Author : Fatima Muhammad Gurin Category : Romance
da jimawa”.
Tace “Tabbas duk wani matsalan rayuwana ya kau da taimakon ubangiji da kuma naka ban ta’ba zaton zan yi dariya ko farin ciki na tsawon awanni biyu zuwa uku ba seda ka shigo rayuwana, Ina sonka Ina kaunarka zaujiii, bani da tamkarka In ka gujemin wallahi zan illata” rungumeta ya kuma yi yace “har abada bazan iya gujemiki ba don In na gujemiki kaman na gujewa numfashina ne kiyi hakuri In har action na ya ‘bata miki rai ba yadda zanyi ne tunda ke kika nuna kina so to dole in sauke duk wani hakki nawa fara daga tun kan d’aurin aure” Tace “na fahimta zaujii ka taya ni adu’a please, ka tayani adu’a Allah ubangiji ya sassautamin kishinka nima zan taya kaina In Shaa Allah” bakinsu ya had’e ya fara sarrafata cikin zallar so da kauna.
Washegarin kuwa ya wuce nigeria sossai tayi kewanshi da kyar ta bar shi ma ya tafin sbd kukan da take mishi, randa ya isa washegari aka d’aura auren zahra kan aka mayar da aurensu da Hamna, da dare aka kaita gidanta wato gidanshi na nan kano sede a kasa yasa aka yi mata nata jeren yace sama na Iman ne kuma be son suyi shearing komai.
Yana kwance a d’akinshi ta shigo ta duka gabanshi ta fara neman gafararshi cikin kuka da komai haka de ta samu ya hakura ya yafe mata sede ya fad’a mata gaskiya ko da ze so ta baze ta’ba iya mata koda rabin so da yake yiwa Iman ba, sun raya sunnah a daren kaman ko wani ango da amarya, sede kwana yayi be rintsa ba kaman yadda Iman ma ta kwana ido biyu a kan sallaya shi abinda yafi komai dugunzuma mishi hankali shine rashin samun layinta yayinda ita kuma tunanin shi da wata macen ya hanata bacci da gangan ta kashe wayanta Don kar ta shiga hakkinta.
Aiko washegari ya fara shirin barin nigeria sbd har a washegarin bata kunna wayanta ba, daga ka ganshi zaka san yana cikin damuwa ko breakfast d’in da Hamna ta mishi be iya ci ba ya wuce gidansu Iman anan ne mama ta matsa mishi yaci kosai yasha kunu, ya samu kaninta me bin hafsy ya dawo ya kamallah secondary school d’inshi har ya fara degree a mutunce suka gaisa kaman yadda sukeyi a waya in Iman na waya dashi tun bayan dawowanshi, sako kowa ya bashi ya kai mata yayinda ikhram da ikhlas ke jin daad’in tsarabar da ya ciko musu yace inji Iman har su mama ko wacce da nata tsarabar da baba da su hafsy da umma duk yace Iman ce ta aikoshi dasu ya kuma tabbatar musu washegari da asuba ze tashi.
Aiko yana dawowa be wani zama da Hamna dake d’an janshi da hira ba ya wuce room d’inshi ya kwanta zuciyanshi fall kewanta, a daren ma haka ya kwana zaune asubar fari yayi wanka ya shirya dayake a daren yaje yayiwa ummu da Abba sallama ummu ta bashi sakon Iman yayin da Abba ya bashi sakon gaisuwa zuwa gareta be fad’awa Hamna tafiyanshi ba hakan yasa tana bacci ya ajiye mata sakon kud’i da short note akan ya tafi.
Yana sauka london ya wuce gidanshi a parlor ya ajiye kayanshi ya karasa d’akinta da sassarfa kwance ya hangeta akan gado tana bacci wani irin wawan runguma ya mata da seda ya firgitata ganin shine yasa itama ta rungumeshi tana jin daad’in ganinshi sakinta yayi yana ‘bata fuska kaman ze yi kuka yace “nayi fushi ma kina nan ke hankalinki kwance kina sharar bacci yayinda ni kuma kika hanani runtsawa” rungumeshi tayi tana murmushi yace “seriously kin d’aga min hankali please karki sake haka kinji? Allah ne kad’ai ya san halin da na kwana jiya da shekaranjiya” bata amsa shi ba se had’e lips d’insu da tayi ta fara aika mishi da zazzafan sakonni da ya sashi rud’ewa ya manta kowa da komai sakon da shine malamin amma ta fishi kwarewa a yau wani irin soyayya ta nuna mishi me tsayawa a kahon zuciya, ranan har rasa kalmar soyayyar da ze mata taji daad’i yayi, washegari motarta da ta za’ba tun a nigeria ya iso har colorn sossai ta ji daad’i tayi ta mishi adu’a.
Haka rayuwarsu yaci gaba da tafiya har ta shiga watan haihuwanta sau d’aya yaje nigeria shima da umarnin ummu da Abba don yaki sam hamna ta biyoshi itace me kokarin kiranshi don in ta biye ta tashi se juma’a juma’a yake d’aga waya ya kirata yasha fad’amata shi bafulatanin mutum ne yana da yafiya amma baya da mantuwa hakan yasa har yanzu ya kasa goge bad image d’insu a fuskanshi shiyasa aka ce ka aikata aiki nagari Don mutane su dinga ganinka dashi ba mummuna da zasu dinga zaginka a bayanshi ba koda kuwa ka tuba, tana zaune office d’inshi tana duba wasu books na psychology kawai taji abu ya soketa a baya gyara zama tayi ta ci gaba da karatunta kaman an tsikareta a lokaci d’aya mararta ya amsa cikin rudewa tace “wayyo Allah na” da sauri ya kalleta yace “Lafiya Hayatee?” Tace “I think our baby is coming” Da hanzari ya mike ya kamata suka fito zuwa mota kan su isa asibiti gabad’aya ta rud’e ta rud’ashi tana kuka yana mata Sannu kaman shima yayi kukan da gudu aka kar’beta zuwa labour room cikin sa’a bata fi awa ba ta santalo yaranta ‘yan biyu mace da namiji.
Ranan taga tsantsan farin cikin da bata ta’ba gani ba a rayuwanta a fuskanshi har kuka yayi adu’a kuwa har ta rasa adadin da ya mata, hotunan yaran na shiga wayanshi seda duk wadda yake da contact d’inshi ya samu yaran kyawawa kamansu d’aya da mahaifinsu ba abinda suka d’auko nata, a ranar ummu, mama, zahra, nenne petel da Anty rahama suka fara shirin tafiya sbd fir yace bazasu nigeria ba.
Hamna ta so zuwa sede In ta tuna yace mata randa ta sa kafanta ta bar nigeria zuwa wani kasa a bakin sauran igiyanta In ta kuwa had’ashi da mahaifiyarshi nan ma a bakin igiyanta d’aya dake hannunshi dukda tayi hankali sossai yanzu tana aiki ba business ba Sannan ta shiga makarantar koyon girke girke ba girkin da bata iya ba ta kuma nemi yafiyar ubangiji kullum tana kai In ta tuna yanzu Ina abokan sheke ayarta umma da jawahir? Umma tayi mutuwar wulakanci yayinda jawahir ke chan a kulle sbd sharrin da wani alhaji ya mata na kashe matarshi Bayan shi ya kashe ta sbd ta ganshi da jawahir suna aikata masha’a sbd kar ta tonashi ya fad’i a siyasa yasa ya mayar kan jawahir, ya kuma sa mata miyagun kwayoyi a jaka da bindinga nan take aka mata d’aurin rai da rai, ita kad’ai ta saura wacce Allah ya nufa da shiriya shiyasa halinta na yanzu ya zama daban da na da, sede ta kasa daraja a idanun mijinta kasancewarshi marar mantuwa kuma tun da chan ba wai sonta yake ba asiri ne yasashi aurenta.
Gidanta ya cika makil da en uwa don musamman nenne ta bada jakadiya aka taho da ita tace bazata koma ba se tayi arba’in ta had’o ta da duk wani abinda me jego zata bukata na lafiyanta da dawowar duk wani ni’ima da ta rasa yayin haihuwa mama ma ta taho da nata haka ummu ma, ta zama wata er gata se shagwa’ba take zubawa son ranta ranan suna yara suka ci sunan ummu da modibbo, Rashida da Abubakar inda zahra da take da karamin ciki itama yanzu ta sa musu inkiyan ziyad da ziyadah.
BAYAN WASU SHEKARU
“Ziyadah bance kiyiwa Aaman, Aayan da Asad wanka ba?” Cikin shagwa’ba da harshen turanci tace “Ammiey please jakadiya should bath them I’m busy with my assignment now” Iman tace cikin fad’a “Ina wasa dake ne? Jakadiyar sa’arkice? Kin wuce kin watsa ma yarana ruwa ko se na mareki Sannan In sake miki magana da hausa ki mayar min da wannan yaren nasaran kiga yadda zanyi dake” mikewa ziyadah tayi tana turo lips d’inta irin na ubanta ta nufi room d’in yaran tana shiga tace “boyssss” ihu suka yi suna cewa “yessss sister” tana murmushin son kannen nata tace “it’s time for bath” ihun first, second and third ne ya cika d’akin girgiza kai Iman dake saurarensu tayi ziyad dake zaune ta kalla tace “se na ce kaje suna fitowa kana shirya su ko?” Mikewa yayi ya shige d’akin en mazan shi d’akinshi daban haka Ziyadah ma, in tayiwa d’aya yana fitowa zai shiryasu ya shafa musu mai da perfume.
Iman bata musu tashin sangarcin kasan waje ba ta musu tarbiyya kaman ba wata kasan suke na turawa ba Sannan ita a tsarinta bata musu turanci duk wadda ya mata turanci kuwa ze sani ne, ziyadah da ziyad na shekaru bakwai yanzu yayinda Aayan wadda yaci sunan me martaba Muhammad ke biyar, Aaman wadda yaci sunan babanta na uku yayinda Asad wadda shekara d’aya ne kawai tsakaninsu da Aaman wadda yaci sunan baba galadima Abdulraheem kuma sunan mahaifinsu, a kullum Malabo alfahari yake da sama musu uwa ta gari me kula da duk wani motsinsu tun haihuwanta na farko suka amshewa nenne jakadiyarta ta zama nasu har tsawon wannan shekarun bata koma ba.
Su da nigeria sede zuwa a wani zuwan da sukayi ne Allah yayiwa inna rasuwa Bayan ta roki yafiyar Iman, iman ta yafe musu gabad’ayansu tun da jimawa tunda suma ba yin kansu bane, har yanzu Allah be ba Hamna haihuwa ba kuma zamansu da Malabo har yanzu kaman da ba wani soyayya sede zaman hakuri da kyautatawa kaman da se yayi wattani biyar be je ba, akwai lokacin da Iman tayi niyyan ba Hamna Asad firrrrr Abdulraheem yaki yayi maganan da ya ‘batawa kowa rai dayake a lokacin sunan zahra ne kowa na nan har ummu, har seda Iman tayi danasanin fara maganan cewa yayi “Ina me rantsuwa da mahallicina ba d’ana guda da zan bata saudah a lokacin da nake son ta haihun ba pills tayi ta sha har ya ‘bata mata mahaifa ba? Aka gayamata anayiwa Allah dabara ne? Aka gayamata se abinda take so Allah zeyi ne?” Yana kai nan ya juya ya fice tayi kuka sossai gashi da gaske mahaifarta ya lalace ta tuba ta tuba har ta gaji, Allah be bata daman haihuwa ba Sannan be had’ata da mahaifinta ba har rana yi tayau (Allah ka rabamu da aikin nadama, Ya kamata mu fara nazartar abu tun kan aikatashi wani laifin ko ka tuba waenda suke tare dakai bazasu ta’ba mantawa ba).
Haihuwan zahra uku, Amaturahman, Abdulraheem da kuma Abdulwaheed, kawancensu da iman se abinda yayi gaba ba abinda ya ragu dukda basa kasa d’aya, zuwa yanzu Iman ta gama phd d’inta itama lecturing takeyi anan kings collage sbd fita da tayi da result me tsananin kyau, itace ke d’aukar duk wani d’awainiyar gidansu iyayenta na matukar alfahari da ita, yanzu haka wani cikin ne da ita dukda ita bata son wannan haihuwan na wabi amma ya ta iya zaujiin ta na tsananin son yara.
Asad ne ya fito da gudu yana mata gwarancinshi Allah ya taimaketa ma nononta me kyau ne yaranta na saurin tafiya da magana, kamashi tayi ta d’aurashi jikinta tace “my boy wa ya ta’bamin kai?” Kur ya mata da idanunshi da suke irin nata ba brown irin na mahaifinshi ba cikin gwarancinshi yace “ciccha” dariya tayi kan tace “oh sister ko? Toh zan yi maganinta se na Zane ta, ko kar In zaneta?” Kai ya gyad’a tayi murmushi tace “ashe kana son sisternkan” Aaman ne ya fito shima cikin kayanshi na bacci yana tura baki tace “ziyad ko?” Se kawai ya fashe da kuka dariya ne ya kamata ganin yadda yake wani ta’be baki kaman Asad tace “Kai kuma da wa fad’amin” yace “big bro ne ya talle min keya wai kato dani se an wani shiryani In ba sangarci ba”.
“Lalala” ta fad’a tana kama baki kan tace “biyu, karka damu zan rama maka” Aayan ne ya fito karshe shikam dama baya barin ko ta kwana shiyasa yafi kowa shan duka a wurin yayyun nashi ga taurin kai, yana fitowa yace “Ammiey am so hungry!!! Wayyo yunwa ze kasheni” dariya ta ci gaba dayi Allah ya gani tana son yaranta sossai, ziyad ne da ziyadah suka fito last suna tafiya suna magana suna dariya da alamu wani gulman suke, kallon Ammieyn sukayi da take cewa “oya a wuce dining it’s time for dinner”.
Duk dining sukayi ta mike da kyar tana cewa jakadiya “sannu da aiki” tace “khaih Ammiey se kace wani aikin kirki ne nayi” dariya tayi tana cewa “kema bakin yaran kika d’auka kenan, bismillah zauna mu ci abinci” zama tayi tana cewa “ba dole ba yaran da suka koyamin turanci karfi da yaji wai su basa son hausa” iman tace “dole kuwa su so don ubansu yaren uwarsu kenan” tayi maganan kasa kasa yadda bazasuji ba daga bayanta taji ance “Allah sarki ubansu de ya shiga uku” ihu sukayi da sunanshi “Abbieyyyyyy” sukayi kanshi suka rungumeshi yana rungume dasu yace “oyoyo my boys” tura baki ziyadah tayi kan ta kalli cikin iman tace “lil sis we are mad at Abbiey right?” Yace “oh my princess what have I done wrong?” Tace “you only know your boys not us” iman ne ta katseshi da cewa “zaujiii dan Allah ka musu hausa” kallonta yayi kan ya kashe mata ido d’aya ya juya kan ziyadah yace “so sorry my only princess oya come and hug daddy” da gudu tazo ta rungumeshi.
Bayan sun gama cin abinci aka dasa kallo chan yaran sukayi bacci ziyad da ziyadah ne sukayi wahalan kaisu makwancinsu kan kowanne ya wuce d’akinshi dama jakadiya ta jima a d’akinta, kashe kayan wutan yayi kan ya d’auki matarshi chak se d’aki a gado ya kwantar da ita fuskanshi cikin wuyanta yana shakan kamshin turarenta me daad’i yace “ya kamata mu gaisa da lil princess kwana biyu bamu gaisa ba” waro ido tayi tana salati tace “ohhh Abbieyy fad’i gaskiya dae” yace “karya nayi kenan” tana dariya tace “na isa?? Ban isa cewa hakan ba amma fah ko ita zata fad’i gaskiya da safen nan taji d’umin mahaifinta” yace.
“I don't know what would I do without you in my life. Your eyes, se ya shafa idanuntan, your smile ya shafa lips d’inta da babban yatsanshi and the way you look at me makes me feel like I am living a sweet dream. Ya fad’a yana kissing eyes d’inta, I don't want to even imagine living a single moment without you. Kin cika min rayuwa da soyayyarki you complete the puzzles of my life, Kin ban yara kyawawa masu sani farin ciki a ko yaushe, banda abinda zan saka miki hayateee, I'm so much in love with you my dearest wife and I will always be for ever and ever”.
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke kan tayi kissing lips d’inshi kad’an tana kallonshi da idanunta da ta narkar dasu tace “I wish there was nothing else in the world to do except for losing myself in your eyes. I could continue doing that for the rest of my lifetime. You gave me everything I wanted. You taught me everything I needed to know. You helped me with everything when I was down. What more can I ask for? I'd rather replace my words of love for you with kisses of love. It's a much better deal, isn't it?” Ta karasa tana kashe mishi ido.
Wani wawan runguma ya mata har seda tace “washhh my baby” dariya yayi yana cewa “our baby da....” sailing bakinta da nashi da tayi ne ya hanashi uttering wani word suka fad’a duniyansu na masoya.
Toh Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Anan na kawo karshen wannan littafin nawa na NOOR IMAN abinda na rubuta daidai Allah ubangiji ya bani ladanshi abinda nayi kuskure kuwa Allah ubangiji ya yafe mini.
Na gode Na gode Na gode kwarai da kaunarku ga wannan littafin bani da bakin gode muku sede In ce “JAZAKUMULLAHU BILJANNAH AL-FIRDAUS” musamman:-
ANNUR HAUSA NOVELS
NOOR IMAN FANS
MU KARU DA JUNA GROUP
MY WATTPADIANS🥰🥰
Dama sauran groups da suke karanta Novel d’innan.
Ina kaunarku sossai Allah ya sadamu a wani book d’in da rai da lafiya Son So.
🖤GUREENJO🖤