AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   65 / 77

192K to 195K   out of 230.9K words

kema Saheeba tafi Nibras a gareni. Dan yanzu haka ma al'amarin Nibras ɗin ya fara kaini wuya wlhy. So nake shima Fawzan ya ƙara aure. Ya duba tsakanin Barirah da Mabrooka ya zaɓi ɗaya. Shekara kusan shida babu wani bayani, sai rikici ya haɗosu ta dinga zuba masa gori kamar ance mata shine baya haihuwar. Shekaran jiya kamar Ajwaad zai daketa, kin sanshi akan ƴan uwanshi ba ragi babu ragowa. Ƴar tsirkun gidan tamu dai da Abahn su suka kwakkwaɓe shi da ƙyar. To gara yay auren mu tantance ina matsalar take.”
       “Tab ɗin amma Aunty kin fa san halin Hajiya Rahane, zata iya komai akan wannan taɓararriyar ƴar tata mace tilo guda ɗaya”.
     “Nima kuma zan iya komai akan nawa ɗan Gambo. Fawzan nada haƙuri a cikin ƴan uwansa. Sannan matsalar rashin haihuwar nan tashi na damuna wlhy”.
     “Dole akwai damuwa kam, ALLAH ma yasa ba munafukar gidan naku ce tai masa wani abun ba kamar ita dan kada ya haihu, kai ni hatta rashin auren Ajwaad ina ji a raina a kwai lauje cikin naɗi. Dan komai matar nan zata aikata tunda ba ƙaunar yaran take ba, kawai munafunci ne su kuma sun kasa ganewa sam. Tunda ba gashi ta dake dawo da mayyar yarinyar nan rayuwarsa ba”.........✍️


_Nifa bara na faɗa gaskiya, bana son babar Saheeba ɗin nan wlhy. Idan nazo wajenta kamar na jawota na fallasa mata maruka haka nake jin raina🥺☹️🙄😲🏃._


      

     






09032345899



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖8️⃣7️⃣


______________


........“Humm taya zasu gane tunda ba haka nan ta barsu ba. Kedai kawai a rufe rufau. Shiyyasa yanzu a shirye nake kan batun dawowarsu wajena. Auren Ajwaad ɗin kawai nake jira na fara ƙaddamar da komai na shiri na.”
      “Ina bayanki wlhy ALLAH kuma ya taya miki. Sai kuma ya ran nan su Naufal uwar tace min kwana biyun nan hankalin yaran ya fara karkata a kanta.”
           “Hummm nima na fahimci hakan. Kin santa kamar mayya take, amma zan sake sabon shiri akan su suma. Yanzu dai ki shirya muje Kano ɗin tare Please”.
    “A'a Yaya Kamila kada muyi haka dake. Ai idan suka gammu tare zasu iya zargin wani abun. Kidai je ko ke da Yaya Raliya mana”.
     “Kema kin kawo shawara. Bari zan yi magana da Yaya Raliya ɗin..”

_________★

       Da mamaki Maanal dake sauka a taxi take kallon Abideen dake tsaye a ƙofar gate ɗinsu. Yana ganinta shima ya tashi tsaye sosai daga jinginar da yay da mashin ɗinsa roba-roba. Da girmamawar data bata mamaki ya ce, “Barka da dawowa sister Maanal”.
       Ɗan zuba masa idanu tayi, sai kuma cikin kasa daurewa ta ce, “Abideen lafiya kuwa? Mi kazo yi gidan mu?”.
    Murmushi yayi tare da shafa kansa. “Magana nazo muyi dan ALLAH ki daure ko mintina biyar ki bani”.
          Shiru kamar bazata ce masa komai ba, sai kuma ta jinjina kanta. “Okay shigo ciki”. Ta faɗa tana shigewa....

    A cikin rumfar bunun da akai adon gidan da ita har uku suka zauna. Ya sake gaishe da Maanal da girmamawar da take sake ɗaure kanta.
       “Humm Abideen ni wlhy sake ɗaure min kai kake. Wai wannan sissinkuy da kan na miye haka?”.
    “Girmanki ne Sister Maanal. Nazo nan ne domin neman afuwarki dan ALLAH. Sannan na roƙeƙi ki bama boss haƙuri kota hanyar Dr RK ne na koma kan aiki na, na san na aikata kuskure. Kuma wlhy sharrin shaiɗan ne dana zuciya. Amma in sha ALLAHU bazan sake ba. Dama ban taɓa aikatawa ba sai yanzu, kuma Alhamdullahi bamma kai ga ƙarasa badu abinda suke buƙatar ba sai wasu kaso a ciki”.
        “Su wanene? Mi kuma suka buƙata ka basu kai kuwa. Ni sai sake rikitani ma kake, miye alaƙata kuma da boss da zan saka shi ko roƙonsa ya maida ka wajen aiki...”
     “Humm Sis... Maanal kenan. Bara dai na buɗe miki zancen. Kusan sati biyu kenan idan baki manta ba ranar wata laraba mun fito daga company ni da ke da Yaqub bayan an tashi, sai ke kika shiga taxi keda Yaqub ni kuma nace zan ƙarasa wajen ɗan uwana a ƙafa dake aiki a companyn AREWABOOKS”.
     Kai Maanal ta jinjina masa alamar eh anyi haka.
    “Yauwa to bayan wucewarku wani dattijon Alhaji mai suna senator Bukar ya tareni da buƙatar son yin magana da ni. Da farko ban damu ba, saboda mutane da yawa irinsa sun sha biyo ma'aikatanmu mata domin suna son su ko sanin inda suke. Ya buƙaci na shiga motarsa, shine yake tambayata miye sunanki? Babu wani damuwa na sanar masa. Ya tambayen aikinki a Mawaad nan ma na faɗa masa har kaɗan daga halayyar ki dana sani. Shine yamun godiya tare da ɗaukar maƙudan kuɗi ya bani, ya kuma ce na bashi number ta dan zan masa wani aiki a kanki. Kin san zuciya bata da kashi, ganin kuɗin daya bani daga tambaya kawai na bashi amsa da batafi ƙwara huɗu ba sai ban masa masu ba na bashi. To tun daga ranar fa duk wani motsinki a Company sai na tura masa. Ina miki video batare da kin sani ba da ɓoyayyar camara ina tura masa kullum. Wlhy ban san taya boss ya gane ba shine jiya yake tuhuma ta akai. Kuma jiya kamar yanda kuka bani shawara na gaya masa gaskiyar komai dana aikata amma duk da haka yace naje gida sai ya nemeni. Wlhy hankalina a tashe yake sis... Manaal. Ina cikin damuwa matuƙa, da aikin nan nake taimakon mahaifana, dan shekarar babana uku kenan yana fama da jiyya, nine babba a gidanmu nine koman su. Na samu aikin nan ne a dalilin Dr Rafeeq, lokacin da aka kwantar da babana a asibitinsa saboda zaman shiru sai naita zane-zane shine ya gani yace zai sama min aiki kodan na kula da iyayena dan a lokacin hatta kuɗin asibitin mun kasa biya duka. Ban san alaƙarki dasu boss ba, amma nasan kina da kusanci da Dr Rafeeq sosai, dan ALLAH ki jagoranceni wajensa kozai taimakeni ya bama Boss haƙuri tunda ɗan uwansa ne jininsa, kuma yana jin maganarsa......”
      Wani irin kallon takaici Maanal ke masa, wato wannan dattijon da yake magana shine yaje Giro wajen mutanen can neman aurenta, ashe akanta ne ma AA yayma Abideen haka. Ranta a ɓace ta miƙe tana faɗin, “Ai Inaga zuwa gareni bashi da wani amfani Abideen. Tunda ai kaima kana da alaƙa da Rafeeq ɗin, kamar yanda ya samar maka aiki nima aikin kawai ya sama min, kaga alaƙar tamu duk iri ɗaya ce”.
    Cikin sauri yasha gabanta. Kamar zai duƙa ya ce, “Dan girman ALLAH ki gafarceni, sannan ki yafe min kuskurena. Wlhy ba rasa aikin bane kawai damuwata, cutar dake da na dingayi ta hanyar miki video ina tura masa batare da kin sani ba. Ban fahimci hakan zai iya zama illa ba sai da boss ya fargar dani. Tabbas yanda rayuwa ta lalace senator zai iya amfani da waɗan nan videos ɗin wajen ɓata miki suna ta hanyar maidasu a mummunar siga, alhalin kuma ke baki ma san an yi ba.”
     Wani irin mugun bugawa ƙirjin Maanal yayi, dan ita kanta hankalinta bai kai can ba sam. Ai bama tasan ta shiga ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”. Shi ko Abideen na faman jera mata kalaman ban haƙuri kamar zai yi kuka. Tsallake shi tai ta wuce ciki, ta barsa yana faman roƙo da magiya....

Koda ta shiga bata iya ta kula su Barrah ba dake mata oyoyo, sama-sama ta tattaɓasu ta wuce ciki. Tana shiga ɗaki ta sakama ƙofa key, sai hawaye shaaa. Haka kawai zuciyarta ke bata kamar abinda AA ɗin ya hango zai faru zai iya faruwa koma yana gab da faruwar. Tunda ita bama tasan wanene Senator Bukar ɗin nan ba ai. Ya ALLAH, tabbas ya kamata ta bincika, kuma a wajen AA ɗin kawai zata samu dukkan information ɗin da take buƙata.  Wayarta ta ciro a bag, sai da ta fara sarrafata sai kuma ta tsaya cak dan tunawa da ai bata da no ɗin AA ɗin. Jagwab takai zaune a cikin sofa. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran RK ta tambaya number ɗin AA ɗin, sai kuma wani sashe na zuciyar ya ƙwaɓeta. Ta hasko AS, shima dai ta ce a'a. Oum. Nanma taji bata gamsu ba. Dama dai tana da layin Yaya Fawzan ne ma, shi kam ƙila ta iya tambaya. To ko RK ɗin zatace ya bata layin Fawzan ɗin?. Gamsuwa da wannan shawarar ya sata kai hannu zata ɗauka sabuwar wayarta sai idannunta suka sauka akan wayar RK daya bata.
       (Mizai hana ki duba a wayar nan ko zaki samu no ɗin ma) Wani gefe na zuciyarta ya ambata mata. Ai da sauri ta ɗauka wayar kuwa ta hau binciken numbers ɗin Kai daki-daki abinda bata taɓa maida hankali tayi ba. Bawani yawane da su ba, dan kusan ma da alama duk contacts na family ɗinsa ne a ciki. Amma sam babu sunan AA babu alamarsa. Har zata ajiye cike da damuwa sai kuma ta sake scrolling ta koma tsakkiya inda taga My S1 da 2 har ma da 3. Sai kawai ranta ya bata My Son yake nufi, babban yaya 1, Fawzan 2, AA 3. Cike da tabbatarwa ta jinjina kanta. Amma gudun samun matsala sai tace bari ta ɗan gwada amma bazatayi magana ba tunda tasan dai RK zai gani ya kira shi ba ita ba.....

______★

      “Kamila Kano kuma? Wace irin tafiya ce haka ta ujila kin san fa gobe juma'a, kuma na sanar muku Saturday zaku rakani Kaduna ko?”.
        “Hakane Abahn su, nima tafiyar ta dole ce. Kuma ai a goben zanje na dawo in sha ALLAHU. Sai nabi jirgin safe na dawo da yamma. Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni, ALLAH idan banje a goben ba da wahala na samu lokaci”.
    “Humm to wai mizaki je yi ne?”.
  “Nafa gaya maka Yaya Raliya ce bata jin daɗi, tunda aka gama hayaniyar bikin nan sai a hankali. Jiya su gambo sukaje, shiyyasa nace nima bari naje gobe ai kaga dai baza'ace ba'aga mutum ba. Da harda Oum ɗin yara ma zamu je, to bana son takura mata tunda jikin bawani yayi tsanani bane ba”.
        Ɗan iska kaɗan Abah ya furzar daga bakinsa tare da lumshe idanunsa ya buɗe kamar yanda AA keyi idan zai yi magana. “Shike nan ALLAH ya kaimu. Aiko sai ki daure ki ƙarasa gidan Baba dan kwana biyu yayi mura shima. Ya hana na faɗa muku ne dan kar Fateema ta tada hankalinta”.
         “ALLAH ya bashi lafiya. In sha ALLAHU can ma zan fara zuwa, har Baban Yola ma saina leƙa su dan kwana biyu bamu je ba. Da bikin nan naso zuwa sai kuma tafiyar nan tamu ta ratsa”.
    Kai kawai Abah ya jinjina mata ya cigaba da aikinsa. Ita kuma ta miƙe cike da farin cikin samun nasara tace masa tana zuwa. Nan ma hannu ya ɗaga mata kawai.....

_________★

       Bugun shigar kiran na bugawa ne da bugun zuciyar Maanal. Sai da wayar tana gab da tsinkewa sannan aka ɗaga. Sosai ta rumtse idannunta ta kasa cewa komai, daga can shima kuma baice komai ba har na tsawon sakanni. Sai zuwa can ƙasa-ƙasa ya furta.
        “Ina massallaci, idan na fito zan kira”.
   Daga haka ya yanke. Da masifar ƙarfi ta saki numfashinta data riƙe, tare da buɗe idanunta. Kai anya zata iya kuwa? Kodai ta barshi kawai. Kai ina bazata iya ba, maganar videos ɗin nan sune tashin hankalinta. Kada mutumin nan yaje ya aikata abinda zai zama sanadin bugawar zuciyarta. Ganin lokacin sallah zai ƙure ya sata haƙura da tunanin ta tashi ta hau cire kaya duk da ba sallar zatayi ba, tana dai son yin azkar ɗinta a irin lokacin kamar yanda ta saba. Jiki a sanyaye ta wuce bathroom yin wanka.
       Har akai sallar isha'i bai kira ba. Ita kuma ta kasa fita dan gudun kada ta fita ya kira. Bata son zuwa da wayar falo kuma ya kirata a gaban Didi da Uncle Sadeeq. Koda Linda ta shigo ta sanar mata abinci ya zama ready catai ta kawo mata ɗaki yau ta gaji ne. Ta kuma ce tana gaida Didi. Da girmamawa Linda ta amsa mata ta fita, ita kuma ta hau shirin barci. A haka Linda ta sake dawowa ɗauke da abincinta. Kasa taɓa abincin tayi, ta zauna a bakin gado ta ɗauka novel ta hau karatun dole wai duk dan cinye lokaci. Sai dai sam ba wani fahimta take ba sam.
      Sai ƙarfe tara da wani abu kiransa ya shigo. Zabura tayi daga kwancen da take tana duba wayar, ganin shine ke kiranta video call ma sai da zuciyarta ta girgiza. Ji take kamar taƙi ɗagawa, amma zuciyarta na ingizata. Haka ta tashi zaune ta warware ƙaramin veil ɗin data naɗa a kanta ta rufe jikinta sannan ta ɗaga dai-dai gab zata tsinke. Ai wani irin faɗuwa gabanta yayi lokacin daya bayyana mata a screen ɗin wayar tar. Jikinta har rawa yake ta kife wayar da sauri tana ambaton sunan ALLAH numfashinta na wani sam da ƙasa da sauri-sauri.....

     Daga can shima AA ɗin kife wayar yayi da sauri yana ambaton sunan ALLAH, harga ALLAH shi duk zatonsa Rafeeq ne fa, ko video call ɗin yayisa ne dan tabbatar da Rafeeq ɗin yana a Kanon ne kamar yanda yace zai je. Dan gaba ɗaya ya manta ne da maganar kiranshi da yace zai yi ɗazun sai yanzu yana cikin wanka abin yazo masa a rai, shine yana fitowa batare da tunanin komai ba ya shiga masa video call daga shi sai guntun towel daya saka iya ƙugu zuwa gwiwa. Gashi ya ajiye wayar a saman mirror ne ta yanda ta hasko jikin nashi sosai. Ya jima tsaye hannayensa duk biyu dafe da mirror ɗin yana ambaton sunayen ALLAH kafin ya samu ya ɗan dai-daita. Wayar ya ɗauka, har yanzu tana online sai dai baya ganin komai sai duhu. Zama yay da ƙyau ya katse kiran, maƙoshinsa sai yawo yake cikin wuyansa da sauri-sauri. Gaba ɗaya yama rasa wane kalar tunani zai yi akan wayar Rafeeq a hannunta. Sai duk yaji zuciyarsa ma na masa zafi. Ɗayar number RK ya shiga kira, sai dai harta katse ba'a ɗaga ba. Cike da takaici ya sake ajiye wayar, sai da ya bada wasu sakanni zuciyarsa ta ɗan sauka sannan ya sake ɗaukar wayar yay mata normal call.........✍️






09032345899



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖8️⃣8️⃣


______________

.........Harta yanke ba'a ɗaga ba. Haka ya sake kira. Kira fin biyar bata ɗaga masa ba. Ya cije lips, dan duk duniya Oum kawai yakema kira fiye da ɗaya sai ko Abah. Amma daga basu ba in har ya maka kira ɗaya baka ɗaga ba shike nan, sai in ka kirashi back, bai kuma zama lallai ya ɗaga maka ba sai yaso koda shike da buƙatar wani abu kuwa.
     Samun kansa yay da sake kiran, yanzu ma har ya fidda rai sai kuma yaji an ɗaga. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke acan ƙasan maƙoshi, tare da kai hannu ya shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake jiƙe da damshin ruwan wanka. Kamar ɗazun yanzu ma shiru tai masa, amma sai ya danne yay sallama. Amsa masa tai murya ƙasa-ƙasa, kai daga ji kasan a cikin kunya take.
         “Am sorry nazata Rafeeq ne, shiyyasa na kira a wannan yanayin”.
     “Uhm”.
Kawai ta faɗa a can ƙasan maƙoshi, alamar matsanancin nauyinsa take ji har ma bata son maganar. Shina ya fahimci hakan, dan haka ya saki batun kawai.
         Cikin son kauda wancan yanayin ya katse shirun da sukayi da faɗin. “Kina son ganina ne?”.
     Da sauri ta ce, “A'a, dama.......”
  Sai kuma tai shiru. Numfashi ya ɗan sake fesarwa, kafin a ƙagare ya furta, “Daman mi?....”
        Sosai tsigar jikinta ke tashi saboda yanda yake magana can ƙasan maƙoshi. Ga wani amo dake ratsa mata zuciya na fita daga cikin silent voice ɗin nashi. Daƙyar ta iya danne kanta, da ɗaɗɗaya ta ce, “D..a man akan Abideen ne”.
          Lips ɗinsa ya ciza da ƙarfi, kamar wanda yake a gabanta idanunsa suka ɗan kaɗa. Muryarsa na ɗan canjawa da ƙara kauri ya furta, “Miye damuwarki da shi ɗin wai?”.
       “Yazo gidanmu ne”.
    “Gidan ku?”.
“Eh har ya sanar min komai daya faru. Wlhy hankalina a tashe yake da maganar videos ɗin nan. Kada mutumin nan ya cutar dani kamar yanda ka faɗa, kuma wlhy ko saninsa banyi ba, bamma taɓa ganinsa ba.”
         “Amma yake iƙirarin an bashi aurenki?”. Yay maganar cike da zafi.
    “Ni wlhy ban sanshi ba ƙarya yake min. Ni dan ALLAH ka bani number ɗinshi zanyi magana da shi”.
       A taƙaice ya ce, “Banda”.
Shiru ta ɗanyi na wasu sakanni dan jin yanda yay maganar a Zafafa. A tunzure, kuma cike da shagwaɓa itama ta ce, “Toni ya kake so nayi?”.
    Shiru ya mata, har sai da ta cire wayar a kunne ta kalla. Ganin yana online ya sata sake jin haushi. Cike da tsiwa ta ce, “Ni zaka wulaƙanta dan na nema taimakonka?”.
    Nan ma shiru. Ai a fusace ta yanke kiran, tare da dangwarar da wayar. Shima a nasa ɓangaren wayar ya ajiye kawai ya miƙe. Zuciyarsa

65 / 77