba yaje duk inda yake so.
Tun yanawa iman mitan dressing da ta koma yi dukda baya bayyana tsiraici har ya gaji ya lura yanzu duk abinda mijinta ke so shi takeyi se suyi kwana uku hud’u basu kwana hotel da suka kama ba sede suyi waya da baba, dasu ummu, da zahra kam kullum se sunyi waya har an saka ranar bukinta da Muhammad wadda basu da tabbacin zasu samu zuwa, randa suka cika sati biyu cib ya saya musu ticket to London da train dukda rabin tafiyar a jirgin ruwa ne rabi a train.
Cikin kewa sukayi sallama da baba inda suka bar mishi patrick da yanzu sun saba sossai da baban tun baya gane turancinshi har ya fara ganewa sossai, kusan trolley hud’u sukayi su biyu kuma manya ba kanana tsabar sayayyan da sukayi plus wadda suka zo dashi biyar, kwanansu biyu a hanya dukda kwata kwata 14 hours ne from miami city to London amma sun kwana a ruwa inda d’ayan kwanan sukayishi a wani neighborhood to London.
In ka gansu gwanin sha’awa yadda suke manne da juna suna shan love a inda ba sa idanawa, abinci ma rabon da d’aya a cikinsu ya ciyar da kanshi sun manta ciyar da juna sukeyi ko ma menene, da rana suka isa London inda aka zo da wasu zafafan motoci aka d’aukesu se madaidaicin kyakyawan gidanshi dake nan cikin heart of London kusa da company d’inshi, fasalta gidan ma aiki ne tsabar kyau da tsaruwarshi.
A d’aki guda suka sauke kayayyakinsu wadda shine ya nuna be son ra’ayin raba d’aki a tare sukayi wanka suka shirya cikin normal house wear na shan iska itakam ma riganta da kad’an ya wuce bombom d’inta gashi me hannun vest peach color, fitowa sukayi zuwa dining area inda aka jera musu dishes kusan kala shidda a kan kafanshi ta zauna yayi serving d’insu a plate guda yasa one spoon ta bashi ya bata In ta ‘bata mishi lips ta lashe da tongue d’inta.
Duk yadda zan fasalta muku irin soyayyar su baza ku fahimta ba ku kiyasta kawai a ranku, ranan yini sukayi bacci da hutawa, se washegari ya fita da ita suka fara zagaya London kuma bayan ya kaita taga company d’inshi nan ta sha ruwan mamaki ganin yadda ya san mutane dayawa a London duk wadda ya ganshi ze tsaya su gaisa yayi musu presenting matarshi, bata tsorata ba seda