NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   20 / 44

57K to 60K   out of 131.7K words

d'inta fah yayi niyyar yi a bainar jama'a badon na dakatar dasuba da ba abinda ze hanasu yi, umma kince nayi kwalliya irin na amare naje nayi amma ko kallo ban isheshi ba, ki duba fah ko event d'aya be zo ba a bukinmu bayan d'aurin aure wai ayyuka sun mishi yawa amma se gashi a wannan".

Umma tace "dan Allah ki kwantar da hankalinki Hamna, naji goben da asuba zamu bar masarautar nan duk abinda nenne zata fad'a sede ta fad'a" share hawayen fuskanta tayi tana cewa "haba ko ke fa umma" ta tu'be ta kwanta bayan uwarta, In ba shashanci ba ace wai tana kishin mijinta ne shine tunda tazo garin bata ta'ba zuwa makwancinshi ba, bata san cinshi ba bare shanshi ko had'uwa sede ta ganshi ya gitta, Allah ka tsaremu da irin wannan zaman.

*****

Abinda ya faru kuwa da zarah tun kan a gama dinner d'in Anty kalthum ta kirata ta fad'a mata akwai matsala ummu fah ta kuma rikice musu akan auren nan musamman da ake event nan se kace wata me aljannu, ta hanata zuwa dinner d'in haka hafeez ma tace In yaje bata yafe mishi ba, Abdul yaje ma ta hana a barshi ya shiga ganinta kuma tayi rantsuwa in ya kara bari suka had'a hanya da shi har ya nuna mata fuskanshi da auren Iman a kanshi se ranshi yayi mugun 'baci.

Itama tana ta nemanta layinta ne yaki shiga, fita zarah tayi ta shiga mota driver ya ja yana tambayarta Ina tayi, cikin sanyin murya tace mishi gida, gidan ya kaita har part d'in Ummu, ya bud'e mata ta fice, zata shiga kenan Abba ya rike hannunta, kallon shi tayi tace "Abba Ina yini" yace "lafiya klau ina daughter na?" Tace "basu dawo daga dinner ba" yace "Ohk, ina so karki shiga wurin ummunku yau se kun gama buki karki bar Iman ita kad'ai ba wadda ta sani nan d'in se ke, in da hali ki sa numbern ummunkun black list zuwa gobe".

Hawaye ne ya gangaro mata tace "Abba me ya samu ummu ne? Ba haka take ba sam ina zargin akwai wani abu, dukda tana son hamna amma son da take yiwa hamma Abdul yafi yawa ta ya zatace kar ya kara zuwa inda take In be saki iman ba, Anya Abba ba chanza mna ita akayi ba?" Abban karan kanshi ya fita zargin hakan kuma duk shima hankalinshi ba kwance yake ba mamakin rashida sam yaki barinshi, ita macece ba irin kowacce mace ba tana da hangen nesa da sanin ya kamata duk abinda yake so ko bata so to fah se ta so amma yanzu ga Abinda take musu ze iya cewa tunda suka shigo ko magana bata kara mishi ba har yanzu. Cewa yayi "Ki kwantar da hankalinki In aka watse buki zamu zauna kinji?" Kai ta gyad'a yace "oya je tafi ki kwanta dare yayi" juyawa tayi tana mishi se da safe, tayi part d'in nenne da kafa dayake ba nisa sossai da part din Abban, mamaki take yadda Hamma Abdul ke kokarin fara'a da sake fuska bayan ta san In har ummu na fushi dashi hankalinshi tashi yake kaman wadda aka mishi albishir da shiga wuta, Da tunanin ta isa hakan ya sa ta kasa sakewa Iman duk damuwan Sabon halin ummunsu ya dameta.

GIDAN BOKA



*jama'una Ina jin daad'in comments d'inku da irin soyayyar da kuke nunawa book d'in nan, waenda na kira da waenda ban kira ba irin khadija salisu, sadiya tijjani da dai sauranku duk kuna cikin raina ba wai na manta bane, Allah ya bar kauna*




                     🖤Gureenjo🖤



🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
             •Gureenjo6763 on wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                          *029*

"Hahahahahhaa Baku da matsala da wannan, Don ko banyi aiki ba akwai me aiki a kanta baze ta'ba kusantarta ba inba an karya wanchan alkadarin ba, in ya matsa kuwa komai ze iya faruwa da shi har ita karan kanta, hahahahhaa" da mamaki Umma tace "wani irin aiki kenan yake kanta boka? Naka ne?" Wani dariyar ya kumayi yace "ba huruminku bane kuma In kun matsa komai ka iya faruwa".

Hamna tace "to boka batun mahaifiyarshi naga kaman ta sakankance da maganar auren ba kaman farko ba" nan ma dariya yayi kan yace "yaro yaro ne, Ai tashin hankalin da muke kara sa mata akan auren ko uwarki wannan bazata iya d'auka ba se ta tsinewa d'an, kaman yadda na gayamuku da farko akwai babban al'amari a kanta duk randa ya karye kuwa ni zan dasa mata nawa, zakuma ki iya tarewa gidansu ba wadda ze ce dake komai a kai, lokacin ku ya kare ku sallameni maza ku tattara ku bar nan".

Kud'i umma ta zuba mishi kan suka mike suna mishi kirari da munmunar kalamai yana washe baki har suka fita, a cikin mota se tunanin wani irin al'amari ne boka ke magana hamna keyi ta kasa Shiru ta fara tambayar umma, umma ce ta hanata tana cewa "baki ji abinda yace ba kar ki matsa da bincike? Toh kar na kara ji kinyi maganan" Shiru duk sukayi ba su suka iso masarauta ba se dare basu san me akayi a gidan da safe ba bare rana.

******

Tunda suka farka daga bacci har sukayi wanka suka zauna karyawa Zarah bata ce komai ba, abin se ya dami Noor cikin jin wani iri tace "Zarah ko akwai abinda na aikata gareki ne cikin rashin sani?" Da sauri zarah tace "ko d'aya wallahi ba wani abu" iman tace "to me yasa kika koma haka? Ko akwai wani abu da ze iya samunki wadda ban kai In sani ba?" Zarah ta kuma cewa "ko d'aya iman ban son damuwana ya shafeki har ya 'bata miki mood kinga yau akwai event wadda shine na karshe, sannan damuwar fa ba wani damuwa bane na azo a gani, in kin koshi tashi mu fara makeup kan waenchan tsuntsayen suzo su damu mutum".

Murmushi Iman tayi kan ta mike kuyangar dake jiran su gama ci ta tattare ta fara tatarewa a tsanake har ta gama ta fice da trays d'in, zama sukayi zarah ta janyo Kit d'inta ta 'bud'e suka fara, ba me cewa komai chan wayan Zarah ya d'auki kara, kallon fuskan wayan tayi da mamaki ta d'ago wayan ganin Muhammad, akan lips d'inta ta furta 'hammad!!' Har seda ya kusa tsinkewa kan ta d'aga.

"Assalamu alaikum" yace "wa'alaikissalam warahmatullah malama zahra" Tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya klau Alhamdulillah ya gd? Baki jini ba ko kwana biyu wallahi kuna raina kasar na bari yanzu saukowata hutawa kawai nayi nace bari In kira inji ya abubuwan suke tafiya?" 'Dan Shiru tayi kan tace "normal, Iman tayi Aure da yayana kuma Alhamdulillah ba wani damuwa ko matsala".

Cikin excitement yace "masha Allah na mata murna sossai, Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba" Tace "Ameen, se anjima" yace "wait wait madam Ai ban gama maganan ba" Tace "uhmm" murmushi yayi kan yace "wata biyar aka bani In fidda mata In ba haka ba Amin auren dole...." katse shi tayi da "Allah sarki se ka fitar ba" yayi murmushi ya fahimci ta fuskanci abinda yake son fad'i amma take fuskewa yace "Da farko da naga Iman se zuciyana ya bani duk duniya ba wacce zan iya zaman aure da ita inba ita ba, bazan boye miki ba sonta lokaci d'aya ya shiga zuciyana kaman abin asiri se kuma Mom taki auren namu irin kin da banyi zato ba, se kuma nayi sa'a babba a ranar da na rabu da Iman washegarin na samu wata me irin halayen Iman, duk kwanakin da suka shud'en nan tana cikin raina daram na kasa fidda ta da tunaninta nake kwana dashi nake tashi".

Kwa'be fuska tayi tace "congrats to ni me nawa a ciki ko kasa fad'amata kayi shine zaka wakilceni gani bbc" dariya yayi har Iman seda ta dara dukda ba jin abinda d'ayar bangaren yake fad'a ba take, on top of that bata ma san wayene ba, cewa yayi "a'a ko d'aya, tabbas wakiltanki zanyi zuwa ga Zuciyarki ki bata Sakon zuciyata, zuciyata tace "tana mata so irin na tsakani da Allah" wani irin dariyar rainin hankali Zarah tayi kan tace "Allah ya baka lafiya" ta kashe wayanta tana tsaki.

Dariya iman tayi tana girgiza kai "Allah ya shiryaki zarah" d'an murmushi zarah tayi kan tace "Ameen ooo" ci gaba sukayi da makeup d'insu bayan sun gama ta shirya cikin Sky blue gown da ya matukar Amsanta zarah ta kafa mata head nan ya zauna d'as, hill ta d'auko mata wadda yasa zarah waro ido tuna fa ya hanata saka hill, "a'a zarah bazan saka wannan ba samomin flat shoe kafana na ciwo" har zata musa se kuma ta fasa ta kawo irin half cover na sarauta me lankwasa ta gaba irin ta mata ta ajiye mata blue.

Alkwabbar da ta sanya ma blue ne me adon fari tayi kyau har ta gaji, hotuna zarah ta dinga mata tana cewa "yau fah akwai comments insta bakiga yadda aurenku ke trending ba duk inda kika shiga zaki ga Noorheem" iman tace "dan Allah dae? Ai duk kece na sani yanzu fisabilillahi se in na koma school ayi ta kallona ana nunani kin san kowa rayuwar instan nan yake" dariya zarah tayi tana cewa "to se me? Daad'in abinde matarshi za'a ce ba karuwarshi ba, ke Ai tun randa aka d'aura aure nake samun followers kaman hauka sbd posts d'in hotunanki da na ango kuma wallahi ya gani ubana ze ci".

Dariya Iman tayi zatayi magana aka turo kofa aka shigo Anty Rahma ce da Su Teema, da gudu zarah taje ta rungumeta tana mata oyoyo, "Sannu da dawowa Anty" iman ta fad'a cikin sanyi, gabanta Anty rahma ta karasa tana cewa "masha Allah, tabarakallah zarah aikinki na kyau tun daga dubai nake ta kallon hotunan buki a Instagram gaskiya habeebty kinyi kyau sossai" a kunyace Iman Tace "na gode Anty".

Zarah tace "Anty Ina boxes d'in?" Anty rahma tace "suna Kano chan na sa aka kai Abban su Halima yaje ya d'auka suna gidana in munje se akai gidansu su gani tukun a dawo mata dashi gidanta" tura baki Zarah tayi tace "kash na so nan aka kawo na kashe kwarkwatar idona" teema tace "Allah kuwa da nan aka kawo" Nabeeha Tace "tunda ana hutu ko zamu roki mommy ta roka mana dad ya barmu mu tafi kanon hutu?" Zee tace "wallahi kuwa Allah de yasa zasu yadda" a tare suka ce Ameen gabad'aya, teema tace "Dada fa na jiran amarya tace mu duba ne ko ta gama shiri a fita da ita zasu wuce filin kilisar" zarah tace "Ai ta gama shiri ku fita da ita zan zo daga baya kinga ko powder ban shafa ba" Nabeeha ce ta kama hannunta suka mike suka fice, su teema suka rufa musu baya duk sun ci kwalliya kaman ba gobe.

Zama zarah tayi tana sauke ajiyar zuciya bayan fitansu Anty Rahma tace "Lafiya kuwa Auta me ke faruwa ne?" Zarah tayi shiru na mintuna kan ta fara bawa Anty rahma labari tana hawaye bayan ta gama ta d'aura da "Anty bakya zaton asiri akayiwa ummu? Abin yayi yawa gashi mun rasa mafita" Daga bakin kofa suka ji ance "ba mamaki ze iya yiwuwa ze kuma iya kasancewa ba haka ba, dama abu irin haka na faruwa shine Ahmad be fad'amin ba? Me ya d'aukeni?".

Anty rahma tace "ba haka bane nenne be son hankalinku ya tashi ne a fara samun matsala da ummu bayan tun tashinta ba'a ta'ba samun matsala da ita ba tsakaninku, amma Ai ya fad'awa su baba galadima" Nenne tace "dukda haka, yau da yamma zamu zauna gabad'aya aji me matsalar mahaifiyarkun In ba haka ba zata iya tursasa Abdul ya saki matarshi wadda In hakan ta faru kuwa Za'a samu matsala babba Don wallahi ba yarda zanyi ba" fita tayi tana me ci gaba da mita.

******

Suna fita aka d'auketa a mota Su Teema suka shiga na baya aka ja suka fice, katon filin masarautar da ake kilisa nan suka nufa canopy's da aka kakaffa a gefen filin suka yada zango inda kujerar da aka tanadar mata zama tayi nabeeha ta mayar mata da hulan baya sossai yadda zata dinga ganin abinda akeyi, mutane ne kad'an ba yawa iyakaci na cikin masarautar wato family ba'a gayyaci kowa ba bayan haka.

Idon da zata d'aga se ya fad'a cikin nashi ido ya kashe mata guda d'aya yana sakin wani murmushin iyayi, da sauri ta kau da kanta yayi kyau kuwa cikin bakaken sport wears da mutanenshi gefenshi duk wurin abokanshi ne family friends 'ya'yan uncles d'inshi sunyi su goma duk kuma sport wears ne jikinsu ance suyi da kayan sarauta sunki wai karin nauyi ne ze hanasu gasa me kyau.

Layi sukayi shi yana daga tsakiya, wani abu aka hura da bata san me ba se kawai taga sun hau gudu da dawakansu, wani irin tsere sukeyi da ya bata tsoro su ko tsoron fad'owa basayi? Har karshen filin suka je da nisa sossai daga inda suke kan suka sake juyowa suka dawo zuwa d'aya 'bangaren shima har karshe kan suka sake kwasowa zuwa tsakiyar filin inda aka fara tseren shine gaba kuma shi ya fara isowa.

Ihu dogaran wurin suka saki suna mishi kirari, murmushi kawai yayi be sauka daga kan dokin ba ya kar'bi towel da ruwa ya sha ya d'an share gumi kan ya buga kafanshi dokin ya zabura sukayi gaba ba gudu yakeyi ba yanzu kam idonta na kanshi har ya kule cikin masarautar ya nufa, sauran ma kowa sauka yayi aka kar'bi dowakan akayi gaba dasu suma kowanne ya nufi cikin masarauta.

Alqaita da ganga irin ta sarauta aka fara a filin tana son kid'an har ranta shiyasa ta natsu tana ta aikin kallonsu har mamaki take kumatun masu hura alqaitar nan be ciwo, ta raja'a da kallonsu da tunani har bata san Ya dawo ba se kamshinshi ne ya sanar da ita zuwanshi, d'ago kai tayi ta ganshi tsaye yana sake murmushi, Dada ce ta taso ta zo gabansu tana cewa "Ango ga amaryarka daga nan ka san inda zakayi da ita Ai" Da mamakin irin wannan tsari nasu take kallon Dada shi ze tafi da ita ba kaita za'ayi ba?.

Sanye yake cikin bakaken riga da wando masu taushi irin na asalin sarauta, sunsha ado da zare farare alkyabbar jikinshi ma baki da fararen ado a jiki, takalmin kafanshima na asalin sarauta ne baki, rawanin nan ya zauna mishi d'as yayi kyau woo kaman In sato muku shi ku ganshi, ajiyar zuciya ta sauke jin hannunshi cikin nata, mikewa tayi a zuciyarta kuma tana mamakin me ya hana en uwanta zuwa wannan event d'in? Bata ga ko d'ayansu ba.

Wata had'ad'iyar mota aka kawo shi ya bud'e mata ta shiga kan ya zagaya aka bud'e mishi ya shiga, driver yaja part d'in baba yarima suka fara zuwa, suka mika gaisuwa dattijo me mutunci Haka iyalanshi kowacce seda ta mata kyautar ban girma, kuyangi na kar'ba suna mika godiyarta, daga nan part d'in baba galadima sukayi shima de the same thing nasiha me ratsa jiki ya musu kan yayi mata kyautar mota, godiya tayi sossai har seda tayi hawaye yau itace da mota? Alhamdulillah tayi ta nanatawa tabbas Abdulraheem Alkhairi ne a rayuwarta daga shi har Zarah sun kasance mata fitila masu haska mata hanyar duhun rayuwarta.

Nenne petel ma gwal tayi mata kyautarshi kaman ba jikarsu bace kishiyarta ya kamata daga nan suje wurin ummu ne amma gargad'inta gareshi yasa be ma yi Gigin kaita ba, suka wuce sashin mai martaba, wai itakam taga karamci dattijo ne me kwarjini da kamala nasihar da ya musu har kuka seda tayi Allah sarki rayuwa, mutanen nan sun mata abinda ko da za'ayi duniya sau nawa inde iyayentan nan ne basu isa yi mata ba.

Kyautar shanukai goma, tumakai goma da salwa ashirin, baru irin na turai manyan nan suma ashirin, se zabbi ashirin da d'awisu guda biyu, qur'ani da sallaya masu azababben kyau sarki ya mata, godiya ta dinga mishi har seda yace mata ya isa haka, ficewa sukayi zuwa wurin nenne, itama nasihar ta musu kan tayiwa Iman kyautar wani Box da bansan menene ciki ba, godiya sukayi kan suka fito zuwa mota kuka ta saka tana ajiye kanta kan kafad'anshi "Bani da bakin gode maku kai da zarah sede har abada bazan ta'ba manta abinda kukayimin ba, zaku zauna cikin raina har gaban abada, kaman yadda bazan ta'ba mancewa da kaina cikin adu'o'i na ba haka kuma bazan ta'ba mantawa daku ba, In har na manta ku to fa na manta kaina ne, zan yi iya kokarina wurin ganin nayi zaman amana gidan aurena bazan ta'ba sanadiyar bullowar wata fitina ba In shaa Allahu".

Kanta ya shafa yace "ya isa haka kukan nan plz, you promised not to cry again right? So is ok" Shiru tayi bata d'ago daga kafad'anshin ba har suka isa part d'in mama, iso aka musu sun jima kan aka basu damar shiga, zama sukayi suna gaidata ta amsawa Abdul kam shima da kyar amma Iman kam kallon wulakanci ta mata taja tsaki, ta so Abdul ya auri jikarta tun kan hamna amma yaki aka zo aka aura mishi hamna, bayan duk cikin masarautar ba wadda be san niyyar ta ba shine da ze kara me makon su neme ta se suka aura mishi wannan bakar yarinyar.

Ganin bata amsawa Iman bane yasa shi mikewa yace "mun barki lafiya" ya taimkaa mata ta mike ya kama hannunta suka fice tsaki me karfi taja wadda su kansu seda suka ji, sam bata damu da abinda maman ta mata ba ita tunaninta ma na ga en uwanta ko me ya hanasu zuwa? Kasa Shiru tayi tace "Su Mama sun tafi ne?" Kaman baze amsa ba se kuma yace "suna nan" Shiru tayi ganin ya kau da kanshi.

Kenan ba'a gayyacesu event d'in d'azu bane ko basu ga saman zuwa bane, ashe anje akan su fito su tafi event d'in suka ce sun gaji baza su iya zuwa ba, daga site d'in mama inda aka sauke en uwanta sukayi

20 / 44