Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
d'arsu a zuciyarshi, ze gwada shiga rayuwanta watakila ya taimaka mata.
Toh ma ya shiga as wa? A fili yace "kawai taimako irin ta addinin musulunci, bayan haka ba wani abu" Shiru yayi yana tunanin irin tsoron da yaji d'azu, "ko shi kuma sbd me?" Ya fad'a yana shafa suman kanshi da sauri yace "sbd na santa, Yes hakane sbd na santa yasa banji daad'in ganinta ba lafiya ba" sake sake kawai ya dingayi har ya isa gidanshi.
Nan ma kasa samun natsuwa yayi duk abinda ya san ze yi don gusar da tunaninta yayi amma abin ya ci tura, buga remote d'in hannunshi yayi da kasa yana furta "what the f***k is happening to me?" Wayanshi ya d'auka ya danna kiran sauban ringing biyu ya d'aga ba tare da ya jira cewar sauban ba yace "Ayi transferring d'inta to amenity right away and pls ka bata special care I pity her".
Kit ya kashe wayanshi tare da yima sauban mobile transfer d'in kud'i masu yawa ya kuma tura mishi sakon "used it in be isa ba yhu should let me know", da mamaki sauban ya ke kallon wayan nashi this is unlike Malabo, really? Ta'be baki yayi tuna irin tausayin shi, amma Ai be fad'a mishi iyayenta marasa karfi bane.
Ficewa yayi don aiwatar da abin da abokinshi ya sashi, Ai ko yana zuwa ya samu baba na mitan shi fa baze iya ba d'an kud'in shi da yake kaffa kaffa dasu zata kama tazo ta cinye mishi bayan ba abinda ta kareshi da shi har abada ma be yi tunani ba, da mamaki sauban ke kallon wadda ake referring as mahaifin yarinyar chan, ita kuwa wani irin uba Allah ya bata?.
Gabansu ya karasa yace "salamu alaikum" baba ya juyo yana amsawa da "wa'alaikassalam aaa Doctor ne" sauban yace "Eh Alhaji, am dama na zo In muku albishir da cewa wani bawan Allah ya d'auke nauyin gabad'aya charges na asibitinku har zuwa a sallameku" washe baki baba yayi cikin jin daad'i yace "masha Allahu mun gode, mun gode, Allah ya biyashi da gidan Aljannah" da "Ameen" sauban ya amsa kan ya kira wata nurse ya bata umarnin kaisu amenity room 13, ba 'bata lokaci aka ciresu daga d'akin yawa zuwa amenity.
**
"Ikon Allah, ko lafiya ya Abdul be zo yayi lectures ba yau bayan ya tara mutane?" Bari de in kira inji kiranshi tayi cikin ringing na karshe ya d'aga "Assalamu alaikum ya Abdul ina kwana?" Yace "Lafiya kalau auta, ya akayi?" Tace "naga baka zo kayi lectures bane yau so I decided to check on yhu, hope all is fine?" Yace "yes sure, wani abu ne ya rikeni" Tace "Ohk bye" yace "bye" kan ya kashe wayan.
Ajiyar zuciya ta sauke "Toh Alhamdulillah saura Noor" ta furta a fili tana danna kiran number d'inta, seda ta kira sau kusan hud'u kan aka d'aga muryar yarinya karama taji tana cewa "Salamu alaikum. Adda Noor d'in bata da lafiya an kaita asibiti" "subhanallah me ya sameta?" Ikhram tace "nima ban sani ba" kashe wayan zarah tayi tare da cewa driver ya kaita gidansu noor, har kofan gidan yayi parking ta sauka ta shiga.
Still ikhram ta gani da wayan noor hannunta dukawa tayi gabanta tace "ya sunanki 'yan mata?" Tace mata "ikhram" murmushi zarah tayi tace "suna me daad'i, ba kowa ne a gidan?" Ikhram tace "umma na ciki" shiga cikin parlorn tayi hannunta rike da na ikhram zaune kawai suka tarar da umma seda tayi sallama sau biyu kan ta amsa tace "sannu da zuwa bismillah karaso mana".
Shiga tayi ta duka har kasa Tace "Ina kwana umma" umma tace "Lafiya kalau, ya mutan gida?" Zarah tace "suna lafiya, dama naga noor bata shiga school bane shine na kira number d'inta kuma ikhram ta d'aga take ce min bata da lafiya har abin ya kai asibiti shine nace bari Inzo inji wani asibiti ne." Shiru umma tayi na mintuna kan tace "kya iya karbar wayarta ki kira mamanta kiji, ni kam ban sani ba kuma banda ra'ayin sani".
Da mamaki Zarah ta kalleta amma ganin she's serious yasa ta cewa "Toh umma" kar'ban wayan tayi Allah ya sa ba password ta duba numbern mama ta kira ba jimawa ta d'aga "Assalamu Alaikum, mama zarah ce kawar Noor na kira ne inji asibitin da kuke da kuma room number".
Fad'a mata mama tayi bayan ta amsa sallaman, mikewa tayi tacewa umma "na tafi umma se anjima" ikhram tayi saurin cewa "zan bi ta wurin Adda noor umma" tsawa umma ta daka mata "ke! Ke!! Ki kiyaye ni na gayamiki ba inda zakije, wuce ki bani wuri anan" da sauri ikhram ta fice tana kuka, da matukar mamaki zarah ta fice.
Da sake sake dayawa a ranta suka isa asibitin direct d'akin da mama ta fad'a mata ta nufa, da sallama ta tura kofan noor dake kwance ido biyu ce ta amsa a hankali, da sauri zarah ta karasa tace "besty!! Sannu me ke damunki haka? Ya jikin?" Noor tace a hankali "hmm da sauki zarah" Zarah zatayi magana kenan wayan noor dake hannunta ya fara kara dubawa tayi se taga "ya hammad" kallon noor tayi da kai noor tayi mata alamar ta d'aga.
Sallama hammad yayi ta amsa kan ta fara mishi bayanin noor ba lafiya tana asibiti cikin tashin hankali da jimami ya ke tambayanta me ke damunta tace bata sani ba tambayanta yayi asibitin da kuma room number ta fad'a mishi, ya tabbatar mata gashinan zuwa, sallama sukayi a lokacin mama ta fito daga toilet suka kara gaisawa kan tace "yauwa tunda kinzo kiyi hakuri ki d'an zauna da ita, bari inje gida in d'auko wasu abubuwan In dawo".
Zarah tace "Toh mama ga driver na a waje ze kaiki se ya dawo dake" godiya mama tayi kan ta fice zarah ta kira drivern ta sanar dashi aikin da ze yi, bayan ta kashe ne ta kalli noor tace "besty wai me ya sameki haka? Kwanciya asibiti farat d'aya?" Girgiza kai noor tayi cikin sanyin murya tace "Doctor be fad'a ba tukuna, Dr. malabo yayi lectures yau ko?" Dariya zarah tayi kan tace "Kai besty kina kwance gadon asibiti amma tunanin lectures d'in ya Abdul kike?".
Noor tace "ba dole ba zarah kin san na rasa attendance d'inshi sau biyu am afraid of failing his course" zarah tace "bazaki fad'i ba In shaa Allahu be ma yi attending class yau ba" ajiyar zuciya noor ta sauke tana dafa kanta dake sarawa sossai da sossai, dr sauban ne ya shigo da mamaki yake kallonta "what har kin tashi kina surutu? Lallai jininki me karfi ne, I have to inject yhu another injection yadda zakiyi bacci da kyau, with this your condition ba'a so kina yawaita surutu".
Murmushi kawai noor tayi zarah tace "ya sauban" yace "laaa autan ummu, dama kin san patient d'ina?" Zarah tace "she's my best friend" yana had'a injection yace "wow, so ya kk ya su ummu?" Tace "ummu tayi fushi tace kwana biyu ka ki zuwa gaisheta haka ka ki kawo su Amir" yace "oh ni kar ummu tayi fushi dani yau d'innan zanje In bada hakuri" ya karasa yana tsikarawa noor allure a hannu, zarah tace "Da ya fi kam" hira suka ci gaba da yi kan kace kobo noor ta yi bacci.
Yana shirin fita hammad na shigowa musabaha sukayi kan sauban ya fice hammad kuma ya karaso ciki, mikewa zarah tayi ta bashi kujera ya zauna ita kuma ta zauna bakin gadon noor suka kuma gaisawa ya tambayeta ya jikin inda tace "Da sauki Alhamdulillah" Shiru sukayi na mintuna kan ya mike yace "ga wannan na san mara lafiya da son kayan fruits, in ta tashi ki ce mata hammad yazo in shaa Allahu zan shigo da dare duba jikin nata".
"Toh In shaa Allahu, mun gode se anjima" shima yace "se anjima".
***
Se after five ya shigo asibitin yayi wanka ya sauya kaya fuskanshi na nan yadda cike da damuwa da suka kasu mishi gida biyu, direct office d'in sauban yayi, ya kuwa ci sa'ar samunshi zaune yana aiki zama shima yayi bayan sunyi musabaha, shiru ne ya ratsa na mintuna kan Abdul ya fara fad'a mishi damuwanshi da irin hukuncin da ya yanke, sossai sauban ya bashi goyon baya akan hukuncin yayi daidai suka kuma tattaunawa.
Sauban ya fad'a mishi abunda yaji baba na cewa inda ya kara da "daga gani mutumin akwai son zuciya da ba don kaiba da Allah ne kad'ai ya san irin hukuncin da ze yanke akan yarinyar don ma ba private ya kaita ba" mikewa kawai Abdul yayi ba tare da ya amsa shi ba ya juya ya fice, da kallo sauban ya bishi kan ya girgiza kai.
*Dan Allah ku sa mahaifiyata a Adu'a bata da lafiya*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*sadaukarwa ga duk wani masoyin littafin nan🙏 Na gode da Adu'o'inku*
*014*
Yana fita yayi amenity room d'in da sauban ya gayamishi take ya ja tunga ya tsaya, contemplating ya d'ingayi ya shiga ne ko kar ya shiga, bud'e kofan da akayi ne yasa shi saurin juyawa da nufin barin wurin se yaji muryan zarah tana kiran sunanshi, tsayawa yayi har ta karaso kusa dashi tace "yaya me kakeyi anan haka?" Kallon kin raina min wayau ya mata kan ya juya se kuma ya juyo "waye ba lafiya?" Tace cikin damuwa "wallahi besty ta ce tun da safe nake nan, baka ganta ba duk ta fige yini d'aya".
Tura baki tayi ta kara da "gashi yaya sauban ya ki barinta ta huta daga ta farka ze kuma yi mata wani alluran baccin wai tana bukatan hutu" girgiza kai yayi In I don't care tune yace "kina gayamin ni me nawa did I ask yhu?" Kuma turo baki tayi girgiza kai yayi ya juya ya fara tafiya bin bayanshi tayi ta rike hannunshi "pls Hamma ka shiga mana ka duba jikin nata baka ga ba da safe tana farkawa Kai ta fara tambaya ta zaci kayi class yau".
Tsaki yaja kan yace "zan sa'ba miki, wuce ma in kaiki gida" sakin shi tayi da wuri zatayi magana ya harare ta, "my handbag" ta furta kan ta koma d'akin ta sallami mama da se ci mata albarka take sbd abincin da ta sa aka sayo musu daga restaurant abincin da taga an kakkawo duk be mata kama da wadda mara lafiya ze yi sha'awar ci ba.
A yinin yau kawai da ta zauna da noor taga abubuwa kala kala da sukayi matukar bata mamaki suka kuma d'aga mata hankali daga wurin 'yan uwan noor d'in, duk wacce zata shigo se tayi bakar magana ko kuma gugar zana a fakaice dukda wacce akeyi da Itan ma bata san sunayi ba, abinda ya bata tsoro shine wacce taji ance itace kakar noor mahaifiyar babanta tace.
Wai ko de ciki ne da ita taga tayi wani iri lokaci guda, ba de abinda jama'a suke fad'amata akan Saude ne yake shirin tabbata ba, sam zarah bata ji daad'in maganan ba amma ba yadda ta iya tunda taga ba wadda ya tanka innar se ma masu kara mata petur, Ai ko tsohuwa kam ta kafe bazata tafi ba se taji gaskiyar alamari, zarahn ce taje ta kira wata nurse daga waje ta fad'a mata abinda zata gayamusu.
A tare suka dawo nurse d'in na kallon inna tace "mama dan Allah kuyi hakuri ku ragu ba'a son ana hayaniya akan mara Lafiya haka" ba yadda innar ta iya ne yasa ta fice tana sababi 'yan koronta suka bi bayanta su goggo saratu.
"Zarah!!" Firgigit tayi tana kallonshi yace "are yhu alright?" Tace "yes sure, akwai abinda ya d'auremin kai yaya da noor zan so jin labarinta" Shiru yayi na mintuna kan yace "wace noor kuma?" Tace "friend d'ina dake asibitinsu yaya sauban, yaya kullum tana cikin damuwa da naje gidansu nayi noticing abubuwa dayawa, and today abun yafi yawa".
"Yanzu ke a kankantar Kin nan har zaki sani if something is fishy? Toh fad'a min abubuwan da kikayi noticing muji" ya fad'a cikin son jin d'an wani abu da ya shafi damuwarta, ba 'bata lokaci zarah ta bashi labarin yadda minti minti noor zatayi maganan ummanta amma da taje gidan se taga ba haka ba, ta bashi labarin abinda ya faru again yau a gidansu noor d'in tsakaninta da umma, Inda ta d'aura da labarin yadda su inna da goggoninta suka d'inga misbehaving a asibitin yau.
She ended up with irin abincin da aka kawo mata, zarah yake kallo amma mind d'inshi na chan wani wuri daman, what could it be? Tabbas 'yan uwanta baza su d'inga mocking d'inta ba se in da akwai abinda tayi but har mahaifiyarta? Is this really serious?? Ta'ba shi zarah tayi yayi saurin gyaran murya yace "Hakane gaskiya akwai ayan tambaya anan, ni ba abinda zan iya mata sede In ce ki taya ta da adu'a ko menene matsalanta Allah ubangiji ya kawo mata mafita" Tace "In shaa Allahu zan taya ta".
Har zata fita yace "wait!! Nace In ba matsala se ki dinga sa maids d'innan abinci kina tafiya mata dashi" had'a yatsu biyu tayi suka bada sauti, tace "yess bro, yhu d best" girgiza kai yayi kan ya fita suka shiga gidan a tare, ummu dake zaune parlor tace "oh Ashe tare kuke" Abdul yace "Eh ummu naje wurin sauban se muka had'u a asibitin shine na dawo da ita dama nan na yo".
Ummu tace "madallah, auta ya kawar taki da jiki" Tace "da sauki sossai ummu, bari inje In watsa ruwa" har kasa ya duka ya gaida ummun kan ya mike ya zauna kan kujera cikin kasa da murya yace "ummu na gaji da halin hamna, kuyi hakuri duk hukuncin da zakuji na yanke for the first time a zaman mu da ita pls ki bani goyon baya" had'e rai ummu tayi tace "Kai magananka kenan kullum hamna kaza hamna kaza, haba me yasa ita bata kawo korafi kullum se kai?".
Runtse ido yayi hafeez ne ya iya cewa "haba ummu meyasa for the first time baza ki saurareshi ba? Kullum ita bata laifi a idonki duk irin rashin mutuncin da zata mishi? Tunda har kika ga hamma Abdul ya....." "dakata min!!! Ba da kai nake magana ba kuma ba akan matarka ake magana ba, dama dukkanku burinku kenan kuga tayi laifi ku aibatata kaman ba 'yar uwarku ba, me tayi nace?".
Abba ne da zarah suka sauko a tare tana bashi labarin kawarta da bata da lafiya, be yi magana ba seda suka zauna tukun Abdulraheem yace "maganin hana d'aukan ciki take sha" Abba da hafeez har zarah sukace 'what!!' Hafeez yace "yanzu duk son haihuwan da kakeyi da duk shekarun da kuka d'auka tare tana sane kuma take shan magani? Unbelievable!!yarinyar nan is unbelievable" shiru kawai Abba yayi zarah ma kasa cewa komai tayi se ma tausayin yayanta da ya rufe ta.
In har ka san Abdul to zaka san yana son yara waenda ze haifa a cikinshi ya nuna kuma yayi tutiyar nashi ne, amma bata kyauta ba kuma In har ummu ta hana yaya Abdul d'aukan mataki ta cuceshi, kai yanzu Abba ne ma ya kamata yayi magana, duk ummu suka zubawa ido suna jiran ta kareta yadda ta saba, cikin sanyin murya tace "anya?? Anya kuwa Abdul gaskiya kake fad'a" wani malolon abu yaji ya taso ya tsaya mishi a zuciya.
Yau ummu ke karyatashi sbd hamna aka ta'ba? Ita ta haifeshi ze iya bugan kirji yace duk duniya ba wata mace da ta sanshi irin ita, ta sanshi shi mutum ne straight forward kuma baya ta'ba yin karya ko kasheshi za'ayi amma kuma take karyatashi? Toh yayiwa hamna karya ya samu me? Mikewa yayi kar yayi magana ya aikata ba daidai ba, Ummun na kiranshi be tsaya ba ya fice Abba ya tashi yabi bayanshi.
Zarah ma haurawa sama tayi, haka hafeez ma ficewa yayi, Tashi ummu tayi ta nufi d'akinta yau ta tabbatar ta ta'ba family d'inta itama ta san bata kyauta ba amma kuma ya zatayi? Bata son 'yar uwarta guda d'aya tal a duniya taga bata rike mata 'ya tsakani da Allah ba, kiran hajiya umma tayi mahaifiyar hamna.
"Hello Adda ya kk? Ya gd?" Ummu tace "Lafiya kalau Ummakalthum hamna ta isa lafiya?" Hajiya umma tace "Lafiya kalau gata tana ta baccin gajiya" se kace a mota tayi tafiyan, umma tace "masha Allah, umma akwai abinda ya taso kuma gaskiya anan hamna bata kyauta ba, sbd me zata dinga shan maganin hana haihuwa da yarantarta In ta 'bata mahaifanta fah?".
Umma tace "Adda don hamna ta sha maganin hana haihuwa wani abu ne? Kiyi mata adalci mana dan Allah, tana fah running business Ina zata iya had'a business da renon yaro? And Ai bata ce bazata haihu kwata kwata ba" Shiru ummu tayi na seconds ita kanta ta san bata yiwa d'anta adalci ba amma se ta kasa yiwa 'yar uwarta musu tace "shi kenan zan san yadda zanyi da shi da mahaifinshi" umma tace "Toh gwara se anjima". Sallama sukayi.
"Babana" tsayawa yayi jin muryan Abba, murmushi ya d'aura a saman fuskanshi kan ya juyo "na'am Abba" Abba ya karaso tare da dafa kafad'anshi yace "kayi hakuri kaji? Sannan ka sani duk wani shawaran da ka yanke In har ba saki bane ko duka ina bayanka, ka hukuntata daidai laifinta na san halinka bazakayi abu ba tare da tunani ba, Allah yayi maka albarka".
Murmushi me kyau ya saki yace "Ameen Abbana na gode" kiran sallahn magrib da ake dokawa a massallacin kofan gidansu ne ya sasu nufan wurin flowers sukayi alwala daidai sun gama Hafeez ya fito suka rankaya massallaci duka, da aka idar zama yayi ya d'auki qur'ani ya fara karatu cikin natsuwa ba shi ya motsa ba har se da aka kira isha, yayi adu'o'inshi kan ya mike aka gabatar da isha dashi.
Alhamdulillah yaji saukin damuwanshi sossai, gida ya dawo ya d'auki motanshi ba tare da ya shiga ciki ba ya fice, direct asibiti yayi a hankali yayi parking a parking lot d'in female ward tafiya ya dingayi kaman me tsoron taka kasa har zuwa jikin windown d'akin