Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
a'a tsohuwa tsaye a tsakiyar kwalta, mutum kwance kasa kaman gawa, jaririn yaro yana kuka, mahaukaciyar mace ta nufi motanshi, dabbobi kala kala irin su mage, maciji, kare, damisa da zaki, duk be tsayawa second though yake bin kansu ya wuce Har akwai inda yazo yaga kwalta ta rabu mishi gida biyu katon rami tsakiya haka yabi ta kai se kuma yaga normal, kanshi har ciwon yake tsabar turirin zafin da zuciyarshi keyi amma haka ya daure ya cije yaci gaba da tafiya be tsaya ba seda ya ganshi cikin fufore wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ganinshi kofan gidan baba.
Unlocking motan yayi ya fito tare da kulle motan da ita a ciki direct babban parlorn baban bayan ya shige katon iron get na gidan, baba dake safa da marwa a parlorn yayi saurin nufoshi ya rikeshi "masha Allah, Alhamdulillah Abdulraheem kun samu isowa lafiya tana Ina?" Lumshe ido yayi ya bud'e baba ya ja shi ya zaunar dashi kan kujera ya dinga maimaita mishi wasu adu'o'i yanayi bayan ya gama ya mike ya d'auko wata galon na ruwa ya tsiyaya a cup ya mika mishi kar'ba yayi ya kafa kai ya shanye yana sauke kofin ya had'a da wata nannauyar ajiyar zuciya.
"Sannu" Kai ya gyad'a baba yace "Ina ita amaryar tawa?" Yace "baba tana cikin mota bari In d'aukota" mikewa yayi ya fita ya bud'e motar ya d'aukota a hannunshi wani almajirin baba ne ya zo da sauri ya rufe mishi kofan da dabara ya karasa da ita parlorn sanyin jikinta har shi karan kanshi ya fara damunshi daga waje zuwa cikin gidan Allah am ita kuma ya takeji ne? Ya ayyana a ranshi yana kwantar da ita kan doguwar kujerar parlorn.
Kanta baba ya karaso yana kallonta yace "hasbunallahu wani'imal wakeel, Lahaula wala quwwata illa billahilaleeyul azeem, Maaarid" ya kira sunan da mamaki, kallonshi Abdul yayi yace "baba marid kuma sunanta fa Saudah" wani karamin murmushi ya saki yace "Abdulraheem ba ita nake nufi ba, black demon d'in jikinta sunanshi kenan" ga wannan d'auketa zuwa d'akin hajja gana (babarbariyar matarshi ta farko wato uwargidanshi) ka shafa mata don farkawanta ba yanzu ba se in baka labari cikakke akan marid wani irin bakin mugun Aljanine sannan what he's capable of doing in dai har ka shiga taskunshi".
Kai Malabo ya gyad'a ya d'auketa ya fice da ita gidan katon family house ne matanshi hud'u kowacce da sashinta se yaranshi maza hud'u dake rayuwa cikin gidan suma duk sashinsu a cikin gidan yake, part d'in baba fuforen ne gaba wadda yake had'e da part d'in baki shima kuma d'akunan daban daban ne akwai waenda ya ware mussaman don su Abdul d'in da yake Hafeez ya Saba zuwa, part d'in hajja gana ya shiga da ita don tunda baba yace ya kaita chan ya san ta shirya tarbanta.
Ai kuwa suna shiga tana murmushi tace "lale maraba barkanku da zuwa, Sannu Lamid'o karasa da ita d'akin chan" murmushi yayi yana karasawa da ita ya shimfid'e ta kan shimfid'ad'iyar gadon da ya sha gyara ba abinda ke tashi part d'in tsohuwar In ba kamshin turaren wuta ba, yana murmushi yace "mun sameku lafiya?" Itama cikin fara'a da jin daad'in ganinshi tace "Alhamdulillah lamid'ona se yau Allah yayi ganinka?" Murmushi yayi kawai akwai sabo sossai tsakaninshi da ita tun suna yara tana musu so na tsakani da Allah in kuwa suka taka kafafunsu cikin gidan baba fufore se abinda suke so za'a yi, tayi ta haba haba dasu shiyasa suma suke sonta ya kai ta makka kusan sau uku.
Yace "hajja baba yace a shafamata wannan, gashi" ya mika mata mikewa tayi ta kar'ba ya mike ya fita dama tunanin ta yadda ze fara shafamata yake baze iya ba, baze iya takalowa kanshi abinda ya fi karfinshi a halin da take cikin nan ba, a duniya be ga macen da da kallo kawai me kyau In ya mata yanayinshi ke sauyawa ba irin Saudah, parlorn baba ya koma ya sameshi zaune yana duba wani littafi, gabanshi ya zauna kallonshi baba yayi yace "bazaka samu cin wani abu ka huta ba kan mu zauna tattaunawan? Kaga azahar ma tayi muyi sallah tukuna Ohk?" Da "Toh" kawai ya amsa yana mikewa da kallon tausayi baba ya Bishi yana ganin tsantsar damuwa shimfid'e a fuskanshi kuma ya tabbatar be wuce ciwon matanshi ba.
'Dakinshi na part d'in baki ya nufa a gyare tsab se tashin kamshin turaren wuta yake murmushi yayi ya tabbatar aikin hajja ne wannan shi yasa yake son tsohuwar har ranshi, ruwa ya sakarwa kanshi wani sanyi na ratsa zuciyarshi tausayi da kaunar matarshi fal ranshi da tunaninta yayi wanka ya fito nan tsakiyar d'akin yaga akwatinshi ya san baba ya sa aka shigo musu dashi, kananun kaya ya sanya bayan ya shafa mai turare kawai ya fesa ya fito sallah Don har baba ya tayar da ikama.
Bayan sun idar da sallah suka dawo parlorn shi abinci baba ya had'a musu da kanshi murmushi yayi ganin favorite d'inshi da ya jima be ci ba, shinkaface da wake da mai da yaji aka yanka salat da tumatur da albasa da dafaffiyar kwai akai se kifi, ya kuwa matso ya zauna da kyau ya amshi cokalin da baba ya miko mishi suka fara ci yana son baba kaman yadda yake son lamid'o dukda yanzu sarauta ya chanza lamid'on sossai ba kaman da ba, In har ance yau sunzo tare suke komai da tsoffin bacci kawai ke rabasu.
Sossai yaci abincin dukda tunanin Iman na makale ranshi bayan sun gama wani almajiri yazo ya d'auke kwanunkan gyara zama sukayi baba yace "Abdulraheem bani labarin matarka yadda zan iya gane tun wani lokaci marid ke tare da ita" gyaran murya Abdul yayi kan ya fara bashi labarinta tun daga farko har kawo yau tsoho mai matukar tausayi da imani se gashi yana hawaye, son Iman na shiganshi Allah sarki baiwar Allah, Aljani ya dad'e yana cutar da ita ba tare da masaniyarta ba.
Baba yayi gyaran murya bayan gama nazarinshi yace "Abdulraheem Ina tunanin mahaifiyarta ta San da matsalarta ta kuma san tun yaushene yake tare da ita itama Ina bukatar ganinta, bazan fara yiwa Saudah magani yau ba har se naji dalilin da yasa mahaifiyarta ta banzantar da rayuwanta bayan ta san tafi kowa bukatarta" Abdul yace "baba ba kuma abinda ze faru aka bar ta haka? Sannan baba abubuwan da na fuskanta yau duk sharrin wannan aljanin ne?" Baba yayi murmushi yace "za'a ci gaba da shafamata Jan miski da za'afaran me d'auke da adu'o'i wadda na bakan nan kan isowar iyayentan sede baza ta farka bane sbd an riga anyi noticing d'inshi jikinta da ba wadda ya gane ne zata ci gaba da rayuwanta normal sede matsalar aure sbd ya riga ya aureta da jimawa"
Da mamaki Abdul yake kallon baba dama aljani na iya auren mace tun daga yaranta har zuwa girmanta ba tare da ta sani ko wani nata ya sani ba? Baba ne ya katse mishi tunanin da cewa "ka dena mamaki sharrin aljani yafi karfin tunaninka musamman marid da yake na biyun ifrit a karfi da mugunta, sannan abubuwan da ka dinga ji ka dinga gani a yau kad'an kenan daga cikin sharrinshi Don ya san inda zaka zo, ze iya ci gaba da tsorata ka da irin muryan matar ka cikin kuka da neman agaji cikin dare ko ido biyu kuskure kad'an zakayi ta 'bata har buzunta In har ka kuskura ka taimaka mata wurin barin gidan nan daga yanzu so kayi kokarin ignoring duk wani magiyar me irin muryanta Don marid ba abinda baya iya zama.
Ka rike adu'a kar bakinka ya rabu da adu'a kaji? Sannan ka tsaya mata cikin dare da ibada da rokon Allah, Allah ubangiji ya bamu nasara kanshi" Da "Ameen thumma Ameen, in Shaa Allahu zanyi iya kokarina wurin taimakawa rayuwanta da ganin ta samu lafiya da dawammamiyar farin ciki dama tun farko abinda ya shigo dani rayuwanta kenan" ya amsa Shiru ya biyo baya chan dae Abdul ya fiddo wayan shi ya kira baba, kad'an ya mishi bayanin abinda ke faruwa ya tabbatar mishi su shirya hafeez ze zo ya d'aukesu ze fad'a musu time in yayi waya dashi, ta waya yayi booking flights biyu ya turawa Hafeez ta email tukun ya kirashi ya bashi tabbacin yayi booking flight na 10 from kano to yola gobe ya je gidansu iman ya d'auki iyayenta ya kaisu Airport ya tabbatar ya nuna musu komai be barsu a duhu ba kan su sauka ze yi magana da sarkin gida.
Amsawa Hafeez yayi a ladabce, sake kiran baba yayi ya fad'a mishi time da zasu taso, dukda tambayoyine fal ranshi sbd abinda ya fad'amishin be gamsar dashi ba amma haka ya amsa yana fatan duk wani abun da ze faru ba kuma mutuwar auren Iman bane ba, d'akin umma kawai ya Leka yace mata ta shirya zasuyi tafiya na kwana biyu gobe, dayake ta kasance Shiru shiru marar hayaniya da sawa kai damuwa tace mishi to kawai.
Anan yola kuwa su nenne Petel sunyi matukar mamakin ganin ummu sede baba galadima be tanka ba se kallon kin zubar da wayonki da yake mata seda ta musu bayanin Ai da izinin mijinta tazo baba modibbo ne ya nemi ganinta kan suka sassauta fuska suka amsa gaisuwarta seda ta mika gaisuwa har wurin mai martaba da nenne kan ta dawo shashinta tayi wanka ta kwanta tana tunanin me ya kawo Abdulraheem yola? Ba de karanta ya kawo ba, In ko haka ne zata ci mishi mutunci kuwa amma dae bari ta jira ta ji da wannan tunanin bacci ya d'auketa.
'Bangaren su hamna kuwa sun gama Shirinsu tsab ganin ba Iman da Abdul ma kwata kwata be damesu ba a ranar jawahir ta tare gidan suka bararraje koli umma Katuwa da ita cikinsu kaman wata sa'arsu.
****
Bayan ya gama wayan ya dubi baba yace "dan Allah baba modibbo wanene marid? Ya yake what is he capable of doing after all what happened today?" Murmushi baba yayi yana girgiza kai kan yace "maridd! Marid!! Marid!!! Hmm shi dae wani...............
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*045*
"Marid ana iya ce musu maradah "rebellious" kaman yadda suka zo a cikin alqur'ani me girma, cikin sura As-saffat Aya ta 7 (37:7) in da Allah mad'aukakin sarki yace "And to guard against every rebellious (marid) devil" marid suna ne na larabci ana iya ce musu giant a turance, suna da karfi they are said to be very arrogant yawancin rayuwansu sunfi yinshi a ruwa, kogi, fadama da duk wani gulbi ko hanyar ruwa ko inda ruwa yake, me kyau ko marar kyau, suna da hatsari very dangerous In aka ta'basu ko mutum ya shiga taskunsu.
Su ba aljanu bane da suke shiga bil Adama domin soyayya kaman jinnul Ashiq sede suna iya kasacewa jikin mace ba tare da ta sani ba kuma sannan suna hana mace jin daad'in rayuwa kaman yadda kowa ke yi, wannan na daga cikin hatsarinsu basuyi rayuwar soyayya ko na aure da mace kaman ashiq ba haka kuma basu barta tayi rayuwan da kowa ke yi ba, suna iya zama a jikin mutum har ya mutu suna kunta ta mishi ba tare da ya sani ba duk da wani sa'in laifin mutanen ne.
Marid marada a jimlance suna iya abubuwa dayawa kaman firewa(fly), dive, destroying abu komai girmanshi, jinsin aljanu ne da suke cikin waenda suka taimakawa Annabi Sulaiman (A.s) wurin kawo throne na queen of shibah, suna da kabila wato (tribe) suna da iyalai Don suna auren junansu su hayayyafa kaman mutane Haka kuma sune na biyun karfi da iko cikin jinsin aljannu In aka cire ifrit. Kaji yadda marid suke"
Cikin gamsuwa da bayanan baba fufore Malabo yace "Allah ya rabamu da sharrinsu" baba ya amsa da "Ameen" hira suka d'an ci gaba dayi baban na tambayanshi yanayin ummu yana bashi amsa anan ne ma ya fitar da abinda ke ranshi ya nuna 'bacin ranshi sossai akan abinda ummu tayiwa Iman kuma ji yake har lokacin ranshi be yi sanyi ba, baba ne ya katseshi da nasihohi akan girman iyaye sbd haka duk abinda zasu maka baka da abinyi se hakuri sede In sun haneka bautawa ubangijinka, "ba'a fushi da iyaye kaji" baba ya rufe da hakan, Kai ya gyad'a cikin gamsuwa nan suka ji ana kiran la'asar.
Sallah suka fita sukayi daga nan baba ya zauna rumfarshi na tsakar gida yara suka fara taruwa Don d'aukan karatu kaman ko yaushe, shi kuwa malabo ciki ya nufa direct d'akin hajja ya zauna suka fara hirar yaushe gamo dayake d'akin da ta sauke Iman yayi masauki minti minti se ya kalleta daga karshe ma hannunshi ya sanya ya kama nata ya riqe dukda sanyin da hannun yayi kaman ya fito daga kankara ko yana ciki.
Tsokananshi hajja ta dingayi wai ita tana kishi gaskiya itace baya sonta, sede yayi dariya kawai "ka kuwa shiga wurin mutan gidan kun gaisa?" Yace "a'a hajja" Tace "ya ko kamata ka tashi ka shiga In ba haka ba yanzu se kaji karamin magana ya zama babba" murmushi yayi yana mikewa yace "bari In gaishesu In zo kar su samin hajjana gaba" murmushi tayi ya fita me makon ya shiga cikin gidan se ya nufi waje ya d'auki mota ya shiga cikin gari.
Wurin da ake gashin kaza ya yada zango ya kuwa sayi dayawa har leda takwas ko wani leda kuwa kaji biyu ne ciki, se godiya me kazan yake cikin jin daad'in wannan ciniki, murmushi kawai yayi ya ja mota, gidan ya dawo ya dinga shiga part part suna gaisawa gidan se murnan ganinshi suke don malabo mutum ne me fara'a da son mutane in kaga yana rashin fara'a to yaga en mata ne musamman na jami'ar bayero. Duk inda ya shiga suka gaisa se ya ajiye musu leda d'aya, part d'in hajja ya shiga a karshe ya ajiye mata ledanta.
Godiya tayi mishi sossai, murmushi kawai yayi yace "Hajja ya kamata a cirewa Hayatee kayan nan a sa mata marar nauyi na san da idonta biyu tayi ta mitan ya takura mata kenan" murmushi hajja tayi tace "Toh kace mana kawai In baka wuri" dariya yayi yana dukar da kai fita tayi da ledanta a hannu, kallon iman ya tsaya yi cikin tausayawa da shaukin so yana sonta har be san adadi ba Haka kuma tausayinta, kab rayuwanshi be ta'ba tausayin mutum kaman yadda ya tausayawa Iman ba.
Trolley d'inta ya bud'e ya d'auki wani cotton dogon riga me karamin hannu ya nufi gadon, skirt d'in jikinta ya zame ya saura underskirt d'agota yayi jikinshi ya sanyata kirjinshi ya lumshe ido na mintuna yana shakan kamshinta me shegen sanyi da shiga rai.
Ajiyar zuciya ya dinga saukewa akai akai kan ya zuge zip d'in riganta a hankali tana kan jikinshi ya cire rigan da kuma bra d'inta be d'agota ba seda ya sanyamata rigan kan ya maidata a hankali yabi bayanta har seda ta kwanta da kyau hancinshi ya d'aura kan nata ya kuma lumshe ido har yayi kewanta a d'an yinin yau d'innan kawai, seda ya nisa Don kanshi ya mike ya gyara mata rigan kan ya zame underskirt d'in ya mike a kasalance ya nad'e mata kayan ya ajiye saman akwatinta, time ya duba shidda saura ya san zuwa yanzu baba ya sallami almajiranshi fita yayi.
A kuwa kan dardumanshi ya sameshi kishingid'e zama yayi gefenshi yana Jin karatun qur'anin da yakeyi, seda aka kira magrib suka mike a tare sukayi alwala suka fito massallaci bayan sun idar da magrib baba ya gyara zama ya fara bawa manya karatun littatafan da suka saba, murmushi malabo yayi a zuciyarshi yace shiyasa wannan tsohon be tsufa.
Matsawa yayi ya d'auki alqur'ani ya fara karantawa ba su suka mike ba seda akayi isha suka gabatar kan suka shige cikin gida suka ci abinci tuwo ne da miyan kuka da yaji man shanu da kyar ya iya yin loma biyu zuwa uku ba wai Don baya cin tuwo ba se Don tunanin Iman da baze iya barinshi ci ba, baba da ya fahimci haka se ya fara janshi da hiran ban dariya da dai wasu abubuwan a haka ya samu yaci kad'an ya wanke hannu.
Mikewa yayi yana cewa "baba seda safe" baba yace "da wuri Haka Abdulraheem?" Yace "eh baba Ina so In kwanta da wuri samun In tashi da wuri" baba yace "hakan ma yayi Allah ya tashemu lafiya" ficewa yayi zuwa cikin gida yayi ma hayateeenshi sallama kan ya fito yayiwa hajja seda safe ya nufi d'akinshi ya kwanta bayan yayo alwala Don baya son abinda baba ya fad'a ze iya zuwa mishi, hakan ya sashi saka qira'a a wayanshi ya kwanta dashi ba don tsoro ba se don za'a iya fooling d'inshi ya tabbatar In har aka zo maganan da ya shafi hayateenshi.
Washegari
Tun da asuban fari umma ta tashi su hamna da kyar suka tashi daga ita har jawahir, wanka sukayi suka shirya umma ce ta sama musu abinda zasu ci yayinda hamna tace ita ba abunda zatayi se mitan rashin zuwan kukunta take na kwana biyu, bayan sun gama ci suka fito ba tare da ko sun tuna suyi sallahn asuba ba drivern jawahir suka samu zaune cikin mota suka shige umma ta zauna gaba suka d'auki hanyar katsina, daga nan zasu shiga nijar abinda ya sa sukayi sammako Don su samu dawowa yau.
'Bangaren baba ma haka ya kasance da wuri ya tada umma ta shirya shima ya shirya me machine dake kai su ikhram school na zuwa ya d'aurasu kai ya mishi bayanin In an tashi yayi dasu gidan inna ya fad'a mata zasu d'anyi wata balaguru na kwana biyu, shi baban be son fad'amata ne sbd tsab zata iya hanashi kwanan nan kullum suka had'u magananta d'aya akan gidan Iman ya rasa me ta tsare mata yanzu da bata ganinta.
Karfe goma nayi Hafeez ya iso gidan ya d'aukesu suka fice direct se airport seda yayi musu komai ya kuma fahimtar dasu yadda zasuyi