Author : Billyn Abdul Category : Romance
haka da kowa ke son ganin ya wulaƙanta rayuwarmu, na taɓa ce musu bazan rayuwu ba sai da wani NAMIJI ne Ammie?. Basa tunanin kafin su ina dake ba! Basa tunanin ba dole bane sai mace ta rayu da namiji zata amsa sunan mace? Basa tunanin na haƙura da wanda ma yay sanadin kawoni wannan duniyar bisa izinin UBANGIJI balle su, su ɗin nan da ba komai ba a rayuwata. Su ɗin nan da zan iya canjawa da ire-irensu a duk lokacin da naso. A tunaninsu dole-dole sai da sune zan RAYU?! Ko babu su zan rayu Ammie, zan rayu dake kaɗai da ƴan uwana kun isheni, kun wadatar dani a wannan rayuwar, bana buƙatar kowanne namiji, suje, suje ban buƙatarsu.....” kuka ya sarƙe ta sai tari. Ɓull!!! Ɓull!! Jini ya dinga ambulowa ta bakinta ta hanci.
Wani irin firgitaccen kukan tashin hankali Ammie ta saki jikinta dake riƙe dana Maanal na rawa. Tuni Shahidah, Manaal da Yazeed sun yo kansu a ɗari. Su kansu su Hajiya Yaya da tawagarta da sauran jama'ar gidan al'amarin ya matuƙar firgitasu. Dan a wai-wai suke jin Maanal nada matsalar ciwo mai haɗari, amma basu taɓa ganinta a ciwon ba, kai zasu ma iya rantsuwa basu taɓa ganin ana aman jini ba sai yau musamman wannan da takeyi ta baki ta hanci.
Kowa ya rikice an rasa mai cewa a tafi asibiti. Sai baba maigadi ne daya iso wajen a hargitse yake faɗin asibiti ya kamata a tafi. Da wannan magana tashi suka zabura gaba ɗaya. Cak Yazeed ya ɗauki Maanal daketa aman jini ya nufi hanyar gate a maimakon motocin gidan saboda tsabar yanda ya rikice. Shahidah, Amal, Ammie suka take masa baya sai Amara da itama ta zabura ta bisu tana kuka. Fitowar Yazeed dai-dai da isowar RK ƙofar gidan, dan haka a cikin rikicewa Amal ta buɗe motar RK ɗin kawai tana cema Yazeed ɗin ya shiga batare data tantance motar waye ba itama. Shima bai wani tantance komai ba ya saka Maanal a ciki, da sauri itama Ammie ta shiga ta rungumeta tana kuka da faɗin, “Haba Maanal ya zaki mun haka, dan ALLAH kiyi haƙuri kada ki tafi ki barmu mu muna sonki, muna tsananin ƙaunar Maanal. Muna buƙatar ki a duniyar mu Maanal...”
Wannan furuci na Ammie shi ya zaburar da RK da ya tsaya yana kallon ikon ALLAH, sai kuma lokacin ya gane Ammie da Amra dake kuka. Duk da halin da Maanal ke ciki itama bai gagara ganeta ɗin ba. Ai da wani irin tashin hankali ya tada motar, Yazeed ya shiga kusa da shi suka bar anguwar. Napep Amal da Shahidah da Amrah suka tare suma suka bi bayansu....
Yazeed ne ya faɗa masa asibitin da zasu je, inda Maanal ke ganin likita kenan. Asibitin kuɗin ne, kasancewar kafin su isa ma Yazeed ya kira abokin nasa doctor Nazeer ya sanar masa zuwansu suna isowa suka samu nurses har huɗu da Doctor Nazeer ɗin kansa na jiransu a waje. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Manaal daga jikin Ammie. A kallo ɗaya idan kai mata zakai tunanin bazata sake rayuwa ba. Dan yanda take yunƙurowa ƙirjinta na ɗagawa tana aman jinin kaɗai ke nuna akwai sauran numfashi a tare da ita. A haka dai aka shiga da ita ciki kowa a kiɗime. Dai-dai nan suma su Shahidah da suka biyosu a napep suka iso...
Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan yanda doctors ke shiga da fita ɗakin da aka shiga da Maanal basa ko sauraren kowa zai tabbatar maka al'amarin yayi tsamari da yawa. Dan har zuwa goman dare babu wani bayani mai daɗi. Zuwa sannan Nene ta iso, (Nene ƙanwar mahaifiyar Ammie ce da yanzu take kallo kamar mahaifiya. Zamu iya cewa ma ta sandinta Ammie da ƴaƴanta suka zo cikin Kaduna. Ita a anguwar dosa take, ita da zuri'arta. Dan itama yaranta huɗu duk maza a yanzu haka duk suna da aure da ƴaƴansu suma, sai ɗaya ce kawai mace itama dai tayi aure).
Har wannan lokacin RK na asibitin, hasalima tuni ya shige cikin likitocin da shi ake bama Maanal taimako kasancewarsa shima ƙwararren likita masani a fannoni da dama daya shafi aikin. I'd card ɗinsa kawai ya nunama Doctor Nazeer ya amince masa shiga cikinsu aka rufu kan Maanal. Haka shina Yazeed tsaye yake da ƙafafunsa. Duk abinda akace ana buƙata kafin wani dogon lokaci zakaga ya kawosa. Sai su Ammie suka kasance ƴan addu'a da share hawaye. Daga can gidan dai babu wanda ya biyo bayansu, sai dai Yazeed ya kira mahaifinsu ya sanar masa. Ya kuma tabbatar masa a yau ɗin nan zai baro inda yake zuwa Nigeria. Domin shima hankalinsa yay matuƙar tashi bana wasa ba. Koda yasa Yazeed ya haɗashi da Ammie kasa magana tayi sai kuka data fashe masa da shi kawai. Sai hakan ya sake birkita masa lissafi gaba ɗaya babu shiri ya fara neman ticket ta online......
___________
Alhaji Usman Chalawa bai iso ba sai washe gari wajen misalin ƙarfe ɗaya na rana. Babu wanda yasan da dawowar tasa a cikin matansa, dan hatta ita ma Ammien bai sanar mata ba. Sai Yazeed kawai ya sani. Shi kuma tashin hankali ya mantar da shi sanar ma kowa sai da Daddyn ya tura masa saƙon yazo ya ɗaukesu sun kusa sauka sannan ya tuna. Ya bar asibitin ne dai-dai lokacin RK na bada shawarar yima Maanal transfer zuwa Abuja. Dan gaskiya jikin nata sam babu daɗi. Su kansu likitocin sun fara karaya, RK ɗin ne ma ke ƙarfafasu duk da shima gwiyawunsa a sare suke yana dakewane kawai da ƙarfafa kansa...
Kai tsaye asibiti Yazeed yayo dasu Daddyn. Rungume Ammie su Waleed sukayi, yayinda take kallon mijin nata cikin karaya idanunta cike da ƙwalla. Cike da kulawa ya girgiza mata kansa alamar kar tai kuka. Sai kawai tai ƙasa da kanta tana mai rungume Hameed da Waleed sosai a jikinta. Idanun nasa ya ɗauke cike da damuwa ya maida kan su Shahidah dake gaishesa. Ya amsa musu da kulawa yana tambayarsu mai jiki. Maimakon amsa sai suka fara hawaye suma. Jiyay gaba ɗaya zuciyarsa ta ƙara karaya, da ƙyar ya iya gaishe da Nene, sannan ya wuce office ɗin doctor inda suke meeting shi da su RK. Doctor ne yay ma RK bayanin matsayin Daddy a wajen Maanal duk da tare da Yazeed suka shigo, dan RK bai ɓoyema doctor alaƙarsa da Maanal ɗin ba. Cikin girmamawa RK ya rissina ya gaishe da Daddyn. Nan ma doctor ya sanarma Daddy RK likita ne, ya kuma masa bayanin shawaran da suke akai yanzu haka game da maida Manaal ɗin Abuja. Babu wani musu Daddy ya yarda, tare da ƙarfafasu cewar ayi komai yanda ya kamata ama bar ɓata lokaci, bari yaje ya bincika ko akwai jirgi mai wucewa yanzu sai su wuce a ciki zaifi mota sauri....
Hakan kuwa akayi, dan zuwa la'asar an gama shirya Maanal zuwa tashar jirgin ƙasa. Zasuyi gaba harda Nene da su Shahidah. Ammie kuma sai zuwa gobe in ALLAH ya kaimu da safe zasu bisu ita da Daddy kamar yanda ya buƙata.
Suna isowa Abuja ambulance ce tazo ta ɗauki Maanal dan tuni RK ya gama booking komai. Shi da Yazeed ne suka bi ambulance ɗin, yayinda mijin Shahidah da yazo shima ya ɗauki su Shahidah ɗin da Nene da Amal. Yaran duk suna Kaduna sai gobe idan ALLAH ya kaimu Ammie zata taho da su nan. KK HOSPITAL asibiti ne mai tsanani ƙyau da kowa ya sani a cikin Abuja. Suna da ƙwararrun likitoci da suka san aikinsu ƙwarai da gaske. Suna ƙoƙari matuka wajen bama mara lafiya kulawa yanda ya kamata, ga sauƙin kashe kuɗi dan talaka da mai arziƙi duk zasu iya biya. Babu wani ɓata lokaci cike da kulawa aka shiga da Maanal, yanda ake girmama RK a asibitin yasa suka fahimci eh lallai yana da wani matsayi babba a wajen.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣2️⃣
______________
Abubuwan da nake saidawa
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
__________
.......Yau kwanakin Maanal biyu a KK HOSPITAL. Zamu iya cewa Alhamdullahi abubuwa sun fara dai-daita, duk da dai har zuwa yau ba'a barin kowa shiga inda take sai doctors kawai. Tun a jiya su Ammie suka iso suma ita da Daddy. Tsabar munafunci na Hajiya Basariyya sai ta ce zata biyosu taga jikin Maanal ɗin. Dan a waccan ranar da Daddy ya dawo tunda ya koma gida ya rufesu da faɗa ita da Hajiya Yaya akan ƙin zuwansu asibiti, sai dai faɗan nasa yafi tsamari akan Hajiya Yaya data zama itace sanadin komai, dan yama sanar mata ya haramtawa Sabuwa zuwa masa gida, idan kuma tai gigin zuwa ALLAH sai ya saka jami'an tsaro sun kamata. Itama kuma ta jira hukuncinsa bayan Maanal ta warke dan yanzu baida lokacinta. Tofa wannan abu da Hajiya Basariyya dake laɓe taji yasa ta dawo ta lallaɓa Daddyn ta bashi haƙuri akan nata laifin daya faɗa naƙin zuwa asibiti kawai, ta kumaji duk halin da ake ciki akan maida Maanal Abuja shine ta maƙale itama zata bisu. Ammie bata san da batun ba sai da suka fito zasu wuce taga Hajiya Basariyyan. Sosai ta sake jinjina makircin matar a ranta, dan ta jima da gane wacece Basariyya, sai dai bata taɓa nuna mata ba ta barta da halinta. A lokacin ma murmushi kawai tai batace komai ba, hakan kuma sai ya ƙonama Hajiya Basariyyan rai, ta rasa wacece Ammie, ta rasa ta inda zata kamo lagon matar, ta rasa ta inda zata shiga jikinta kamar yanda take shiga jikin Hajiya Yaya tasan sirrinta. Amma ba komai, idan tasan wata ai bata san wata ba.
Anan Abujan itama ta kwana dan Daddyn nada gida anan ɗin dan yana harkar sayen gidaje da sayarwa ne. Kasancewar komai akwai a gidan yasa sauka kawai sukai anan ɗin. A yanzu ma haka tana a asibitin tare da su. A ɗakin da aka kwantar da Maanal ɗin ɗakine na musamman kamar palor da bedroom, dan haka duk suna a palor ɗin zaune itama Maanal na daga ciki babu mai shiga sai dai su leƙata ta jikin ƙofar glass ɗin. Shahidah da Amal suka iso ɗauke da abinci, bayan duk sun gaishesu suna ƙoƙarin zama Daddy da RK suka shigo ɗakin sai wani ba'indiyen likita da shine akan case ɗin Manaal ɗin ma. Gaishe da Daddy su Shahidah sukayi, sannan suka gaisa da su RK da suma suke gaida su Ammie. Su RK na ƙoƙarin barin wajen kamar daga sama sai Hajiya Basariyya cewa tai, “Nikam likitan nan kamar na sanka”. Yanda tai maganar idonta akan RK ya sakashi fahimtar da shi take, kallonta ya ɗan yi sai kuma ya rissinar da kansa tunda bai san matsayinta ba a garesu ya ce, “Mommy zata iya yiwuwa. Sai dai ban san a ina kika sanni ba”.
Batare data damu da kallon harara da Daddy ke mata ba ta ce, “A zaria gidan Alhaji Saminu Ashafa”.
Cikin jinjina kai RK ya bata amsa da, “Ni ƙanin amaryarsa ne Majdiya”.
Kafin Hajiya Basariyya ta samu yin magana Ammie da Daddy suka dubeshi. Abinda ya faru a ranar da sukaje ɗaurin aure gidan Alhaji Saminun ya shiga dawo mata a rai. In dai batai kuskuren fahimta ba shine yaron da Hajiya Majdiya ke mata bayanin yana son Maanal kenan. Wani irin sanyi taji a ranta, dan koba komai ita dai yaron ya shiga ranta a lokaci guda, sannan ta samu karɓuwar addu'ar ta akan al'amarin Maanal ɗin da Yazeed tunda ga raba gardama yazo.. Shikam Daddy murmushi yayi cike da nuna mamaki ya ce, “Ikon ALLAH ashe ma kai ɗin na gida ne doctor. Ai nasan Hajiya Majdiya kuwa sosai saboda Alhaji Saminu aminine kuma ɗan uwana ta fanin mahaifiya, zan iya cemaka ma neman auren Majdiya da komai dani akayisa”.
Wani ɗan karen daɗi ne ya ratsa RK har cikin maƙwallaton zuciya. Sai yake jin gaba ɗaya matsakarsa ma shi ta ƙare kenan. Nan take ya ƙara sakewa da Daddy. A karo na farko Daddy ya shiga ɗakin da Maanal ke kwance shi da Ammie da Nene kawai. Sosai tausayin Maanal ya ƙara mamayesu, dan Ammie kasa daurewa tayi sai da tai kuka. Duk wanda yaga Maanal ɗin sai yayi matuƙar tausaya mata. Numfashi ma sai da taimakon na'urori take yinsa. Duk ta sake figewa. Sun mata addu'a suka fito aka bar Nene kawai dan doctor ya buƙaci a ɗan goge mata jiki a canja mata kayan jikinta. Da ance Ammie tayi amma ta nuna bazata iya ba. Sai dai Nene tayi. Tsaf Nene ta gogema Manaal jiki aka canja mata kaya. Doctor da RK suka shigo, hakan yasa Nene fita ta basu waje dan suyi aikinsu. Ta tarar da Hajiya Basariyya cike fam da takaici, wai tana fushine ita ba'ace ta shiga ta duba Maanal ba, shine taima Daddy ƙorafi akan hakan. Shi kuma yaƙi tanka mata shine ta cika tai fam. Ita dai Ammie haƙuri ta bata, yayinda su Amal ke mamakin abinda Hajiya Basariyyan tayi. Ita kanta Nene abin ya bata mamaki, dan bataga abin wani ƙorafi ba a wajen tunda gasu Shahidah suma ba'a barsu sun ganta ba. Ita kanta dan Ammie tace bazata iya gogema Maanal ɗin jiki bane aka barta ta shigan. A haka Yazeed da yaje Kaduna ya dawo ya samesu, tare da duk yaran gidan yake tafe, amma abin mamaki yau ɗin ma Hajiya Yaya bata zo ba....
Da mamaki Amrah ke kallon RK, har dai ta kasa haƙuri sai da tayi magana. Murmushi yay mata da tambayarta ya gajiyar biki. Hakan data faru tsakanin Amrah da RK sai ya tsayama Yazeed a zuciya har sai da ya kira Amrah ɗin gefe ya binciketa. Kanta tsaye ta sanar masa abinda ta sani. Yayi mamaki ƙwarai da gaske. Haba no wonder yake mamakin yanda RK ɗin ke tsaye very serious akan case ɗin Manaal ɗin. Ya jima yana son haɗa al'amarin a ransa amma ya gaza samun makama, tunda shi dai sun fitone kawai suka samu motar RK ɗin a ƙofar gida, daga wannan taimakon kuma na kawosu asibiti baiyi tunanin cigaba da ganinsa ba amma sai yaga ya tsaya tsayin daka komai anayi da shi, yayi tunanin kawai tausayi da taimakone sai da aka dawo Abujar nan ya ɗan fara zargi a ransa sai kuma dai yay saurin kaudawa tunda bashi da tabbas musamman ganin RK ɗin matsayin likita shima. Ashe kuwa hakanne.
A ranar su Amrah suka koma Kaduna harda Hajiya Basariyya data wuce bisa tirsasawar Daddy dan kuwa badan taso ba, taso ace sai taga kwal uwar daka. Ta zata da Daddyn zasu tafi sai yace mata shi yana nan har sai yaga yanda hali yayi akan jikin Maanal ɗin. Hakan ya masifar ƙona mata rai, dan ta kalla abunne a sigar rainin hankali irin na maza kawai. A ganinta Daddyn nason holewa da Ammie ne a wannan ƙayataccen gida shine ya fake da ciwon agola. Ita Ammie tsaf ta fahimci manufar Hajiya Basariyya ɗin, amma sai ta basar kawai tama dinga ƙarfafa Daddy ɗin akan yaje suma suna da hakki a kansa, tunda dai Maanal ɗin tana samun dukkan kulawa anan ɗin gasu kuma ga Yazeed shi yaje ya huta gashi ya dawo daga tafiya. Sam Daddy ƙin saurararta yayi, daga ƙarshe ma ya fara fushi da ita dole tai shiru ta zuba masa ido kawai su Hajiya Basariyyan suka wuce...
A ɓangaren Yazeed kuwa ya fara janye jikinsa daga RK. Tun RK ɗin bai fara fahimta ba har ya fahimta. Dan sai wani isa ma Yazeed ke nuna masa akan Maanal ɗin yanzu da gadara. Mamaki hakan ya bama RK, dan shi a zatonsa Yazeed da Maanal uwa ɗaya uba suke ko uba ɗaya dan yana ɗan tantamar Ammie ta isa haihuwar kamar Yazeed ɗin. Bai daiyi magana ba yabar abin a ransa dan ganin iya gudun ruwan Yazeed ɗin. Ana cikin wannan dambarwa a tsakaninsu Hajiya Majdiya yayarsa tazo duba Maanal ita da yaranta tun daga Zaria. Dan shine ya kirata yake sanar mata, aiko baiwar ALLAH sai gata tazo. Ammie tayi mamakin hakan kasancewar batai waya da Hajiya Majdiya ɗin ba akan hakan. Sai Hajiya Majdiyan ke sanar mata, “Sirikinki ne ya kirani yake sanar min ai.”
Murmushi Ammie tai da faɗin, “Haba nayi mamaki fa, sai kuma hankalina bai kawo nan ɗin ba. Ai babu abinda zamuce da Rafeeq sai fatan alkairi. ALLAH yay masa albarka”.
“Amin ya rabbi. Yaya jikin nata yanzu? Dan naga hankalinsa a tashe yake matuƙa yau har cewa yay na nema masa masu saukar Alkur'ani yana son ai mata”.
Ajiyar zuciya Ammie ta sauke. Zuciyarta na sake jin nutsuwa da RK ɗin. “ALLAH sarki, ALLAH ya saka masa da alkairi. To Alhamdullahi zamu ce. Sai dai har yanzu bata san wanda ke kanta ba. Amma dai suna tabbatar mana bugun zuciyarta na dai-daita zuwa yanzu. Kowane lokaci kuma zata iya farfaɗowa cikin hayyacinta.”
“ALLAH ya bata lafiya, yasa ya zama kaffara. Abin tausayi yarinya ƙarama haka da wannan irin babban ciwo mai haɗarin gaske, ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawoyinmu. Shiyyasa gata nan sanyi-sanyi ko kuzarin kirki bata da shi. Ban taɓa sanin tana da wannan lalurarba ai da tuni na haɗaku da Rafeeq ɗin dan aikinsa ne. Yanzu haka reshen wannan asibitin suka buɗe acan garin jos shine yaje can da kansa yake