Author : Billyn Abdul Category : Romance
dukkan idanunta a kansa, fuskarta tuni ta ƙwaɓe da shagwaɓa ta ce, “Kuma sai ka rama ɗin?”.
Shima kallon nata yake sosai cikin ido, sai kuma a hankali ya rissinar da nashi yana mai girgiza kai. “Zanyi tunani, idan da yiwuwar na yafe to”.
Baki ta tura tare da masa harara, shi kuma ya taɓe nasa yana sake kawo mata abincin daya ɗibo a spoon saitin baki.
Kafaɗa ta maƙe masa zatai magana ya ce, “Shiiii”.
“To ka bani zanci da kaina”.
“Kin tabbatar?”.
Da sauri ta jinjina masa kai. Plate ɗin ya miƙa mata babu musu. Dan shima dai ya fahimci idan bai batan ba za'a iya samun matsala. A hankali ta cigaba da cin abincin, sai kuma ta sake ɗakko masa batun Abideen kodan kauda wannan kallon da yake mata. Idanun nasa kuwa ya janye, sai kuma ya a harɗe hannayensa a ƙirji da kwantar da jikinsa a kujerar sosai. Tsohon minti ɗaya kafin ya amsa mata da.
“Miye damuwarki wai da zancensa? Ko shima saurayin naki ne? Dan naga ke samarin naki basu da adadin ƙirga”.
“Eh mana, farin jini ai kenan, ko kuma kana kishi ne?”.
“Mizai sa nayi kishi kuwa ina matsayin Yaya. Kidai sani sai na tantance wanda ya dace kozan bashi ke”.
Har ƙarƙashin rai zancen nashi ya soki zuciyar Maanal. Amma sai ta dake itama cike da basarwa ta ce, “Ba damuwa Yayana, ai duk yanda kayi dai-dai ne. Amma dai inada zaɓina gaskiya, nasan kuma bazaka min auren dole ba, kaima shine zai kasance zaɓinka ai ko?”. Ta ƙare maganar cikin salon waro idanunta a kansa. Wani hayaƙin takaici ne ya turniƙe sa, dan har launin idanunsa sun sauya. Janyesu yay daga cikin nata batare daya amsa mata ba. Itako saita wani ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki. Ta ce, “Koda yake ai kasan zaɓin nawa ma. Kai dai kawai ka fara shiri nan da wata biyu zaka aurar da ƙanwarka in sha ALLAHU. Dan Rafeeq ya tabbatar min baya son ya wuce hakan, nima kuma hakan nafi so. Dama ya kawo min ƙararka daren jiya”.
Da ace Maanal na kallon kalar mugun kallon da AA ke mata data tsuke bakinta, koda yake tana jinsa a jikinta. Amma ta daure ta danne abinta. Karo na farko yaja tsaki. Kallonsa tayi, amma shi kuma sai ba kallonta yake ba yanzu. Hasalima ya jawo laptop dake a saman desk ɗinne kamar a fusace. Gabanta ya tura, babu wasa a muryarsa ya furta, “Ki duba za'a tura miki saƙo a email ɗinki. Next week akwai tafiyar da kamfani zai yi har da ke ciki zuwa ƙasar Chaina. Tafiya ce ta kwana goma zuwa sati biyu. Wannan zanen nake son ki duba min shi kafin lokacin tafiyar, kije da laptop ɗin”.
Da mamaki ta ce, “Kamar ya? Amma dai kasan baza'a barni a gida ba, dan mi zaku saka sunana?”.
“Saboda dolene kiyi tafiyar”.
Dangwarar da plate ɗin abincin hannunta tayi, tare da faɗin, “Idan na ajiye aikin gaba ɗaya fa?”.
“Wannan ne baki isa ba ai”.
“A matsayinka na wa?”.
“Mi kike ci na baka na zuba”.
“Ajwaad kana shigar min hanci da yawa fa”.
“Ki fyatoni kawai ki huta mana”.
Rasama abin cewa tayi dan takaici. Shi ko da yasan ya kaita maƙura idanu kawai ya zuba mata cike da kallon ƙurullar daya saka illahirin jinin jikinta yamutsawa. Zuciyarta ta shiga kumburowa kamar ƙwaɓaɓɓiyar fulawar burodi bugun ƙato. Da ƙyar ta danne rawar da muryarta ke neman yi cike da masifa ta ce, “Wai wannan wane irin haramtaccen kallo ne dan ALLAH. Nifa wlhy ana takura rayuwata, ana shiga haƙƙinna, idan ba'a son aikin nawa a koran a kamfanin mana.....” daga ƙarshe ma harshen nata ya harɗe ta yanda ita kanta bata ma fahimtar abinda take faɗa. Shi dai ya zuba mata ido kawai yana hukuntata da su. Sai da tayi mai isarta ta gama sannan ya tura mata goran ruwa gabanta.
“Ai bance ina so ba”.
Ta faɗa cike da tsiwa.
“Hakane”.
Ya bata amsa shima baki a taɓe. Sai kuma ya tsuke fuska kamar bashi ba ya gyara zamansa ƙafafu a harɗe hakama hannuwansa harɗe a ƙirjinsa. Babu alamar wasa a tattare da shi ya furta, “Kinyi abinda na saki?”.
Harrarsa tayi, duk da yanayin nashi ya sa zuciyarta shiga tsoro, amma a dake ta ce, “Kai ka isa ne ka sakani abu nayi?”.
“Oh haka kika ce?”.
Baki ta murguɗa masa kawai.
“Hummm ki cigaba da min wannan gatsinan zanyi maganinki soon. Na kuma baki nan da gobe ki dakatar da Rafeeq daga yaudarar da kike son masa. Idan ba hakaba zan baki mamaki”..
Murmushi tayi mai ciwo da zuba masa idannunta da suka kaɗa. “Oh mamaki? Ai ka daɗe da bani mamaki tun shaiɗan na baƙauyensa. Ajwaad ka daina wahalar da kanka da tunanin wannan abubuwan da kakeyi zaisa na ji tsoronka. Kasa a ranka ni Maanal matar Rafeeq ce in sha ALLAHU. Ina raga maka ne saboda Oum da Abah da Mamy, amma wlhy idan ka cigaba da shiga sabgata zaka sha mamaki na”.
Daga haka ta miƙe tana ajiye masa key ɗinsa tai ƙoƙarin wucewarta. Amma sai ya saka mata ƙafa babu shiri ta koma cikin kujerar daɓar ta sake zama. Cike da isa ya ƙara jawo tashi kujerar gabanta ya wani tattare ko'ina ta yanda ko space ɗin fitar numfashi mai ƙarfi bai rage mata ba. Idanunsa da suka juye gaba ɗaya ya sauke a cikin nata, ya kuma hanata janyewa duk da ƙoƙarin hakan da take yi. Sai kawai taji kamar ta saki kuka ta huta.
Wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata, batare da ya sake cemata komai ba ya kamo hannunta ya ɗaura mata ƙaramar shopping bag mai tambarin apple a jiki, ya sake ɗakko key ɗin motar nan ya saka mata shima, ya ɗauka laptop ɗin itama ya ajiye a saman ƙafarta. Har lokacin idanun nasa a cikin nata yaja kujerar baya ya miƙe abinsa cike da takunsa na isa ya zagaya ya koma kujerar zamansa, desk ɗin ya dafe da duka hannayensa biyu ya ranƙwafo, duk da ba kusa suke da juna ba sai da taji wajen ya sake mata nauyi da matsatsi.
“Fatan nasara”.
Ya faɗa a hankali sannan ya kai zaune a kujerar ya hau ayyukansa. Tsuru kawai tai tana kallonsa na tsawon lokaci. Shiko ya cigaba da aikinsa kamar ma ya manta da ita, dan kalamanta wani mugun saka zuciyarsa tafasa suke ainun. Itama kasa cewa komai tayi, sai kawai ta miƙe tana mai ajiye masa key ɗin motar ta wuce abinta da shopping bag ɗin da laptop ɗin kawai. Dan wadda ya bata ranar ce ta kuma fahimci wayace. Tana buƙatar wayar ne a yanzu dan har sim cards ɗin suna a hannunsa dama, bata sani ba kuma ko ya haɗa mata da su. Sai da ta fice ta maida ƙofar ta rufe sannan ya ɗago a hankali ya sauke idanunsa akan key ɗin. Janyewa yay ya maida kan ƙofar kamar yana hangota har yanzu a wajen. Sai kuma ya furzar da iska yana mai ajiye document ɗin hannunsa da ɗan ƙarfi ya tura duk hannunsa biyu cikin sumar kansa ya shiga yamutsata, tare da kwantar da bayansa jikin kujerar yay sama da kan nasa yana furzar da zazzafan huci. Tsohon lokaci ya ɗauka a haka da shima bai san adadi ba, kafin ya sake sauke numfashi mai nauyi ya cigaba da aikinsa...........✍️
_😂Jaraba, idan aka haɗu kamar abin arziƙi, amma daga ƙarshe da wahala a rabu lafiya sai da bala'i🤣, wai mike damun gayun nan ne😆😆? Maga dai yanda za'a ƙare da batun zuwa chaina😌🥱. 🏃🏃_
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣6️⃣
______________
.........A Kaduna kam shirin biki ake sosai, dan a yau laraba akai gagarumin kamun amarya daya zaga ko'ina na media. Waje suka kama yasha ado da kwalliya kamar yanda itama amarya tasha ado. Dj ya warware sauti ƙawayen amarya da amarya da ƙawayen uwar amarya da ƙannen ango har ma da gayyar soɗi suka cashe gwargwadon iko. Amarya tasha turare har yana hawar mata kai. Ango dai baima ƙaraso ba sai bayan sallar isha'i. Shima a media ya tsinta shagalin kamun. Tsaki kawai yay ya dinga wuce videos ɗin dan shi a nasa tsarin baya buƙatar duk waɗan nan bidi'oin. Amma yasan bai isa cewa baza ai ba Mammah ta hargitsa masa hazo. Yau ɗin ma itace ta kafa masa dogon gargaɗi akan ya dawo Kaduna domin halartar events ɗin da za'ayi. Duk da dama dai yayi niyyar hakan shima bisa umarnin Daddy. Yaso fara tsayawa Abuja wajen Maanal amma sai aka samu akasi, dole ya haƙura ya wuce akan zuwa gobe zai koma Abujan, dan baya tunanin Maanal zata zo wajen bikin nan. Shima a karan kansa baya son ma tazo ɗin...
Ammie da Nene da surukan Nene da Sakina sunje wajen kamun, duk da da dai Ammie batayi niyyar zuwan ba Hajiya Majdiya tace suje. Dan zuwa yanzu kam sun ƙulle da Ammie sosai bisa umarnin Oum da tuni ta zayyanema ƙanwar tata komai dake tsakaninsu da su Maanal. Su Ammie sun sha habaici, dan har Hajiya Yaya ma taje wajen kamun. Amma kamar yanda Ammien ta saba sai ta nuna bama tasan suna yi ba. Su Hajiya Basariyya dai anata safa da marwa su amarori. Ta shige taro tayi damal-damal dan ta san sirrin komai da takun komai, gefe kuma ta gogama Ammie kashin kaji da bata haushi. Sai dai kuma hakan bai samu ba, dan ta firgita da ganin su Ammie a taron kamun batare da tayi tunanin zatazo ɗin ba. Duk sai jikinta yay sanyi.
Itako Ammie bama ta nuna ta san da zamanta a wajen ba. Sai da tsabar munafuncin Hajiya Basariyyan ya sata zuwa ta wani ranƙwafo tanama Ammie magana a cikin kunne. Ba wata magana bace mai ma'ana, amma mutane sai su ɗauka wani sirrin ne akeyi irin na iyayen biki. Nan ko tambayarta tai kawai wai mi za'a kawo ma baƙinta. Murmushi Ammie tayi tana sake jinjina makirci irin na Hajiya Basariyya, itama sai kawai ta amsa mata da komai ma a basu zasu ci. Daga haka ta maida hankalinta ga wata ƴar uwar Daddy da yaranta da suka ƙaraso wajen, dan suna ɗasawa sosai da Ammien....
______★
A media su Manaal sukai kallon kamun, sai kuma ga Amal ta kira Shahidah. Nan suka ɓige da zancen suna dariya. Dan sun fahimci duk anayi ne wai a basu haushi. Ita Maanal ma tunda suka fara wannan zancen sai kawai tai shiru ta maida hankalinta ga saita wayarta. Dan tunda ta dawo ta cireta a kwali ta sanyata a caji. Ganin ta cika ta ciro ta dan ta saka sim card ɗinta, ɗayan kuma ta ajiye akan gobe in sha ALLAHU zata sayo wata wayar dan riƙe waya biyu ya kamata kenan. Shiyyasa bata taɓa damuwa da wannan iPhones ɗin banzar ba ita kam. Bayan sun gama wayar ma tashi tai ta nufi ɗaki domin kwanciya....
_____________★
Kamar yanda RK ya faɗa a safiyar yau yay shirin zuwa Kano, dan haka misalin goma na safe daga asibiti daya leƙa Mawaad Company ya wuce. Maanal na tsaka da aiki Yaqub na mata bayani aka sanar da ita tana da visitor a waje. Ta ɗan yi mamaki, amma sai zuciyarta ta hasaso mata RK ne. Dan shi kaɗai ne ke zuwa companyn wajenta. Amma to miya hanashi shigowa har office ɗin nasu?. Rashin mai bata amsa ya sata miƙewa tana cema Yaqub tana zuwa. Kai kawai ya jinjina mata, dan haka kawai yaji kishi a ransa da koma waye wannan visitor ɗin. Canjawar yanayin nasa ya saka su Zaharadeen.. kwashewa da dariya. Bai kulasu ba, dan ya fahimci sa'idonsu ya fi na mata....
RK dake tsaye jikin motarsa ya zubama Maanal dake nufosa idanu. Sosai tai masa ƙyau cikin atamfar jikinta data kasance skert da riga. Daka ganta kaga cikakkiyar bahaushiya ƴar asali. Zazzaƙar muryarta data rangaɗa sallama ta ratsa kunnuwansa. Amsa mata yay fuskarsa da murmushi, sai kuma cike da tsokana ya furta “Anya bazan saceki ba daga nan a biyomu da kayanmu kawai”.
Batare da niyya ba ta saki guntun murmushi, tare da ɗan jan gyalenta ta rufe fuskarta. Sai hakan ya sashi sakin dariya cike da shauƙi. A haka ta gaishe shi, tare da ɗorawa da faɗin, “Amma miyya hanaka shiga ciki?”.
“Boss ɗinki mana, yace in dai da soyayya nazo na dinga tsayawa a waje nayi, in ba hakaba kuma zai hukunta mu ni da ke”..
Sosai mamaki ya kashe Manaal a tsaye, a ranta tana sake jinjina halayyar Ajwaad. Yanzu ashe sai da ya iya yima RK maganar nan? ALLAH ta ɗauka wasa yake yi iya kanta gargaɗin nasa kawai zai tsaya. A fili kam sai cewa tai, “Yanzu kai kuma kaji maganarsa ka daina shiga kenan?”.
“Kai haba shi ɗin mi, kawai dai dan ina a hanya ne shiyyasa. Jirgina nanda minti arba'in zai ne”.
“Kanon dai?”.
“Eh mana, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe my queen. So nake next week in sha ALLAHU a gama komai na mallaki ƴar baiwar nan kafin na zube ƙasa”.
“Humm daɗin baki”.
“Oh haka kike tunani kenan? Ai tsakani na da ke har abada babu daɗin baki. Duk abinda kika ji baki ya furta shine har a ƙarƙashin zuciyata”.
“To ALLAH ya tabbatar da hakan”.
“In sha ALLAHU ya tabbatar. Na ganki a online jiya da dare, ya dawo miki da wayar ne?”.
“Oh kaga ma na manta shaf, ya dawo da ita, gashi na manta da taka a gida”.
Murmushi yay mai sanyi da faɗin, “No taki ce, ki cigaba da amfani da ita kawai. Dan ma nasan bazaki yarda muje a sai wata ba shiyyasa nayi shiru”.
“Amma Yaya Rafeeq.....”
“Shiiii!!! Don't say anything madam. Yimin addu'a kawai na wuce kar naje airport a makare”.
Murmushi ta masa, tare da jera masa addu'ar daya buƙata. Cikin nuna jin daɗi yake amsa mata da amin. Kafin suyi sallama ya shiga mota. Tana daga tsaye a wajen har sai da ya fice yana ɗaga mata hannu sannan ta juya ta koma ciki fuskarta cike da murmushi. Koba komai zuciyarta na girmama RK, yana da wani kaso mai girma kuma a wajenta, dan yana sakata a farin ciki da sauƙin kan nan nasa. Jinin Oum ai ba abin da zata taɓa wulaƙantawa bane a rayuwarta har abada....
Cikin wani irin takaici da raɗaɗin zuciya AA dake kallonsu ta jikin gilashin office ɗinsa ya kai hannu ya shafa ƙasumbarsa. Babu abinda ya tsaya masa a ƙahon zuciya ya ƙi ya wuce sai sassanyan murmushin da yaga sunama juna da wanda ta shige tana yi. Wato ya fahimci Rafeeq bazai gane karatun kurma ba, sai ya fito masa a ainhinsa sunyi uwar watsi tukunna.
Ji yay gaba ɗaya ma aikin ya fita masa a rai. Sai kawai ya fito a office ɗin. Ko kallon AS baiyi ba ya wuce. Gaba ɗaya yabar companyn, sai ma ya nufi villa dan dama yana da meeting da ministar yau.....
Yanda basu haɗi ba yau kwata-kwata baya buƙatar su haɗun, dan yana son ya bata lokaci shima ya nema mafita....
A ɓangaren Maanal ma dai tayi mamakin yau bai tsakura mata ba. To sam bama su haɗu ba har lokacin tashi, sai tayi tunanin ko dai baizo office ba yau, kokuma yaji gargaɗin data masa. Koda yake tasan mutumin nan tasan halinsa. Gargaɗinta bazai sa ya fasa abinda yay niyya ba, akwai dai abinda yake shiryawa. Hakan na nufin dole ta saka ido, dan tayi alwashi a ranta saifa ta tabbatarmasa a yanzu WUTSIYAR RAƘUMI TAYI NESA DA ƘASA. Rafeeq da kowa yake ganin bazata iya aura ba shine zaɓinta....
_🏃Yauwa ƙawalliya, ina bayanki sai Uncle Rafeeq ko Abuja ba kowa🤪. Dangin AA ku kama Nuratu da Huznahn ku yafi muku🥱🏃_.
____________★
“Yanzu ke wane mataki kika shirya ɗauka ne Kamila?”.
Numfashi Mamy ta sauke mai nauyi, sai kima ta dubi Maman Saheeba datai maganar. “Inaga zanje Kano a weekend ɗin nan”.
“Kano kuma? Yin me? Wajen wa kuma?”.
Sai da Mamy taja fasali, ta sake furzar da numfashin takaici sannan ta ce, “Abbu”.
“Mahaifin Fateema fa kenan?”.
“Yes shi, harma da Baban Yola da Baba Sardauna. Ita kanta Gwaggo Khadi ɗin da Mah-mah ɗin duk zanyi magana da su”.
Sosai yanzu kan Maman Saheeba ke murmushi. Ta ce, “Wato dai tarihi ne zai maimaita kansa?”.
“Wannan itace kawai mafita ai. Idan ba haka ba narasa ta inda zan ɓulloma al'amarin. Ke dai kawai mu fara shiri ma Nuratu. Amma fa kamar yanda na sanar miki ina son a haɗa masa da yarinyar nan da su Abdull suka kawo, dan so nake na birkita Fateema matuƙa fiye da akan su Fawzan”.
Gimtse fuska Maman Saheeba tayi. Mamy ta kamo hannunta cike da lallashi. “Dan ALLAH ki fahimceni ƙanwata, badan na tozarta Nuratu bane ko ƙuntata mata. Dan babu wata ɗiya da za'a auro da zata kasance a sama da su jinina. Shiyyasa ko'a yanzu a komai kin san