AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   77 / 77

228K to 230.9K   out of 230.9K words

nagama Safa da marwar jawoka a bakin rami kamin fitsara fa. To bari kaji bar ganin ka samu, yanzu nan saina maidaka doguwar suma da allura”.
         Dariya Uncle Mahmud harda da Uncle Hussain harda hawaye, duk da wannan irin drama ɗin tsakanin AA da RK abune a bayyane a tsakaninsu kowa ya sani. Amma yau ɗin daya haɗa da tasu Fawzan sai ta saka kowa nishaɗi. Yayinda sashen su Mamy ke jin kamar zasu mutu. Ƙarshe dai Umma ce ta kira RK akan ya tafi wajen amaryarsa da aka kai tun ɗazun dare nayi. Suma su Uncle Hussain duk sai suka musu sallama. Ganin haka su Maman Saheeba da takaici ke neman kashewa suma sukace zasu wuce dare nayi. Sai Nuratu da muryarta ke faman rawa alamar danne kuka tace ita zata zauna a wajen Mamy ta kwana. Amma sai mamanta tace a'a tazo su wuce, dan su mamy gobe zasu wuce Abuja da safe. Haka babu yanda ta iya ta bisu, suna fita ta rushe da kuka kuwa dan yanda ko kallonta AA baiyi ba ya zafeta matuƙa. Dan kasa jan motar data tuƙosu sanda zasu zo tayi, sai Maman tata ce ta amsa. Nibras ma dai kukan take a kaikaice. Bata taɓa jin tsanar family ɗin Fawzan ba irin yau a rayuwarta. Dan duk yanda ake bata labari da misalta mata yanda suka shaƙu da su Maanal bata san abin yakai har irin haka ba gaskiya. Duk rashin magana irin ta babban Yaya kaga yau yana biyema wannan iskancin nasu ai kasan abin babba ne. Shi kansa AA da kowa yasan baƙin halinsa jiba yanda yake ma yarinyar nan ko kunyar su Oum babu..
      Oho AA dai yama maida hankali akan amsar naman da Maanal ke bashi cike da jin nauyi, gashi dan wulaƙanci da son bata kunya sai ya wani riƙe hannun nata a duk sanda zata kai masa a baki. Kallon kuwa da ya ke binta da shi gaba ɗaya tayar mata da tsigar jiki yake yi. Shi ko da alama ta lura ko'a jikinsa. Kamar kuwa ta sani ko'a jikin nasa, duk da adukan abinda yake yana cijewa ne kawai saboda Mamy, dan sam yaƙi yarda ya kalleta tunda suka shigo. Har cikin rai kuma yana tsoron keɓewarsu da ita duk da yasan itama tasan yayi biyayya ga umarninta, saboda har yanzu ji yake al'amarin kamar mafarki wai Maanal matarsa ce. Tunda ya farka da yamma su babban Yaya dake tare da shi da su Uncle Hussain sun sanar da shi komai. Shi kansa a yanzu baima san irin ƙaunar da yake ma RK ba. Duk kuwa dama can a kaf dangin nasu ƙaunar da yakema Rafeeq daban ce a rayuwa. Duk da basu rayu tare ba tun ƙuruciya, kusan ma sai bayan faruwar abinda ya faru tsakaninsa da Maanal a jiyyar da yayi ce shaƙuwar tasu ta fara da Rafeeq ɗin. Amma tabbas har yanzu jinsa yake kamar barci yake komai a mafarki ne zai farka yaga Rafeeq ya auri Maanal, shi kuma an aura masa zaɓin Mamy...

       Har sha biyu Mamy, Umma, Oum, Hajiya Majdiya da su Babban Yaya, Saheeba Nibras sai Maanal suna asibitin. Sai da baba Sardauna ya kira waya yace su taho haka nan Doctor nason yima AA allurar da zai samu isasshen barci sunje sun tsare su kuma suna jin kunyar yin magana sai da ɗaya daga cikinsu ya kira Baba Sardauna ɗin a waya sannan. Haka badan sun so ba suka hau shirin tafiya. Dan hira ake mai daɗi. Amma Maanal gaba ɗaya a takure dama take jin kanta da rayuwarta. Dan ma inda ALLAH ya taimaketa bayan ta gama bashi farfesun sai romon ya ɗan zubar mata a jiki shine ta shiga zuwa toilet ɗin ɗakin wankewa kamar yanda Umma ta umarceta, data dawo sai ta canja wajen zama. Duk da kallon da AA ke mata ƙasa-ƙasa da mata alama ta dawo da ido taƙi kulashi, tama maida hankalinta ga Najma suma hirarsu ƙasa-ƙasa duk da Najma ɗin ce ke tsiyaya surutun ita nata murmushi. Sai Fawzan dake kusa da su dake saka musu baki jefi-jefi. Hakan da Maanal tayi ba ƙaramin birge Umma tayi ba. Dan ta sake yarda da tarbiyyar yarinyar ɗari bisa ɗari, hakan na nuna musu koda aka rabu mahaifiyarsu batai sakacin cigaba da inganta tarbiyyar su ba kenan. Ana cewa za'a tafi itace gaba-gaba a fita kuwa. AA ya bita da kallo yana jin kamar ya jawota ya hanata tafiyar yace anan zata kwana. Sai dai babu yanda ya iya. Suna haɗa ido da Fawzan ya wani ɗage masa gira cike da tsokana, kafin ƙasa-ƙasa yanda kowa bazai ji ba ya ce, “Kota dawo ne Auta? Kaga sai ai amarcin a gadon asibiti kawai”.
         Kunnen Fawzan Babban Yaya da yaji komai ya kama, a haka ya jashi yana faɗin, “Kai dai bakin nan naka ko”.
     Dafe hannunsa Fawzan yay yana kiran Oum, yayinda AA ke murmushi da faɗin, “Babban Yaya dan ALLAH ka cire kunnen duka”.
    Oum ce ta ƙwaci Fawzan a hannun Babban Yaya tana faɗin, “Haba Babban Yaya cire min kunnen yaro zakai. Kai kayi Auta yayi kun saka min shi tsakkiya”.
       “To Oum ALLAH yaron nan ne Inaga sanda kikai wankan jegonsa baki gasa masa shi ba da ƙyau”. Ya harari Fawzan ɗin ya fice. Murmushi Oum tai ta kama Hannun Fawzan dake harrar AA dake masa murmushi da gwalo suka fice.........✍️

    
     ALLAH ka bani aron rayuwa da damar gina Family ɗina like wannan zuri'a. ALLAH suna kasheni da ƙyaƙyƙyawar rayuwarsu🥰🥰🥰😘😀🥱.



09032345899



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖1️⃣0️⃣3️⃣


______________




......Alhamdullah washe gari safiyar Lahadi kowa yay himmar kama gabansa. Duk da jikin AA baya gama yin ƙarfi bane dole Doctors ɗin suka sallamesa dan ya matsa. Ya kuma dage ko sun koma Abuja bazai cigaba da kwanciya a KK HOSPITAL ba kamar yanda suka so. Zama na musamman Baba Sardauna yay da su da Baban Yola. Sukai musu nasiha irin ta iyaye. Sun nuna musu su riƙe junansu da amana da haƙuri, kar su ɗauka wannan soyayyar da suke ma juna saɓani bazai shiga ba watarana. Ita rayuwar aure zomu zauna zo mu saɓa sunanta. Sannan ibada ce tana da banbanci da soyayyar waje. A karo na farko kuma AA ya bama iyayen nasa haƙuri. Ya kuma tabbatar musu zai riƙeta amana iya iyawarsa. Zai kuma basu mamaki in sha ALLAHU. Haka kuma ya roƙa gafarar Abah da Mamy da Oum harma da su Babban Yaya, amma bai fito ya faɗi dalilinsa na waccan dagiyar ba. Ya dai ce su yafe masa akan kuskurensa.
      A take duk sukace sun yafe masa ai komai ya wuce. Sai dai Mamy dai ta ciki na ciki, dan ba ƙaramin a ƙule take da shi ba da wannan kauce-kaucen da yake na hana kansa koda haɗa idanu da ita da yake yi. Amma dai kamar yanda ta saba ta fuske abinta. Sai dai shi da kansa yasan ita ɗin BALBELA ce, wajenta fari cikinta baƙi. Ya kuma san ba lallai ta yarda babu haɗin bakinsa akan wannan aure ba, amma kuma ya ɗauri aniyar tunda fa ALLAH ya bashi to fa mutuwa kawai zata raba, sai dai Mamy ta yafe masa kuma. Dan ya tabbatar a yanzu mataki na biyu da zata bijiro masa da shi shine ya saki Maanal. Shi kuma magana ta ALLAH abunda ko a cikin ciwon hauka yake bazai iya ba kenan, da dai ba'a aura masan ba zai gwammaci yay biyayar ya rasa ransa kamar yanda yay ƙudiri a baya.
     Bayan dai doguwar nasiha da addu'a sukai shirin wucewa airport. Masu aikinsu tuni sun kama hanyar Abuja a motoci kamar yanda suka zo. Su dai jirgi zasu bi. Hankalin Maanal ya fara tashi ganin har suna niyyar wucewa su Didi basu zo ba kamar yanda sukai mata alƙawari. Dan haka ta kasa dannewa ta tambayi Oum. Murmushi kawai Oum tai mata da tabbatar mata ai zuwa yanzu ma su Ammie suna cikin Kaduna. Dan tafiyar sassafe sukayi ma su sun bar Kano. Aiko sai Manaal ta sanya ma Oum kuka. Lallashinta Oum ɗin ta dinga yi, amma ina hawayenta sun kasa tsayawa. Ita gani take miyasa zasuyi mata haka, kenan haka za'a wuce da ita Abujan babu danginta ko ɗaya da nufin rakkiya kamar wata mara gata. Salon ma AA ɗin ya samu na wulaƙantata da jin ya sameta a banza kamar yanda ya tsara, dan ita fa har yanzu bata yarda dama RK da AA shiri sukai ba, tunda da bakinsa ya tabbatar mata kota halin ƙaƙa sai ta sameta. Sai kawai dan rainin wayo ranar ɗaurin aure ace mata RK ya sadaukar da ita ga AA kamar wata wayar salula ko motar hawansu...
      To haka dai taketa wannan mita a ranta har suka fito domin tafiya. Tsabar son ƙular da AA sai tai wuff ta shige motar da Mamy ta shiga. Aiko Fawzan ya dinga kwasar dariya dan a idonsa AA ya wani waro ido na mamaki yana kallon Maanal ɗin. Daƙuwa Abah da shima abin ya bashi dariya yay ma Fawzan, shi kansa Baba Sardauna sai da ya murmusa. Haka kawai shi dai yake matuƙar jin ƙaunar yarinyar, sannan yin auren nan sai yake jin kamar an sauke masa wasu kaya ne da suka jima a saman kansa, sau kusan huɗu yana zuwa har saudia yana addu'a akan alaƙar AA da Maanal kawai, tare da fatan bayyanarsu garesu a duk inda suke. Dan a ganinsa bai kamata jininsu ya lalata yarinyar su kasa mutunta rayuwarta a ƙarƙashin inuwar aurensa ba. Shi kansa Abah ji yake ko yanzu yabar wannan duniya burinsa ya gama cika, fatansa ALLAH ya basu zuri'a masu albarka su da su Fawzan.
      Da suka fa iso airport ne duk kauce-kaucen Maanal dole a waje ɗaya suka zauna da AA. Sai dai inda ALLAH ya taimaketa akwai Naufal a tare da su, sai kawai ta canjama yaron sit ya koma tsakkiyarsu. Kallonta kawai AA keyi ta gefen ido, amma bai tanka ba. Data zauna ma sai ta ƙirƙiri barcin ƙarya tabarsa da surutun Naufal ɗin. Sun sauka garin Abuja a mintoci. Inda Alhmdllh suka samu drivern Abah da su AS na jiransu domin tarba. Dan abin sha'awa motocine reras har goma ciff idan ka cire drivern Abah da Uncle Sadeeq mijin Didi Shahidah sauran duk staff ɗin Mawaad Company ne. Har cikin rai Maanal taji sanyi da zuwan Uncle Sadeeq ɗin. Dan ya dai kankaro mata mutunci itama. Aiko Oum itama sai tai yakana ta saka Maanal ɗin a motarsa, itama ta shiga. Sauran kuma suka shiga sauran motocin harda AA daba haka yaso ba.
            Har ƙaton harabar gidan duka motocin suka shiga. A mamakin AA da Maanal Oum ta shige sashenta. Shi kuma akan barsa da ma'aikatansa dake ta masa yaya jiki da addu'oin samun lafiya mai ɗorewa. Sai da komai ya lafa suka wuce har Uncle Sadeeq sannan Fawzan ya taimaka masa zuwa upstairs dan jikinsa babu wani ƙarfi har yanzu ƙarfin hali ne kawai......

__________★

        A ɓangaren su Hajiya Basariyya suma yau dai suka koma Kaduna. Dan tazararsu da su Ammie kaɗan ne. Sai dai kuma Daddy ya kafa ya tsare yace Hajiya Basariyya bazata shigar masa gida ba ita da Hajiya Yaya tunda bai san da zuwansu Kano ba. Aiki rigima ta kaure shi kuma yasa aka rufe masa gate ɗinsa. Dole Hajiya Yaya tai kiran Babbanta a waya. Ganin haka sai itama Hajiya Basariyyar tai kiran yayanta tana masa kuka. Kamar haɗin baki duk basu sauraresu ba sukace sai sunji ta bakin Daddy, dan haka su kamo hanya su taho gidan da yace. Hankulansu ya sake tashi amma sun san dole suyi hakan tunda iyayen nasu suka basu umarni......

     A cikin gida kuma su Shahidah na sashen Ammie suna ƙoƙarin kimtsawa ita tana sashen Daddy suna tafka rigima tana masa kuka akan ya saka maigadi ya buɗema su Hajiya Basariyya gate. Shi ko yay mata banza, data damesa ya buɗe mata wuta akan babu ruwanta. Ita kuma cikin fushi tace bazata zauna ba itama tafiya zatai. Randa ya shirya su dawo sai su dawo gaba ɗaya. Shi kuma cikin ɓacin rai ya rantse mata in har ta fita sai ya bata mamaki tunda tsoron su Hajiya Basariyyar take.
         Sosai ranta ya ƙara ɓaci, ta wuce sashenta tana kuka. Ta ce su Shahidah su shirya su wuce gidajensu. Kamar Daddyn ya sani sai gashi a sashen. Yace bata isa ba babu inda zasu sai sun gama abinda suke yi. Kai koda ma yau ɗin sukai niyyar tafiya shi ya hana hakan. Suma hankalinsu ya tashi da ganin abinda basu taɓa gani ba tsakanin Daddyn da Ammie. Kai ko mahaifinsu a sanda yake wulaƙantata bata yarda ta nuna musu. Hankali tashe Shahidah tai kiran Nene da suma suka wuce nasu gida ita da zuri'arta ta sanar mata. Tashi sosai hankalin Nene yayi ta kira Ammie a waya. Itace ta mata faɗa da nasiha ta kwantar mata da hankali, tare da gargaɗinta fita a abinda babu ruwanta. Can tsakaninsa ne da matansa ta saka musu ido. Wannan faɗa na Nene ya saka Ammie haƙurin dole.....

______★

        A can kuma Kano dangin Nuratu sun gama shirinsu na tahowa Abuja suma, dan suna akan bakansu na aure a sati mai zuwa babu fashi babu canji kamar yanda Mamy ta ɗorasu...........✍️



    _Hummm tofa tirƙa-tirƙa kenan. Masu karatu Amin afuwa, Amin afuwa zan dakata anan. Duk da naso gama book ɗin nan gaba ɗaya amma na fahimci yin haka zai tarwatsa ginin labarin tun farko ƙarshen yazo bai gamsar da ku ba. Ni kuma ba haka nake buƙata ba. Ni kaina ban san zai yi tsawon haka ba labarin nan. Amma tarihinsu ya wawurar mana kaso mai yawan gaske wlhy🥺. To wannan fa shine kana naka ALLAH na nashi. Dan haka ina sake neman afuwarku muyi hakuri sai zuwa bayan salla idan muna da sauran rayuwar kaiwa, muna ma fatan kaiwar in sha ALLAHU 😥🙏. Nafi son labarin ya gamsar damu yanda ya kamata kamar yanda ya faro kansa ne shiyyasa._


Kar ku manta shi kansa part 2 ɗin ɗauke yake da tirƙa-tirƙa tasa ta kansa.

  Yaya zaman AA da Maanal zai kasance. Zai yi maganin ƙudirinta da wuri kodan lagon soyayyar da take masa duk da yana basarwa da dannewa😆🥰?

Yaya batun aurensa da Nuratu, zai yiwu kuwa? Kun dai san mamy bata wasa bace😆🥺😩.

Yaya Mamy zata haƙura ta amshi Maanal kokuwa itama zata fiddo mata da ainahin halinta ne kamar yanda AA ya sani? Idan ta fito ɗin yaya zasu kwashe da Maanal? Kun san fa ance ko Giwa ta faɗi tafi ƙarfin wawason karnuka.

Da alama AA na shirin farfaɗo mana da Maanal ɗin data mutu a baya mai tsiwa da rashin ragowa. Dan haka tsakaninta da Saheeba da Nibras fa akwai zazzafan wasa dan za'a zuba facalanci ne fa zazzafa, saboda kowa da nasa ƙudirin akan Maanal tsakanin Saheeba da Nibras. Humm gidan Ambassador Aliyu Darma fa zai koma ƙarƙashin jam'iyu guda biyu ne. Itama Oum ta samu mai tayata faɗa a yanzu wato Maanal, kunga kuwa dole a buga zazzafan wasa dan Mamy zata shigo da sabon salon da dole ne Maanal ta shiga wasan....🤣👍

A ɓangaren dangin su Maanal ya zasu ɗauki wannan aure da basu san anyi ba. Dan kar ku manta Senator Bukar fa ya basu lokaci, tare da kuɗi kuma kun san sai sun ci kuɗin nan. Shi ko bai gaji asara ba dole ai masa aman kayansa...🤣👍

Ɓangaren Babu kun dai san alƙalamin Bilynku baya yafiya, dole kowa ya girbi abinda ya shuka. To dole fa Babu sai ya biya bashi shi da Gwaggo walle😌😆🏃

Hummm mai kankat, rayuwar Maawad Company, yaya zata kasance tsakanin waɗan nan masoya biyu a yanzu, idan kuma Mamy tasan AA ya jima da raba Company biyu rabi nasa rabi na Maanal har anyi komai a rubuce tasa hannu ya saka yaya kuke gani🤣😌👍?.

Yaya soyayyar Najma da Fawzan zata kasance? Mi kuma kuke tunani idan aure ya ƙullu? Oum nada Maanal da Najma kenan a jam'iyyar ta. Mamy nada Saheeba da Nibras ga Nuratu idan ta shigo🤪🤣👍.

Sai amarya Huznah a gidan Man Sageer. Auren can zai rabu kuwa? Zata haƙura da AA ko kuwa alkawarin da uwarta tai mata da ƙawarta zai cika🥱?.

Ɓangaren Hajiya Yaya, itama fa akwai zazzafan wasa tsakaninta da tata surukar idan sun gama shan honeymoon sun dawo. Hakama tsakanin uban Nazeefa da Daddy akwai zazzafan wasa. Shi kansa Yazeed ɗin fa. Hummmm zai bama kowa mamaki💃💃💃🤣👍

Kudai karna cikaku da surutu, muyi fatan ALLAH ya kaimu bayan salla da rai da lafiya. Ya rabbi kasa muyi ibada karɓaɓɓiya. Ya rabbi kasa mu kasance a cikin ƴan tattaun bayi a wannan wata mai albarka. ALLAH kasa mu zama jajirtattu a wajen ibada🙏. Dan ALLAH ina barar addu'ar ku dukkan masoyana koda a ranar farko ce ta azumin. Har ƴan bati a min dan ALLAH 😌 tare da al'ummar Musulmai baki ɗaya 🙏.

Ina ƙara dai neman afuwarku Please Please nasan wasu zasuce ba haka sukaso ba. To ayi hakuri, ayi hakuri kamar yau ne zamu dawo in sha ALLAHU.🙏🙏🙏


San so, ƙaunar ƙauna Zafafa ke muku baki ɗayanmu kamar yanda kuke mana❤️🥰🥰🥰🥰🥰🥰🙏
      
    
Bilyn Abdull ce😘
      
       Kumuje zuwa book 2 🏃🏃🏃
        
  
09032345899
   


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

77 / 77