Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
sunanta sau ukku a duk inda take zata haukace tabi duniya, Farin kuma ki sawa shi mijin naki a abinci ko abin sha an wuce wurin In dae har ya sha ko yaci komai kankartar abin".
Tace "Boka an gode" yace "ki godewa Aljannu" Ai ko ta gode musu ta hanyar cire makudan kud'i Don har d'akin Abdul ta shiga ta lalu'bo kud'ad'e dayake ta san ma'ajiyarshi ta zubewa wannan mushriki, kan umma ya koma ya fad'i wasu kalmomi se ga layu sun bayyana manya guda uku, yace "d'auka" ta d'auka ba ko tsoro yace "ki binne d'aya bayan d'akin ita 'yar uwartaki, d'aya bayan d'akin shi mijin nata d'ayan kuma shine ze kasance na yaran ki samu kan bola tsakiyar dare ki binne shikenan Aljannu zasu karasa aikin ki tabbatar ba wadda ya ganki in sun binnu kuma ki tabbatar ba wadda ze iya tonowa".
Jawahir ma ta nemi karin shiri akan alhazawanta suka sallameshi da makudan kud'i suka fito cikin jin daad'i gani suke kaman har sun aikata komai ya faru suna fantamawa cikin arziki, machine suka samu bayan sunyi tafiyan kafa sossai suka d'ane ya fito dasu suka hau motansu se Nigeria cikin zakuwa.
*******
"Wannan surutu ya isa hakannan ga abinci sauko kici kan wannan yaron ya dawo miki da magani kisha ki kwanta ki huta" tray d'in ta ajiye mata umma tace "wai sannu da kokari" murmushi kawai ummu tayi Iman tace "na gode ummu Allah ya saka da alkhairi" hancinta kawai ummu ta ja zatayi magana wayanta ya d'au kara dubawa tayi taga zahra murmushi tayi kan ta d'aga tace "Autana" kawai se zahra ta sa mata kuka ta manta when last taji ummun ta kirata da haka murmushi ummu tayi tace "ke kam bazaki girma ba ko? Yanzu me abun kukan?" Tace "ummuna nayi missing d'inki dan Allah yaushe zaki dawo? Ko In zo?" Ummu Tace "makarantan kuma wa ze je miki zamu dawo ne da daughter ta samu sauki" zahra tace "ummu zan iya yi mata magana yanzu?" A sanyaye ummu tace "ga ta".
Ta mikawa Iman wayan kar'ba tayi tace "besty" nan fah zahra ta kuma fara wani sabon kukan wadda hakan yasa hawaye ya cikawa Iman idanu kan ma ita Iman tayi magana zahra tace "ki yafemin besty" murmushi Iman tayi tana share hawayen da ya gangaromata tace "Anki se kin yarda Hamma Muhammad ya turo kin san ina lissafe? Saura sati date d'in da aka bashi ya cika" a shagwa'be zahra tace "to ya na iya" dariya Iman tayi tana cewa "masha Allah kice mu shirya shan buki bari inzo In mishi albishir" murmushi kawai zahra tayi me sauti se kuma tace "innalillahi gaban su umma kike wannan magana?" Iman tace "kwarai ma kuwa gashi handsfree kike kuma ba" ihu zahra ta sa zata kashe wayan Iman tayi saurin cewa "ke ke wallahi ba kowa sun fita" ajiyar zuciya ta sauke tace "amma ke ba!" Sukayi dariya a tare sauka Iman tayi a hankali sbd jikinta da take jin kaman an mata tsinannen duka a kasa ta zauna ta sa chokali ta fara cin abincin rice ne da sous d'in hanta se miyan cabbage girkin da yake kad'an ne ba karamin daad'i ya mata ba, har ta kusa gama ci hira suke da zahra nan take fad'amata su teema ma sun koma yolan jiya duk wani abin da basuyi hiran ba seda sukayi, wayan taji an zare daga kunnenta ko bata d'ago ba ta san waye sbd kamshinshi da ya cika mata hanci.
'Dagowa tayi se tayi saurin ja baya sbd kusancin dake tsakaninsu a duke yake gefenta wayan ya sakala a kunnenshi yace "ke sarkin surutu ki bar min mata ta huta haba" dariya tayi tace "hamma dan Allah ku dawo da wuri" yace "yes zamu dawo ne ko don maneminki da ze turo next week" Da sauri ta kashe wayan shi kuma yayi dariya 'yar kaniya se kace da gaske tana da kunyan dama surutun yake son yankewa don ya san In ba hakan yace ba se ta dameshi Don ita surutu baya damunta "yarinya se kace aku mutum ne baya gajiya da surutu" murmushi Iman tayi ta d'ibo abincin a spoon da take ci ta kai mishi bakinshi bud'ewa yayi ta zuba mishi ya lumshe idanunshi ya bud'e fes akanta yace "wannan kam daad'in abincin ne ko har da albarkar hannunki hayatee?".
Siririyar dariya ta sake tana sa hannu a baki tace "a'a nide inaga santin daddad'ar girkin ummu ne bari In sa maka waigi" ta karasa da janyo pillow ta sa mishi bayanshi dariya yayi yana gyarawa ya zauna da kyau yana tankwashe kafa yace "I missed yummy foods d'in ummu wallahi" Tace "Alhamdulillah" shima ya maimaita ta ci gaba da bashi Don ita ta riga da ta koshi shikam daad'in girkin da kuma soyayya ya d'ibeshi ya ma manta be jima sossai da cin abinci ba seda yaji cikinshi na shirin fashewa yace "wayyo hayatee zaki fasamin ciki" dariya tayi tana ajiye spoon d'in tace "to na bari haka, ga ruwa" ta mika mishi kar'ba yayi ya sha tace "wai da gaske ne za'a tambayar auren bestyn?" Yace "eh d'azu munyi magana da Muhammad d'in da kuma Abban na sa an min binciken halinshi be da wani nakasu ko matsala matsalar dai mahaifiyarshi ce da ta cika matsawa matan 'ya'yanta"
Tace "Toh yanzu haka zata aureshin mahaifiyarshi bata sonta?" Hancinta yaja yace "me a ciki komai ai lokacine zata dena ne in lokacin hakan yayi sannan yace ma ba kano zasu zauna ba ya koma aiki Lagos chan zasu zauna" shagwa'bewa tayi tace "Allah sarki yanzu zan rabu da bestyna kenan" murmushi yayi yace "ga ni se in maye gurbinta dama chan ni ya Kama ta In zama bestyn" murmushi kawai tayi.
Kwana biyu suka kara a fufore an cika ta da gata da kulawa daga hajja, ummu, umma, baba fufore da babanta se kuma me gayya me aiki wato malabo sossai taji daad'in kwana biyun nan fiye da ko wasu kwanaki cikin ranakun ta na duniya duk abinda take so shi ake yi se abinda take so zata ci, umma ta manta da wani kunyan d'iyar fari ta rungumi erta don d'aki d'aya ma suke kwana, yayin da gefe d'aya Abdul ya takura mata Allah Allah yake su tafi ya samu lokacin matarshi seda yayiwa baba fufore maganan tafiya sau kusan biyar kan baban yace zasu iya tafiya ko washegari ne cikin murna yazo ya sanar dasu yayinda Iman kam batayi wani farin ciki sossai ba sbd zatayi missing wannan kulawar da yadda take kwana jikin mamanta kaman wata er goye.
Sede bata nuna a fuska ba don ta san In ta kuskura ta nuna ta shiga uku da rigiman shi, nan fah aka hau shirin komawa gida, washegarin kuwa suka tafi suka bar su baba da kewa baki sunyi halinsu, kan su tafi seda baba ya basu wani ruwan magani a half jarkan da wani mayuka da ya had'a banda na Iman da ya bata wadda zasu zama na shafawanta har su kare kan taci gaba da shafa duk abinda taga dama, yace a bawa inna, goggo saratu, goggo hindatu da goggo kamila su sha In sunsha se su shafa komenene da wannan aljanar ta sa musu ze narke yabi fitsari ko kashi godiya sossai baba da umma sukayi har da Hawaye shi kam har 'bacin ranshi ya nuna akan godiyan Don yadda ya d'auki su Abdul Haka ya d'auketa.
A 'bangare d'aya ma Abba da zahra sun matsu sossai su dawo musamman Abba da yake cikin farin ciki da natsuwa matarshi ta dawo daidai Allah kad'ai ya san irin halin damuwan da shiga akan halayenta na sihiri, baki bud'e baba da umma ke karewa wannan masarauta kallo cike da mamakin inda aure ya kawo 'yarsu wannan ba Don aure ba ko wucewa sun isa yi a kofan masarautar bare su shigo? Khaih gaskiya dukkan godiya ya tabbata ga Allah mad'aukakin sarki.
Basu kara sakankancewa da al'amuran masarautarba seda suka ga wani tarba na karamci da suka samu daga wannan gari gaskiya sun jinjinawa karamci da iya tarbar baki irin na mutanen Adamawa, nenne da kanta ta musu iso ga mai martaba suka mika gaisuwa inda dama meeting ake na family waenda suke kusa kawai sbd irin abinda ya shafi nan cikin gida, anan ummu ta wanke kanta ta basu labarin abinda ya faru fufore harda matsalan Noor Iman gabad'aya kowa a wurin seda ya jinjina wannan al'amari nan mai martaba ya tofa albarkacin bakinshi inda yayi nasiha sossai akan kula da shiga harkar aljannu da mutane suke se kuma yayiwa ummu nasihar karta zargi kowa Allah ba azzalumi akan bayinshi bane da kanshi ze toni asirin mugu daga karshe aka rufe taro da adu'a.
Gabanta ke luguden bugu jin nenne ta sa kuyangi kai musu kayayyakinsu part d'insu na gidan shikenan yau kam ta kad'e har buzunta gashi hajja ta sata dole shan wasu abubuwan da ma bata sansu ba na kwana biyun nan da tayi da ita ga wasu fitinannun turaruka da ta had'ata dasu, akwai randa ta shafa d'an kad'an wallahi saura kad'an komai ya faru a d'akin hajja, hajjan ce ta katseshi kunya kaman ya kasheta, to gashi yanzu part d'insu zasu ware su kad'ai Don har nenne ta ma umma iso d'akin da zata kwana, ummu kam part d'in iyayenta ta sauka.
Wanka ta farayi bayan shiganta d'akinta ta shirya cikin cotton doguwar riga me guntun hannu sbd zafin da ake, bayan ta fesa rexona kawai se ta fesa Oud mood spray kawai ta sa hula akanta, zama tayi bakin gado tana amsa wayan hafsy cikin kuka hafsyn tace "Adda wallahi muna cikin matsala da damuwa ban dae fad'awa baba ba kar hankalinsu ya tashi" cikin damuwa Iman tace "me ya faru hafsy?" Tace "mijina ne ya sayi fili na about 1.5million har ze fara gini se ya shiga kariyar arziki hakan ya sa ya sayar da filin ga wani mai kud'i ashe tun farko wadda ya sayar mishi da filin irin 'barayin filin nan ne yanzu asalin mai filin ya kaishi court na sayar mishi da fili yanzu an nemi ya biya Alhajin da ya sayarwa kud'inshi shi ya d'auki asaran sbd shine marar karfi cikinsu, shi suke son d'aurawa asaran gashi mun karar da kud'in da aka saya d'in a jinyar ciwon diabetics na mahaifiyarshi".
Shiru iman tayi cikin nazari da tunani chan tace "Toh Hafsah na san yanzu kika fad'awa su baba ma d'aga hankalinsu zasu yi kinga ga jinyar mama dukda hamma Abdul ke yi, gashi nima ba wasu kud'ad'e bane hannuna, sede Zan duba a cikin kayan lefena In mun dawo gobe akwai d'an kunnayen gwal se In baki ki sayar watakila kud'in su kai a bawa court d'in" hafsa cikin Hawaye tace "anya kuwa za'ayi haka Adda? Zaki taimaki mutumin da be ta'ba nuna miki soyayya ba kullum se...." katseta iman tayi tace "kayya hafsy ban son jin komai gobe in mun iso Zan kiraki, se munyi waya ki gaida maman nashi da jiki" ta kashe wayanta d'ago kan da zatayi se ta ganshi tsaye jingine da gini yana kallonta murmushi ta mishi ga mamakinta kai ya kawar ya nufi ficewa har ta bud'e baki da niyan mishi magana se rufe kofanshi ta gani bata kawo komai ba ta gyara tayi kwanciyarta tana chat da zahra a haka har tayi bacci bata ji gogan nata ba gashi ita kunyar zuwa d'akinshi take kar yace wani abu take nema.
*****
Ta 'bangaren su umma da hamna kuwa a lokacin da suka dawo me umma taci ne se Allah cikinta ya rud'e se gudawa haka ta kwana tanayi daga baya kuma amai ba shiri hamna ta garzaya da ita asibiti ba tare da ta fad'awa Abba halin da take ciki ba, bayan an mata komai an bata gado tayi tahowarta ta kira kukunta a waya ta balbaleshi da masifar me ya hanashi zuwa na kwanaki dayawa nan ya fad'amata ai oga Abdul ya sallameshi ya Bashi aikin yi a company d'inshi bala'i ta dingayi har seda ya kashe wayanshi.
Haka take zuwa ta sayi abinci a restaurant ta kai asibitin yau kwananta d'aya kenan hakan yasa basu aikata ayyukan da boka ya basu ba har yau da ta kai mata abincin sukayi fad'a sbd mitan da umma ke yi akan bata damu da ita ba bata kwana wurinta iyakaci ta kawo mata abinci tayi tafiyarta kaman ba mahaifiyarta ba masifa ta hau yi akan ta zo ta zama mata liability a haka suka rabu tana shigowa gidan kawai ta ganshi tsaye gaban fridge na parlorn da ruwa rike a hannunshi da sauri ta saki jakan hannunta ta saka ihu da gudu tayi kanshi ta rungumeshi.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*049*
Janye jikinshi yayi yana satan kallon inda Iman take bama su take kallo ba tv ta kurawa ido cikin tunanin laifin da ta mishi da ta gaisheshi da safe be amsa ba Haka har suka shiga jirgi be tanka mata ba har suka sauko drivers biyu suka zo se Hafeez da suka zo da zarah, murmushi ta d'anyi tuna irin ihun da Zarah ta yi Don ganinta da gudu tazo ta rungumeta har seda tayi hawaye Allah kad'ai ya san irin kewar kawartan nan da tayi, sun so su tsaya hira sede Abba na jira suka d'auki ummu suka tafi.
'Daya driver ya d'auki su Abba da Umma su kuma d'ayan ya d'aukesu haka sukayi zaman kurame kaman ba shi ba har gida, zama kawai tayi shi kuma ya nufi fridge shan ruwa kenan wannan matar tashi ta shigo, su take kallo amma idanunta kan tv yake wani kullutun bakin ciki ne ya tokareta a kirji ganin ya rungumeta shima yana wani murmushi wadda shi a wuri shi yake ne don bata haushi amma ita gani take na soyayya ne.
"Yanzu shigowarka?" Kai ya gyad'a mata yana cewa "kina lafiya?" Tace "kalau wallahi umma ba lafiya tana hospital" yace "subhanallah shine baki kira kin fad'amin ba?" Tace "jiya ne kawai fah amma da sauki watakila gobe a sallameta" Kai ya gyad'a tace "a d'akina zaka sauka ko?" Kai ya kuma gyad'a mata tace "wow I missed you so much muje In had'ama ruwan wanka" ta ja hannunshi ya kuwa bi ta zuwa d'akinshi.
A zuciye ta mike tayi d'akinta har kwalla tayi tana fad'awa gadonta ita karan kanta bata ta'ba sanin tana da kishi haka ba kaman yau da wannan tunanin bacci ma ya d'auketa bata sani ba, se zuhur ta tashi tayi sallah yunwa ne ya fara kwakwalarta hakan yasa ta mike ta fito kitchen Indomie biyu ta dafa da kwai biyu ta juye a plate tana fitowa ta ganshi zaune parlor da wasu kayan daban kawar da kai tayi zata wuce se kuma taga rashin dacewar hakan ta kalleshi ita yake kallo tace "barka da rana Hamma" yace "yauwa".
Har ta kai kofan room d'inta yace "cikinki kad'ai kika sani kenan?" Yayi tambayar yana kallonta tace "a'a Hamma wai naga ba nice da girki bane kuma naga Anty hamna bata fito tayi wani abin ba gashi Ina jin yunwa yasa na dafa, amma In zaka ci gashinan bari In dafo wani" ta kai gabanshi ta ajiye ta bashi tausayi har ze yi mata magana se kuma yayi tunanin barinta ta gane kuskurenta.
Itama bata tanka ba ta juya kitchen ta dafo wani tazo ta wuceshi zuwa d'akinta taci ta koshi tayi tagumi nan gaban plate d'in ko me tayi mishi? Amma in tace a haka zasu zauna taga ya chanza mata bata iya magana ba zata cutu don tana da saurin shiga damuwa akan abinda take so, ajiyar zuciya ta sauke tana d'ago kai se ta ganshi tsaye, idanunta da suka cika da hawaye ta saka cikin nashi tace "hamma ko akwai wani laifin da na maka ban sani ba?" Gabanta ya karaso ya duka ya rike hannayenta yace "kin d'aukeni abokin zama?" Kai ta gyad'a yace.
"Toh Ina so daga yau hayatee ina so In zama best friend d'inki, your shoulder to cry, your favorite person no matter what the situation is, ki dinga sharing happiness ko sadness d'inki dani kinji?" Kai ta gyad'a yace "words pls" Tace "Toh" yace "yanzu Hafsat ma ba kanwa bace a wurina?" tace "kanwarkace" yace "to me yasa in abu ya sameta bazaki iya shawara dani kan ki yanke hukunci ba? Komai nawa naki ne habeebty kud'i na naki ne base kin sayar da wani abu naki don fitar da kanwarki/kanwarmu cikin matsala ba, zanyi magana da mijin ohk?" Tace "Ohk kayi hakuri bazan sake ba In Allah ya yarda".
Murmushi yayi yace "that's my girl" yana lakace mata hanci murmushi tayi itama ta mike shima ya mike suka fito tare ya shige room d'inshi itakuma ta kai plate kitchen, aiko chan yamma hafsat ta kirata ta dinga zuba godiya harda kuka, wai har Abdul yayi settling case d'in, don tun bayan ta dawo da plate taji fitansu da matarshi, watakila asibiti yaje ya duba umman da taji d'azu tana cewa ba lafiya daga nan ya wuce gidan hafsan.
Taji daad'i sossai har ranta se ga mijin hafsyn ma ya kirata hakuri ya bata akan abubuwan da yayi ta mata, bata nuna mishi komai ba tace ita wallahi ta yafe mishi bata rikeshi a ranta ba, nan ya ba mamanshi itama ta nemi yafiyarta, bayan ta ajiye wayan take tunanin rayuwanta na baya tabbas zahra da Abdulraheem Alkhairi ne ga rayuwanta sun shigo mata da haske ya haskake bakin duhun rayuwanta Alhamdulillah ta furta a fili.
Fita tayi ta d'aura musu abinci sbd tana ganin In batayi ba bata kyauta ba sbd Ai asibiti hamnan taje so ta lalla'ba ta dafa musu jollof na taliya da yaji veggies da busashen kifi ta shirya duk kan dining ta koma d'akinta ta watsa ruwa ta murza mai da turare kan ta nemi wasu English wears marasa nauyi trouser da shirt d'inshi da ta baya yake dogo kaman