AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   75 / 77

222K to 225K   out of 230.9K words

gane maganar nada muhimmanci Maman Saheeba na ganina tai saurin fargar da su kasancewata, sannan a jiya sai bayan mun wuce asibiti da fin awa guda sannan ta zo ita da ƴan uwanta. Bazan ɓoye maka ba ranar bikin Yazeed a Kaduna da suka je wlhy wani mugun kallo naga tanama Hajiya Asiya, sai dai ban yarda hakan bane ba tunda ni dai ban san akwai wata matsala tsakaninsu ba a labarin rayuwar zamansu da naji ta baya, naso ɗan tuntuɓar Aunty Babba to amma kasan halinta akan Aunty Kamila”.
        Sosai RK ke kallon Hajiya Majdiya har takai ƙarshen zancenta, kafin ya ɗan yi jimm na wani lokaci. “Tab ɗin inji mata, to ai nima dai bayanan naki sun sakani a ruɗani, mizai saka Aunty Kamila tai wancan furucin? Kuma miya haɗata da Ammien su Maanal da zata mata kallon banza?”.
      “Ai shine, nima dai abin da ban wani ɗaukesa da muhimmanci ba, sai dai furucin nata na yau ya girgizani tare da dawo min abinda ya shuɗe. Shiyyasa nace bari na tuntuɓeka kodai akwai abinda kake ɓoye mana dan kowa yana mamakin haƙurewarka akan sadaukarma Ajwaad yarinyar nan, musamman ma ni dana san kana sonta sosai”.
         Fuskarsa da ɗan murmushi ya ce,............✍️


09032345899


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*




*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖1️⃣0️⃣0️⃣


______________



.......“Aunty wannan maganar sai mun zauna kawai zan fahimtar dake komai. Amma maganar Aunty Kamila kamar ya kamata muɗan saka mata ido mu nazarceta dan karmu yanke hukunci kai tsaye akan abinda ba haka yake ba. Amma bazan ɓoye miki ba nima zuwanta Kano akwanaki game da auren Ajwaad ya tsaya min a rai na kuma jima abin bai bar zuciyata ba gaskiya, musamman dana san yaran data kawo akan ya aura shi hankalinsa baya akansu, sannan basu da nagartar da zaka zaɓesu a matan aure nagartattu ma ɗan daka haifa. Dan haka harna kasa haƙuri na tambayi Mah-mah akan Fadeel da Fawzan sune suka zaɓi matansu na aure ne? Bayan rikicin daya hana wancan auren na farko? Amma sai ta bani amsa da cewar ta manta gaskiya, amma kamar Aunty Kamila ce ta bada shawarar shi Fadeel ya aura ita Saheeba ɗiyar ƴar uwarta a lokacin, Fawzan kuma shine ya kawo matarsa da kansa, daga baya suka fahimci akwai alaƙa tsakanin Maman yarinyar da Aunty Kamila, amma hakan ai ba komai bane tunda Fawzan ɗin ne da kansa yace yana so”.
       “Tofa, kaji wata kuma sabuwa.”
    Shi dai RK baki kawai ya ɗan taɓe da faɗin, “To koma dai miye su suka sani. Yanzu yaya ake ciki? Yau za'a kawo amaren ne?”.
    Harararsa Hajiya Majdiya tayi, shi kuma ya sanya dariya yana susar kai...

Tattaunawar da Hajiya Majdiya tayi da Rafeeq ta sake sakata aune-aunen abubuwa, amma dai sai ta ajiye komai kamar yanda suka ajiye magana akan zasu nutsu su sake tattaunawa bayan biki...

________★

         Ana yin sallar la'asar iyaye suka sanya Maanal a tsakkiya, nasiha akai mata mai ratsa jiki tana kwasar kuka. Ji take ita da zasu tausaya mata da sun barta. Dan tunda taji ana faɗar yau za'a kaita hankalinta ya sake tashi ta ƙara langarewa ita a dole bata da lafiya. Amma su Nene sun nuna idan taje can ta warware gara ta matsa tai jiyyar mijinta dake cikin halin ciwo. Duk da tun a jiya taji AA ɗin baida lafiya sai taji zuciyarta na ƙara shiga tashin hankali a yanzu. Amma dai ta danne. Kafin magrib an gama shiryata tsaf cikin lafaya ƴar ubansu mai ƙyau da tsadar gaske da Ammie ta tanada domin wannan ranar kawai ga autar ta, dan lokacin su Amal ma haka tayi. Aka kuma kawo alƙyabba data amsa sunanta alƙyabba aka ɗora mata akan lafayar, sannan aka baɗeta da ƙamshi na musamman.
      Ana idar da sallar Magrib jerarrun motoci daga zuri'ar Darma suka iso domin ɗaukar amaryar su. Anan fa ne sabon kuka ya tashi. Maanal ta ƙanƙame Ammie da su Shahidah tace babu inda zataje. Babu wanda kukanta bai bama tausayi ba, dan ita kanta Ammie kukan take sosai balle su Amaal, duk da tasan inda Maanal ɗin zataje baida maraba da gabanta, zama ta iya samun kulawar da ƙila bazata samu a gabanta ba, dan Oum ba akan Manaal ba ita kanta uwace a gareta kuma babbar Yaya da kake jin alfahari da samunta a gareka. To a haka dai da ƙyar aka raba Maanal da su Ammie.
     Yaya Fawzan da kansa zai ɗauki amarya, wannan alƙawarine da yay ma kansa dama shine zai kaima Auta Maanal a duk randa aka ɗaura musu aure. To Alhamdullah alƙawarin ALLAH kuwa ya cika. Kasancewar ba wani yawa ne da su ba ƴan kai amaryar tunda dangin Ammie ne kawai sai wasu a dangin Daddy da yay musu magana tun ɗazu suka baro  can gidan bikin Huznah suka dawo nan a wadace suka shiga motocin, a kuma nutse babu hayaniya babu hargowa. Su Aneesa ƙawayen amarya na tare da ita. 
     Sauran amare biyu dama sun iso suma tun ɗazun daga gidan Baban Yola, dan jiya da suka iso daga Yola a gidan baban Yola suka sauke turuga ba'a ƙaraso da su nan gidan Baba Sardauna ba da za'a amshi amaren gaba ɗaya sai yau. To su tun bayan sallar la'asar aka ɗakkosu, dan haka yanzu hankalin kowa ya koma kan isowar amaryar AA ɗin wato Maanal.
        Lokacin da suka iso bayan Oum ta gabatar da sujudar shukur ta fita da kanta har harabar gidan inda motar amarya kawai ta shigo ta fiddo Maanal da kanta daga mota. Aiko Maanal najin maganar Oum sai ta sake ƙanƙameta ta fashe mata da kuka. Itama Oum ɗin sai kawai ta fara hawaye da murmushi a lokaci guda. Nan ko wayoyi suka fara aikinsu na hotuna da video, a gefe dama Yaya Fawzan ya tanadi mai ɗauka dama na musamman da zai ɗauki komai na bikin nan dan AA idan ya samu lafiya yaga komai yanda ya kasance. Tunda ALLAH ya ƙaddara za'ai bikin yana a halin ciwo.
      An shiga da amarya Maanal har ɗakin Umma inda sauran amaren biyu suke, su Nene kuma aka basu masauki mai ƙyau dan Hajiya Majdiya ce tsaye akan komai. To da yake ma basu zo da shirin daɗewa ba sai suka wuce da wuri akan zuwa gobe zasu zo wajen walima in sha ALLAHU. Sai dai su ƙawayen amarya na tare da ita. Aiko sun haɗe da ƙawayen sauran amaren nan ko suka dunƙule anata kwasar hira. Maanal dai bata kula kowa ba, hasalima a kwance take zazzaɓi yay mata rijif. Suko sauran amaren Nuwaira da Raihana nata dama-dama da ita. Suma dai ƙyawawa kuma yarane kamar dai Maanal ɗin, garama Raihana ta girme musu dan itace yayar Nuwaira. Daka gansu suma kaga jinin Darma Family, dan kamaninsu da su Oum a bayyane suke sosai. Sun san Maanal a zamanin ƙuruciya, musamman Nuwaira da Maanal ɗin tasha jibgarta idan suka zo Kano a wancan lokacin. Sai wancan lokacin yayta dawo musu a rai suka amshi Maanal ɗin hannu bibbiyu, to dama dai baka gayama jinin Darma wulaƙanci, dattakonsu da mutuntawarsu ga kowa a bayyane take yaransu da manya. Sai dai su kuma basa ɗaukar wulaƙanci da raini ga kowa....

  _________★

      Zuwa washe gari hankalin su RK ya fara tashi akan rashin farkowar AA. Dole suka fara kaikawo a kansa da gwada dabaru. Amma dai babu alamar hakan, cigaban kawai da aka samu shine daidaituwar bugun zuciyarsa. Normal zuciyarsa ta koma dai-dai tana aiki, sai dai bayan ita babu wani ɓangare na jikinsa dake motsawa balle akai ga batun numfashi. Gashi dai nan kwance samɓal abinsa zagaye da na'urorin a ƙirjinsa da hancinsa har ma da baki. RK ne da yay wani tunani ya bama su Abbu shawarar ko a kawo Maanal asibitin ta gwada kira musu sunansa a cikin kunne.
        Babu wani ja inja su Abbu suka amince da hakan, dan irin wannan abubuwan duk dabarune na likitoci. Babu ɓata lokaci kuwa RK yay kiran Oum ya mata bayani. Dama shirin zuwa asibitin suke yi sai kawai aka saka Maanal ta shirya itama. Dama dai tayi wankanta kamar sauran amaren tun safe. Tana sanye da atamfa data mata ƙyau sosai. Sai farin mayafi daya sake ƙawata ƙyawunta da ɗaurin da Najma ta mata akan dole harda ƴar kwalliya. Sam fuskarta babu walwala sosai, dan kanta ciwo yake mata har yanzu. Ga kukan data sha a kwana biyun nan idanunta duk a kumbure. Koda suka taho ma tana kwance a jikin Oum ne. Bata wani yi mamakin ganinsu a asibiti ba tunda an sanar mata dama AA na asibiti, sai dai wani abu daya ɗan zunguri zuciyarta bayan sun fito a mota suma su Mamy dake a cikin wata motar sun fito, risinawa tai ga gaishesu, kanta a ƙasa shiyyasa bata banbance wanda ya amsa mata da wanda bai amsa ba. Sai da ta ɗago saboda kama hannunta da Oum tai zasu shiga cikin asibitin sai idonta ya sauka akan Mamy, wani mugun kallo ta samu idon Mamyn na mata akai-akaice, harga ALLAH sai da gabanta ya faɗi, amma kuma Mamyn tai saurin janye idonta dan dama a yanda take mata kallon bai zama lallai kowa ya lura ba gaskiya, da alama itama ta kamata ne a bazata. Sai dai kuma komai ya faru ne a idon Hajiya Majdiya, dan haka itama zuciyar tata sai da ta girgiza...
      Sun dai shiga ciki, inda suka samu su Babban yaya da su Abah su Baba Sardauna, Baban Yola da su Abbu duk acan, kusan ma duk mazan family ɗin na'a asibitin ne. Hakan ya ƙara saka Manaal a cikin matsanancin kunya, ta ƙara jan mayafinta ya rufe mata rabin fuska kanta kuma a ƙasa. Cike da girmamawa taje har gaban su Baba Sardauna ta durƙusa tana gaishesu kasancewar su iyayen duk suna a waje ɗaya ne zaune. Dukansu babu wanda fuskarsa bata kasance a cikin fara'a ba. Suka shiga amsa mata da kulawa da sanya albarka shi Baba Sardauna ma harda tsokanarta irin wasa na jika da kaka. Ita dai kanta a ƙasa fuskarta a rufe babu wanda zaice ga'a yanda take. Hakan sai ya ƙara saka musu ƙaunarta da jin gamsuwa da ita, dama kuma a binciken da sukai basu samu wani aibu a tare da ita ba kamar yanda suka sami akan Huznah, balle ma sun san ƙuruciyarta kaf ɗinsu musamman ma shi Baba Sardauna da Baban Yola da Abah. Abbu ne kawai sai tsintsa-tsinta saboda lokacin ba'a ƙasar suke ba.
      RK ne ya jagoranceta zuwa ɗakin da AA yake, karon farko kuma kenan da wani zai shiga ya ganshi idan ka cire likitoci da kullum ke kai-kawo a kansa. Wani bala'in girgiza zuciyar Maanal tayi da ganin yanda AA ɗin yake zagaye da na'urori tun kan su shiga, sai jikinta ya fara rawa. RK ya riga yasan tata matsalar itama, dan haka da sauri kuma cike da lallashi ya ce, “Please Maanal relax, ba wata babbar matsala Ajwaad yake a ciki ba, numfashinsa ne yay nisa da tun a daren jiya muke saka ran dawowarsa amma shiru, amma in sha ALLAHU idan yanzu kikai juriya ringa kiran sunansa a cikin kunne muna fatan nasarar dawowar tasa dan bugun zuciyarsa ya dawo normal. Dan haka ki kwantar da hankalinki nutsuwarki muke buƙata. Sannan zaki kira shi da sunan Besty ne ba sunansa ba.....”
      Da sauri Maanal ta kalla RK a karo na farko. Kansa ya jinjina mata. “Hakan shine mafita Maanal, dan wannan halin da yake ciki yana da alaƙa da tsoron rasaki da ya shiga, idan kuma ya jiki a kusa da shi a yanzu in sha ALLAHU muna fatan nasara.”
     Sosai ta zubama RK ɗin idanu saboda kalamansa, da alama jin cewar a kanta ya shiga halin ya girgizata. Shima RK ɗin ya fahimci hakan, dan haka yay murmushi da faɗin, “Maanal wasu abubuwan ba kai tsaye muke fahimtarsu a rayuwa ba sai dalili ya ratsa. Shiyyasa barin wasu al'amuran a dunƙule yafi alkairi sama da buɗesu ma duniya ko mu mu sansu. Yanzu dai kece hope ɗinmu na ƙarshe akan Ajwaad, dan haka bismillah”.
       Gaba ɗaya jikin Maanal ya gama mutuwa, hawayen da take ta faman riƙewa suka shiga zubowa, dole ta saka gefen mayafinta ta share sannan suka ƙarasa shiga cikin ɗakin. Sun sami likitoci biyu sai Abbu a tare da AA ɗin, dan haka kai tsaye gaban gadon da AA ɗin yake kwance aka kaita, tare da nuna mata kujerar dake gab da gadon ajiye. Sai da ta zauna sannan ɗaya daga cikin likitocin ya matso ta ɗayan ɓangaren AA ɗin hannunsa riƙe da file, umarnin riƙe hannun AA ɗin ya bata, dan haka tai diri-diri na jin kunya tana satar kallon inda Abbu yake. Murmushi Abbu yay a karo na farko, tare da ƙarasowa gaban gadon cike da lallashi ya ce, “My dear karki damu kinji, ki saka a ranki ceton rai zakiyi dan Ajwaad na a gaɓar rayuwa ko mutuwa ne a yanzu, in har zuciyarsa ta tsaya daga aiki to shike nan dan itace kawai ke nuna mana yana a raye a halin yanzun. Ke kuma mun tabbatar kina a cikin wannan zuciyar tasa, wannan abun da zakiyi shine zai motsata da ƙarfin ikon ALLAH ƙarfin bugunta ya gauraye raunin gaggangar jikinsa dukkan hanyoyin numfashinsa su buɗe”.
       Kanta dake a ƙasa ta jinjinama Abbu, kafin a hankali ta kai hannunta dake zane da baƙin lalle da ja saman nashi dake ajiye a kan shafaffen cikinsa. Jitai wani irin shock ya shigeta, ta ɗan ja hannun baya tana rumtse idanu, fin sakan biyu kafin ta sake kaiwa saboda maganar da Doctor ya sake mata. Gently ta sarƙe tafukan hannunsu cikin juna, sai ta samu kanta da matsesu, wata rarrauniyar ajiyar zuciya na suɓuce mata. Sanyin tafin hannun nasa ratsata yake har cikin ƙwaƙwalwa, yayinda nata dake da ɗumi na tasiri a daskararriyar gangar jikinsa. Sai da ta sake matsar da kujerar sosai gaban gadon kafin ta samu damar rankwafar da fuskantar a saitin kunnensa nunfashinta dake fita a sarƙe na sauka a ciki. Bugun zuciyar ta na ƙaruwa saboda yanda tasirin ƙamshinsa da ya gama kama masa jiki ke shiga cikin ƙofifin hancinta. Idannunta a lumshe, lips ɗinta na rawa, muryarta da wani irin rauni da sanyi kamar mai raɗa ta furta, “Besty! Besty! Besty ka tashi gani a tare da kai, Maanal ɗinka ce, Bestyn ka, ƙanwarka daka raina da hannayenka,  ka buɗe idonka dan ALLAH ka ganni kaji Besty, muci abinci tare, muyi wanki tare, muyi hira tare, ka kaini kitso ina maka kuka kana lallashina. Na takalo faɗa ka tare min koda su Didi ne.” sai hawaye sharrr suka shiga sakko mata daga idanu suna sauka akan jikinsa. Sosai kuka ya sarƙeta harta kife fuskarta a jikinsa ta sake shi mai ƙarfin gaske a cikin kunnen nasa..........✍️


09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖1️⃣0️⃣1️⃣


______________


........Babu wanda ya dakatar da ita a cikin likitocin, saboda hakan su ya musu dai-dai ne, dan RK ma gefe ya maida kansa yana murmushi. Hakama Abbu tausayin yaran ne ya wani sake mamayesa. Al'amarin kamar wani film sai ga yatsan ƙafarsa babbar ya motsa. Ai wata irin zaburar farin ciki likitocin da dama idanunsu tsaye suke kyam akan duka gaɓɓan AA ɗin sukai. Ita dai Maanal da gaske kuka yaci ƙarfinta ta yanda tama manta da ba ita kaɗai mace ba a ɗakin. Sai da hannun AA dake cikin nata yay wani irin nasifar matse nata, shi kuma yay wata irin yunƙurawar zabura har sai da gadon yay girgiza wasu a cikin igiyiyin na'urorin dake jikinsa suka fincike kansu da kansu. Da wani kalar sauri ta ɗago itama, yayinda su RK suka zagayeshi suna ambaton Alhamdullahi a tare. Sosai riƙon da AA yayma hannun Maanal ke azabtar da ita, dan riƙo ne na mazan gaske, amma ta daure dan anyi-anyi a raba hannun nasu hakan ya ta gagara, sai Abbu yace a barshi kawai a hankan. Haka yana riƙe da hannunta a gaban idonta suketa ƙoƙarin dai-daita numfashinsa da zaburar da yake yi. Fin mintuna talatin kafin komai ya daidaita ya koma dan kansa ya nutsu, yayinda numfashin nasa ke fita a hankali a hankali...
      Ƙasa-ƙasa Abbu dake kallon Maanal ya ce, “Sake kiransa”. Kanta ta jinjina, a hankali ta sake ɗan matsawa gab da gadon ta ce, “Besty!!”. Hannunsa dake riƙe da nata ya ɗan motsa, sai kuma ya ɗan ƙara damƙe natan ta yanda har sai da ta ɗan yamutsa fuska dan zafi. A hakan ta cigaba da kiran sunan nasa. A yanzu kam idanunsa dake rufe ya ɗan fara motsawa, sannu a hankali dogayen eyelashes ɗinsa dake baƙaƙe siɗik kwance suka fara rawa suma, sai kuma ya fara ɗaga su kaɗan-kaɗan tsagar idanunsa suka sake bayyana. Nuni Abbu yake mata da hannu alamar ta cigaba da kiransa dai. Ita kuma tanata maimaitawar batare da gajiyawa ba, har ALLAH ya bama AA damar buɗe gaba ɗaya juyayyun idanunsa dake a kumbure kuma jazur. Lumshesu ya sake ƙoƙrin yi irin luuuu ɗin nan, sai dai kafin su gama rufewa ya sake ɗagasu suka buɗe saboda tasirin da muryar Maanal ke cigaba da yi masa a cikin kunne. A buɗewa ta biyun kam sosai ya buɗesu, ya kuma tsaidasu a kanta, yanda ya zuba mata su cikin tsakkiyar nata idanun kamar ɗan maye yasa tsigar jikinta tashi. Dole bakinta ya kasa cigaba da motsawa

75 / 77