Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
and heart attack, a fili ya ce "ya subhanallah" ya karasa da shafa kanshi yana lasan lips d'inshi da yaji sun bushe, baze iya kwatanta how broken she is in there ba, yana nan tsaye yana ta aikin kallon bayanta Pakistan ne a jikinta riga da wando pink se gyalenshi da ta d'aura akanta.
Kallon bayanta ya ci gaba da yi anan a tsaye kaman an dasa shi ya san for sure se tayi kukan wannan rabuwan, Allah sarki gashi she don't have any shoulder to cry on, Ai ko kaman yadda ya tsammata yana nan tsaye ta mike zaune a hankali ta sid'ad'a ta zura silifas d'inta ta nufi kofa.
Da sauri shima ya zagaya don kar ta 'bace mai se kuma suka kusa cin karo don itama bayan ta nufa bata kula bama shine ta wuce abinta a hankali zuwa wurin wani itace dake d'an chan gaba, wurin duhu ne zalla sbd ya d'an bar jikin amenity d'in.
Hannu tasa a bakinta kan ta zame a hankali ta zauna tare da fashewa da kukan dake cinta a rai, a bayanta ya tsaya yana kallonta with so much pity, wani abu yake ji da be san menene ba ke taso mishi daga kasan zuciyarshi zuwa kan harshenshi zafin kukanta yake ji kaman ana zuba mishi ruwan zafi a zuciya, ajiyar zuciya ya d'inga saukewa kaman shine ke aikin kukan, ta kai mintuna goma tana kukan bata ko hutu hannunta kuma still yana toshe da bakinta.
Ganin baze iya jurewa ba yasa ya karasa ya zauna kusa da ita wadda hakan ya sata saurin yin Shiru tana share Hawaye handkerchief ya mika mata fari sol kaman baza ta amsa ba se kuma ta kar'ba ta kai fuskanta, wani kamshine me daad'in ji ya bugi hancinta wadda bata ta'ba jin wani me irin turaren ba, "Karki manta Allah yana nan kuma ya na kallonki, gareshi kad'ai zaki kai kukanki hawaye da damuwa ba sune mafita ba, Allah ya yaye miki damuwanki" ya fad'a cikin husky masculine voice d'inshi, yana karasa fad'in haka ya mike ya fice ba tare da ya kar'bi hankyn ba, bayanshi tabi da kallo bata samu daman ganin fuskanshi ba sbd duhun da wurin yake dashi bayanshi kawai tabi da kallo.
Ta de san bakaken kananan kaya ne jikinshi a saman riganshi akwai jacket me hula shima baki kuma ya sanya hulan, hakan yasa tayi ta kallonshi har ya fice ta de san ingarman namiji ne don ko daga tafiyarshi za'a iya gane hakan, hankynshi dake hannunta ta maida ido kai, ta jima tana kallon hankyn yayinda hankalinta ke kan magananshi se kuma take ji kaman ta ta'ba jin muryan, mikewa tayi ta koma d'aki tare da fad'awa toilet tayi alwala tazo ta tada sallah.
A hankali take komai sbd jikinta da ba karfi ita karan kanta ta san karfin hali kawai takeyi amma iska me karfi ze iya kadata.
Be tafi ba seda yaga shiganta d'aki kan ya sauke ajiyar zuciya ya ja motanshi ya fice, be san me damuwa da shiga tunani ba se akan yarinyar nan Kwata kwata kwakwalwanshi yaki barinshi ya huta da tunaninta, ringing d'in wayanshi ne yasa shi maida hankali kan wayan "Hajiya umma" ya gani yana yawo ajiyar zuciya ya kuma saukewa shi ya manta ma da wata hamna Allah ya gani.
Rage speed yayi kan ya d'aga "Assalamu Alaikum umma mun yini lafiya?" Cikin fad'a tace "lafiya, ba wai na kiraka don mu gaisa bane na amsa gaisuwanka, na kiraka In fad'amaka halin da kanwarka take ciki tun jiya taki cin abinci taki ko da shan ruwa ne sbd kai ta kira layinka In be yi sau 100 ba ze yi hamsin amma ka ki d'agawa akan wani dalili?".
Ta'be baki yayi a kan lips d'inshi yace "oops ashe?" be san taji ba ashe kuwa taji se cewa tayi "Abdulraheem ni kake cewa oops ashe? Wato ga sa'an ka ko? Ina a matsayina na surkarka kuma kanwar mahaifiyarka ina fad'amaka matsalar da matarka take ciki sbd kai shine kake ce min Ashe? Yayi kyau" tana jira ya bata hakuri se cewa "whatsoever" kit ya kashe wayanshi.
*****
Waii ina wuta hajjiya umma ta saka malabo inda take shiga bata nan take fita ba, masifa take kaman ta ari baki, tanayi tana kallon hamna dake zaune bakin gado tana kuka, cikin kuka Tace "kayya de umma ki bar masifan nan ki zo ki nema min mafita, tun fah kan na auri Hamma Abdul kika ce In na aureshi se yadda nayi dashi ke fah kika ciremin son Hafeez kika sa na Abdul sbd Abdul yafi shi kud'i amma gashi kullum ni akan korafi da damuwan hali irin nashi ke baki d'auki wani mataki ba, har fah dukana fah yakeyi".
Waro ido uwar tayi tace "duka? Duka fah kikace auta shine baki ta'ba fad'amin ba? Lallai Adda Rasheeda d'anki ya ja muku gabad'aya matsala babba ba karama ba, gobe da asubar fari zamu tafi mambila chan taraba akwai wani kwararren boka da Hajja Zubai ta min magananshi aikinshi ci yake kaman yankan huka, bari kiga In kirata ma drivernta ne ze kaimu tunda shi ya san wurin" hamna tace "yauwa se a kara kama ummun nan ma naga kaman jikinta na yin sanyi idan waennan fakarun yarantan sun mata magana, a kara kama mana ita se yadda mukace kuma bazata ta'ba ganin laifinmu ba" hajjiya umma tace "haka za'ayi 'yata, watakila ma mu samu wannan ya kama mana shi banzan mijin naki da kyau tunda duk waenda muka kashe makudan kud'i muka mishi a banza yake tafiya" hamna tace "Ameen dae, yayi ta fushinshi yanzu lokacinshi ne bari ya dawo tafin nan" ta yi maganan tana nuna tsakiyar hannunta wani irin dariya uwar tayi tace "Ai har dukanki se kin rama" dariya suka sake tare da shewa suka tafa se kace wasu kawaye.
*****
"Aisha je ki ki kiramin yayanku babba" mom ta fad'a tana kallon autanta da yanzu take da aure da yaro kwaya d'aya, Aisha ta mike ta fice, Amina dake gefe tace "wai ni mom me yake damunshi ne haka tunda muka zo naga ko da su Arif be sake kaman yadda ya saba ba daga gaisuwa kawai ya shige yayi tafiyanshi" murmushin takaici mom tayi tace "sbd na hana shi soyayya da bazawara karuwa" Khalid da shine d'anta na uku yace "subhanallah mom ba fa a shedar karuwanci ba'a tabbatar ba plz ki tuba kar Allah yayi muku hisabi ranar gobe sbd furucinki".
Mom tace "kayya Khalid wani hisabi bayan kowa ya sheda aurenta fah hud'u duk ba wadda tayi mishi kwakwaran wata hud'u ta fito ta ci gaba da yawon bin mazanta yanzu ma haka wacce na sa ta min bincike akanta tace tana kwance a asibiti cikin shege ne da ita" Amina tace "a haka kuma yake sonta kuma yake son aurenta?" Mom tace "kwarai kuwa muhammad da be ta'ba min musu ba se gashi yana min sbd yarinyar nan nafi kyautata zaton asiri tayi mishi shegiya 'yar gidan mayu kawai".
Ahmad da shi ke bin Muhammad yace "plz mom ki dena, ko me tayi be kamata ki dinga zaginta haka ba ita chan ta sani tunda kin hana hammad d'in aurenta" Shiru mom tayi tana kwafa ita kad'ai daidai lokacin Aisha da hammad suka dawo a tare zama yayi akan kujera yana karewa kannenshi kallo ganin irin kallon da suke mishi ganin baza su dena ba yasa shi cewa "wai lafiya? Haaa'aa kun sa mutum a gaba kuna ta kallo kaman na ci muku bashi ban biya ba?" Da zafi zafi yayi maganan, Mom na kallon Ahmad tace "ba kun ga abinda nake fad'a ba?" Aisha tace "this is unlike yhu ya hammad, baka da fad'a yaushe ka fa..." cikin harzuka yace "just shut up!!" Duk Shiru sukayi.
Khalid kam tausayinshi yaji don ya san wannan yarinyar itace wacce ya fara mata son so a duniya bayan mahaifiyarsu tunda har ya zama haka don an raba su, ganin irin hararan da yake watsawa Aisha da Amina ne yasa mom Tace "tashi ka fice ka bani wuri kar ka kora min yara daga zuwa ganin uwarsu" dariya duk sukayi da a da ne shima dariya ze yi ya fara mayar da zolaya amma se ya harzuka ya fice fuuu kaman kwa'babben fulawa da aka saka mishi yist😅
Mikewa Khalid yayi yabi bayanshi, kan gadonshi ya sameshi rub da ciki zama yayi gefen gadon yace "I'm so sorry bro, karka manta da Allah ya ce karka sawa ranka abinda kake so dole se ka samu sbd ze iya zama ba alkhairi bane a wurinka, ka fawallawa Allah ze kawo maka wacce tafita" Hammad yace "baza ka gane bane Khalid, yarinyar chan is innocent, she really is, Khalid am a jerk da na iya furta mata kalmar rabuwa tana gadon asibiti tana fama da hawan jini da heart attack, kha..." rawa da muryanshi ya fara ne yasashi yin Shiru, matsawa Khalid yayi tare da hugging d'inshi, a hankali hammad ya furta "I really love her" hawaye na gangaro mishi.
*Assalamu Alaikum jama'u ya kuke ya gd😊 hope duk kuna cikin koshin lafiya Allah ya sa haka ameen, kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu na d'anyi zazza'bi ne amma yanzu Alhamdulillah naji sauki, na gode fah da damuwa da kulawar da kuka nuna a kaina ko ince akan Noor iman....... Ahhhh am jealous 😡, shaa Noor Iman is saying hi from here🖐 thank yhu.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 On Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and Super writers)
*017*
Aiko kaman yadda suka tsara asubar fari suka tashi suka shirya suka fice tafiyar kusan 8 hours ya kaisu har mambila suka parker motar suka dinga hawa tsaunuka kaman yadda duk wadda ya san mambila ya san garin Allah yayisu da baiwar tsaunuka, sun wahala sossai kan suka karasa wani kungurmin dutse me duhun tsiya. Fili ne kawai babba daidai wani d'an rami suka ji an daka musu tsawa, "Kai ku dakata daga nan" tsayawa sukayi aka ce "barkanku da zuwa hanyar 'bata tabbas kun zama 'batattu 'yan uwan shaid'an daga kun taku kafafunki cikin nan kun zama 'yan wuta masu taya shaid'an hira a cikin jahannama, ku rufe idanunku".
Rufe ido sukayi mintuna biyu sukaji ance "ku bud'e" budewa sukayi se suka ga wani bukka gabansu, ku shigo sukaji an fad'a da karfi shiga sukayi wani warjejen mutum suka gani kato dashi mummuna (Astagfirullah) ko kyaun gani bashi dashi, bajewa sukayi a gabanshi suna mishi kirari, kan suyi magana ma ya fad'a musu abinda ya kawosu, da mamaki suke kallonshi yace "ku dena mamaki, Aljannu sun riga da sun fad'amin komai, saide ku sani Mijinki ze yi aure, ba da jimawa ba kuma baze ta'ba kamuwa ba sbd yana da wani baiwa daga Allahnshi".
Cikin tashin hakali hamna tace "boka ba yadda za'ayi ka hanashi? Ko ka kassara matar? Who dears to cross my way?" Wani irin dariya bokan yayi kan yace "ba ta yadda za'ayi a hana auren sede zamu bi ta 'bangaren mahaifiyarshi zamu sa mata tsanan yarinyar daga baya kuma In muka samu wani d'an 'buli daga yarinyar se mu yi aiki akanta, karku damu zaki mallake duk dukiyar Abdulraheem".
Hamna zatayi magana hajiya umma tace "Toh boka mun gode, mun gode ka taimakemu Ai da yanzu bamu ma san ze yi wani aure ba, munafukar uwarshi ma ta 'boye mana" dariya ya dinga 'ba'bakawa kan yace "maza ku sallami aljnnu ku 'bacemin da gani lokacinku ya kare" kud'i hajiya umma ta cire bandir na 1k biyu ta ajiye mishi, suka mike da baya baya suka fice.
Hamna de se kumbure kumbure take itafa bokan nan be mata ba tunda ya kasa hana Abdulraheem kara aure, seda ta kasa hakuri ta furtawa hajiya umma, hajiya umma tace "ke Ai ba da boka kad'ai zamu dogara ba, kinga yanzu In ya mana aiki akan Adda rasheeda, idan har shi Abdulraheem d'in ya bayyana auren nashi se ki d'aga hankali ki hanashi zaman lafiya, in hakan be sa ya daddara ba ana kai ita shegiyar Amaryan washegari zan bayyana kuma a gidanki zan sauka se mu san yadda zamuyi maganinta har ta gudu da kafanta, ko kuma In boka ya samu hanya akanta ya 'batar mana da ita a duniya".
Cikin Jin daad'i hamna tace "wow yhu the best mom, gaskiya shawarankin nan yayi, haka za'ayi duk wata 'yar iskar da zata shigo gidan Abdulraheem se ta d'and'ana kud'arta a wurina, shima na rasa me yasa ko wanni boka ke cewa baze iya mishi aiki ba sbd yana da wani baiwa daga Allah" kwafa kawai hajiya umma tayi itafa har ga Allah ta tsani Abdulraheem nan kawai ba yadda zatayi dashi ne, da wannan hiran suka karasa wurin mota a gajiye, ba 'bata lokaci suka kama hanya ba su suka shiga yola ba se after 10 seda driver ya ajiyesu Wuro hausa kan ya juya ya nufi gidan aikinshi bayan sun mishi alkhairi.
********
Jin kanta takeyi wani iri zuciyarta fayau ba tunanin komai, don da gaske tayi iya yadda zatayi daga jiya zuwa yau ta shafe maganan hammad a rayuwarta, ta ci gaba da adu'a Allah ya za'ba mata abinda yafi alkhairi In har tallarta ko tace sadakarta da mahaifinta ze yi da ita shine alkhairi Allah ya bashi dama, itama zuwa yanzu ta gaji da rayuwar gidansu ta gaji ba kad'an ba.
Wayanta da take sauraren qira'ar sheik Abdulrahman sudais ne ya d'auki kara, dubawa tayi se taga hafsy, d'agawa tayi suka gaisa cikin muryan tausayi hafsy tace "kiyi hakuri Adda iman baki ganni ba, wallahi umma ce ta cewa Usman kar ya kuskura ya barni na zo gaidaki, ban ji daad'i ba wallahi" d'an Shiru noor tayi kan tace "ba matsala hafsy karki damu na warke ma ai Ina kyautata zaton ko gobe da safe za'a sallameni, kiyi ma mijinki biyayya plz" cikin rashin jin daad'i hafsy tace "Toh Adda na gode, ki kuma kara hakuri da umma plz komai me wucewa ne" murmushi kawai iman tayi a zuciyarta tace tunda har na shekara 23 ban ta'ba tunanin ze wuce ba, sallama sukayi.
Qira'arta ta ci gaba da ji tana duba contacts d'inta bata bar wani kofa da damuwar abinda umma ta gayawa mijin Hafsy ze dameta ba, daidai kan numbern Nafeesah dake aure a bauchi ta tsaya kan tayi dialing ringing biyu ta d'aga "Assalamu alaikum Adda iman yau an tunda damu kenan?" Murmushi iman tayi kan tace "wa'alaikissalam warahmatullah, dama chan bamu manta da ku ba, ya Abulkhairi?" Tace "yana lafiya ina ummana da mama?" Tace "umma na gida mama kuma na asibiti tare da ni" Nafeesah tace "oh haka fah inna ta kirani take gayamin abinda ya faru, yanzu ya za'ayi da cikin? Kema Adda iman be kamata ki dinga abinda kikeyi ba kin san de haramcin zina, da irin azabobin da Allah ya tanadarwa masu yi, Adda why not wannan karon ki tuba ki samu miji na gari kiyi aure ki natsu a d'ak...."
"Dakata Nafeesah ba wa'azi na kira ki min ba, last time I check na rigaki sannin abubuwan da kike fad'an nan, na kiraki ne mu gaisa mu sada zumunci ki shafamin kan Abulkhairi, se anjima" bata jira cewar Nafeesah ba ta kashe wayanta, tana me runtse ido Allah ne kad'ai ya san yawan mutanen da inna ta fad'awa tana da ciki, ji take kaman ta tashi tayi ta tafiya kawai se inda Allah ya kaita, tayi nesa da family d'inta sossai yadda har abada baza su kara ganinta ba.
Bud'e kofan da akayi ne yasata maida hankali kai zarah ce ta shigo, murmushi suka sakarwa juna kan ta zauna bakin gadon tace "bestynah ya jiki?" Noor tace "jiki da sauki sossai besty, da kin daina d'awainiyar nan haka wadda kika yi ma mun gode" hararinta zarah tayi kan tace "rufemin baki, Ina mama" noor na murmushi tace "Mama na waje ta shimfid'a taburma tana shan iska inaga bata lura da wucewarki ba" zarah tace "Ai ko nima ban kula ba kin san ance hankali shine gani" noor iman tace "hakane, ya anyi lectures yau?".
Zarah tace "Eh amma na miki attendance Allah ya sa be kira suna ba" gyad'a kai noor tayi, zarah tace "yauwa Besty se inga kaman kina cikin damuwa ga waswasi da zuciyata takeyi plz ki bani labarinki waye asalin mamanki? Kinga ai yanzu mun zama d'aya ba abinda zamu 'boyewa juna" ajiyar zuciya Noor ta sauke tare da mikewa ta zauna da kyau tace "besty kina so ki sani kuka kenan, amma de bari na baki but plz don't judge me".
Natsuwa Zarah tayi nan fah noor iman ta fara bata labarin rayuwanta tun daga farko har karshe da kuka ta karasa yayinda zarah ta jima tanayi, bata ta'ba zaton nan duniya akwai wadda ze yi rayuwa kaman wadda Noor iman tayi ba, ashe ita har yanzu bata san me rayuwa ba tunda da gatanta da komai kowa na gidansu na sonta yana ji da ita.
Hugging noor tayi tana bubbuga mata bayanta yayin da itama hawayenta yaki tsayawa, abin ka da farar fata tuni fuskan zarah ya kumbura yayi jajir, seda suka tsagaita kukan tukun zarah tace "In nace zan yi magana akan rayuwanki ba abinda zan iya cewa besty sede ince kiyi hakuri wadda na san shi duk me tausayinki yake furtawa a gareki but trust me ze wuce ne, zaki ji daad'i soon in shaa Allah, sannan hammad be kyauta ba sam kuma wallahi se ya san yayi abinda yayi marar mutunci kawai, mu ci gaba da adu'a In na fita zan yi sadaka gobe Thursday in shaa Allahu zanyi azumi samun In miki adu'a da kyau tunda ke baza ki iya ba sbd medication da kike taking, Allah ze kawo mafita kan karshen wani satin".
Noor na girgiza kai tace "na san ba abinda yafi karfin Allah but Zarah am scared ban san wani irin miji Allah ze za'ba min ba, ban damu da talaka bane ko me kud'i, ban damu ko yana da wani nakasu ba babban damuwana zarah shine ze iya rikeni? Zarah naga wadda suka