AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   74 / 77

219K to 222K   out of 230.9K words

kuka na fitar hankali. Tana rantsuwar bata son Sageer AA take so, itama ɗin dai Kawu Sani ɗin ne yay mata jan ido dole tai tsit. An gama shirya amarya Huznah tsaf, ashe abokan ango ana gama ɗaurin aure dama sun ɗakko hanyar Kano domin ɗaukar amaryar su. Zancen dinner ɗin da Hajiya Basariyya ta shirya anan Kaduna tasha ruwa kenan. (Sageer dai ya jima yana son Huznah tun tana ƙarama, sai dai Hajiya Basariyya na taka masa birki ganin ubansa bai kai Daddy arziƙi ba. Shi kuma sai kawai ya janye jikinsa ya barta ya cigaba da dabgarsa. Kwatsam sati uku da suka wuce Daddy ya samesa har kano ya zaunar da shi tare da masa tambayar har yanzu yana son Huznah? Sosai ya daburce a lokacin, dan harga ALLAH yana sonta har yanzu, kawai dai ya kama kansa ne dan ya fahimci uwarta da ita kanta sai a hankali. Da ƙyar ya iya jinjinama Daddy kai, aiko a take yace ya bashi ita, yaje kawai ya hau shiri biki nan da sati uku. Amma yana son yay shiru da bakinsa har sai ranar ɗaurin aure. Mamansa da Babansa ma sun sake kwakkwafarsa akan ya kame bakinsa ko a cikin dangi ba'ason kowa ya sani sai ranar. Amma zasuyi shirin biki normal sunan amarya ne kawai bazai fito ba sai ranar. Sauran ƴan uwa ma zai ce musu Daddy ne yakai kuɗin aure da kansa. Lamarin ɓoyewar ya bama Sageer mamaki, sai dai bai iya ya tambaya ba dan baya iya musu da iyayensa. Sannan yana matuƙar ganin girma da kimar Daddy a rayuwa, bazasu manta da halaccinsa ba, shine ya tsaya tsayin daka akan iliminsu da ginuwar iyayensu da dukiyarsa. Ai ko baya son Huznah akace gata zai amsa da hannu bibbiyu. Balle ma yana son abarsa).
        Sai da aka fara wucewa da amarya Huznah da tawagar dangin Hajiya Basariyya da babu yanda suka iya, dan ƴaƴansu Sani yace kowa ya shirya a wuce da shi akai amarya, wanda bazasu je ba anan cikin Kaduna suke su koma gidajensu biki ya tashi anan gidan Daddy ba'a buƙatar ganin kowa. Hakan kuwa dole sukayi, aka bar Hajiya Basariyya na faman kwasar kuka, sai manya da basu wuce biyar ba aka bar mata akan su ƙarasa haɗa kayan Huznah ɗin kafin gobe a bita da su. Kayan ɗaki dai dama kai tsaye can Daddy ya tura aka shirya a gidan Sageer, na Maanal kuma aka kai Abuja gidan su AA, ita kuma Hajiya Basariyya ta saki baki Abuja na Huznah aka kai, dan ko kaɗan Daddyn bai basu wata ƙofa ta fahimtar komai akan auren ba....

      A ɓangaren Ammie tana son ƙarin bayani daga Daddyn itama amma babu fuska, dan ya haɗe gabas da yamma yace su shirya kawai, zasuje can Kanon sai a ƙarasa bikin acan ya tanadar da gidan da zasu zauna. Ita mai biyayya ce akoda yaushe a gareshi, dan haka ta fara shiryawa ita da kaf ƴan uwanta. Wanda zasubi mota suka fara yin gaba. Musamman ƙwai da ƙarkwatar iyalan Nene, tunda dama dai sune dangin kawai, sai abokan arziƙi da ake gaisawa daga haka sukai addu'a suka kama gabansu. Wanda kuma zumuncin yay ƙarfi sosai suka shiga tawagar ƴan wucewa a mota.
        Ƙarfe biyar Ammie, Shahidah, Amaal, Nene, sai Maanal da aka tada da ƙyar daga barci aka shiryata tana faman layi suka wuce airport dan su jirgi zasu bi, harda shi kansa Daddy ɗin. Wannan abu ya ƙona ran Hajiya Basariyya da sauran danginta. Dan haka suka bata shawara itama ta shirya gobe duk su tafi Kanon gara a ƙarasa komai akan idonta, dan sun fahimci wai Daddy na fifita agolarsa sama da ƴarsa. Haka kuwa akayi, a daren suka fara shirin komai daya dace acewarsu fitar sassafe zasuyi....

     Kuce min ina uwargida ran gida Hajiya Yaya. Ai tana sashenta ita da ƴaƴanta da su Aunty Sabuwa na kwasar dariya. Dan su tun farkon faɗan daɗi yay musu. Acewarsu ai Hajiya Basariyyar ce dai-dai da Ammie. Zuwan ƴan sanda a gidan ne ya su nutsuwar dole suka cigaba da gulmar daga ciki. Koda Daddy ya dawo kuma Hajiya Yayar tazo domin bugar cikinsa sai yay mata banza, dan dama haushinta yake ji akan tura Yazeed honeymoon ɗin dole da tayi. Itama ganin yanda yay matan sai tai zuciya wai ya dizgata saboda bata da muhimmanci a garesa. Bai kulata ba taja ƴan matan ƙafafunta ta koma sashenta cikin ƴan uwanta suka sake buɗe babin zagin Ammie da Hajiya Basariyya ɗin ma. Koda za'a wuce da Huznah babu wanda yay niyyar bi a cikinsu, sai kuma Daddy yasa aka tattaro masa kaf ƴaƴan yace su shirya su bi masu tafiya Kanon. Babu yanda suka iya suna tura baki da ƙunƙuni dole sukai shirin tafiyar. Ganin haka sai Aunty Sabuwa ta zuge Hajiya Yaya akan ai ta shirya kawai suma subi ayari dan ayi komai akan idonsu. Dan Jaraba da masifa Hajiya Yaya fa bata jurar doguwar tafiyar mota saboda ƙiba amma haka ta shirya ɗin suka wuce batare da ko sanin Daddy ɗin ba......

      __________★

     Su dai su Ammie kasancewar tafiya ce ta jirgi sun isa cikin mintuna ne, dama kuma sai biyar na yamma suka wuce. Sunbi taxi ɗin cikin airport zuwa anguwar da Daddy ya tanadar musu gida. Da gani gidane sabo amma komai a kwai a cikinsa. Wannan ba abun mamaki bane dan sana'ar Daddyn kenan sayen gidaje da sayarwa. Maanal dai dana barci take ko'a hanya. Dole suna shiga aka nema mata wajen kwanciya ta kwanta. Su kuma suka fara ƙoƙarin gabatar da sallar magriba. Shima Daddy ta fita massallaci. Bayan an idar da sallar ne ya dawo yace suyi shirin zuwa asibiti, amma da nufin za'a bar Amaal saboda yara da kuma Maanal. Dan masu tahowa a mota ma na gab da shigowa cikin Kano. Wanda suka taho da Huznah ma su har sun iso, dan ita kai tsaye gidan nata mijin aka isa da ita ita da ƴan rakkiyarta...
     Su Ammie sun iso asibiti dai-dai gama jawabin Abbu, su Oum na ƙoƙarin shiga massallacin asibitin dake da ɓangaren mata dana maza domin gabatar da salla. Dan asibitin mallaki ne ga Abbu, shine wanda ya fara ginawa bayan dawowarsu Nigeria. Kafin aima RK nashi a Abuja kamar yanda ya buƙata. Suka kuma sake yin reshe a wasu sassan jihohin a yanzu haka domin dai taimakon al'umma...........✍️


09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖9️⃣9️⃣


______________


........Sosai Oum taji daɗin ganin Ammie, hakama su Babban Yaya dama su Baba Sardauna isowar su Ammien akan lokaci batare da sun fifita shagalin biki ba ya faranta musu rai matuƙa. Sun kuma sake jinjina martabawar Daddy. Ammie dama ƴa ce ga wannan family na Darma, dan duk an santa musamman ma su iyaye da ta ɗauka matsayin iyaye a sanda tana rayuwa tare da Oum. Cikin girmamawa ta dinga gaishesu da yima AA addu'ar fatan samun lafiya. Suma sunta amsawa cike da dattakonsu da mamakin ganin yanda ta canja kamar ba ita ba. Dan shi Baba Sardauna ma kasa haƙuri yayi sai da ya mata ɗan ƙorafi na gudarsu da tayi. Haƙuri kawai ta bada ita dai, dan tasan zaman kace nace da kare kanta kamar raini ne take musu. Hakama Shahidah sai da su Babban suka tsokaneta cikin ƙarfin hali. Itama dai murmushin kawai take saki kanta a ƙasa...
       Nene ce ta bama Oum labarin halin da Maanal ke ciki. Dan tunda suka iso taketa faman tambaya. Kowa yay mata addu'ar samun lafiya itama amma banda Mamy da ahalinta. Dan su fa farko ma yi sukai kamar basuga su Ammien ba sai kuma mi suka gani oho musu suka ware dai aka gaisa. Bayan sallar isha'i su Ammien sukai musu sallama da addu'a ga AA tunda ba'a bar kowa ya ganshi ba gaskiya. Suma kuma su Oum ɗin gida ma zasu wuce Fawzan da RK da Uncle Hussain kawai za'a bari. Har mota sukai musu rakkiya, bayan sun wuce suma su Oum ɗin suka wuce...

    Su Ammie sun samu ƴan tahowa a mota sun iso. Dama da abincinsu nacan Kaduna duk suka taho, dan haka sai aka samu sauƙi babu wata damuwar abinci ko ruwa balle lemuka. Sai a wannan lokacin Daddy ya samu zama da su Nene da Ammie, dan suma su Yaya Nuhu sun iso, dama suna a Kanon su ai tun daurin aure tunda Daddy ne kawai da Yaya Sani suka wuce ɗazun. Dalla-dalla Daddy yay musu bayani da tabbatar musu dama can tun kawo kuɗin aure da akayi bada sunan RK akai ba, da sunan AA su Abbu suka kai kuɗi Kaduna. Kuma sun tabbatar masa RK ne da kansa ya sakasu yin hakan, amma sun roƙesa akan dan ALLAH kada kowa yasan hakan har sai ran ɗaurin aure. Suka kuma bashi haƙuri akan al'amarin AA da Huznah bamai yiwuwa bane, dan da'a haɗa auren shi AA ɗin ya cutar da ita gara a aura masa Maanal ɗin kawai kamar yanda kowa yasan hankalinsa akanta yake. Dalilin ƙin bijirewarsa ne kawai basu sani ba kuma sun gagara ganowa. Da kuma suka binciki miyyasa shi RK ya haƙura ya sadaukar masa, sai yace musu wataran zai faɗa, yanzu dai shi buƙatarsa duk rintsi AA ya samu auren Maanal ne kawai. Shi kuma ya basu zaɓin koma wacece zai amsa da hannu biyu kuma zai riƙe amana in sha ALLAHU.
      Wannan zance shine ya girgiza Daddy, yaji zuciyarsa ta karaya sosai game da son haɗa Yazeed da Maanal daya dage a baya. Bayan wucewarsu kuma washe gari ya zaunar da Yazeed yay masa nasiha sosai sannan ya gaya masa gaskiya akan yabama AA Maanal dan shine yafi cancanta. Abinda ya shiga tsakaninsu a barshi kawai a matsayin ƙaddara da babu makawa sai ta faru su basu isa hanawa ba. Yazeed mai biyayya ne a garesa, dan haka ko jayayya baiyi masa ba. Daga ƙarshe ya bama Ammie da Nene akan ɓoye musu da sukayi tun farko shi da yaran Nenen.
          Murmushi kawai Ammie tayi, sai Nene ce keta faman sanya albarka da tabbatarma Daddy cewar baiyi laifin komai ba. Hakan ma da yay shine dai-dai. Dan ɓoye aure alkairi ne kodan gudun maƙiya da mahassada. Yanzu ba gashi anyi komai cikin kwanciyar hankali ba babu wani tsugunne-tsugunne. Amma da ace an bayyana ai ba'asan irin ƙurar da zata tashi ba sam. Hakan kuwa hankalin kowa kwance. Shi kuma Ajwaad ALLAH ya bashi lafiya da ita kanta ma Maanal ɗin. Itama Huznah suka sanya ma nata auren albarka sosai tare da roƙar Daddyn a lallaɓata dan ALLAH harta haƙura. Dan an mata laifi sosai.
     Murmushi kawai Daddy yayi. Ya kuma basu labarin yanda ya ƙulla shima auren na Huznah bayan wucewar ƴan Kano da yay nazari. Ya kuma shawarci Yazeed suka yanke hukuncin hakan dan a samu masalaha, itama a taimaketa da zaman gidan tana kara tsofewa.....

      WASHE GARI

           Zuwa washe gari duka ɓangarorin uku sai muce Alhamdullah. Idan ka cire AA dake kwance a gadon asibiti har yanzu bai farka ba. Amma dai ana saran daidaituwar al'amura da yawa a tare da shi. Maanal ma ta tashi jikinta da sauƙi, sai rashin ƙarfi da rashin walwalar fuska. Dan ko abinci sai da Nene ta zaunar da ita ta bata da kanta a baki cike da kulawa, tana kuma mata nasiha cikin hikima. Zuwa tashin hantsi Daddy da Ammie da manyan gaba ɗaya suka je asibiti suka duba jikin AA, har yanzu dai ba'a bari a shiga inda yake. Dan sun tarar da su Oum duk a waje, suma kuma basu jima da zuwa ba, tare kuma suka baro asibitin da su, saboda manyan family ɗin na Darma sun yanke a cigaba da bikin kawai, dinner ce da aka shirya gaba ɗaya sai walima, sai suka soke dinner ɗin za'ai walima kawai. A jiya ya kamata a kawo amare ayi dinner da daddare da safe ai walima da buɗar kai kowa ya ɗauki matarsa. Da kuma abin ya juye sai ya zam yau za'a kawo amaren ayi walimar zuwa gobe kowa ya kama gabansa.
        Wannan yasa shi kansa AA ɗin farkawarsa kawai ake jira dan za'a wuce da shi can KK HOSPITAL na Abuja ne. Idan kuma an samu yanda ake so ma falillahil hamdu.....

________★

    A ɓangaren su Hajiya Basariyya kam dole ta sauka a gidan ƴan uwarta, su kuma can dangi suna gidan amarya wasu kuma a gidan iyayen angon musamman dangin su Daddyn, ita kuma dangin Hajiya Basariyya ɗin aka barsu a gidan Huznah amarya da har safiyar yau kuka ya gagara tsaya mata. A hakan ma dan Maman Yaseerah na tsaye a kanta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta auren nan sai sun kashesa ta auri AA ta fidda Maanal. Dan haka ita da wata ƙanwar Hajiya Basariyyan itama hatsabibiyar kanta sune zagaye da Huznah ɗin suna ta ɗorata akan mugayen abubuwa da zata dinga tafkawa mijin dama iyayensa duk da kuwa ƙanin ubantane uban nasa uwa ɗaya uba ɗaya. Itako tsaf take ɗauke komai harma tana ƙara nata a cikin zuciya. Oho sudai dangin Daddy ko'a kwalar rigarsu, shahalin bikinsu sukeyi cike da farin ciki, Hajiya Yaya kuwa ta shige cikinsu tayi kane-kane danta ƙona ran Hajiya Basariyya, dan su basu san su Ammie suma suna nan Kanon ba sam, tunda sai da suka taho sannan Daddy ya taho da su Ammie, kuma sunji ance ango babu lafiya a tunaninsu ai biki ya tsaya tunda anata kai waketa kaya, shiyyasa taga gwara ta maida hankali tayi maganin Hajiya Basariyyar kafin ta koma kan Ammie, duk da ma dai case ɗinta da Ammien yanzu kaɗanne ALLAH ya raba ɗanta da ƙarfen kafa, sai dai hassadar wanda yarinyar ta samu a matsayin miji ne ya kasa wuce musu a ƙahon zuciya daga ita har ƙanwarta Sabuwa...
       Duk abinda Hajiya yayan keyi yana komawa kunnen Hajiya Basariyya, tayi niyyar shiryawa kuma itama ta koma can cikin dangin mijin nasu da ƙyar ƴan uwanta suka dinga tausarta akan tabar komai a gama bikin lafiya idan suka koma gida ayita. Amma yanzu kam ta shanye kodan su san ta yanda zasu raba wannan aure na Huznah.....

________★

        Hajiya Mamy kam duk mai hankali yay mata kallo ɗaya zai san a harmutse take, sai dai da yake za'a iya danganta yanayin nata da halin da AA ke a ciki kai tsaye, tunda an san duk kawaicin da zata nuna dole hankalinta ya tashi. Amma a ɓangaren Hajiya Majdiya wata kalmar data fita daga bakin Mamy karaf ta shige a kunnenta batare da su sun farga da ita ba, sai dai kafin Mamy ta cigaba da surutunta yan uwanta na tausarta Maman Saheeba ta lura da Hajiya Majdiya ɗin, shine tai saurin ƙwaɓar Mamy da fargar da sauran kasancewar Hajiya Majdiya ɗin a wajen ta hanyar ambaton sunanta. Ita dai Hajiya Majdiya ta fita tana juya kalmar Mamy ɗin da tace, _“Nifa bana jin zan iya cigaba da wannan kauda kan, gara ayita kawai ta ƙare tunda basu da wuta basu da aljanna”._
       Hajiya Majdiya ta wuni da waɗan nan kalamai na Mamy, sai kuma abinda ya faru a Kaduna na hararar da Mamy tai ma Ammie ya shiga dawo mata. Ta auna da yanda Rafeeq ya tsara kasancewar auren batare da ko su kansa dake ƴan uwansa ciki ɗaya sun san manufarsa ba. Kai hatta Mah-mah bata san da wannan shirin ba. Daga shi sai baba Sardauna sai Abbu da Alhaji ƙarami da Baban Yola. Kai itafa magana ta ALLAH zuciyarta ta fara mata rawa akan Mamy. Daga ƙarshe ta kasa haƙuri tai kiran RK a waya tace tana son magana da shi, dan ita irin mutanen nan ne mara iya riƙe abu a rai yayta damunsu, tafi son sha yanzu magani yanzu dan ma karta shiga haƙƙin mutum.
     Babu wani jimawa kuwa RK ɗin yazo tunda dama suna a kusa da gidan ne. Gefe suka koma yana tsokanarta da faɗin, “Aunty wai ko kuɗin zaki ƙara min ne, dan dama a talauce nake wlhy babu daɗi ango ya kasance babu kuɗi a jikinsa”.
      Dariya tayi da faɗin, “Kai dai son kuɗinka yayi yawa Rafeeq. Sai kace kayi wata tsiya a bikin ne kuda akaima auren gata. Ni yanzu ma da zaka saka min ƴar miliyan biyu zan so hakan ina son shiga kasuwa kafin na bar kanon”.
        “Ni da ke ba'a san wanda yafi wani son kuɗi ba ai, ina ma laifin kice dubu ɗari biyar”.
    “Ko ita na samu ɗin na gode”.
“To wannan kam zaki samu ɗin”.
“Aiko na gode ALLAH ya saka da alkairi angon Nuwaira”.
         Murmushi yayi da ɗan taɓe baki, itama sai ta murmusa ɗin kawai. Sai kuma ta kallesa da ƙyau. “Wai nikan Rafeeq na tambayeka mana”.
     “Ina jinki Aunty miya faru?”.
   “Ya akai al'amarin aurarrakin nan ya canja haka wai, tun jiya kowa abu ke cinsa a rai halin da Ajwaad ke ciki ya danne komai.”
         “Kai aunty dan ALLAH ku bar wannan zancen kawai, mu ɗauka haka ALLAH ya tsara dama tun farko, ni banga wani abun kace nace ba....”
   “Ba kace nace bane ba Rafeeq, wani abu ne ya ban mamaki yanzu, Aunty Babba da Umma sun sakani kira musu Aunty Kamila zasuyi magana sai na samesu cikin wani yanayi ita da ƴan uwanta, yayinda wani furuci nata ya daki zuwciyata, _wai ita bata jin zata iya cigaba da wannan kauda kan, gara ayita kawai ta ƙare tunda basu da wuta basu da aljanna._ To su waye? Kauda kan mi kuma ta daɗe tanayi har take jin bazata jureba a yanzu? Dan inda zaka

74 / 77