Author : Billyn Abdul Category : Romance
wuce inda aka tanada dominta da sauran ma'aikatansu. RK ma tare da su Oum ya zauna. Sai wani dama-dama Mamy keyi da shi, ta yanda Oum tama gagara ko yimasa kallon banza balle zazzage masa abinda ke ta faman cimata zuciya..........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣6️⃣
______________
96
........An fara gabatar da addu'oi sannan. Daga haka shugaba *_CEO Ajwaad Aliyu Abubakar Darma_* ya gabatar da bayanin sannu da zuwa ga dukkan wanda suka halarci zaman. Tare da jinjinar ban girma ga ma'aikatansa jajirtattu. Ya ɗan sauke idanunsa akan Maanal da tunda suka iso taƙi yarda su haɗa ido, janyewa yay a hankali ya sake maidawa ga mutane ya cigaba da jawabinsa. Bayan ya kammala sauran manyan ma'aikata sukayi nasu daki-daki. Kafin ya fitar da hoton ƙayataccen agogon a cikin ƙaton magijin dake a bango guda na ɗakin taron. Babu wanda bai ambaci woow da Masha ALLAH ba. Dan gaskiya agogon ya matuƙar fita da fitarsa. Kai da ka gani kasan bana ƙananun yara bane, agogo ne na masu ƙumbar susa da sarakuna. Karo na farko aka buƙaci ganin Maanal. Ta jima kafin ta miƙe, dan jitai kamar ta fasa ihu. Amma haka ta daure ta fito cike da dakiya. Fitowar tata ya saka idanu da yawa kasancewa a kanta, ita dai ta dake ta hana kanta kallon kowa harta ƙarasa in da ake buƙatar ta. Bayan sallama da gaisuwar girmamawa ta gyara tsaiwa. A karo na farko idanunta suka sauka akan RK. Murtantanin murmushin da yake mata ta mayar masa tare da janye idanun ta. Sai kuma karaf a kan na AA daya zuba mata idonu shima. Da sauri ta janye tana sake bama kanta nutsuwar dole kafin ta fara bayani mai cike da ƙayatarwa. Tasha tafi sosai, dan jawabanta sun matuƙar ƙayatarwa musamman yanda ta tsara su akan matasa da iyaye da manyan ƙasa masu mulki akan su tallafi matasa da aikin yi. Bayan jawabanta mutane da yawa sun cigaba da jawabai masu ma'ana da muhimmanci kafin a bama HALIFA SK ƊORAYI dama zuwa ya ɗan bada nishaɗi da waƙarsa mai sanyi mai taken BAZANA DAINA KUKA BA wanda shi uban gayyar ma bai san da tsarin yin hakan a wajen ba. Tunda baitin waƙar ya fara fita wajen yay wani irin tsitt, dan cike suke cike da wani irin amo mai kassara karsashi da kuzarin masoya musamman masu rauni a zuciya. Dan shi kansa AA da ba damuwa yay da jin waƙoƙin ba samun kansa yay da tsitstsinkewar jini, dan ji yake tamkar shi yake rairata. Tuni da ga shi har Maanal sun wani kalar zubama juna idanu cike da rauni da karaya gushewar tunani tare da hauhawar jinin jiki.. A bazata hawaye suka cika idanun AA, haka itama Maanal jitai kuka na taho mata, dole ta duƙar da kanta kawai waƙar na cigaba da ratsata har ya kaita ƙarshe. Tafi sosai hall ɗin ya ɗauka, manyan mutane suka fara fadar kyaututtukan da suka bashi a take a wajen. Aiko bakin Halifa ya kasa rufuwa😂 (A gayama HALIFA SK ƊORAYI Nima na bashi ƙyautar mota😂🥱 dan waƙar nan fa tayi😋😋😋🥰🥰😀).
Bayan an dawo daga break an fara bada Award na girmamawa ga waɗanda suka taimaka wannan agogo ya fito, an fara daki-daki ga duk wanda sukai hidar aikinsa har kan mai gayya mai aiki data zana wato *_Maanal Habib Giro_*. Mabanbanta mutane suka bama sauran ma'aikatan award ɗinsu, amma ita mai gayya da aiki ne zai bata da hannunsa wato AA Darma.
A hankali ta miƙe kamar ɗazun cike da nutsuwa ta tako har inda yake tsaye, yayinda shi kuma ya zuba mata kallon ƙasan ido. Sai taji duk tsigar jikinta na tashi, yayinda shima yake jin kamar bazai iya daurewa da sadaukarwarsa ba. A haka dai ya daure da ƙyar ya bata shiryayyen award ɗin da yay matuƙar ƙyau da tsaruwa dan nata yama banbanta dana sauran. An bata mic tayi godiya da jinjina ga Mawaad Company gaba ɗaya, tare da ƙara ɗorawa da wasu jawaban masu muhimmanci. Lokacin data koma wajen zamanta sai ta samu kanta da kai handky ɗinta ta share hawayen da suka cika mata ido, dan har cikin jininta waƙar ɗazun ta kekketa mata zuciyarta har yanzu, gani take kamar AA ɗin na isar da wani saƙone a gare ta kai tsaye. Shi kansa uban gayyar tunda ya bata award ɗin nan har aka tashi bai sake tashi daga inda yake zaune ba.....
__________★
Alhamdullah shirye-shirye biki nata kankama. Dan ta kowane ɓangare shirin akeyi ɗan gaske. Musamman ɓangaren Darma Family masu gayya da aiki. Hakama gasu Shahidah babu zama. Itama Maanal ta ƙara dakewa ta tattara dukan hankalinta akan RK. Yanzu kam kullum ma shike kaita office yaje ya ɗakkota. Sam bata haɗuwa da AA, Dan rabonta da shi tun ranar taron kamfani. Alhamdullah a litinin data rage saura kwana goma sha uku bikin aurensu aka bata office nata na kanta matsayin Assistant ta Director Steven. Wannan muƙami ya zafi su Zaharadeen, dan a ganinsu duka yaushe ma tazo companyn. Duk da kuwa aikin da tayi a bayyane yake, dan agogon da aka ƙaddamar ya dawowa kamfani da ninkin kuɗin da aka fitar da shi fin sau ashirin a kwana ɗaya na jiya kacal. Wannan al'amari ne da bai taɓa faruwa da kamfani ba. Wasu kuwa na ganin Maanal ɗin tama cancanci fiye da hakan ai, duk da ba'ita kaɗai tayi aikin ba, hasalima ita nata zane ne kawai. Amma dai ta taka rawar gani ai. Dan da batai zanen da ƙyau ba suma masu ƙerawar da basu yi yanda ya kamata ba. To ita dai bata cema kowa komai ba, iyakaci wanda ya tayata murna tayi godiya. ALLAH sarki Yaqub da kansa ya taimaka mata ta kwashe tarkacenta zuwa sabon office ɗinta. Dan zuwa gobe ma zata fara aiki a ciki.
Aiko hakan ce ta faru, washe gari Maanal a sabon Office ɗinta ta zauna. A kuma ranar ne batun bikinta da RK ya fasu a kamfanin, tare da auren boss ɗin su da duk shima za'ai rana ɗaya. Kowa dai ya sake fahimtar kusancin Maanal da boss tunda dai RK ɗan uwansa ne na jini kowa yasan wannan. Sai ko ƙananun magana ta tashi akan shiyyasa akai saurin bata matsayi kenan. Sarai zantukan na dawo mata amma tai kunnen uwar shegu. Washe gari laraba ma ta ɗauki hutu, sai kuma bayan biki zata dawo bakin aiki. Alhamdullah duk da ɗan munafunce-munaguncen dake kai kawo haka suka taru sukai mata fatan alkairi, tare da tabbatar da zuwansu duk da shagalin ya zama biyu gana boss a gefe. To ita dai ta musu godiya da tabbatar musu tana saka idon zuwansu....
A ranar suka wuce Kaduna. Dama Shahidah nata masifa akan gyaran jikin da akema Manaal ɗin kullum yana bin iska ne saboda galauniyar da take na zuwa aiki kullum. Suna kuwa isowa Kaduna Nene ta tisa ƙeyarta zuwa gidanta. Wani irin gyaran jiki mai ban mamaki Nene ta fara mata ɗan gaske. Tunda ta shiga kuryar ɗakin Nene ko falo an haramta mata fita, hakama wayarta an kwace gyara kawai take sha ciki da waje, ita kanta abin har tsoro yake bata. Abubuwan da ake danna mata tana sha kuwa har kamar zasu sanyata amai take ji. Shiyyasa data faki ido sai ta zubar. Ga wani irin mahaukacin ƙamshi da ko yaya ta motsa sai kaji waje ya buɗe. Fatarta yayi wani irin ƙyau na tashin hankali. Sau ɗaya Nene ke bata damar yin waya da RK a rana. Shima na minti goma kawai. Duk wani abu ta bashi damar yaje su tattauna da su Aneesa, ga Najma, ga Amrah duk da ma ita Hajiya Yaya ta hanata sakewa...
_______★
Tunda fa su Hajiya Yaya suka tabbatar bikin za'ai da gaske sai kuma sabuwar hassada ta tashi. Kullum cikin habaice-habaicen suke da gugar zana. Hajiya Yayan ta saka Yazeed ɗaukar amarya Nazeefa akan dole sun tafi honeymoon. Ammie kuwa ta tattarasu ta bama banza ajiyar su. Hakama ɓangaren su Hajiya Basariyya shirin biki ake na garari da kece raini. Rashin zuwan ango sam ba damuwarsu bace. A cewarsu adai ɗaura koma minene zasuyi maganinsa ne. Itama danginta sun cika gida tab, dan wannan ne karo na farko da zata aurar.
Ranar talata aka kawo lefen Huznah, lefen da su Hajiya Basariyya aka dinga iyayi da gwalangwaso da shi har ana sakarma su Ammie habaici. Laraba akai kamu, amma na iya Huznah. Dan ita Maanal tace bata buƙata. Sai kawai akai mata feshin turare normal dai na mutanen da shike nan. Tako ci kuka a ɓoye, gashi dama dannewa kawai take yi, amma ƙirjinta gaba ɗaya a kwanakin nan jin gim yake da nauyi na tsiya. Amma tanata daurewa dan bata son kowa ya fahimci halin da take ciki har ƴan uwanta da Ammie......
________★
A ɓangaren su Oum gasu nan ne dai, kowa ka gani babu wani karsashi ko ɗokin auren a tare da shi. An dai kwashe gaba ɗaya kayan sashen AA ana masa gyara duk da kuwa komai fes yake babu wani damuwa. Bayan an canja komai anyi sabon fenti suma sauran sassan gidan an ɗanyi gyaran. A ɓangaren Mamy kuwa cike take da farin ciki mara misaltawa duk da ita Nuratu sai wani satin za'a ɗaura nata auren kamar yanda aka tsara. Amma tun yanzu cikin shirinsu suke suma tunda za'a kawo suruka ɗaya Huznah. Tsaff Mamy ta gama shirya yanda zata tarwatsa Oum. Duk da a yanzu ma damuwar da take kallon Oum ɗin a ciki wani kalar nishaɗi da farin ciki yake sakata. Amma tanata ƙoƙarin dannewa yanda ta saba.
Ranar Laraba suka tarkata suka wuce Kano suma. Dan za'aje can a haɗe bukukuwan ne gaba ɗaya. Idan taro ya tashi lafiya sai su taho da tasu amaryar. Amma na wani satin anan Abuja za'ai komai basai sun je Kano ba, shiyyasa Mamy tafi shiryama bikin Nuratun fiye dana Huznah. Kwanaki fin biyar kenan babu wanda a cikinsu zaice yaga AA da idonsa, sai ta waya shina Oum ce ke naci kiransa. Dan yayi tafiya zuwa Lagos ta kwanaki biyar ɗin. A Kano ma zasu haɗu da shi bazai dawo tanan Abuja ba. Sunyi tunanin zuwa su sameshi a can ɗin kuwa. Amma sai suka samu bai iso ba. Suna isa da yamma ƴan kawo lefen Maanal Kaduna suka wuce. Ta mota aka tafi da kaya, su kuma suka bi jirgi bayan sallar la'asar. Dan haka Oum suna sauka ko zaman hutu batai ba ta bisu su dan tana son ganawa da Ammie. Sai Nibras data maƙale domin zuwa taci uban Huznah a cewarta. Sai uwar gulma Saheeba, tunda basuga lefen ba sanda aka taho da shi basu isa Kano ba yasa ta biyo mutane dan ganarma idonta ko lefen RK ɗin dai-dai yake da wanda suka kai na Huznah. Itama Mamyn taso zuwa Mah-mah ta janye hankalinta da wani abun acan...
To lefen dai Maanal ya iso cikin garin Kaduna, gidan Alhaji Usman Chalawa. Gida fa cike da ƴan gulma musamman ta fannin Hajiya Yaya da Hajiya Basariyyar ma tunda danginta duk suna cike fal a gidan ranar suke mothers event ɗinsu. Itako Ammie komai tace bazatayi ba sai yinin biki a wuce da amarya ɗakinta. Lokacin da aka faka dalla-dallan motoci ƴan gaske har guda biyu, ɗaya kuɗinta ya tasarma naira miliyan 90 matsayin gift wa amarya Maanal, hakama ta biyu zata iya kaiwa miliyan ashirin da biyar, ai gaba ɗaya gidan sai da ya gigice. Dan motar 90m ɗin sabuwace dal a ledarta da ba'ako kware ba, itama kuma ɗayar haka. Gashi an ƙawatasu da ribbon. Hakama akwatina jerarru na kece raini da ƴar gata kawai ake kaiwa tuni sun cike waje set-set. Ai sai kaji bakin kowa ya mutu musamman lokacin da aka sanar da cewar motar 90m fa gift ne daga Yayan Amarya AA Darma. Ɗayar itace ta kayan lefe daga ango.
(😩😩ALLAH matan novel sunji daɗi, ƙyautar motar 90mil fa, ni mai rubutawa ina nan sagadede da baki banda ko keke😭😭, dan ALLAH azo a haɗa ƙarfi da ƙarfe a saya min mota mutanena😥😥🥺)
Babbar bala'i kenan inji Hajiya Basariyya jin wai ƙyautar motar 90mil daga AA Darma wanda zai auri ƴarta. Amma ita ƴar tata kota miliyan biyu ba'a sakko mata ba dan ita babu mota. Hajiya Yaya da su kam ba ƙaramin girgiza zukatansu sukayi ba. Ita kanta Saheeba sai da zuciyarta tayi masifar girgiza. Jikinta har rawa yake ta turama Mamy text massage. Nibras ma dai sumar zaune tayi. AA ɗinta ne da ƙyautar irin wannan ƙatuwar mota haka. Oum kuwa wani irin sanyi ne ya shiga ratsa mata zuciya. A take ta kira Abah ta sanar masa dan babu wanda yasan AA zai yi wannan ƙyauta. Su kansu masu kawo lefen a hanya suka haɗu da motar. Sai da sukazo cikin Kaduna suka fahimci cikin tawagar su take saboda ganin Modibbo ne ya tuƙo ta. Bayan Oum ta yanke waya da Abah AA ta kira, sai dai ya sanar mata yana airport ne zai baro Lagos, idan ya sauka zai kirata...
Ammie ta matuƙar shiga ruɗani ita kanta da wannan ƙyauta ta AA, sai ma taji ta rasa abin faɗa dan mamaki. Ga wannan uban lefe na girgiza hazo kamar za'a buɗe wani ƙaramin kanti. Kasancewar guri ya ƙure yamma tayi su Oum basu wani jima ba suka wuce. Duk da akwai tattaunawa sosai da Oum da Ammie ke son yi babu isasshen lokaci. Haka suka rabu akan zasu ƙarasa a waya tunda dama dai sunatayin na kullum tunda aka fara kaikawon bikin nan.......
Har su Oum suka koma Kano babu AA babu labarinsa. Dangi sai tambayarsa akeyi dan sauran anguna sunata kai-kawo amma shi babu shi babu alamarsa. Zuwa bayan isha'i dai Oum ta kasa haƙuri ta nemo su babban Yaya a waya. Shine ya tabbatar mata suma mamakin rashin isowar tashi suke. Dan ranar mazan family ɗin suke partyn su, ga shi har za'a fara shi babu shi babu alamarsa. Kuma ya ce musu zai baro Lagos suma tun ɗazun...........✍️
Jama'a kar dai Yayan su o'e ya gudu ne😲☹️.
Ashema matsoraci ne, da Uncle RK ɗinmu ne babu inda zai je😌🤣🏃🏃🏃.
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣7️⃣
______________
.......Sai ƙarfe kusan goma AA ya iso gidan baba Sardauna. Dan anan gaba ɗaya ake shagalin bikin. Hankalin Oum yayi mummunan tashi da ganin yanda AA yay masifar zabgewa a tsaye. Duk mai hankali yay masa kallo ɗaya yasan baida isashiyar lafiya sam. Jiki na rawa Oum ta kama hannunsa suka shige bedroom ɗinta, Dan suna a tsohon sashensu ne na gidan baba Sardauna ɗin da suka zauna a can shekarun baya.
Muryarta har rawa take wajen tambayarsa, “Ajwaad baka da lafiya ne?”.
Hannunta ya kama fuskarsa ɗauke da murmushi mai sanyi ya zaunar da ita a kusa da shi. Kafin ta kwantar da kansa a kafaɗarta. Idanunsa a lumshe hannunsa cikin nata ya ce, “Oum ki kwantar da hankalinki lafiyar Autan ki ƙalau. Zirga-zirga ce kawai taimin yawa a kwanakin nan. Tunda naje Lagos ban zauna na huta ba saboda kayan nan namu da gaske ɓata suka so yi. Amma Alhamdullah ALLAH ya kiyaye haka dan yanzu haka har sun sauka Abuja suma. Yaya hidimar bikin?”.
Hawaye ne suka zubo a fuskar Oum. Tasa hannu ta share, kafin tace, “To Alhamdullahi ALLAH ya kiyaye gaba. Amma Ajwaad har yanzu kana akan bakanka naƙin amsa kana son Maanal daren yau fa kawai ne da mu”.
A hankali ya tashi daga kan kafaɗarta, fuskarsa da wani ƙayataccen murmushi ya ce, “Oum maimaita zancen nan bashi da wani alfanu. Bara naje na ɗan watsa ruwa na kwanta na huta a gajiye nake matuƙa”.
Kai kawai ta jinjina tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar data cika mata ido. Har ya kai kofa zai fita ta katseshi da faɗin, “Munga mota tayi ƙyau ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci”.
Guntun murmushi ya ɗan saki kawai, kafin a saman laɓɓansa ya furta, “Amin”. Ya fice. Ta ƙofar baya ya fita, dan sam baya son haɗuwa da Mamy. Kai tsaye daga nan masauki ya nufa, inda duk samarin family dama masu auren kan zauna in har ana biki. A hannun Uncle Mahmud ya amshi key ɗin nasa ɗakin, dan shine da alhakin hakan dama. Shi kansa Uncle Mahmud ɗin ya tsaresa da tambayar baida lafiya ne. Amma yace masa shi ƙalau yake, yayi busy ne kwana biyu akan wasu injinansa da suka nema ɓacewa a bakin ruwa Lagos shiyyasa kawai. Badan Uncle Mahmud ya yarda ba ya ƙyalesa kawai. Shima yana samu ya shige ɗaki ya kulle kansa. Duk wanda yazo ya buga sai yace su barsa barci yake son yi ya gaji ne. Dole kowa ya ƙyalesa tunda dare yayi.
Dole sai a washe gari kowa ya iya ganinsa a ɓangaren mazan dai. Aiko suka tasashi gaba akan sai yaje an masa gyaran fuska dan ya tara uwar ƙasumba yaƙi yay gyaranta. Da farko ƙi yay, sai da Uncle Mahmud ya sashi gaba. Dan adai cikin iyayensu maza daga Abah sai Uncle Mahmud ɗin (ina fatan baku manta da ɗan gwaggo Khadijah da itama ta baiwa Baba Sardauna ba bayan Abah da Oum. To shine Uncle Mahmud).
An masa gyaran fuska mai ƙyau yana kumbure-kumbure yana jin haushi. Sai kuma gashi yayi ƙyau sosai duk da ramar da yayi ta