NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   23 / 44

66K to 69K   out of 131.7K words

zaka min akan munafukar matarka zan saukeshi wallahi" ficewa tayi zuwa d'akinta ta fad'awa Ummanta duk abinda ya faru.

Bayan fitanshi ta cire gyalen jikinta da d'an kwali itafa a rayuwarta d'ankwali takura mata yakeyi, d'akin ta bi ko Ina ta karewa kallo tana mamaki, garin ta'be ta'benta ta ta'bo wani abu kaman button fari se gani tayi wani abu ya sauko daga sama ihu tayi tana matsawa, labule ne me kauri sossai cotton fari sol gwanin kyau, ciki ya raba da parlorn, dariya tayi tana kama baki, se taga parlorn ya fita da kyau babba sossai haka ta bud'e labulen ta shiga d'aki nan ma ya fita kato dashi, komawa tayi ta kara danna abun labulen ya koma ta kara dannawa ya sauko cikin nishad'i ta dingayi kaman wata yarinya seda ta gaji ta bari, toilet ta shiga ta dinga bin komai na ciki shima da ta'be ta'be.

Bayan ta gama ta fito ta fice babban parlorn saman, katuwar plasmar parlorn ta gani kunne bayan d'azu da suka shigo ba'a kunne ba, boom tv ke kai se wani rawa akeyi itakam ko kyaun gani be mata ba, hakan ya sa ta nufi gaban tv ta d'auki remote ta fara chanza tasha, daga bayanta taji ance "eyeee ashe su en kauye kuma talakawa an san tv tunda har an iya chanza channel" juyowa tayi se taga Hamna, idanunta ta kawar kan tace "Ina kwana Anty, wai naga abinda ake yi a wanchan tashar ne ba kyaun ga...." tsawa hamna ta daka mata "ke dallah rufewa mutane wannan kazamammen bakin ke har kin san abinda yake maras kyau da me kyau? Ni wuce ki 'bace min da gani kan raina ya 'baci In sa'ba miki kammani yanzun nan".

Umma da yanzu shigowarta ta kalli Iman sama da kasa kan tace "ke kin san ni?" Kai Iman ta girgiza umma tace "Toh bari In fad'amiki wacece ni, ni kanwar mahaifiyar Abdulraheem ne kinga kaman mahaifiya nake a gareshi kuma ni mahaifiyar Hamna ce kin fahimta?" Kai Iman ta d'aga umma ta ci gaba da cewa "so ina da hurumin saki abu kiyi a matsayina na uwar mijinki, ki wuce ki samamin abinda zanci yunwa nake ji".

Kitchen Iman ta nufa ba tare da tace komai ba, kitchen d'in fes dashi kaman ka lashe ba datti ko guda d'aya, komai na bukata akwaishi cikin kitchen d'in store ta bud'e shima akwai kayan abinci jibge se ma suyi shekara suna ci be kare ba, to sede bata san me zata dafa musun ba ganin safe ne yasa ta d'auko doya ta fere dube dube tayi tayi har ta samo inda kwai yake ta fasa, ta koma store inda taga an shanya albasa, garlic, turmeric da ginger d'anye ta d'ibo abinda zata bukata tazo ta had'a nan take tayi musu yam ball ta juye gabad'aya a cooler, tana fitowa da shi Zarah na shigowa.

Da mamaki zarah ke kallonta "besty yaya ne yace ki mishi girki?" Kai Iman ta girgiza itama zarahn ta san baze ta'ba sata ba sede tayi don ra'ayin kanta ko...... se kuma ta waro ido "Hajjiya Umma!!!" Murmushi Sossai Iman tayi ganin yadda tayi maganan wato irin ta d'ago d'in nan, tace "ke menene don nayi girkin? Muje In ajiye mu wuce room d'ina kigani, and Yauwa bazaki tafi yanzu ba Allah karma ki fara ce min zaki tafi waya mutu waya farko".

Kau da sauran maganan Zarah tayi tace "Amma wallahi Iman baki had'u ba, meyasa kikayi? A garinku ne Amarya ke girki a washegarin tarewarta?" Ta'be baki tayi tana ajiye tray d'in da ta d'auko kan dinning, sauka tayi ta kama hannun zarah suka nufi d'akinta tana cewa "wace Amarya? Ni kam ba Amarya bace ban ma san me zan kira kaina ba, plz mu bar maganan ya kikaga room d'ina?" Santin d'akin zarah ta fara.

Tayi ta zagayawa, bayan ta gama ganin komai ta kunna tv suka zauna kallo, kiran azahar ne ya d'agasu sukayi sallah, bayan sun idar suka hau hira inda take tambayar zarah ina su zee, tace mata "sunje yawo ko hutawa basuyi ba ingayamiki haka suke In sun shigo kano kaman an saki tsuntsu daga keji kin san a fada ba yawo ake barinsu yi ba".

Dariya Iman tayi tana cewa "Allah sarki, ki sa min numbers d'insu" kar'bar wayar tayi ta d'auko nata ta saka mata gabad'aya tayi mata saving "Zarah saura ke kizo kiyi aure mu shaa buki" murmushi tayi tana cewa "ke barni ba yanzu ba, haka kawai Ina rayuwa freely azo a kulle mutum a gida fita ma se ka roka har ganin Abbana se ya min wuya" ta karasa tana tura baki, dariya Iman ta saki tana girgiza kai tace "kema de kin san aure dole ehe yarinya se ki shirya Don kina saken da na san saurayinki sace wayanki zanyi in turamishi text message baba yace a turo".

********

Gud'ar da ake tayi ne ya cika unguwan har ya sa duk makwabta fita ganin gulma a daidai lokacin da en yola suka iso, manyan motoci land cruiser ne guda Biyar suka shigo layin, bayan su inna sun shige, akwatuna aka fara fitarwa d'aya bayan d'aya ana shigar da shi gidan wow, ko daga nesa ka hangesu zaka san ba harkar yara bane harkar manya ne Ina tsaye Ina kirge seda aka shigar da guda Goma sha biyu.

Shidda milk color shidda Purple, sakan baki su inna sukayi suna kallon wannan kaya kap family d'insu gabad'aya ba wacce bukinta ya kai na Noor Iman wasu har Allah ya isa suke ja se kace ita ta za'bowa kanta mijin, da aka fara bud'e kaya kuwa harda masu kwallan bakin ciki, kayayyaki ne naji da fad'a waenda baza su ma iya kirguwa ba, tun suna kirga yawan zannuwan har suka dena manyan zanuwa da manyan laces Anty rahma ta kwaso mata da d'an kunnaye da sarkoki har da su gold and diamond.

Turaruka kuwa zaka ce karamin perfume store za'a bud'e, umma karan kanta se da ta jinjina kayan bata karasa kallo ba ta tashi ta shige d'aki kawai, Mama kam harda kukanta na farin ciki dukda bata jin daad'i har yanzu ita kad'aice ta zage tayi ma su Anty rahma karamci, Anty rahma ce da kanta ta kasa ta tsare a kan kayan duk makwabtan da suka shigo kallo seda sukayi dana sani.

Anty rahma tacewa Mama "Am In ba damuwa zaku wakilta mutanenku se a kai mata kayan daga nan tunda ga motoci" cikin jin daad'i mama tace "to bari In kira babanta yazo ya ga kayan arziki" mikewa tayi ta fice zuwa d'akinta ta kira baba, mintuna kad'an se gashi da yake yana kusa, inna da tayi zaman en bori gaban kayan ya duka ya gaisar bata amsa ba, su goggo saratu ya kalla duk sunyi wani iri da su, Mama ce ta katse mishi hanzari da rangad'a gud'a kan tace "ka ga kayan d'iyar Albarka" kallon kayan yayi yace "wace haka?" Mama tace "Noor Iman Mana In ba ita ba waye?" Da wani irin murna ya nufi akwatinan mama ta fara bud'e mishi yana kallo har kukan daad'i yayi.

Ba 'bata lokaci bayan ya gama kallo ya cewa su Anty rahama su tattara su kai mata kar su barshi nan a mata sata Allah yayi mata albarka ya bada zaman lafiya, da murna Duk suka amsa banda Hajiya inna da su Anty saratu, tattarewa su Anty rahama sukayi suka fice bayan mama ta d'an had'a kud'ad'en hannunta dubu d'ari ta basu, godiya suka dingayi Anty rahama na yaba karamci irin na mama.

*********

A nan kuma basu jima suna hira ba su zee suka zo nan aka had'u aka dinga chapter sossai suka sha hira a cikin irin hirar ta d'ibi experiences dayawa sbd an ta'bo mutane dayawa waenda zama da kishiya ke basu wahala an ta'bo rayuwar aure sossai, Anan ne ma teema ta bata sakonnin Nenne tare da yi mata bayani kaman yadda nenne tayi suna yi suna mata tsiya, kar'ba tayi ta adana a kunyace.

Su sukayi mata shara da mopping na room d'inta da parlorn saman suka shiga kitchen suka hau girki, 'buruntunsu ne yasa hamna fitowa don ganin waye, da mamaki take kallonsu basu ta'ba zuwa gidanta wai don sun zo hutu gidan Abba ba, bare kuma har su mata girki haka zarah, cikin masifa tace "Lallai ma yaran nan yaushe kuka zo?" Teema tace "tun azahar Anty hamna me ya faru?" Da fad'a tace "ban son munafurci tambayata kike abinda ya faru? Kuzo tun d'azu ina er uwarku ku kasa shiga d'akina se d'akin kishiyata? In ni banda darajar hakan goggonku fa?".

Zee Tace "haba Anty hamna Don mun shiga d'akin iman menene ciki sannan itace sa'armu kuma itace kawarmu" Nabeeha tace "beside kuma ai itama er uwa ce so Don mun shiga wurinta ba laifi bane" hannu ta sa a baki kawai ta juya d'aki ta d'auki wayanta ta kira Baba yarima bayan ya d'aga yayi mata ya gajiyan hanya kawai se ta fashe da kuka cikin tashin hankali yace "lafiya kubra wani abin ne ya faru?" Cikin kuka tace "Baba su Ameera ne......." "me suka miki?" Ya katse mata hanzari "zuwa sukayi gidana suka had'u da kishiyata sukayi ta zagina, ashe tun da suka zo nan suka sauka ko umma basu zo sun gaisar ba".

Cikin fad'a yace "Abinda suka je yi kenan kanon? Suna da hankali kuwa kiyi hakuri zan kirasu amma bawa uwar taki wayan" bawa umma tayi tana mata magana da hannu kar'ba tayi ta wani sanyaya murya yace "haba hasfa babba dake kuma kina matsayin kanwata zakiga yaran nan suna ma yarsu haka baza ki iya magana ba?" Kuka tasa na munafurci tace "na musu magana Hamma amma ganin suna neman su zageni yasa na fice na kyalesu" rai 'bace ya kashe wayan ya kira Ameera da yake itace babba.

Suna turara had'ad'en fried rice d'insu zarah na had'a coslow yayinda Iman take had'a musu zo'bo duk da yadda suka so hanata sa hannu a aikin taki sam, wayan Ameera da suke jin waka ne ya d'au kara matsawa tayi ta duba tana kallon sunan ta waro ido ta kalli sauran tace "baba" duk matsowa sukayi ta amsa tare da sanyawa speaker ko sallamanta be amsa ba ya hau musu fad'a kaman ze ari baki daga karshe yayi musu rantsuwar ya sake Jin sunje gidan Abdulraheem ma gabad'aya ransu ze 'baci tunda ba arziki ke kaisu ba, In kuma suka kuskura suka tsallake magananshi ba su ba kara zuwa kano, Kit ya kashe wayanshi.

Dukkansu a wurin seda ransu ya 'baci Iman har ta fara hawaye Allah sarki yanzu baba yarima ze na mata kallon maras hankali da tunani, Zarah ce tayi karfin halin karasa abinda suka bari ta sassaka musu kula dama duk sun kamalla kad'an ya saura rabawa biyu tayi ta sa musu nasu ta sawa en gidan ma nasu, Duk sun kasa magana daga karshe Teema ce ta fara magana "Amma matar nan anyi bakar munafuka" Zee tace "daga ita har mahaifiyarta ban cire kowa ba, In ba munafurci ba yaushe muka mata rashin kunya har muka zagesu?" Nabeeha tace "ko ganin hajjiya umman munyi ne In ba sharri ba gashi baba in ya rike abu kullum se ya muku fad'a akai" Ameera ta d'auki wayanta ta danna kiran Abdulraheem bazasu iya tafiya su bar Iman haka ba duk tayi wani iri cike da damuwa bata so en uwan mijinta su fara tsananta sam, waennan d'in sune kawayenta kuma en uwanta tunda duk kannentan mazajensu sun hanasu zuwa aurenta.

Yana d'agawa ta fashe da kuka, Shiru yayi na seconds kan yace "Ameera!!! Lafiya?" Cikin kuka tace "yaya ba kaga Anty hamna ba Don mun zo taya Anty Iman ayyuka da gyare gyare shine ta Kira baba ta d'aura mana sharri wai mun zageta gashi Yace kar mu kara zuwa gidanka tunda abinda ke kaimu kenan se kuka Anty Iman takeyi" Shiru yayi kaman baze yi magana ba se kuma yace "on my way" ya kashe wayan.

Kusan 30 mins suna zaune jugum jugum se gashi ya shigo Iman kam ma bata nan tana cikin d'akinta, Zarah ya kalla yace "me ya had'aku da ita?" Bayani tayi masa, lumshe ido yayi Hamna na so ta kureshi wallahi, wayanshi ya zaro ya kira baba yarima, bayan sun gaisa yake ce mishi "yanzu baba gidana ne kace kar su Ameera su kara zuwa? Baba ka fa san hajiya umma kuma ka san irin tarbiyar su Nabeeha baza su ta'ba iya zaginta ba, kuma ka yarda da maganganunsu?".

Da tunanin hakan yace "me suka ce maka su?" Nan Abdul ya mishi bayani, baba yace "dukda haka in basu fad'a mata abinda ba shine ba baza ta kirani ba, ba wai na yarda da maganganunsu duka bane yasa na yanke musu wannan hukuncin, ba ta yadda za'ayi hamna na er uwarsu suna kawance da kishiyarta dukda hakan shirme ne irin ta mata but ka duba maganan".

Abdul yace "baba kaji labarin Iman kaima kana son rabata da su Ameera sbd kana ganin da gaske bata da tarbiya?" Yayi maganan a sanyaye, Auzubillah Baba ya furta, "shikenan Abdulraheem su dinga zuwan amma dan Allah ka ja musu kunne bana son fitina" godiya ya mishi sukayi sallama, dayake duk sunji yadda sukayi murna suka hau yi, zarah ta dube shi da ido ya mata alamun Ina Iman.

'Daki ta nuna mishi da kai ya mike ya nufi room d'in, tana kwance ta kifa kanta kan pillow daga ita se karamin towel iya cinyarta da alamu wanka ta fito tayi kwanciyarta ba tare da ta shirya ba, jikinta yabi da wani irin kallo chocolate fatanta se yalki da sheki yakeyi, a bakin gadon ya zauna kan ya d'aura hannunshi kan fatar bayanta zabura tayi ta juyo se taga shine, juye juye ta fara Don neman abinda zata rufe jikinta amma ba komai kusa, hannu tasa tana gyara d'aurin towel d'in kanta kasa.

Duk ta rud'e wadda hakan yasa shi sake murmushi kunyarta ya mugun burgeshi muskutawa tayi zata matsa yayi saurin kamo hannunta da karfi batayi balance ba hakan yasa ta fad'o jikinshi "Ashhh" ya furta yana riketa Don ta buge shi kuma yaji zafi, da sauri ta d'ago tana shafa kai tace "sorry" karkata wuya yayi yace "kika karyani se kin biyawa ummuna ni" Siririn dariya ta sake ganin yadda yayin kaman wani karamin yaro, murmushi ya saki ganin tayi dariya yana cewa "ko ke fa Haka kawai mutum yayi ta kunci? Ki dena d'aga hankalinki akan abu kalilan haka kin san ba Lafiya ce ta isheki ba" zatayi magana kenan suka ji gud'a mikewa yayi yace "tashi ki shirya su Anty rahma ne" mikewa tayi shi kuma ya juya ya nufi akwatinta dukawa yayi ya 'bude waro ido tayi tana kallon me yake shirin yi, wani orange lace ya ciro mata riga da skirt da d'an kwalinshi, da karfi ta runtse ido tana danne lip d'inta na kasa da hakori ganin ya zakulo mata inner wears d'inta duk blacks.

Juyowa yayi ya kalleta yana sake murmushi ya san za'a rina yana mamakin yadda take abu kaman bata ta'ba rayuwa da maza ba bayan aurenta hud'u, mikewa yayi ya zo dab ita ya duka ya ajiye mata kayan kumatunshi na gogan nata kuma danne idonta tayi jikinta na d'aukan rawa girgiza kai yayi yana mikewa murmushi kwance a fuskanshi ya juya ya nufi kofa seda ya kai dab fita tukun ya had'e rai sbd masu mishi tsiya irinsu wa'e🤨😜😜 bande kira suna ba.








                   🖤Gureenjo🖤


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
         *Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                             *33*

Murmushi yaki barin fuskanta har ta gama shiryawa tare da yafa katon mayafi ta rufe fuskanta ta zauna kan gado, a parlorn kuwa yana fita kaman ya sani Anty rahma ta fara mishi tsiya kara had'e rai yayi yana hararanta. Sauran friends d'inta da na ummu biyu da suka kawo kayan se wasu daga cikin en uwan iman se dariya suke.

'Dakinshi ya shige yana shiga Hamna da Umma na fitowa baki bud'e suke kallon kayan, har muryar hamna na rawa wurin cewa "wannan kayan fa Anty rahma?" Murmushi Anty rahma tayi kan tace "na Amaryarki ne mijinku ya mata" bata san sadda ta furta "kambalastii!! Yanzu duk wannan kayan er kutumar uban chan??? Wai me hamma ke nufi da ni ne? Wato kaskanci ya shirya nuna min to wallahi Allah ya isa ban yafe ba" tsabar takaici abinda zata fad'a ma bata sani ba.

Akwati shidda ya mata don bala'i ba irin mitan da batayi ba yayi rantsuwar baze kara ba amma shine yanzu yayiwa Banzar matarshi goma sha biyu kuma sunfi nata kyau, da karfi ta fashe da kuka tana kallon ummanta tace "wallahi umma ba zan yarda ba ki san yadda zakiyi dani Allah bazan yarda ba wani irin cin fuska ne wannan??? Ko fah kayan fad'ar kishiya be min ba, duk wacce za'ayi sede ayi ni kam se an raba kayan nan biyu an bani d'aya".

Dafe kai Anty rahma tayi tana kallon umma dake rungume da ita tana buga mata baya se kace wacce akaywa mutuwa, tana cewa "dole ma hakan za'ayi Ai wallahi duk cikinsu ba wadda ya isa ya wulakantamin ke ya zauna lafiya har shi Hamma Ahmad d'in, bari kiga In kira Addan, In ni Abdulraheem ya rainani Ai ita be isa ya rainata ba".

Ummu ta kira cikin masifa tace "Adda zama da d'anki fah ba dole bane ba In bakwa bukatar mu a family d'inku se mu tattara muyi gaba haba wannan wulakanci da kaskanci har Ina" ummu tace "me ya faru hafsat?" Umma tace "Ki zo gidanshi yanzu ki ganewa kanki" ba musu umma ta mike ko sashin Abba bata shiga ta fad'amishi ba ta fito ta shiga motanta ta ja se gidan.

Nan ta gansu tsaye cirko cirko Anty rahama kam mamakinsu ne ya kusa kasheta taya za'ayi a raba kayan da akayi Don Amarya a ba kishiyarta Ai Abinda baze ta'ba sa'buwa ba kenan, bayanin da sukeyiwa ummu ne ya sa ta dawowa tunaninta,

23 / 44