NOOR IMAN Bayan Rufaffiyar Kofa By Fatima Muhammad Gurin

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   15 / 44

42K to 45K   out of 131.7K words

ba kuma a haka nake so ya aureta, sannan ku shirya daga ke har kubra da kika hanata komawa gidan mijinta zamu wuce yola gobe bayan d'aurin aure a chan za'ayi buki" ummu tace "yanzu ka san ita d'in karuwace? Ka san ta zubar da ciki sunfi biyar? Ka san irin asirin da ta dingayiwa tsoffin mazajenta tana juyasu son ranta ta rabasu da iyaye..." cikin tsawa Abba yace "enough Rashida bana son kara jin irin waennan kalmomin akan Iman dukda ban ta'ba ganinta ba am very sure yarinyace me kamun kai da ilimi ga tsoron Allah tunda har ta iya tsallake wannan bakar kaddara, so na fad'amaki abinda zakiyi In baza kiyi ba fine".

Ya maido da kanshi kan Abdul da yake ta kallon ummunshi gaskiya an chanza mishi uwa ba haka take ba sam, yace "kana ganin events ukun ya wadatar?" Abdul yace "Eh Abba samun mu dawo da wuri kaga tana school kar a tsayar mata da karatu" kuka ummu ta saka musu cikin tashin hankali Abdul ya mike yana furta "ya subhanallah, ummu dan Allah kiyi hakuri kiyi Shiru hawayenki ba alkhairi bane a gareni karkiyi min haka" ya karasa a karye tace "toh ka za'ba ko umarnin mahaifinka ko nawa? Na rantse da Allah kana auren yarinyar nan Abdulraheem bazan kara koda kallon inda kake ba har duniya ta nad'e kuma sena tsine maka albarka, so yanzu se ka za'ba ko ni ko ita?".




*Anjima da dare zaku samu wani In shaa Allahu, Amma fah se na ji ra'ayoyinku*



                       🖤Gureenjo🖤


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
           •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*


💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                           *023*

"Ummu" ya furta muryanshi na rawa ta daka mishi tsawa "just choose I said!!" Wayanta ne ya d'auki kara hakan ya sa ta maida hankali kai Abbu ta gani da sauri ta d'aga ta d'aura a kan kunnenta se jin muryanshi tayi cikin fushi da fad'a yana cewa "Abinda kike yiwa mijinki da 'ya'yanki kenan dama Rashida?" Cikin kasa da murya tace "Abbu ba fa haka bane ba yarinyar da za..." tsawa ya daka mata "shut up!!! Toh bari kiji da kyau ina me miki rantsuwa da Allah duk kika tilastawa Me suna ya za'beki a kan matar da yakeso na cire ki daga cikin 'ya'yana sede ki nemi wani uban, kuma rashin kunyar da kika d'auka kika yafa wadda ba halinki bane ki ci gaba karki fasa ki bari mijinki ya sake kawo min kararki zanzo har kanon In sa'bamiki a gaban 'ya'yanki In yi dawowa ta don kin haifi samarin 'ya'ya ba shi ze baki lasisin 'bata tarbiyarki da mai da kanki wata kabila ta daban ba".

Me yasa ba wadda ze fahimceta ne? Me yasa take ji kaman In Abdulraheem ya kara aure mutuwa kawai zatayi? bata san sadda ta fashe da kuka ba, se jin muryan Nenne petel tayi tana cewa "Haba rashida ke da kike da tunani da hangen nesa me ze sa kiyi tunanin hana d'anki kara aure bayan ba haramun bane a addini? Ko aka gayamiki don yana auren 'yar uwarshi se baze auro wata ba? Ke fa ba yarinya bace meyasa rashida ba'a ji kanki da mijinki tun kina yarinya ba seda kika girma kika mallaki fiye da hankalin kai? Kar ki 'bata wayonki na gayamiki wannan ba yi bane, and ki sani kaman yadda mahaifinki ya fad'a matukar kika yi sanadiyar da yasa yaron nan fasa aurenshi to ki nemi wasu iyayen ba mu ba". Se ta kashe wayan.

Kuka sossai ummu ke yi wadda yasa Abdul jin hawaye ya cika mishi ido. Yanzu shine sanadiyar hawayen mahaifiyarshi? Takawa ya farayi a hankali ze je gareta se Abba ya mishi hannu da ya fita, fita yayi Abba ya tashi yaje kusa da ita ya zauna tare da sa hannunshi ya kamo nata se kawai ta kwanta jikinshi ta kara fashewa da wani kukan, bayanta ya dinga shafawa a hankali da alamun rarrashi, Mamakinta sossai Abba ke yi, me ya samu rashida haka? Ba haka take ba, ta d'auki abinda ba shine ba ta d'aurawa zuciyarta, tabbas da ze iya da ya hana Abdul aure sbd kwanciyar hankalinta amma kuma Saudah d'in fah?.

Da kyar ya samu tayi shiru jin ba kukan yasa shi zame jikinshi yace "ki shirya akwai tafiyarmu yola goben, bayan d'aurin aure amma mu nan flight zamu bi da amaryar se 'yan uwanta su bi mota" Kai ta gyad'a mishi kan ta mike ta fice.

A inda ya barsu nan ya fito ya samesu zarah na kallonshi ta san ba Lafiya ba don idonshi ya kad'a sossai fuskanshi yayi ja abinka da farin namiji, goshinshi ya fito da wani jijiya babba, Anty rahma ta mike tana cewa "Lafiya kuwa Abdul?" Zarah tace "me ya faru Hamma?" Ko kallonsu be yi ba ya fice daga parlorn, da sauri zarah ta bishi har ya d'aura hannu akan handle na mota ta d'aura hannun ta akan nashi kallonta yayi da alamun gargad'i.

Ta dukar da kanta tace "yhu can't drive in this situation, plz let me drive" sake mata handle d'in yayi ya bud'e baya ya shiga, shiga itama tayi ta danna button d'in key tare da jan motar gate man ya bud'e mata ta fice, har suka isa gidanshi kanshi na jikin kujera yana son mahaifiyarshi fiye da zato ko kad'an baya son abinda ze bakanta mata rai amma gashi yau shi ne yasa iyayenta yi mata fad'a harda barazanar tsinuwa da girmanta.

"Idan ummu ne kayi hakuri Hamma ka kara mata lokaci tabbas Ina matukar zargi da kokonto kaman ba haka kawai ummu ke abinda takeyin nan ba, duk don da takeyiwa hamna ta san daidai ta san akasinshi, kar pressure d'inta ya sa ka fara dana sanin aikata aikin ladan da kayi niyya, haka karka manta komai rubutacce ne ko kana so ko baka so, ko ummu na so ko bata so kai ko duk duniya suka taru suka ce basa so In har Allah ya riga ya rubuta ba yadda aka iya, so dan Allah karka tsani kawata" ta bud'e motan ta fita d'ankwalin kanta ta warware tayi gyale har ta fara tafiya ya fito yace "Auta" ta juyo ya nuna mata motan alamun ta d'auka tare da kakaro murmushi ya sakarmata be kara kallon inda take ba ya shige gidan.

Dawowa motar tayi ta shiga tare da ja ta fice, Bata ma shiga gida ba Anty rahma ta fito da akwatinta ta shiga motar tare da cewa "kaini Airport kawai zarah" jan motar kuma ta sake suka fice Shiru duk sukayi chan de Anty rahma ta fara bawa zarah labarin abinda ya faru kaman yadda Abba ya sanar mata, zarah tace "da be kirasu ba ai yanzu ya karawa ummu tsanar iman" Anty rahma tace "ke wai meyasa damuwanki iman ne kawai bakya tunanin akwai abinda ya faru da ummu? Haka take?" Shiru zarah tayi yanzu Anty rahma ranta 'bace yake In tace zata ci gaba da magana ba karamin aikinta bane ta maketa, har suka isa Airport ba wadda ya sake magana, seda taga tashinta kan ta juyo kan motan ta nufi hanyar gida se kuma ga kiran Nenne.

'Dagawa tayi da sallama "wa'alaikissalam Fatima zan turo miki isassun kud'i yanzu Ina so ki samu best designer da take da ajiyayyun gowns da za'a iya sayawa Saudah se kije ki d'auketa ku za'bo size d'inta. And plz look for a presentable gown, ba na shirme ba kinga abin ya zo urgent ba wani d'inki za'a jira ayi ba" zarah tace "Toh nenne amma fah ita iman bata san waye mijin ba bakya tunanin hakan ze sa ta cikin damuwa In ta sani tun yau?" Nenne tace "ko me zatayi ai ba za'a fasa auren ba so do as I say."Zara tace "yes ma'am" nenne ta kashe wayan, searching contacts d'inta tayi ta lalu'bo numbern Maymz kawar Anty kalthum ce so suna da contact d'in juna.

Bayan ta d'aga sun gaisa tace "Ermm Anty Muna da Amarya ne kuma a gobe zamu wuce yola so muna son wasu sets d'in wedding gowns daga gareki Allah ya sa za'a samu?" Tace "Eh I think za'a samu zuwa de gobe karfe bakwai kaman guda nawa and colors da size?" Zarah tace "kaman biyar I think yanzu haka ina hanyar gidansu amaryan ne zamu zo wurinki yanzu se a d'auki measurement d'inta" Tace "Ohk se kunzo and ki tambayi events d'in sbd mu san yanayin gown d'in da za'a bata" zarah tace "Ohk se mun zo" suka datse wayan, nenne ta kuma kira "hello nenne nace events d'in me da me dame za'ayi?" Nenne tace "na sa a fara de shirin walima gobe da yamma In kun zo se dare ayi dinner washegari da safe se ayi sukuwa bayan nan se su tare a part d'inshi na nan in yaso daga baya ya tsara yadda zasu koma".

Sallama sukayi ta kira Anty kalthum "Anty if possible plz mu had'u malabis zamu za'bawa iman dresses d'inta na events" Anty kalthum tace "Ohk toh ganinan zuwa" suna kashe wayan zarah na parking kofar gidansu iman, da sallama ta shiga ta samu mama ma bata nan se umma suka gaisa bata tambayeta iman ba kawai ta shige d'akin Mama nan ta sameta kwance akan gado ta takure kan gado wai gobe ake aurenta amma ba kowa gidan nasu kaman gidan mutuwa.

Tun d'azu Mama ta fice ta gayamusu angon ya turo a fad'awa baba cewar gobe da asuba kan a d'aura aure a had'a 'yan uwan amarya da zasu d'auki people choice biyu nauyin kud'in mota da abinda zasu ci duk yana kanshi kar su samu damuwa duk wadda zashi kawai ya shirya, dukda baba yayi mamaki da aka ce people choice biyu kuma Adamawa bayan uban yace basu da kud'i talakawa ne amma se ya share duk abinda za'ayi ayi ruwansu ya ayyana a ranshi damuwanshi kawai a d'aura auren.

"Iman lafiya kike?" Iman tace "wallahi zarah kaina ke bala'in ciwo na rasa inda zan sa kaina zarah zanyi aure ban san miji ba ban san 'yan uwanshi ba, 'yan uwana ba wanda ya damu se ma matsuwa da sukayi da ayi aure a tafi dani su huta, zarah Angon fah cewa baba yayi baya bukatar ko tsinke a kai mishi me makon baba ya Musa ko yaji ba daad'i se daad'i ya dinga ji yana ambatun kud'inshi ya huta, zarah abinda za'aci In an zo bukin ma kin saya yayi wai be gayyaci kowa ba amma da angon ya turo buhuhunan abinci se gashi da kanshi yake gayyatan 'yan uwanshi" tana maganan ne tana kuka duk In ka ganta zaka san a firgice take.

Rungumeta zarah tayi tana dinga shafa bayanta "is Ohk besty, is okay komai me wucewa ne kuma Ina miki albishir da kiyi farin ciki mijinki irin mijin da kan a sameshi se an taki sa'a ne, zan iya cewa duk cikin 'yan uwanki ba wacce ta auri irin mijin da zaki aura, ki dena damun kanki Ina tare dake haka kuma na san mijin da zaki aura baze ta'ba bari ki zubda hawaye ba" Da sauri iman ta d'ago "kin san shi zarah?" Zarah ta gyad'a kai "waye ne shi? Plz gayamin?" Zarah tace "Abdulraheem Ahmad malabo" wani irin hantsulowa Iman tayi idonta kaman zasu fad'o tace "Fatima dan Allah ki gayamin In da gaske kike?".

Zarah tayi murmushi tace "wallahi da gaske nake yayana zaki aura, so damuwa ya kare yanzu kin san mijinki ba wani me mummunan hali bane and plz ki barshi a ranki karki gayawa kowa kar ki nuna kin san mijin don ban yarda da 'yan uwanki ba sorry to say kema kin sanni abinda na san shine gaskiya ta nake gayamiki" iman de har yanzu shock d'in be sake ta ba, zarah ce ta lalu'bo mata hijab ta sanya saman doguwar rigar material d'in jikinta ta janyo hannunta ta cewa umma "umma mun fita" umma de bata amsa ba se idon da ta bi su dashi.

A mota ta sanyata itade ta shiga, tana shiga kuwa seda ta san motan na waye don kamshinshi ba boyayye bane sam, ita Allah ya gani bata san me zatayi ba, bakin ciki ko farin ciki? Gatanan de kaman mutum mutumi zuciyarta sam ba tunanin komai har suka isa malabis bud'e baki kawai tayi tana kallon wurin da irin designers gowns da suke wurin kaman ba mutum ke d'inkawa ba.

Sun samu Anty kalthum ma ta rigasu isa iman na ganinta ta gane 'yar uwarsu zarah ce sede bata san ko rahama bace ko kalthum seda taji zarah tace "Ina yini Anty kalthum" kanta na kasa itama ta gaidata murmushi Anty kalthum tayi kan tace "masha Allah Amaryarmu ta had'u" zarah tace "Ai kuwa fari kawai Anty hamna Zata nuna mata" wayan zarah ne ya fara kara ta d'auko ta kalli fuskan ta kalli su Anty kalthum tace "Ango fah ke kira" kan ta d'aga "salamu alaikum hamma" yace "kina Ina ne?"

Ta mishi bayanin inda take da abinda sukeyi se taji yace "nima abinda yasa na kiraki kenan, ba wa maymz d'in wayan" mika mata tayi suka gaisa kan yace "ermm plz ki had'a mata da wrappers d'in da zata sa a gida ba wedding gowns d'in Kawai ba, and bana son anything zani yeah, ehmm something like skirt and gowns and bana son atamphopi masu saukin kud'i".

Cikin ladabi ta amsa mishi ya kara da "just send me the bill through this number" ta kuma amsawa kan ta dinga godiya suka tsinke wayan da yake a handsfree yake su Zarah sun ji komai kallon juna sukayi da Anty kalthum suka sake shewa zahra tace "amm bana son anything zani yeah, something like skirt and gown" tayi maganan da yanayin accent d'inshi suka kwashe da dariya yayinda Iman taji kaman ta nitse cikin kasa.





  
                    🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
           *Gureenjo6763 on Wattpad*


*'yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this is dedicated ta ANNUR HAUSA NOVELS a gaskiya Ina matukar jin daad'in comments d'inku irin sossai d'in nan ga wannan page d'in kyauta ne kuyi yadda kuke so dashi naku ne, Allah ya bar zumunci and 🚎🚎🚎🚎🚎 ga motocin fah da zasuyi yola an kawo inji Abdulraheem duk wadda ya shirya yazo da jakar kayanshi kar ayi babu shi😅😅*

🛩🛩wannan kuma yace na 'yan MU KARU DA JUNA Ne yana son ganin khadija Queen a gaban jirgi da kawata ta jikin window🤣🤣


                          *024*

Nan fah suka za'bi matching colors duk abinda suka san zasu bukata basu manta ba sukayi list ta had'a kud'in gabad'aya ta turawa Abdul ba'ayi minti biyar ba alert ya shigo mata, ta kirashi tayi ta godiya ta tabbatar kuma bazata bashi kunya ba In shaa Allahu duk kayan da zata had'awa iman se ya so su, Anty kalthum ne tace "Toh zarah kud'in da nenne ta turo d'in nan bakya tunanin mu saya mata jewelries da shoes and pose da su? Tunda kinga dae Anty rahma se jibi zata dawo bare ace a jira na lefe".

Zarah tace "hakane Anty akwai wani jewelry store nan kusa da nan shagon muje wurin suna da d'an kunne masu kyau da tsada dukda ba gold bane amma basa fading" mikewa sukayi iman de bata iya ko d'aga kai, har kasa maymz ta rakasu suka wuce, Da kafa suka taka suka fad'a shagon zarah da Anty kalthum de se hirar bukin sukeyi suna jin haushin ya akayi yazo a kurarren lokaci Ai da ba Haka
Ba, zarah tace "donma fatan Besty fresh ne be da wani ta'bo ko kuraje da Ai an samu matsala Amarya ba gyaran jiki" Anty kalthum tace "Ai kuwa, kuma na tabbatar se nenne ta sa an mata na kwanaki biyun nan da zatayi a part d'inta kuma na san zatayi kyau".

Juyawa tayi ta kalli iman tace "kinga bestyn Auta kuma matar yaya ki dena jin kunyana plz ki sake muyi hira" murmushi kawai iman tayi zarah tace "hmm Ai kan ta sake dake se kina da fitina da irin surutu nawa" Anty kalthum tace "kenan nima surutun zan d'inga mata har ta sake don bana son wannan kunyan, kuma In gayamiki gaskiya? Toh ya Abdul be son wannan kunyan yafi son rayuwan turawa In gayamiki" wani irin kunya ne ya kara rufe iman.

Da wannan hirar suka shige jewelries stores d'in suka za'bi d'an kunnaye da sarkoki masu abin hannu harda masu sarkar kafa golden da silver masu tsada da kyau, itade iman kud'in abubuwan kawai takeji tana mamaki musamman kayayyakin wai itace da sa atampha na fiye da dubu arba'in hamsin? Lallai duniya kenan baba da be ta'ba sayamata atamphar dubu biyar ba sbd wai asarar kud'inshi zeyi, to yau gashi mijin da ze aureta ya kashe mata kusan million a lokaci d'aya kuma kayan da basu fi kala goma sha biyar ba.

Tana nan tana ta aikin tunanin rayuwarta yadda ya zama kaman wani kwallo har suka karasa wurin takalma nan ma su zahra suka za'bi matching colors da gowns d'inta kuma hills itade kallonsu kawai takeyi ba wai don zata iya sakawa ba, Anty kalthum tace "wai zarah lalle da wanke kai da kuma kitso fah? Se yaushe za'ayi?" Zarah tace "kin san nenne ce ta shirya komai watakila In mun isa I think flight d'in 10 ma zamu bi" Anty kalthum tace "nice kad'ai kenan banyi booking ba na san ku Abba ya muku, bari kiga inyi ta wayana tunda baban fadeel ya yarda inje".

"Wai Ina yake ne ma? Shi da ba'a yaye ba bade har kin fara barinshi gida ba" Tace "ke to bazan iya ba isana yawo dashi yake yi wallahi" ta waya ta musu transfer d'in kud'insu suka fito suka dawo harabar malabis sukayi sallama, Anty kalthum ta shiga motanta zarah da iman suka shige na Malabo suka wuce.

Da mamaki iman ke bin gidansu ganin yadda ya cika pim da 'yan buki ko kuma tace 'yan gulma daga yamma

15 / 44