AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   63 / 77

186K to 189K   out of 230.9K words

bai faru ba ta cigaba da aikinta. Ba kuma ta taɓa key ɗin da takardar ba. Ji suke kamar su taso su ɗauka su buɗe suga mike a ciki, dan suma dai gulmar zuwan Manaal ɗin a motar Boss harta iskesu. Kai yau hatta da Yaqub ji yake kamar ya ɗau takardar ya duba. Amma dai sai ya dake.
      Haka suka cigaba da ayyukansu har lokacin break yayi. Maanal da tasan ba salla zatai ba bama ta motsa ba. Dan da safen nan taci karo da baƙonta na wata. Sai dai koda Yaqub yace ta taso suje catai masa yaje tana nan zuwa zata ƙarasa wani abu ne. Badan yaso ba ya fita, suma sauran duk sun fice sai ita kaɗai. Aikinta ta cigaba da yi, dan Maanal akwai himma da nacin aiki, kamar yanda take da nacin karatu. Can idonta ya sauka akan takardar nan da key, ɗan zuba mata ido tai, sai kuma ta kai hannu ta ɗauka ta warware. _Kiyi hakuri boss ne yace na dawo da shi ki kai masa da hannunki_. Iya abinda aka rubuta kenan. Kanta kawai ta girgiza ta naɗe takardar ta jefa a kwandon sharar su dake office. Shi kuma key ɗin ta jefa shi a wani ɗan basket mai ƙyau da take zuwa kayan sweet da take sha, sai dai yanzu babu komai a ciki dan ta shanye ta kuma mance tazo da wasu. Ta sake maida kanta a aiki bayan ta ɗauka meat pie ɗaya ta fara ci. Kamar abin almara taji ƙamshin mayataccen turarensa na sake ƙarfi a hancinta. Da farko ta share da tunanin iska ce ko hancinta ne. Sai kuma dai taji abin na neman wuce wuri dan haka ta ɗago.
       Samun zuciyarta tai da girgizawa sakamakon saukar idanun nata a kanshi, sai kuma ta janyesu da gudun tsiya ta hau waige-waige a office ɗin nasu alamar dai tabbatar da babu kowa dai ko........✍️

      🤣Ko waye oho.


09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖8️⃣4️⃣


______________


........A hankali ya wani kalar taɓe baki. Cikin halin ko'in kula da ganin yanda ta ke waige-waigen ya ƙarasa shigowa cike da izzar nan tasa da ƙasaita hankalinsa a kwance. Sai da yaje jikin desk ɗinta ta kashe-kashen daya kasance daga ita babu kowa sannan ya tsaya. Kaɗan ya ɗosana jikinsa a desk ɗin yay irin tsaiwar maza tare da harɗe ƙafarsa akan ɗayar daya dogara, gaba ɗaya ƙarfinsa naga desk ɗin. Idanunsa har yanzu akan Manaal da kamar tayi suman zaune ne ma oho mata😂.
         Babu wani ko ɗar balle tunanin wani ya shigo ya gansa ya kai hannu ya zare meat pie ɗin dake hannunta da take ci. Bakinsa ya kai ya gutsira, ya lumshe idanu yana mai taunawa a hankali...
     “Amma kasan hakan na nufin sakani a masifa ko? Dan ALLAH dan mi zaka zo nan a wannan lokacin da kowa ke can yana salla kai kana nan ɗaukar magana?”.
       Shiru kamar bai jita ba. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe lumsassun idanun nasa a kanta. Cikin halin ko'in kula ya cigaba da cin meat pie ɗinsa hankali kwance. Marairaice masa tai sosai idanunta na cika da ƙwalla, dan ta fahimci masifar bazata kaita ba. “Please dan ALLAH ka fita kada wani ya shigo ya ganka anan ka jamin surutu. Salla fa akeyi”. Da kaga yanda take maganar kasan bata da nitsuwa, dan sai leƙe-leƙe take kamar mai shirin yin satar naman miya a gidan soja.
      Baki ya sake taɓewa da janyo bowl ɗin da meat pie ɗin yake ya sake ɗaukar wani. “K miya hanaki zuwa sallar?”.
           “To ina ruwanka dan ALLAH da abinda ya hanani, ni dai dan ALLAH ka tafi kada ma'aikatanka su sakani a bakin duniya”.
       “Tunda babu ruwana da abinda ya hanaki zuwa salla. Kema ina ruwanki da ganina anan to. Naga dai company na ne, ina da damar shiga duk inda nake so a lokacin da nake so ko”.
         Yanzu kam sosai hawayen suka ciko mata idanu, ta tsatstsaresa da kallon da bama tasan tana yi masa ba. Cike da rauni ta ce, “Kadai fi son ka ganni a masifar ko Ajwaa....” ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya watso mata. Baki ta sake tunzurawa sosai. Baki ya ɗan laɓe ya janye idanun ya sake kai hannu zai ɗauka meet pie ɗin da ya rage saura biyu kawai. Ai babu shiri ta kai hannu ta buge nasan cike da tsiwa ta ce, “Malam wai miye haka zaka cinye min abinci”.
       Bai kulata ba ya ɗauke bowl ɗin ma gaba ɗaya, sai da ya gutsira sannan ya kalleta cike da iskanci yana wani ƙanƙance su ƙasa-ƙasa ya furta, “Ko mai meat pie ɗin ta kama ba sai na.....”
           “Na shiga uku. Sai kayi mi?..” Maanal ta faɗa tana mai waro dukkan idanunta a kansa. Kaɗan ya rage ya kwashe da dariya. Amma dai ya dake ya basar. Sai ma dan neman magana ca yay, “Ni kibar min wannan kallon karna ƙware. Sannan miye wani kin shiga uku bana son fassara zance. Sai nayi ƙyautarki nake nufi”.
    Harara ta watsa masa ta koma kan kujerarta ta zauna. Dan ta fahimci idan ta biye masa ALLAH zama ta iya zubewa a wajen. Pretending ɗin danna keyboard ta koma yi, shi kuma ya cigaba da cin meat pie ɗin yana duba drawing papers na zanen da tayi dake yashe a desk ɗin. A haka ya kammala cinye mata tas babu ko tausayi balle ya rage mata, ya ɗauka ruwan da tasha ta rage ya shanye. Sannan ya maida gaba ɗaya hankalinsa ga papers ɗin. A bazata taji saukar furucin sa cikin kunneta.
        “Kiyi gaggawar dakatar da Rafeeq yin abinda kika saka shi, in ba hakaba zaki haɗa rigimar da ke kanki baki san ƙarshenta ba”.
      Kallonsa kawai ta ɗago tana yi dan kamar ba shine yay maganar ba. Dai-dai nan Ema... Da Zaharadeen suka shigo suna dariya. Cak suka tsaya tare da jan birki saboda cin karo da abinda basu yi tunanin gani ba. Boss da kansa a office ɗinsu. Tashin hankali. Cikin firgicewar bazatar ganinsa da sukai suka shiga gaisheshi. Sai lokacin ya ɗago ya zuba musu kaifafan idanunsa. Yayinda Maanal ke jin kamar ta fasa ihun da sai Abuja tayi girgiza gaba ɗayanta. Dai-dai nan suma wasu biyun suka sake kawo jiki,  ai a sukwane suka taka birkin da yafi nasu Deeni. Shiko tuni ma ya ɗauke idonsa a kansu ya cigaba da dube-dubensa kamar bai san da kowa ba a wajen sai kansa. A haka har suka gama shigowa, babu kuma wanda zai shigo bai taka birkin firgici ba da ganin CEO ɗin. Shi kuma yaƙi kulasu sai jeruwa suke kamar ƴan layin tuwon dare a boarding school (lolx🤣😂). Maanal kam ai ta kasa kallon kowa, tai ƙasa da kai kamar maƙaryaci a gaban sarki. Sai ta gefen ido ake ƴar kallan kallo tsakaninta da su Yaqub.
      Fin mintuna biyar sai da ya mula dan kansa ya ajiye Drawing papers ɗin ya gyara tsaiwa sannan ya ɗago idanu ya sauke a kansu bayan ya zuba duka hannayensa a aljihun wandon suit ɗinsa. Babu alamar wasa a tare da shi ko sassauci ya ce, “Waye Abideen a cikinku?”.
        Cikin tashin hankali Abideen ya ce, “Nine sir”.
     Kallon sama zuwa ƙar AA ya masa. Sai kuma ya ja idanunsa ya maida a kan fuskar Abideen ɗin yana sauke masa wani zafafaffen kallo. Tsohon mintuna biyu kafin ya janye a matuƙar daƙile. Pen ya ɗauka a gaban Maanal da ƙaramar takarda ya fara rubutu, sai kuma can ƙasa ya furta, “Nawa suka biya ka?”.
        A tare su Zaharadeen har ma da Maanal suka maida kallonsu ga Abideen da duk ya rikice. Rantse-rantse ya fara. AA da ko nuna yana ma jinsa baiyi ba ya ajiye pen ɗin da short note ɗin da yay a gaban Maanal ya miƙe sosai, batare da ya sake kallon kowa ba yay hanyar fita yana faɗin, “Ka tattara komanka ka saman a office”. Daga haka ya ratsa ta tsakkiyar hanyar da suka dare suka bashi ya fice abinsa.
     Shi ko Abideen hankali tashe yake kirama kansa ya shiga uku ya lalace. Sai da AA yay nisa sannan su Yaqub suka sami damar baibayesa da tambaya. Maanal dai suman zaune tayi da mamakin mugun sabon halin da AA ya ɗauka yanzu. Koda yake tuni fa yana da mugun halinsa, kawai dai ƙuruciya yasa bata fahimta a wancan lokacin. To dan ALLAH in ba mugun hali ba taya zaka zo ka turke staff ɗinka a bainar nasi kana masa wannan kausasan tambayoyin na nuna isa da izza. Wai mi masu kuɗi suka ɗau kansu da rayuwarsu ne?......
      “Sis.. Maanal dan ALLAH kizo muje ki bashi haƙuri, wlhy zan faɗa masa gaskiya....” furucin Abideen da ke binsu da wannan furucin su duka a birkice ya dawo da ita a hanyyacinta. Yayin da su Zaharadeen ke ƙoƙarin kamashi dan ya nutsu asan mafita. Amma ina duk ya ruɗe. Sai da ƙyar suka danna shi ya zauna a kujera. Ema ya bashi ruwa yasha.
      “Ni dai shawarar dazan baka Abideen ka tashi kaje kasan dai boss baya son jira. Kuma tabbas tunda ya shigo office ɗin nan da kansa case ɗin nan naka babba ne. Amma ka rufama kanka a siri ka gaya masa gaskiya a tambaya ɗaya nasan zaka iya samun sassauci tunda ya tsani ƙarya ko kwalo-kwalo akan laifi kaima ka sani”.
     Musa ne da wannan magana cikin damuwa. Dukansu sun gamsu da shawarar Musa ɗin. Dan haka duk suma suka shiga cema Abideen ɗin ya tashi yaje. Da ƙyar ya iya miƙewa ya fita. Duk suka bisa da kallo. Sai da ya fice gaba ɗaya Zaharadeen ya kalla Maanal cikin sauke ajiyar zuciya da ƙwarewa a gulma. “Sis... Manaal wai tun ɗazun boss yana nan ne dama? Sannan yayi wata magana ne?”.
      Karan farko Maanal ta watsa masa harara. Cike da tsiwa ta ce, “Miyyasa baka tambayesa ba sanda yake nan? Ko sai ni marainiyar wayonka”.
      Mutsut Zaharadeen ya haɗiye gulmarsa. Dan wani irin kwarjini ma yaga Maanal ɗin ta ƙara masa. Ga shi ta wani tsare sa da mayun idanunta masu haske. Harara ta rakashi da shi, sai kuma taja siririn tsaki ta maida kanta ga aikinta. Akan rubutun da yay ta sauke su. _“Ki saman ki bani amsata nan da awa ɗaya a office, in ba hakaba wlhy zan dawo da kaina na ɗaukeki na kaiki. Kar kiga ba canja topic yanzu tausayi kika bani”_. Muƙut ta haɗiye yawun daya maƙale mata a maƙoshi. Ita kam ga shiga uku da mutumin nan. Kafin ta samar ma kanta mafita Yaqub ya zauna dan su cigaba da aikinsu. Dole ta haɗiye komai da bashi hankalinta dan aikin mai muhimmanci ne. Sai dai kaso sittin na hankalinta ya tafi ga al'amarin AA ne da ƙarfin halinsa.....

_________★

         Tunda taga awa ɗayan daya bata ya kusa cika hankalinta ya ƙara tashi, dan ta tabbatar AA baya faɗar magana bai cikata ba, tun ma kan yakai haka. Ta kasa samun nutsuwa, ta kasa tsaida zuciyarta waje guda. Ga Abideen har yanzu bai dawo ba tunda ya fita. Office ɗin nasu yanzu kam yay tsitt kowa damuwa shimfiɗe a fuskarsa. Sai dai fa kowa ya maida hankali akan aiki tuƙuru. Ganin fa saura mintuna biyar rashin nutsuwarta ya ƙaru. Kamar ance ta ɗago ta kalla ƙofa sai idonta akan AA ya wani kafe office ɗin nasu da kaifafan idanunsa. Ai bama tasan ta miƙe ba har Yaqub na ɗagowa shima ya kalleta. Key ɗin motar nan da wasu documents ta ɗauka tana faɗin, “Sorry Yaqub ina zuwa. Na manta CTO yace na kai masa documents ɗin nan tun ɗazun.” bata jira amsarsa ba ya fito. Dai-dai AA na gittawa da baƙonsa da alama ya nuna rakkiya ya masa, tsabar wulaƙanci yi yay kamar bai ganta ba, sai da ta ɗan kallesa taga ya mata wani salo da yatsu biyu ta baya yana saki wani ɗan iskan murmushi. Jitai wani ƙululu ya tokare mata maƙoshi. Amma babu yanda ta iya dole ta nufi elevator. Tana isowa AS ya bata umarnin ta shiga kawai. Harararsa tayi sannan ta wuce fuuuu ciki, tako bugo ƙofar har sai da AS ya ɗan zabura, dan harga ALLAH tsoro yaji saboda abin yazo masa a bazata..........✍️

🤣🤣 An dai ji kunya AS da tsoro.😂








09032345899




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖8️⃣5️⃣


______________


.........A nutsensa ya turo ƙofar ya shigo. Ya kuma maidata ya rufe sannan ya shiga takowa cikin office ɗin. Duk da ƙamshinsa da motsinsa bai sa ta motsa daga tsayen da take ba. Sai ma sake kumbura take yi taf har ya ƙaraso bayanta daf ya tsaya. Tsabar yanda ya fita tsaho har tsakkiyar kanta yana gani tsaf, gently ya ranƙwafo a bayan nata batare da jikinsa ya taɓata ba ko kaɗan, fuskarsa a saitin kunnenta yana busa mata numfashinsa saman dokin wuya cikin raɗa ya furta, “Ko sai na ƙarasar dake ɗin ne dai saman kujerar?”.
      A wani irin zabure Maanal tai gaba camak kamar wadda aka sarrafa da remote. Sai kawai hangota yay a saman kujerar. Murmushi ya saki da wani lumshe idanu sai kuma ya buɗe su yana miƙewa tsaye sosai ya shafo kwantaccen gashin sajensa zuwa wanda ya zagaye madaidaicin bakinsa. Maimakon yaje ya zauna a kujerarsa sai ya zauna visitor chair ɗin shima dake kallon wadda ta zauna. Basket ɗin saman desk ɗin nashi ya jawo, ya ciro ƙyawawan kulolin da aka shirya abinci. Tuni wani irin ƙamshi ya cika mata hanci, duk da shekaru sun shuɗa, ƙamshin girkin Oum bazai taɓa shuɗewa daga zuciyarta ba sam kamar yanda tasan shima kansa Ajwaad bazai taɓa manta na Ammienta ba. Dan haka ta fara satar kallon abincin. Sai da ya gama zubawa dai-dai cin mutum ɗaya sannan ya sake matsowa sosai da kujerar, sai dai duk da hakan sam jikinsu bai taɓa na juna ba akwai ɗan space. Abincin ya ɗebo a spoon ya kai bakinta. Ƙin buɗe bakin tayi, shiko ya wani zuba mata idanu. Hawaye ne suka fara taruwa a nata idanun, dan haka ta kauda kanta gefe a hankali tana mai haɗiye abinda ya tokare maƙoshinta.
Shima idanun nasa ne suka kaɗa sosai, amma da yake namijin duniya ne sai ya saki ɗan murmushi irin na danne damuwar nan. Muryarsa da wani kalar sanyi da kulawa ya furta, “Karfa na cinye ki dawo kina min rigima”.
Shuuuuu hawayen da take faman riƙewa suka ziraro daga idannunta tai murmushi, wasu abubuwa ne masu nauyi da suka shuɗe ke tsikarin zuciyarta, ƙirjinta ya mata nauyi matuƙa. Slowly ya kauda nasa kan shima daga kallonta, idanunsa sun sake masifar kaɗewa. Kusan minti ɗaya suna a haka kafin ya juyo, tissue dake saman desk ɗinsa ya zara biyu ya miƙa mata batare daya kalleta ba. Itama bata kallesan ba ta amsa tissue ɗin, hawayen ta share, tare da dunƙule tissue ɗin cikin hannunta taƙi zubarwa.
“Ka kori Abideen ne?”. Ta faɗa batare data kallesa ba har yanzu. Shi kam juyowa yay ya sauke nauyayyun idanun nasa a kanta, sai kuma batare da ya bata amsa ba ya furta, “Ci abincin first”.
“Ni bana jin yunwa.”
“Na sani”.
Ya bata amsa a taƙaice yana sake kai spoon ɗin bakinta. A hankali ta furta, “Bani zanci da kaina” tana kai hannu zata amsa spoon ɗin. Matsar da hannunsa yay kaɗan yana zuba idanunsa sosai cikin nata. Dole tai ƙasa da nata ta buɗe bakin kaɗan. Ƙaramar ajiyar zuciya sukayi a tare bayan ya zare spoon ɗin ita kuma ta fara tauna abincin a hankali...
Lips ɗinta kawai dake motsi yake kallo, sai kuma ya ɗan murmusa kaɗan da faɗin, “Kin tuna ranar da kika fara girki, da irin abincin nan kika fara har na samu wannan ciwon?”. Yay maganar yana kallon gefen babban yatsar hannunsa na dama gab da wajen tafi. Itama hannun ta kalla, dai-dai wajen akwai madaidaicin tabo da akallo ɗaya zaka fahimci sanda aka jisa ba ƙaramin ciwo bane.
“Oum!! Mamy!! Babban yaya ku kawo taimako hannun Besty ya gundile, ya gundile Abah kalla jini, wayyo Yaya F mun bani Besty ya zama mara hannu”. Ya faɗa yana kwaikwayon ƙaramar muryarta a wancan lokacin. Ai bama tasan ta sanya dariya ba. Taja mayafinta ta rufe fuskarta tana mai kifeta a desk ɗinsa komai na dawo mata kamar a yanzu yake faruwa. Shima dariyar yake sosai kamar ba shi ba. Ya ɗan girgiza kansa... “Kai yarinyar nan kinyi rashin ji wlhy. Kefa kika jimin ciwon, amma kika fini ihu da raki da cika kunnen mutane, ban isa kuma nace kece ba ki isheni da rigima da tsiwa. Ai naci girkinki na farko da wuya dai”.
Batare data ɗago ba ta ce, “Amma ai kaine kasa na ji maka ciwon ko, ba kaine kace na yanka albasan a hannunka ba”.
“Amma sai nace ki yanka ni? Anya bazan ramaba ma yanzu?”.
Da sauri ta ɗago tana waro

63 / 77