Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
ke dashi a kanshi, sannan se ta jaa wa su rahma shati akan shiga harkar da ba nasu ba, duk zasu gamu da ita.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjoh6763 on Wattpad•
*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*010*
Duk kasa suka sauka suna gaida Abban banda Abdulraheem, dayake duk se yanzu suke ganinshi sa'banin Hafeez da tare suka je sallahn asuba kuma sun gaisa achan amma yanzu ma seda ya kara gaidashi, amsawa yayi da fara'a yana tambayansu rahma iyalansu duk da lafiya suka amsa, "auta ina nawa smoothie d'in ko yayunki kawai kika sani?" Ya ja zarah da wasa idonshi na kan Abdulraheem da ya mike zaune daga ganinshi ka san ranshi a matukar 'bace yake sede sam hakan be nuna a yanayin fuskanshi da idanunshi ba sbd Allah yayishi mutum me danne 'bacin ranshi irin Abban.
"A'a Abbana Ai In kana nan Ina na san wasu Anty rahma? Yanzu kaima zan je In maka irin zobon da kake so" duk dariya sukayi Abba yace "yauwa 'yar albarka bari In je parlor na In jiraki" da gudu ta mike tayi kitchen suna mata dariya, wucewa Abba yayi parlornshi yayinda Abdulraheem ya tashi a kasalance ya bi bayanshi.
A kasa ya zauna kanshi kasa yace "ranka shi dad'e barka da rana" Abba yayi murmushi kan yace "yauwa babana ya ayyukan?" 'Bata fuska yayi kan yace "so stressful wallahi ni Abba na gaji da lecturing d'in nan, haba Abba ga aikin gomnati ina dashi, sannan ga business inayi Amma ka sawa mutanen nan hope akan zanyi aiki dasu".
Wannan dattijo Allah ya halicceshi da fara'a murmushi kam be d'aukewa a fuskanshi "Abdulraheem koyarwa fah lada ne dashi ba wai samun kud'i kawai ba, ni da Ina da yadda zanyi na koma koyarwa da na koma, don ma ban saka kayi a secondary school ko islamiyya ba" nyamutsa fuska yayi a zuciyarshi yace Tab!!! Murmushi Abba ya kara fad'ad'awa kaman ya san abinda Abdulraheem d'in ya fad'a a zuciyarshi.
"Rayuwa d'an hakuri ne Babana musamman harkar mata ka kara hakuri amma In kaga zaka cutu ka kara aure, ban de goyi da bayan ka saki matarka ko ka wulakantata ba kaga de 'yar uwarkace" kanshi a kasa yace "In shaa Allahu Abba, bari naje Ina da meeting" Abba ya ce "Toh Allah ya bada sa'a ya taimaka, Allah yayi muku albarka" da "Ameen" ya amsa yana mai jin daad'in adu'ar ya fice.
A parlorn Ummu ya tsaya tare da bankawa su Anty Rahma harara kaman baze yi magana ba kuma se yace "Munafukai kun had'ani da uwata ai kun huta" dariya suka kwashe dashi Hafeez yace "mu de ba ruwanmu ai kun fi kusa wa ze san shiryawarku?" Kalthum tace "yanzu haka se a shirya dashi mu ba'a shirya damu ba" Anty rahma tace "kya fad'a 'yar uwa" kara hararinsu yayi kan ya haura saman Ummun da sallama ya tura d'akinta ciki ciki ta amsa.
Seda yayi murmushi ya girgiza kai kan ya karasa ya zauna a gefenta tare da d'aura kanshi kan kafad'arta yace "Allah huci zuciyar uwa ta gari, ki dena damun kanki plz akan zancensu Kalthum, ba me ta'ba miki 'yar gwal d'inki bare kuma ayi maganar yi mata Kishiya ita kad'aice ba Kari in shaa Allah" a take ta saki fuska tace "yauwa Son ko kaifa se yanzu na ji magana su kuma kilbabbun chan zasu gamu dani Ina daidai da zamaninsu".
Murmushi ya saki tare da d'an ta'be baki yana mikewa yace "muna neman albarkanku ummu zan wuce" tana murmushi ta shafa kanshi tace "Allah yayi muku albarka gabad'ayanku, ya tsareku daga sharrin masharranci ya bada sa'an aiki" yace "Ameen thumma Ameen" kan ya fice tana bashi sakon gaisuwa wurin d'iyarta.
***********
"Assalamu Alaiki yake ma'abociyar kyau da kwarjini" d'an ta'be baki tayi kan tace "wa'alaikassalam, Ina yini" yace "Lafiya kalau dear ya gd? Ya su ummanmu?" Tace "Lafiya" yace "ya kaman baki gane me magana ba? Lallai na san matsayina wato ko numberna ba'ayi saving ba?" Siririyar dariya ta saki tace "yanzu fisabilillahi ni yaushe nace ban gane me magana ba?" "Toh Ai yadda kike amsawan ne kaman baki gane me magana ba, Toh In kin gane bawan Allahn, me sunanshi?".
"Ya hammad" ta fad'a tana wasa da harshenta, lumshe ido yayi yana jin daad'in sunan nashi daga bakinta, a hankali yace "ni de ba yayanki bane" tace "Toh me kake so in kiraka dashi?" Yace "honey, dear, sweetheart, baby and rest" bata san sadda ta fara dariya ba Lallai ma hammad d'in nan, shima yana murmushi yace "au dariya na baki ko?" Tace "sossai ma" yace "Toh na kuwa ji daad'i tunda nayi silan dariyarki Allah na gode ma" wani murmushin ta kuma yi kan tace "mama na kirana bari inje" yace "Ohk baby take care, I love yhu".
Dip tayi bayan kashe wayan, ba maman dake kiranta kawai ta fad'i hakan ne don yanayin da taji ta fara shiga akan hammad tabbas yana da kirki kuma yana da saurin sabo, idan har Allah yayi ta aureshi toh fah tayi sa'ar miji, sede tsoronta d'aya kar shima irin sauran ne dukda be yi yanayi da su ba, kirkinshi kaman hamza 'Allah sarki Allah yaji kanka ya gafarta maka' ta jima tana irin tunanukan nan kan ta mike ta fita parlor.
*********
Tuntu'be yaci da bottle d'in cock har yana shirin fad'uwa da sauri ya daidaita kan ya maida idanunshi kan bottle d'in a hankali ya fara juya idon yana karewa parlorn kallo a take yaji ranshi yayi bala'in 'baci, parlorn kwata kwata ba kyan gani duk da kayan alatun dake zube a cikinshi, tun cups da plates da tayi using d'inshi daga jiya da safe zuwa yanzu da yamman nan suna zube a parlorn, trow pillows duk ba wadda ke wurin zaman shi kai har wasu kujerun.
Center table d'in ma yana manne da jikin gini ga d'ankwalinta da riganta ga empty bottles na drinks, parlorn de kaca kaca abin takaici, ashe gwara parlorn kasa da nan tunda shi ba komai na kaya sede kura, shi d'inma sbd bata zama cikinshi ne, rai 'bace ya nufi room d'inta da kafa ya banke kofar ya shiga tana kwance kan gado daga ita se wani half gown gashin nan baja baja ba d'ankwali a kai.
Tana da gashi kam masha Allah, da sauri ta mike zaune ganinshi kanta ko sallama babu kuma ta san ba halinshi bane 'shittt' se yanzu ta tuna da gargad'inshi na safe, fuskewa tayi tace "boo ka dawo?" Harara ya zabga mata kan yace "a'a Ina chan, hamna me na ce miki kan na fita?" Juya ido tayi kan tace "ni me ka cemin?" Ranshi kara 'baci yayi ganin tana shirin raina mishi hankali alhali yasan ta tuna.
"Ina me miki rantsuwa da Allah na shiga nayi wanka na fito na samu baki yi abinda na saki ba ranka In yayi dubu zai 'bace, hamna karki yarda na fara nuna miki the other side of me!! Ki kiyaye ni na gayamiki, na tsani kazanta da mai yinta" fita yayi ta kuwa ta'be baki ta koma tayi kwanciyarta.
Har yayi wanka ya shirya ya fito cikin shigar shan iska three quarter da sleeveless shirt parlorn nan na yadda yake ba abinda ya chanza, ranshi a matukar 'bace ya shiga d'akinta yadda ya barta haka ya dawo ya sameta da waya a hannu tana danne danne, fisge wayan yayi ya buga da kasa cikin 'bacin rai yace "hamna wuce kije ki share parlorn nan kiyi moping" itama cikin fushi tace "me haka Abdul? Sbd wani banzan sharan parlor shine zaka fasa min waya? Ka kuwa san nawa na cire na saya? Wallahi baze ta'ba sa'buwa ba kuma sharan bazan yi b....."
Tasss taji saukan mari a kuncinta hannu tasa ta dafe kuncinta tana mishi kallon mamaki Don duk abinda zata mishi be ta'ba kai hannu jikinta ba se yau, kuka ta fashe dashi ya daka mata tsawa "ki wuce kije ki share parlorn nan kiyi moping kuma ki girka min abinda zanci kan In kakkaryaki a wurin nan" sautin kukanta ta kara jin wai harda girki wani tsawar da ya kuma daka mata "get up jare!!" Yasa ta saurin sauka kan ta kara jin wani marin ta fita tana kuka.
Da kuka da komai akayi Shara da moping d'in shi ma ba wani fita yayi ba sbd bata iya sossai ba, girki kuwa daga indomie se ruwan tea ta iya dafawa hakan yasa ta mishi indomien da Kwai se ta dafa mishi coffee ta had'a a tray ta kai d'akinshi, yana kishingide a three seater d'in d'akin yana kallon wrestling a kan center table ta ajiye har lokacin tana Hawaye kallo d'aya ya mata ya kau da kai shi ba halinshi bane dukan mutum musamman macen amma hamna In ba da Haka ba bazata ta'ba shiga taitayinta dashi ba.
Yayi alkawarin baze sake dukanta ba daga yau sede barazana da hakan tunda ya ga ta tsorata dashi, dukda ta bashi tausayi amma be ce mata komai ba har ta fice, wayanshi ya d'auka ya mata transfer d'in 350.000 Ya san kud'in wayanta kenan, kan yasa fork ya fara cin indomien, tana shiga d'aki wanka tayi kan tazo wurin fasasshen wayanta ta d'auki SIM card d'inta a wani karamin wayanta ta sanya.
Se kuwa taga kud'in bata san sadda murmushi ya subuce mata ba, a take ta shirya cikin riga da wando ta yafa gyale d'an karami ta d'auki keyn motarta ta fice don sayo sabon waya.
Washegari
Tafe suke suna hira da zarah duk akan test d'in da dr malabo yace ze yi next week "dr malabon nan daga gani questions d'inshi zasuyi tsauri ba kad'an ba" murmushi noor tayi, ita har yanzu bata san wai zarah sister d'inshi bace sbd ta ma manta da surname d'in zarahn balle ta d'ago daga nan, tace "kayya zarah tuntuni kike mita akan test d'innan, ba wani tsaurin da zeyi In har kinyi karatu tunda de dole abinda ya yi mana shi ze tambayemu".
Zarah tace "na lura kare mutumin nan kikeyi bayan sarai kin san halinshi na wulakanci" girgiza kai noor tayi tana tuna taimakon da yayi mata tace "kayya zarah ba wani karewa daad'in abun kan yayi wulakancin se ya fad'i abinda bayaso so be da laifi don yayi hakan, kayi abiding rules se ka zauna lafiya".
Zarah da mamaki take sauraran noor Tab da ita ce ya Abdul yayi ma abinda yayiwa noor da zagi kam se ya sha cikin kwanduna amma ji yadda take kareshi🤔 wakar da wayanta ya d'auka ne yasa ta kallon wayan "Ya Abdul" shine sunan da ya bayyana da hearts a gabanshi, da sauri ta d'aga tace "hamma" yace "sallaman fah? Ko shine hamman?" Baki ta tura tace "Toh salamu alaikum, jam banduna(ina kwana) Hamma?" Yace "wa'alaikissalam jam gaaji(lafiya auta) sameni a office" ya kashe wayan.
Kallon wayan tayi ta kalli noor tace "brother na yace In sameshi office d'inshi muje plz ki rakani" noor tace "dama ku fulani ne?" Zarah tace "Eh duk iyayenmu 'yan adamawa ne zama ne kawai ya kawo mu kano" noor tace "Tab zan so kuwa koyan fulatanci don daad'i yake min, gashi yaren ummana" zarah tace "amma bata muku ne yasa baki iya ba ko?" Shiru noor tayi tana tuna halin ummanta.
Bata iya cewa zarah komai ba har suka karasa varender d'in da office d'in yake, bata kalli kofan ba balle ta ga sunan da aka rubuta a jiki kawai sa kai tayi a bayan zarah suka shige da sallama muryan da taji ya amsa sallaman sun ne yasata saurin d'ago kai gabanta na fad'uwa, karab idonsu ya fad'a cikin na juna da sauri ta kawar da kanta gefe, dama yayan zarah ne shine zarah bata ta'ba fad'a mata ba se ma zaginshi da takeyi a gabanta? Allah ya taimaketa da ta kasance me zagin mutane da taji kunya gaban zarah, muryan zarah da taji tana sake gaidashi ne yasa ita ma tace "Good morning sir" kaman baze ce komai ba kuma se yace "morning" yana kallon zarah yace "Da nace kizo na ce kimin gayya?".
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*this page is dedicated to yhu Hafsat Sulaiman Mrs Ibrahim Allah ya barku tare, a jima ayi lasting🥰*
*011*
"Khaih Hamma gayya toi mi wad'i? Useni ta viwu ko d'ume fahin to a andi Allah, sobaje am on"(gayyan me nayi? Plz karka ce komai kuma, kawata ce), baki ya ta'be tukun ya mika mata wasu manyan files guda biyu yace "ga wannan kaiwa sauban pls kiyi sauri, ta jiraki anan sbd na san In ku biyu ne bazaki yi sauri ba" "Toh Hamma, noor zauna bari inje In zo sorry".
Zama iman tayi kanta na kasa taji fitan Zarah, wani irin uneasiness take ji na zaman su su kad'ai a office d'in zuciyarta kuwa se race yake yi shi kad'ai har hannunta na had'a zufa tsaban nervousness, daurewa tayi ta fara karewa office d'in kallo ko hakan ze rage mata abinda take ji, office d'in babba ne sossai akwai manya manyan shelves me d'auke da littatafai Arabic da boko a kowace kusurwa na office d'in.
Se babban desk da desktop d'inshi ke kai desk dinma kad'ai abin kallo ne sbd had'uwarshi ta bayan desk d'in kujerarshi yake kaman yadda kuka sani, kujerar ma me irin juyawan nan ne, a gefen desktop d'in files files ne dayawa amma a tsare suke so clean and neat, kasan desk d'in akwai extension wear wani babba gefenshi babban printer ne da blue gate.
Kasan office d'in shimfide da tattausan red carpet ba abinda ke tashi a office d'in se kamshin air freshener da sanyin Ac gefe chan leather cushion ne three seater, sossai office d'in ya mata kyau gashi a tsare daga ka gani zaka san ba na kananan lecturori bane, wani kofa ta kalla tana tunanin ko wannan kuma kofan me? Allah masani amma tafi kyautata zaton toilet ne, satan kallonshi tayi don ganin me yakeyi Ai ko se suka kuma had'a ido a tare suka kawar da kai.
Gyaran murya yayi kan yace "sarauniyar kuka" kallonshi tayi da mamaki se taga shima ita yake kallo, juya idonta tayi da ya kasance d'abi'anta kan tace "ni dr.?" Yace "Yes yhu were always crying what's your problem?" Shiru tayi tana tunanin matsalolinta raurau tayi da ido tana kallonshi, waro nashi brown oily eyes d'in yayi yace "sorry plz don't cry, I just ask ne ko zan iya taimakawa but tunda kuka zakiyi you don't have to answer".
Zatayi magana wayanta ya hau kara bud'e jakanta tayi ta fiddo wayan ganin hammad ne yasata murmushi kan ta d'aga "Assalamu alaikum" yace "wa'alaikissalam Cutie barka da rana, ni Kin min adalci kenan yau kwata kwata fah baki neme ni ba" murmushi ta saki tana girgiza kai rigiman hammad se shi "sorry lectures nayi da safe yanzu fitowa na shiyasa ban kiraka ba but kana raina, ya ciwon kan?" Dayake jiya ya ce mata headache na damunshi, yace "naji sauki, ni bazan yi hakuri ba se an ce min sorry darling ko sorry sweetheart" murmushi me kyau ta saki wadda yake fitar da dimple d'inta guda da kuma wushiryarta.
Ita kanta ta san tana kyau in tayi irin murmushin sede ba kasafai takeyi ba, kallo kawai yake binta dashi wadda ya rasa dalilin kallon, wayan kyau yake mata in tayi magana da muryarta se yaji wani natsuwa na saukar mishi tsabar rashin hayaniyarshi da sanyinshi, lasan lips tayi tace "nop zan fad'a amma ba yanzu ba" yace "se yaushe?" Tace "In naje gida" yace "Ohk baby ki kular min da kanki, plz kar ki bari ko wani namiji yaji wannan muryar taki da da hali ma da na hanaki magana da kowa" murmushi kawai tayi tace "ohk bye".
Ta kashe wayan tana murmushi a lokaci d'aya tana taune lip d'inta na kasa, sharp ta manta office na waye take seda ta d'aga kai suka kuma had'a ido kau da kanshi yayi yana mamakin kanshi, Allah ya gani shi ba mutum bane me shiga harkar mutane bare kuma me kachokan kafin ya d'aga ido ya kalli mutum hmmm amma ya rasa ya akayi yau ya sa 'yar mutane a gaba yana mata kallon kurilla, karan wayanshi ne yasa shi kallon wayan.
"Alexandra" sunan da ya fito akai kenan, d'agawa yayi da hello, kan yayi Shiru yana saurari cikin mintuna kad'an ya mike ya fara zuba masifa cikin wata had'ad'iyar British ascent da ya sata kallonshi da kyau wow sossai turancin ya mata daad'i tabdijam Ai idan tayi turanci gaban wannan se a mata dariya don gani za'a yi bata iya ba, masifa kawai yake da bama ta gane me yake cewa, kafe fararen Zara zaran tender fingers d'inshi tayi da ido mai d'auke da wani had'ad'an azurfa, sossai yatsun hannunshi suka mata kyau.
Imagining take da hannun mace ne da idan yasha jan lalle irin kyaun da ze yi, tsabar tsabtarshi faratunshi a yanke suke a gyare tsab farare sol, kau da kai tayi da sauri kar ya kamata tana mishi kallon kurilla gashi yana masifa kar ya sauke kanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin shigowar zarah, zama zarah ma tayi tana kallon yayanta, ta juya ta kalli noor ta kuma kallon time, se ta mike tazo kusa da noor tace "besty tashi mu tafi se mufi hour anan hamma be gama wayan nan ba, gashi 20mins kawai ya saura mu shiga lectures".
Mikewa noor tayi ta kuma satan kallonshi gaskiya bata gaji dajin muryarshi na zuba British English d'in nan ba amma ba yadda ta iya haka ta sa kai ta fita zarah tabi bayanta bayan ta d'agawa Abdul d'in hannu.
Cikin sauri suka karasa hall d'in ba tare da sun samu lokacin magana da juna ba lecturer da ze musu lectures lokacin ya shigo, Bayan sun fito daga lectures d'inne noor ta dubi zarah tace "amma ke yarinyar nan baki kyauta