AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   35 / 77

102K to 105K   out of 230.9K words

mai girgiza kai, tasan Maanal da ƙiriniyarta, damma taga yanzu kura tayi lafiya kamar ba Maanal ɗin ba.....

______________★

       Jikin Maanal ma Alhamdullah, dan tama hana Shahidah sanarma su Ammie. Dama kuma Shahidahn ma batai niyyar sanarma Ammie ɗin ba kamar yanda mijinta ya fargar da ita cewar tunda da sauki karsu tayar musu da hankali.
      Abinci Maanal ɗin keci RK ya shigo, sai da ya gaisa da su Shahidah kafin ya maida hankalinsa a kanta. Cikin tsokana ya ce, “Madam ba tayi”. Ai baima gama rufe baki ba ta miƙa masa plate ɗin. Mi mijin Shahidah zasuyi ba dariya ba. Uncle Sadeeq ya ce, “Doctor kai baka san dama neman kai take da abincin ba, an turketane tana ci dan dole”.
     Fuskar RK da murmushi ya ce, “Ai naga alama Babban yaya. Irin wannan bani da sauri haka. Ni dai dan ALLAH kici abinci ki ɗan ƙara kumari”.
    Hararar RK ɗin tayi, sai kuma ta tura baki gaba cike da shagwaɓa. Zama Shahidah tai kusa da ita cikin lallashi ta ce, “Kinga ƙyalesu Auta kinji, bari ma na baki da kaina”. Haka ta amsa ta cigaba da bata cike da kulawa da so. Sai RK ya samu kansa da shagala a kallonsu. Shi kaɗai yasan yanda yake jim ƙaunar yarinyar nan a ransa. Komai tayi birgesa yake. Yasan hakan daga ALLAH ne. Dan yana jin feeling akanta irin wanda zai rantse bai gaɓa ji ga sauran ƴamata ba. Kodan bai taɓa yin budurwa bane oho. Sam shi ada matsoracin mata ne, babu ruwansa da harkarsu, badan bai cika namiji bane, kawai dai karatunsa na likitanci daya ƙwallafa rai da aikin nan sun kwashe mafi yawan lokacinsa na rayuwa. Idan ka cire ibada da yake matuƙar bata hakkinta. Shifa ko irin ƴar soyayyar ƙuruciyar nan baiyi ba. Kuma a turai aka haifesa anan ya girma yay dukkanin karatittukansa. Gaba ɗaya bai wuce shekara huɗu da dawowa Nigeria gaba ɗaya ba. Amma ALLAH bai ɗora masa damuwa da mata ba. Shiyyasa shi da kansa yake sake yarda da son Maanal yake bana wasa ba. Hakama ƴan uwansa kowa murna yake da batun Maanal dan sun tabbatar da gaske son nata yake tunda shidai ba'a taba kamashi da case na mace ba.
       Sosai Maanal ta matsa ita sai an sallameta ta warke. Amma Dr Ranjet ya dinga lallaɓata akan tayi haƙuri zuwa gobe. Dole badan taso ba ta haƙuran...

______________★

       Kusan ƙarfe uku na yamma Abdul da amaryarsa Yaseerah sai Huznah suka iso katafaren family house ɗin na Ambassador Aliyu Darma. Dan a gidan su Yaseerah Huznah ta kwana. Daga Mawaad Company can ta wuce ranta a ɓace tana hawayen abinda AA ya mata. Shine Yaseerah taita lallashinta da tabbatar mata a yau zasuzo Darma's house. Hakan kuwa akai, tun a daren take lallaɓa Abdull akan suje har ya amice. Sai kuma gasu sun iso yanzu.
        Sun sami tarba daga Mamy, ƙyaƙyƙyawar mace ƴar ƙwalisa data gama tafiya da zuciyar Huznah. Kai tun kafin ma Mamyn Darma's house ya gama tafiya da Huznah. Ta gama sallamawa da jinjina kuɗi irin na gidan su AA ɗin. Ta kuma yarda kuɗin ma hawa-hawane. Tasan mahaifinta nada kuɗi, tunda suka tashi suke jin ana sakashi a jerin masu kuɗin jihar Kaduna, kai bama Kaduna kawai ba a dattawan arewa masu kuɗi za'a iya sako mahaifinsu. Sai dai kuma Baba ma fa da babansa. Ta shaida hakan a yau kuma ta aminta.
         Yanda take ta faman sinne kai da kaffa-kaffa da komai sai ya baka mamaki, ko gaishe da Mamy sai da ta duƙa har ƙasa. Sai Mamyn ce dake binta da kallo ta kamata ta tadata ta zaunar a kujera. Still dai Huznah ta kasa kallonta. Ita ma dai Yaseerah bata da wata sakewa, dan dangin mijin nata ƙalilan ke sonta, duk da dai ita Mamyn na sonta. Kawai dai dan Abdull ɗin ya dage sai ita ne yasa suka ƙyalesa. Hakan yasa su biyun duk suka nutsu, sai Mamy da Abdull ne ke hira. A haka Saheeba ta shigo suka gaisa tare da saka masu aikinta jere abincin da Mamyn tace tayo a sashenta na tarbar baƙin. Saheeba dai ta danne sun gaisa da su Yaseerah, sai dai hankalinta nakan duk motsin Huznah ne. Bisa umarnin Mamy sukaje d/table, anan ɗin ma dai Huznah bata sake ba ita adole mai kunya. Ita dai Mamy sai kallonta take tana murmushi. Dan haka kawai kuma sai taji son yarinyar a ranta saboda kunyarta da nutsuwa gefe ga ta ƙyaƙyƙyawa. Dan duk ƙyawun Nuratu da da take kallo dai-dai da AA sai taga ai Huznah ta takata ta shanye. Dama dai a ƴan kwanakin nan wasu abubuwa na Nuratu sunsa ta fara shakkar haɗa aurenta da AA ɗin, amma bata fito ta faɗama kowa ba. To tana ganin yarinyar nan itace zata zama raba gardama. Dan kodai ya aurenta ita kaɗai kota sakashi ya haɗa da Nuratun su biyu a masa auren gata auren huce takaice auren da tasan zai baƙanta ran Oum fiye da auren su Fawzan.
      Bayan sun kammala cin abincin ta umarcesu da suzo su duba AA. Abdull ne ya tambayeta “Baida lafiya ne Uncle AA ɗin Grandma?” (dan haka yake kiranta kasancewarta ƙanwar kakarsa uwa ɗaya uba ɗaya). Amsa ta bashi da “Eh son, yau ko aiki ma bai fita ba yana kwance”.
    Gaba ɗaya ji Huznah tayi hankalinta ya tashi, dan har fuskarta ta nuna hakan ɓaro-ɓaro, amma dai ta daure batai magana ba. Mamy dai na lure da ita. Hakama Saheeba dake jin kamar ta shaƙo Huznah ɗin. Sai faman tsine mata take a zuciya. Sashen Oum suka fara zuwa, Oum ta tarbesu da kulawa kamar yanda ta saba ma ƴan uwan Mamyn, dan haka cikin girmamawa Abdull ya gaisheta, hakama Yaseerah da Huznah data kusa zubewa a tsaye da mamaki tana satar kallon Oum. Tabbas bata manceta ba, itace ta gani a gidan Shahidah tare da namiji mai kama da AA ɗinta. Rashin sanin alaƙarsu da su Maanal ɗin kuma yasa har yanzu bata sanarma mahaifiyarta ba, gefe kuma ta ɗan shiga ruɗani, shin tsakanin Mamy ɗin da matar wacece mahaifiyar AA ɗin? A dai kamanni yafi tsananin kama da Oum, shin yaya take ne?. Da ƙyar ta iya dannewa dai suka baro sashen bayan Oum ta cika su da abin arziƙi, sai dai fa da alama ita Oum bata gane Huznah ba. Koda yake a gidan Shahidah da suka haɗu ita bawani ta maida hankali a kanta bane lokacin.
      Daga nan sashen AA suka nufa kamar yanda Mamy ta sanarma Oum cewar zata kaisu su dubashi. Wani irin lumshe idanu Huznah tai lokacin da suka shigo main falo ɗin sashen da wani irin ƙamshi mai daɗi ke tashi. Suna isowa falo na biyu taji zuciyarta na wani kalar tsaitsinkewa saboda haɗuwarsa. Falo kamar bana tuzuru mara mata ba. Anan Abdul ya dogare, fuskarsa da murmushi ya ce, “Grandma bari mu dakata anan a masa magana idan zai iya sakkowa mu gaisa. In ba hakaba bara na haura ni kaɗai sai na dubashi kin san Uncle baya son wargi bakamar Uncle Fawzan ba”.
     Murmushi Mamy tayi, dan itama dai tasan maganar Abdull ɗin gaskiya ne. Dan in har ta hau da su Yaseerah sai yaji haushi. Su Saheeba ma dake matsayin matan yayyansa kuma ƴan uwansa na ƙut sosai yake tujara idan suka shiga masa koda falon sama ne balle. Yanzu haka ko ɗazun tana jin yanama Fadeel mitan shi matansu su daina shigo masa har bedroom.
          Mamy ce ta haura saman da kanta. Dai-dai AA daya farka daga barcin da Doctor ya sakashi dole ya fito wanka. Knocking ƙofar da akai ne ya sashi yamutsa fuska cikin yanayin mara lafiya, muryar shi ƙasa-ƙasa da kamar baya son buɗe baki ya furta, “Ina zuwa”. Daga haka ya ajiye towel ɗin hannunsa da yake goge sumarsa da ruwa ya jiƙa saboda ciwon da kansa ke masa har yanzu kaɗan-kaɗan ya sakarma kansa ruwan. Boxer ya saka tare da cire bathrobe ɗin ya saka jallabiya sannan ya nufi ƙofar dan duk zatonsa Oum ce. A hankali ya buɗe ƙofar, cikin ɗan shagwaɓa ya furta, “Oum sai yanzu, ni nayi fush.......”
    Kasa ƙarasawa yay saboda yin tozali da Mamy ba Oum ba. Ta koyi kicin-kicin da fuska tana masa wani irin kallo, kansa ya duƙar ƙasa yana mai haɗiye busashen yawu ya furta, “Am sorry, nazata Oum ce”.
        “Humm” kawai ta furta batare data kula zancensa ba ta juya tana faɗin, “Kasameni a ƙasa baƙi zasu gaisheka”.
    Kallo ya bita da shi, harta fara taka stairs case ɗin. Kaɗan ya lumshe idanunsa ya buɗe, sai kuma ya ɗan furzar da iska ya koma cikin ɗakin..........✍️







✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖4️⃣7️⃣


______________


........Fin mintuna goma bayan sakkowar Mamy sannan ya sakko. Duk da sanye yake da slippers masu taushi hakan bai hana bayyanar tahowarsa ba. Ga wani mayataccen ƙamshin turarensa mai ratsa zuciya na rige-rigen shiga hancinansu tun kan su fara ganinsa.
       Ai tuni zuciyar Huznah ta fara gudu a ƙirjinta, yayinda take satar kallon hanyar ƙofar upstairs ɗin ta gefen ido. Bayan wasu ƴan sakanni ƙofar ta buɗe slowly, ya bayyana garesu. Sanye yake da wando da riga duk baƙaƙe masu kamar kayan sanyin nan dan harda hula a bayan rigar, sai dai bai saka ba ya saketa a dokin wuyansa ta kwanta. Sam babu wasa ko alamarsa a saman fuskarsa datai wani irin fayau ya ƙara haske. AA ba fari bane, amma yanada hasken fata da ko'a cikin baƙaƙen irin baƙin nan ne mai matuƙar ƙyau da shining ga wani glowing da yake tamkar jinin mutanen ƙasar Labanon. Yanada hanci dayay dai-dai da tsarin tsaka-tsakin fuskarsa daba doguwa can ba, ba kuma faffaɗa ba. Ga shi da cikar gashin gira dana ido da ko wata macen bazata nuna masa eyelashes ba. Kwantaccen gashin sajensa daya zagaye har matsaikaitan lips ɗinsa pink shine yafi komai sake ƙawatashi. Kamar koda yaushe idanunsa manne da eyeglasses ɗinsa fari ƙal da kamar ba'a amfani da shi na ƙara ƙarfin gani. Yanda oily idanun suka sake wani fita tar-tar kamar an watsa ruwan madara sabon tatsa dole kaji wani iri idan ya kalleka da su. Gashi dogo masha ALLAH.
      Tunda ya gama sakkowa kallon kowa baiyi a cikinsu ba. Sai takowa da yay a hankali zuwa cikin falon sosai. A kujerar farko dake bangon daya fito ya zauna kawai, sai a lokacin ya ɗan dubi Abdull dake gaishesa cike da girmamawa. Cikin yanayin ɗan zuba masa ido batare daya amsa gaisuwar ba ya ce, “Ango ne a gidan namu”.
    Murmushi Abdull ya saki mai ƙayatarwa tare da duƙar da kansa yana sosa ƙeya. Cike da jin nauyi ya sake gaida AA ɗin. AA ya girmi Abdull sosai, dan shi a yanzu bazai wuce 26+ ba gaskiya. Kawai dai an masa auren gata ne. Sai yanzu AA ɗin ya amsashi da tambayarsa iyalin. Sake duƙar da kai Abdull yay da faɗin, “Ai Uncle gata nan ma tare mukazo dubaka”.
     Batare da AA ya kalli inda Abdull ɗin ya nuna ba ya furta, “Oh Masha ALLAH, Thanks”.
     Gaisheshi Yaseerah ta shiga yi da tambayarsa yaya jiki, ya amsa mata a taƙaice still dai bai kalleta ba. Dan kowa yasan wannan kam ba ɗabi'arsa bace kallon mata ko'a sanda yake a ganiyar samartakar balaga balle yanzu da wasu dalilai suka saka shi sake kame kansa ga komai, dan AA akwai tsantsar kame girma, ko wanda suka girmesa sukanga ya cika musu guri balle wanda ya girma. Sai a lokacin Huznah data kasa numfashi mai ƙarfi ta fara gaisheshi itama, AA akwai iya haddace muryan mutane da riƙeta idan yaso, dan haka ya ɗan kalla sashen da suke a karo na farko, a mamakinsa kuwa wadda yay tsammanin ce. Wato budurwar yarinyar nan mai shegen naci da iyayi data takurama rayuwarsa a kwanakin nan. Ƙoƙarin janyewa yake suka haɗa ido da Mamy data kafesa da nata idanun. Sai kawai ya kautar da kan nasa cike da basarwa. Haka kawai Mamy ta saki murmushi. Dan ta tabbatar da abinda take son tabbatarwar, da gaske AA ɗin yasan Huznah ba ƙarya sukai masa ba. Saheeba ma dai sai faman raba idanu take a tsakanin Mamy da AA da Huznah. Itama kuma taga reaction ɗin AA ɗin a sanda Huznah tayi magana. Tuni hankalinta ya ƙara tashi, wani kalar tsanar Huznah na ratsa zuciyarta.
      AA ne daya miƙe ya katsema kowa tunaninsa. Dan hankalinsa kwance ya nufi ƙofa, sai da ya kama handle ɗin batare da ya juyo ba ya furta, “Abdull thanks you ALLAH ya baku zaman lafiya”. Daga haka ya shige tare da maido ƙofar ya rufe. Kusan lokaci ɗaya Yaseerah da Huznah suka saki ajiyar zuciya. Dan ita kanta Yaseerah ɗin sai yau da take ganin AA ɗin da ƙyau. Rayawa take a ranta (Ashe haka guy ɗin ya haɗu, ya subahannallah mutum kamar shi ya zana kansa da ƙyawu. Ga aji ga kwarjini. Wannan shine irin mijin da take fatanma kanta, dan Abdull yana da ɗan irin qualities ɗin kaɗan shiyyasa ta aminta da shi. Ashe ga inda ake mazan nan na gaskiya. Ya ALLAH gaba ɗaya an wargaza mata dukkan lissafinta. Sai a yanzu ta sake tantance abinda ya haukatar da Huznah ashe). A ɓangaren Huznah ma sambatu kawai take zubawa a zuciya. Wani irin ƙyau da kwarjini AA ɗin ya sake mata. ALLAH badan kar ace tayi ƙarya ba daya kalleta da wannan idanun nasa mai kamar an watsa madara da oil a ciki kaɗan ya rage ta suma. Kai dole dole ne ma ta mallaki mutumin nan, idan ba hakaba zata iya rasa ranta.
     Da ire-iren wannan tunanin suka koma sashen Mamy, kasancewar lokacin sallar Asr yayi Abdull ya wuce massallaci. Su kuma Mamy ta haura dasu sama a ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ta tace suyi salla. Ita kuma ta nufi nata.....

____________★

        Senator Bukar dai yaje Kebbi cikin garin Giro, bai kuma sha wahalar samun ainahin gidan kakannin su Maanal ba. Dan gidane sananne a cikin garin. Alhamdullah kuma ya samu tarba irin wadda bai mayi zato ba. Dan cike da farin ciki suka dawo garin Abuja dama jirgi yabi shi da Rabilu da Oler. Yanda yake ta famar washe baki da zumuɗi ya saka uwargidansa a tashin hankali, dan ta tabbatar ya samo abinda yake so. Batace da shi komai ba yay shiri ya wuce gidan matarsa ta biyu dan yau itace da shi...
       Itama dai a yau ya zazzage mata batun ƙarin aurensa, a ɓangarenta mace ce mara haƙuri da iya shanye abu, dan haka tun a daren sukaci uwar watsi ƙarshe kowa a part ɗinsa yay barci. Dan ya tabbatar mata akan Maanal fa zai iya saita mata hanya ne shi ba damuwarsa bane. Dole taja bakinta ta kulle dan tasan kaɗan daga abinda zai iya aikatawar kuwa.....

     _Ikon ALLAH miya faru a Giro🥱 to?._

_____________★

       Yanayin da take jin jikinta Alhmdllh yasa ta ce Shahidah taje gida kawai ta huta yau zata kwana da nurse. Da har Shahidah ɗin taƙi Dr Ranjet yace karta damu taje ɗin. Dama asibitin bawai suna barin masu jiyya bane ba ai kawai dai sune oga ke bari. Zuwa yanzu Shahidah ta fahimci asibitin nan mallakin RK ne. Duk da yanata dojewa bai son su sani. Dan haka koda Dr Ranjet ya ce ogan ta fahimci RK ɗin yake nufi.
        Mijinta ne yazo ya ɗauketa, basu tafi ba sai da ta tabbatar ta mata duk abinda take buƙata duk da jikin nata Alhmdllh sannan. Bayan tafiyar tasu Maanal ɗin na zaune tana karatun novel ɗin data ɗauka na AA ranar a office ɗinsa, dan yau ta matsama Shahidah ta kawo mata shi asibitin tare da glass ɗinta. Sosai take zumuɗin karatun book ɗin saboda labarinsa da aka bata. Tayi matuƙar zurfi a karatun dan tana jin daɗinsa, bata damu da shigewar lokaci ba dan kusan 11 ma da rabi. Sai can ƙasan zuciyarta dake ɗan kawo mata tunanin ina RK, rabonta da shi tun safe da ya shigo ya dubata a gaggauce ya fice. Tana son tambaya tana tsoron kar Didi tai mata wata fassara daban dan haka taja bakinta tayi shiru. Sai dai lokaci-lokaci yana zuwa mata a rai.
      Kaɗan-kaɗan wani irin daddaɗan ƙamshin turare ke shigo mata hanci, tun tana fuskewa da cigaba da karatunta har dai yanda turaren ke sake ƙarfi a ɗakin ya addabeta. Cikin nutsuwarta da rashin rawar kai ta ɗago idanunta kaɗan tana bin ɗakin da kallo, dai-dai saukarsu inda ƙofa take ƙirjinta yay wani irin motsawa alamar zuciyarta tayi zallo. Sosai ta zuba masa ido tana masa kallo irin na  mamaki ko ruɗani zamuce oho. Sai dai fuskarta a dake babu alamar wani shock a kanta. Sai ma janye idanun tai a slowly ta maida ga littafin kamar bataga komai ba.
         Gently shima ya lumshe nasa oily idanun da ke a ɗan kumbure kaɗan da kuma ɗan sirkin ja a cikinsu dan har yanzu basu komai dai-dai ba saboda ciwon kai yaƙi barinsa. Sai dai da ɗan haskensu fiye da jiya da yake a halin ciwo sosai. Sake buɗesu yay a kanta yana mata wani irin kallo mai wahalar fassara. Fin mintuna biyar suna a haka baka jin komai a ɗakin sai sanyin ac da aka saka mata kaɗan daya gauraya da ƙamshin mayataccen turarensa mai kashe garkuwar jiki. Gaba

35 / 77