AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   59 / 77

174K to 177K   out of 230.9K words

daya ma lura da ita ba ya sata fahimtar fa ba mafarkin bane gaske ne. Sai taji zuciyarta na neman tarwatsewa. Karan farko ta motsa jikinta kamar mara laka ta fice itama tabi bayansa. Tasan halinsa sarai baya ɗaukar raini ko rawar kai, dan haka ta tsaya har ya fito daga cikin bakery ɗin hannunsa ɗauke da ledoji guda biyu. Yanzun ma sam hankalinsa bai kai gare ta ba, dan haka cikin kwantar da murya ta ce, “Assalamu alaikum Yaya AA”.
      Cak ya tsaya daga tafiyar da yake yi, sai kuma kamar mai ciwon wuya gently ya dubeta, irin duban nan na sau ɗaya ya ɗauke kansa yana shanye dukkan sassaucin fuskarsa. Da sauri ta matso inda yake sosai. Muryarta har rawa take wajen gaisheshi. Sau ɗaya ya amsa mata, har yayi kamar zai wuce sai kuma a daƙile yaɗan sake dubanta. “Mikike yi anan?”.
            Wani irin sanyi taji a ranta da ƴar kulawar tasa. Saita samu kanta da sake kwantar da murya cike da yanga ta ce, “Munzo sayen snacks ne a bakery ɗin nan”.
      “Okay”.
Ya faɗa yana wucewarsa. Binsa tai da kallo kamar mayya, hawaye na ciko mata idanu. Ƙawarta da itama jikin nata ke a sanyaye ta ƙaraso gareta. Batace mata komai ba ta share hawayenta sai kuma ta miƙa mata hannu ta amshi bag ɗinta. Wayarta ta ciro ta shiga laluben number yayarta. Bugu ɗaya kuwa Saheeba ta ɗauka. Sai kawai ta sakar mata kuka. A ruɗe Saheeba ta shiga jera mata tambayoyi. Da ƙyar cikin garsheƙar kuka Nuratu ta sanar mata komai. Sai dai maimakon taji Saheeba ta amsa mata sai taji muryar Mamy, ashe lokacin suna tare ne Saheeban na'a sashenta.
     Cikin ɓacin rai Mamy ta ce, “Ki bisa wajen Saloon ɗin ki ɗauka min hotonsa shi da yarinyar”.
        “Amma Mamy zai gane nice na ɗauka na tura muku, kuma ALLAH sai ya hukuntani”.
      “Okay kinfi tsoronsa kenan akan umarni na ko Nuratu?”.
    “Ba haka bane Mamy. Dan ALLAH kiyi haƙuri”.
    Ƙwafa Mamyn tayi, tare da yanke kiran kawai. Hakan yasa Nurry sauke ajiyar zuciya. Ko giya tasha ai bazatayi gangancin aikata abinda Mamyn tace tayi ba. Yaya AA fa, tab ɗin wlhy dandaƙar ɗan akuya zai mata har gaban uwarta ba damuwarsa bace. Dama dai ace bai ganta bane da zata iya ta ɗauka ɗin. Amma ya ganta ta gansa har sunyi magana ai ko zata cika duniya da rantsuwa yasan itace ta aikata. Haka ta samu kanta da zama a cikin mota ita da ƙawar tata suna dakon jiran fitowarsu.....

____________★

          “Daddy wannan shine bayanin dana samu a kansa. Sunansa Bukar Bala Ɓatagarawa. Senator ne kuma.”
     Murmushi mai faɗi Daddy yayi tare da gyara zaman wayar tasa yana kallon Yazeed dake masa bayanin dan video call suke yi. Kafin ya iya cewa komai Yazeed ya ce, “Daddy wai miya haɗaka da shi ne kake masa irin wannan binciken?”.
     Kai tsaye Daddy ya ce, “Maanal yake so”.
        Cikin matuƙar mamaki da razani Yazeed ya ce, “Maanal kuma Daddy”.
    “Ƙwarai da gaske, dan har yaje ya samu iyayenta acan Giro sun gama magana......”
    Tsaf Daddy ya zayyane masa komai. A take yanayin Yazeed ɗin ta canja, idanunsa suka kaɗa jazur. Cikin tsananin damuwa ya ce, “Daddy wannan nake gudu dama tun farko. Yanzu shike nan na rasata? Wannan fasiƙin mutumin zasu bata saboda zalunci?”.
          “Baka rasata ba Yazeed, sam baka rasata ba. In har ina raye in sha ALLAHU bazaka rasa Maanal ba. Ka kwantar da hankalinka kai dai kabar komai a hannuna. Yanzu yaushe zaka dawo? Kwana biyar fa ya rage ɗaurin auren nan amma babu ango babu alamarsa”.
       Sai da Yazeed ya haɗiye yawu mai ɗaci sannan a sanyaye ya ce, “Daddy zan taho zuwa alhamis insha ALLAHU. Kayan dana maka bayani nake son naga saukarsu akan idona. Kuma sunce sai Wednesday zasu iso. Shiyyasa na bari alhamis sai na dawo”.
      “Bazai yiwu ba Yazeed. Ka taho Wednesday ɗin kawai. Kada mutanen nan suga rashin damuwarka akan ƴarsu tayi yawa. Ita ɗin ƴar uwarka ce kada ka wulaƙantata kodan Baba da Inna dan ALLAH. Ka kwantar da hankalinka ka ƙyautata mata sai ALLAH ya mallaka maka abinda kake so cikin sauƙi. Maganar Alhaji Bukar kuwa kada ma ta dameka, dan bazatai wani tasiri ba da izinin UBANGIJI.”
        “In sha ALLAH zanyi duk yanda kace Daddy. Bara naje akwai meeting da zamu shiga dama”.
    “Okay babu damuwa sai na jika, ALLAH yay maka albarka. Ya azurtaka da zuri'a masu albarka da zasu maka biyayya kamar yanda kake mana”.
     “Amin Daddy na gode”.
   Kai kawai Daddy ya jinjina tare da yanke wayar. Sai kuma ya maida dubansa ga Ammie da tun fara wayar tasa ta shigo, har zata juya ta koma ya hanata ta hanyar dakatar da ita da hannu. Dole ta dawo ta zauna. Akan kunnenta sukai duk zantukansu, sai taji zuciyarta ta raunana da tausayin Yazeed ɗin. Yaron kirki mai natsuwa da sanin mutuncin iyayensa.. har ga ALLAH tana son Maanal ta auresa, sai dai tana tsoratar mata wahala da ƙiyayyar uwar miji dan itama ta ɗanɗana a baya tasan ciwon da hakan ke da shi......

____________★

       Kafin a kammala kitson nan babu kalar fitinar da Maanal batai ma AA ba. Damma manya akayi mata shikku. Sosai kitson yay mata ƙyau, amma sai faman haɗe fuska take yi. Shi dai wanda take yi domin shi ɗin bai kulata ba. Sai hotuna da yay mata a kaikaice batare data fahimta ba. Fuuu ta fice a wajen, wanda sukai mata kitson na mata bye ko kulasu batai ba. Suma dai sunayi ne don neman fada kawai, dan zukatansu sun gama yarda ƙanwarsa ce ita. Dole ta bari ya ƙaraso ya buɗe motar dan key ɗin na hannunsa, sai dai yanda taga kamar yana tafiya slowly ga hannunsa saman cikinsa ya sata zuba masa ido dan tun ɗazun dama ta lura kamar yana shiga wani ɗan yayi na kai ciwo amma jarumar fuskarsa na dannewa. Fuskarsa ama a yanzun a ɗan yamutse take alamar dai something is happing.
      “Baka da lafiya ne?”.
   Kallonta yay da idanunsa da suka canja launi, sai kuma ya janye kamar baya so ya ce, “Mi kika gani?”.
       Kallon nasa ta cigaba da yi batare da tace komai ba. Shima sai ya basar kawai ya buɗe motar ya shiga. Kafin ta zagayo ta shiga dole ya kife kansa a steering saboda yanda cikinsa ya sake murɗa masa. Dama tun jiya haka yake sama-sama. Dauriya kawai yay ya fito aiki dan baya son ɗagama Oum hankali. Wannan yanayin nasa kuma a garesa normal yanayi ne daya daɗe ciki tsahon shekaru. Dan ma ƙaddarar rayuwa ya ɗan lafar da al'amarin nasa a baya kaɗan.
       “Ajwaad”.
  Maanal ta kira sunansa. Sai da ya ɗan cije baki sannan ya ɗago ya zuba mata firgitattun idanunsa da suka saka zuciyarta harbawa. Babu shiri ta janye nata da sauri. Lumshe idanun yay cikin ƙarfin hali ya motsa lips ɗinsa kaɗan.
      “Bazaki daina kirana da Ajwaad ɗin nan ba ko?”.
     Batare data kallesa ba ta ɗan tura baki da faɗin, “To ba sunanka bane?”.
         “Sunana ne, amma ke baƙya cikin masu faɗarsa. Idan kuma kika ƙara i will teach you a lesson”.
    Baki ta taɓe kawai. Shima sai bai sake cewa komai ba ya sake maida idanunsa ya rufe. Kusan mintuna biyu batare daya buɗe ba ya ce, “Har yanzu kina driving?”.
        Kamar zata gaya masa baƙar magana sai kuma ta danne a taƙaice ta ce, “Uhmm”.
   Numfashi ya ɗan sauke kaɗan, sai kuma ya buɗe murfin ya fita a motar. Ta side ɗin da take ya zagaya, ita dai tsoro ne keson shigarta da tunanin mike damunsa ne. Buɗe inda taken da yay ya sata juyowa tana kallonsa.
          “Fito ki koma can”.
     “Amma ni fa gaskiya.....”
  “Please Besty bana son surutu cikina ke ciwo”.
     Haɗiye sauran maganar tai kawai, ta zuro ƙafafunta ta sakko. Ɗan matsawa yay ya bata hanya. Sanda ta shigo shi har ya zauna ya rufe ma, bayansa ya kwantar a jikin kujerar idanunsa a lumshe. Sai da ta rufe sannan ta ɗan zuba masa idanu, sai kuma a hankali ta ce, “Na kaika wajen Rafeeq ne?”.
    Fuskarsa ce ta ɗan sake tsukewa, sai kuma ya buɗe idanun slowly a kanta.........✍️









✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖7️⃣9️⃣


_____________

.........Zuba mata su yay kamar a fusace, dan haka ta janye nata.
     “Nace miki ina buƙatar ganinsa ne?”. Ya faɗa cikin nuna jin haushi.
    Baki ta taɓe batare data tanka masa ba, sai da ta tada motar tai reverse sannan ta fita a wajen. Idanunsa a kanta yana kallon yanda take tuƙin. Shine ya koya mata mota kusan gab da ƙaddara zata rabasu. Dan in bai manta ba bayan sun kammala jsce ɗinsu ne ta damesa tana son iya mota. Da farko Oum taƙi tace sai ta kammala secondary. Amma tai ta damunta dole tace ya koya matan. Da yake tasa kanta a lokacin cikin abinda baifi sati ba ta iya. Wani lokaci idan an aikesa ya fita da mota suka tafi tare takan matsa masa sai ya bata, idan yaƙi ta tasashi gaba da rigima dole yake batan duk da yana jin tsoro dan tayi ƙarama sosai.... Ganin tana shirin ɗaukar hanyar asibiti ya dakatar da ita. “Malama nace bazanje asibiti fa. Normal ne idan naje gida nasha lemon tsami zai daina”.
     Gefen titi ta ɗan gangara, cike da damuwa a fuskarta ta ce, “Kana wasa da lafiyarka ko, lemon tsami magani ne, kuma ni ban taɓa gani ko jin dan mutum na ciwon ciki ya sha wani lemon tsami ba”.
       Murmushi ya ɗanyi da lumshe idanunsa ya sake buɗesu a kanta. “Kece dai baki sani ba saboda yarinta”.
     “Niba yarinya bace ba wlhy”.
   Ta faɗa tana murguɗa baki.
“Oh really?”.
“Kaima ka sani ai”.
“Yanzu dai na sani ɗin kam, tunda ni dai yarinya na sanki a gabana. Amma tunda ke da kanki kin yarda kin girma zanfi kowa farin cikin hakan kodan halin da nake ciki”. Ya faɗa cike da shaƙiyanci. Harararsa tai da sake tada motar ta ce, “Kai dai ka sani.”
      Murmushi yayi mai faɗi ya maida idanunsa ya lumshe da harɗe hannayensa duka a ƙirji. (Humm In ba Maanal ɗin ba wake ganin yawan murmushin AA haka arhar banza).
      “Saka belt ɗin ki, ki kaini gida kafin tunani na ya canja na nema hanyar tabbatar da girman naki a titin mutane to Madam Maanal Giro”.
        Sam ba fahimtar inda zancen nasa ya nufa tai ba. Amma taji a ranta akwai shaƙiyanci a ciki. Bata kulashi ba ta sanya belt ɗin ta sake tada motar. Hanyar anguwarsu ta ɗauka, dan gara ta masa yanda yake so su rabu lafiya kawai.....

     Ganin hanyar da Maanal ta ɗauka ya saka Nurry dake binsu a baya tun daga shagon Saloon saurin dannama Mamy kira. Bugu biyu ta ɗaga, ko sallama batai ba ta ce, “Yauwa Mamy ga su nan sun nufo nan gidan, kuma itace ma ke tuƙasu, amma kamar baida lafiya ma”.
        Kai ta jinjina tana sauraren abinda Mamyn ke faɗa daga can, kafin ta yanke kiran sannan taja motar zuwa hanyar nasu gidan. Ƙawarta ta ce, “Amma Nurry baƙya tsoron ya gane kece kika faɗa ma mamansa”.
     “Bazai gane ba, shiyyasa nake so ta gansu da idonta ai.”
     Kai kawai ƙawar tata ta jinjina alamar gamsuwa.....

        A ƙofar katafaren gate ɗin gidan nasu ta tsaida motar, hakan ya sashi buɗe idanunsa ya kalleta. Ganin tana ƙoƙarin kunce belt ya ce, “Yanaga kin tsaya anan? Ki shiga mana”.
        “No ka ƙarasa da kanka, ni zan koma daga nan”.
    “Bazaki gaida su Oum ba?”.
“Next time”.
Kansa ya jinjina kawai ya cire nasa belt ɗin. “Kije da motar zan aiko driver ya amsa”.
        “A'a zan hau taxi”.
    Dakatawa yay daga ƙoƙarin fitar da yake, ya ɗan juyo yana kallonta. “Kin san fa bana son musu, taxi kuma na haramta hawanta daga yau”.
        Komai batace da shi ba saboda yanda ya tsatstsareta da idanu. Shima sai bai sake cewar ba ya buɗe ya fita. Sai kuma ya ɗan duƙo ta glass ɗin windown. “Kije gida magrib ta kusa. Kuma kiyi tuƙi a hankali”.
      “Ni Company zan koma ɗaukar kayana”.
    “No ban yarda ba kije gida. Driver zai taho miki da su. Ki kula da kanki”.
         “ALLAH ya ƙara lafiya”.
    Ta faɗa itama tana maida glass ɗin ta rufe duka tare da yin baya. Yana tsaye yana kallonta har sai da ta ɓace masa. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da furzar da iska. Sai kuma ya shafa cikinsa yana yamutsa fuska kaɗan. A hankali ya juya yay knocking gate ɗin gidan nasu. Maigadi ya leƙo yana tambayar waye. Ganin AA ya sashi haɗiye sauran maganar, mamaki fal ransa na ganinsa a ƙafa. Bai dai ce komai ba ya gaisheshi. Shi kuma ya amsa masa yana wucewa ciki. Da Mamy ya fara cin karo zaune a gaban sashen Oum, sai Naufal da Anum dake wasa da keke. Yanda ta wani zuba masa idanu tun daga nesa ta sashi janye nasa da ga kallonta. Cikin dauriya ya ƙarasa inda taken, su Naufal da sai yanzu suka gansa suka sheƙo da gudu suna masa oyoyo. Daurewa yay ya tarbesu, sannan ya shiga gaishe da Mamyn. Bata amsa ba, sai mugun kallo da take jifansa da shi.
      “Ina motar taka?”.
Ta jefa masa tambaya a bazata. Bai iya ƙarya ba, ya kuma tsani mai yi, amma ya fahimci yau dolensa ma ya yi tan. Batare daya yarda sun haɗa ido ba ya ce, “Tana gareji Salihu ya kaita. Nima taxi na biyo”.
     Rasama abin cewa Mamy tayi, dan yayi wani kicin-kicin da fuska, sai kawai ta zuba masa idanu. Shiko ya sake ciɗin-ciɗin da fuska. Batare daya yarda ya sake kallonta ba ya saki hannun su Naufal ya nufi sashensa dan ruwa kawai yake buƙatar sakarma kansa. Ko Oum baya son ta gansa a wannan yanayin. Ita kanta Mamy ɗin bai so ta ganshi a hakan ba....
       A ɗan tsawace ta dakatar da shi, dole ya tsaya yana mai lumshe idanunsa, sai kuma ya dawo da baya inda take. Miƙewa tai batare data sake kallonsa ba cike da bada umarni ta ce, “Anjima ka sameni zan yi magana da kai”. Daga haka tai wucewarta. Da kallo kawai ya bita, wani abu mai nauyi na masa kai-kawo a cikin wuya da maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sosai. A hankali ya furzar da iskar numfashi, sai kuma ya nufi sashen nasa....

__________★

     Baki a wangale maigadi ke kallon Maanal daya buɗema gate. Taja motar a hankali zuwa cikin gidan. Bawai tuƙin nata ne ya bashi mamaki ba, dan yasan tana jan mota idan tazo. Ganin ɗirkekiyar motar da take ja ɗin ce da kuma sanin da yay mata bai taɓa ganin ta tuƙa wata mota ba sai ta gidan ya sashi a mamakin....
       Turus itama ta tsaya tana kallon motar RK lokacin da take fitowa. Sai kuma ta ɗan leƙa gaba kaɗan. RK ɗin ne shima da kansa zaune a cikin motar tasa ya zubama motar data ajiye ido ko ƙyaftawa bayayi. Ta tabbatar kallon ƙurillar da yakema motar ya gane ta wacece ne. Sai kawai ta dake abinta ta ƙarasa garesa. A hankali ya janye idanun nasa daga kallon motar ya maida kanta. Batare da ya amsa sallamar da take masa ba ya furta, “Dama kina jan mota haka?”.
       Guntun Murmushi kawai tai masa ta ce, “Uhmm!”.
     “Masha ALLAH, kinyi ƙyau kuwa da motar”. Ya faɗa yana fitowa da ƙyau daga motarsa.
    “Oh harda zolaya ma abin kenan?”.
“Babu wata zolaya gaskiya na faɗa miki. Naje ɗaukarki a office AS ɗin Boss ɗinki yace kun fita tare tun la'asar. Shiyyasa na wuto nan dan na matsu na ganki”.
       Murmushi tayi batare data tanka maganarsa ta farko ba ta ce, “Kamar wanda ya shekara bai ganni ba?”.
    “Miye maraba my queen. Kwana huɗu fa. Ya kuka baro su Ammie?”.
    “Lafiya Lau suke, suna gaisheka. Ya aikin?”.
    “Alhamdullahi munata fama. Shi AA ɗin yana office kenan?”.
    Murmushi ta saki a taƙaice, dan ta fahimci dole dai so yake sai anyi maganar AA ɗin nan. Sai kawai kanta tsaye ta ce, “Yana gida baida lafiya. Dan da wajenka ma zan kaishi yace na dai ajiyesa a gida”.
         “Mike damunsa?”.
     “Kamar ciwon ciki yace”.
  “ALLAH ya bashi lafiya, yasa kaffara ne. Bari nai salla zanje na duba shi.”
     “Okay ai ni dama da motar tashi ka wuce, sai driver ya bika da ita”.
   “A'a, bashi ya baki ba da hannunsa”.
“Dama yace zai turo driver ya ɗauka ne. Ni kuma bana ma so Didi taga motar a gidan ne”.
       “Dan mi to?”.
  “Kawai”.
Shiru kawai yay yana kallonta. Yasan ƙarshem zancen kenan. Yau ma ai babu laifi an amsa masa magana da tsaho sosai. Ajiye zancen yay shima gefe ya fara wanda ya kawo shi ganin magrib na sake gabatowa. “Magriba na gabatowa. Ga shi inada uziri da daddare. Kuma ina son muyi magana yanzu ALLAH yasa ban takura ki ba”.
    Kanta

59 / 77