Author : Billyn Abdul Category : Romance
sake bayyana kanta. Gaba ɗaya an haɗe ɗaure-ɗauren auren anan Kano ne. Dan shima Daddy tuni shi da tawagarsa sun kama hanyar Kano. Anyi haka ne domin sama ma mutane sauƙin, tunda shima dai Daddyn asalinsa bakanon ne. Danginsa duk a can suke, daga can suke zuwa Kadunar duk wani biki...
Tunda sha biyu tayi kowa yake ƙarasa shirinsa a gaggauce, musamman anguna da bakunansu suka kasa rufuwa. Sai dai banda AA da tunda suka dawo daga aski shi da Uncle Mahmud da Babban Yaya ya shige ɗaki ya kulle kansa. Ba'a farga da rashin fitowarsa ba sai da suka ɗauki hanyar tafiya massallaci. Babban Yaya ne ya ɗaga waya ya kira shi, tare da tambayarsa yana ina? Sai cewa yay gashi nan zai biyo bayansu wani abokinsa ne ya tsayar da shi. Babban Yaya bai kawo komai a ransa ba dan AA yay masifar saita kansa kafin ya ɗaga wayar. Wayar na yankewa ya kasheta gaba ɗaya yana mai kai hannu ya shafo jinin dake ziraro masa ta hanci. Murmushi ya saki tare da saurin dafe bango jin jiri na neman zubar da shi. Tun yana bin bango domin kai kansa cikin toilet harya gaza, dole ya zube a ƙofar bayin saboda wani irin nauyi da ƙirjinsa yay masa, idanunsa suka fara juyewa duhu ya fara mamaye ganinsa. Duk wani motsi ya fara nisa da kunnuwansa. Kafin cikar abinda bai wuce minti biyu ba ya nema kansa ya rasa, sai damshin ɗumin jinin dake fita masa ta hanci kawai yake iya ji a fatar jikinsa kafin a hankali komai ya koma masa ɗiffff....
_________★
A massallaci su Babban Yaya suka haɗe da Abah, koda Abah yace ina AA sukace yana nan tahowa, wani abokinsa daya iso ne ya tsaida shi. Kamar Abahn zai yi magana sai mutane suka ɗauke masa hankali. Ga shirin fara sallar juma'a anayi, dan har an fara khuɗuba. Daga can itama dai Oum hankalinta na akan AA ɗin, dan tun safe da sukai waya bata sake jinsa ba. Garama Babban Yaya dake sanar mata sun tasashi gaba sun kaisa aski shi da Uncle Mahmud har taita dariya. Duk yanda take ƙoƙarin samunsa a waya hakan ya gagara, ga mutane sai ɗaukar hankalinta suke yi, dole ya tattara wayar ta ajiye ma ta maida hankalinta garesu...
Bayan idar da sallar juma'a aka fara gabatar da ɗaure-ɗauren aure. An fara ɗaura auren Uncle Najeeb Umar Ishaq Darma da amaryarsa Raihana Kabeer Yola. Sai na Rafeeq Kasheem Kura da amaryarsa Nuwaira Kabeer Yola. A rikice Babban Yaya da Fawzan har ma da Abah suke kallon RK da su Baba Sardauna. Amma duk sai sukai murmushi kawai, Abbu ya sake bada sadaki ga Daddy matsayin na AA. Ana jira aji an ambaci sunan Huznah sai akace ga sadakin Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, ga Maanal Habib Giro. Babu wata damuwa ko gargada ga Daddy ya amsa fuskarsa da murmushi aka ƙulla auren. Ɗaurin auren ƙarshe shine na Sageer Ahmad Isa Chalawa, da amaryarsa Huznah Usman Isa Chalawa...
Kan babbar buta, ai a rikice Abah yace, “Alhaji Usman nifa ban gane ba. Baba kun sakani a ruɗani, yaya duka aurarrakin suka canja kansu?”.
Murmushi Baba Sardauna da Baban Yola da Daddy da Abbu duk sukayi, hakama RK hankalinsa kwance sai ma murmushi yake saboda kallon da Babban Yaya da Fawzan suka zuba masa. Baba ne ya bama Abah amsa da, “Dama can a haka suke. Kai ne dai kake kallonsu ba'a haka ba. Kowa an bashi matarsa ne”. Daga haka ya juya aka ƙarasa addu'oi ga ma'auratan da fatan alkairi da zaman lafiya na har abada.
Ai sai hawaye suka shiga zuboma Yaya Fawzan. Kasa hakuri yay a take ya ɗaga waya yay kiran Oum shima kuma babban Yaya Oum ɗin yake nema. Sai ALLAH ya bama Fawzan sa'a tashi ta fara shiga. Tana ɗagawa ko sallama baiyi mata ba cikin muryar kuka ya ce, “Oum ALLAH ya mallakawa Autanki Maanal. Maanal ta zama mallakin Ajwaad Oum an ɗaura Oum an ɗaura.....” sai hawaye. Gaba ɗaya daburcewa Oum tayi, ai bama tasan tayi wani kalar tafiya jagwab ta zube a kujera wayar hannunta ta suɓuce. Hannayenta gaba ɗaya a saman fuskar ta ta fashe da kuka da ambaton sunayen ALLAH a bayyane, tare da miƙa godiya da kirari ma UBANGIJI mai hukunci bisa hukuntawarsa da rahamarsa...
Kafin kace mi mutane sun zagayeta ana tambayar lafiya-lafiya. Ta kasa cewa komai ila amfaton UBANGIJI. A haka ƴan ɗaurin aure suka fara dawowa gida. A take zancen ɗaurin aure da yanda ya kasance ya fara bayyana a cikin gidan....
Mamy na tsakiyar ƴan uwanta da suka zo wani dake matsayin kamar Yaya a wajenta na kusa kuma, dan da babansa da babansu uwa ɗaya uba ɗaya suke suka shigo domin yimata ALLAH ya sanya alkairi dan zasu wuce, daga Jigawa suka zo shiyyasa. Tanata faman washe baki bata san mike faruwa ba sai da suka gama jerama ma'auratan addu'oi sannan wanda ke kamar yaya a wajen nasu ke faɗin, “Ai ni na shiga ruɗani ma a wajen ɗaurin auren. Kuma naji mutane nata mamaki suma har wasu na tambaya”.
Cike da isa Mamy ta dubesa, dan haka take musu daman saboda akaf dangin nasu itace mai auren mai kuɗi, itace ke raba musu kayan azumi dana salla, duk da ba wani na kirki bane ba hakan bai hana su girmamata ba. Kuma su babban Yaya ne da Abah ke badawa duk shekara amma sai ta sayi ƙananun atamfa da yaduka ta manna musu. Hakama abincin bawani na kirki ba. Fuska a yamutse ta ce, “Wani abu ne ya faru a wajen ɗaurin auren?”.
“Eh to bana ce ba. Akan dai canji da mukaji ne ga ita sunan matar shi Ajwaad da kika sanar mana ne da farko.”
“Kamar ya canji Yaya Lurwanu?”.
Kafin ya bata amsa Saheeba ta iso kamar an jehota tana ƙwala kiran Mamy! Mamy!. Idanu sosai Mamy ta zuba mata, haka suma sauran mutanen dake wajen. Bata jira amsar Mamy ba ta miƙa mata waya tana faɗin, “Abah ne keta kiran wayarki, shine na ɗaga yace na kawo miki”.
Amsa tayi, dai-dai nan kiran ya ƙara shigowa. Sai kawai ta ɗaga takai kunne cike da kissa tai sallama. Cike da fara'a Abah ya ce, “Ina kuka shige haka ke da Fateema sai nemanku nake a waya babu wanda ya ɗaga min, ki sanar mata ina mata albishir da cewar an ɗaura auren Autan ta da da Autarta Maanal....”
Wani irin dimmmm Mamy taji a kunneta kawai, tamkar an ɗaga irin curarren ƙarfen nan an bugama mutum a tsakkiyar kansa babu zato babu tsammani.......
🤣🤪🏃🤐
________★
Acan massallaci kuwa mutanene cikin ɗunbin mamaki. Musamman ma'aikatan Mawaad Company da mafi yawansu suka halarci wannan aure. Tuni musu ya kaure akan batun. Wasu suce Maanal ta kamfani wasu suce ba ita bace ba. A gefe kuma suma kansu su babban Yaya harma da Abah a rikice suke. Ga mutane, dole suka danne dan daga nan an ɗunguma ne ƙaton hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci ga mahalarta wannan ɗaurin aure. Sai dai kuma hankali ya fara komawa akan rashin ganin AA a wajen. Dole aka fara neman layukan wayarsa, amma duk switch off. Hankali tashe Babban Yaya da Uncle Hussain suka koma can gidan dan dubawa. Sunko iso ɗakinsa a garƙame har yanzu. Tun suna bugawa da kiran sunansa har suka fara ƙoƙarin ɓalle ƙofar amma sun kasa. Ga su Abah nata kiransu a waya. Ai kafin kace mi su Aban suma dole sun iso. Nan fa aka taruma ƙofa da ƙyar aka ƙaryata.
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kowa ya faɗa ganin AA yashe a ƙasa babu alamar rai a tare da shi sai uban jini dayay masa kaca-kaca, ga alamun zubarsa nan ta baki ta hancinsa. Gaba ɗaya babban Yaya ya ɗagosa jikinsa na rawa, hawaye tuni sun gama wanke masa fuska, da wani irin ƙarfi yake girgiza AA yana kiran sunansa, amma ina gaba ɗaya jikinsa ya gama saki. Babu alamar akwai sauran numfashi a tare da shi.
Wani irin baya Abah da jikinsa ke rawa ganin yanda AA ɗin yake yarab yayi, sai da aka taresa dan kaɗan ya hana ya zube ƙasa. Baba Sardauna ne ya samu ƙarfin halin faɗin a ɗaukesa zuwa asibiti. Haka kuwa akayi duk da duk wanda ya kalli AA zaice yama rasu basu fidda rai ba, Uncle Najeeb da Alhaji ƙarami suka kamosa. Daka gansa kaga gawa kawai. A haka suka fita da shi aka saka a mota, suma duk suka shiga aka wuce.....
😭😭😭🥲🥺🤐
___________★
A Kaduna duka amare biyun sunyi ƙyau, sai dai Maanal kwance take zazzaɓi ya mata rijib, tun su Aneesa na ɗaukar abin wasa har suka fuskanci gaske take dan rawar sanyi ma take yi bana wasa ba. Da sauri Najma ta lulluɓeta da ƙaton duvet. Kafin ta fice tai kiran Amaal. Hankalin Amaal ya tashi, amma ta daure cikin hikima tayi kiran Shahidah dan bata son su ɗagama Ammie dake a tsakiyar mutane hankali. Ganin halin da Maanal ɗin ke ciki ba wasan yara bane ba Shahidah ta bada shawarar su sanarma Nene. Aikuwa haka akayi, da taimakon Nene aka bama Maanal magani, sannan ta zauna ta dinga tofa mata addu'oi. Ga ƙawayen Hajiya Basariyya sun cika gidan da kiɗa na hauka dan sifiku suka warware a harabar gidan saboda duk mazan sun wuce Kano sai mata kawai a gidan.
A dai-dai wannan lokacin kiran Oum ya shigo wayar Ammie. Kasancewar wayar tana a hannun Amaal sai kawai ta ɗaga. Ko sallamarta Oum bata amsa ba tace, “Ƴar uwata”. Muryarta na rawar kuka. Cikin faɗuwar gaba Amaal tace, “Oum ba Ammie bace nice, wayar tata na hannuna ne ai. Amma Oum mike faruwa kamar fa kina kuka?”.
“Dole ne nai kuka Amal dole ne. Yau ALLAH ya tabbatar da Maanal a matsayin matar Ajwaad”.
Suɓucewa wayar ta nema yi, sai da ƙyar Amal ta tarota, da wani irin mamaki ta ce, “Oum! Kina nufin Ajwaad aka aurama Maanal?”.
Ai da wani kalar sauri kowa dake a ɗakin ya juya yana kallon Amal. Manaal dake kwance tana faman rawar sanyi a bargo tai wani irin yakice duvet ɗin itama ta tashi zaram kamar wadda ke amfani da magic sai gata a gaban Amaal. Wayar kawai ta fige jikinta da muryarta na mazari ta ce, “Oum wace Maanal ɗin? Badai ni ba? Dan ALLAH kada kuyimin haka ni Rafeeq nake so, shi na zaɓa, da shi nake son rayuw.......”
Batare data karasa ba kawai ta sulale ƙasa yaraf wayar tai nata waje. Ai da gudu kowa yay kanta ana ƙwala mata kira....
A dai-dai lokacin da Maanal ke sulalewa acan a sume anan sashen su Hajiya Basariyya itama ƙaninta ne ya kirata cike da mamaki yake tambayarta yaya haka, yaji ɗaurin aure ya juye akan Sageer ɗan ƙanin Daddy maimakon AA Darma data sanar musu. Shi kuma AA Darma ɗin sunji an aura masa wata wai ita Maanal Habib Giro.
Gaba ɗaya Hajiya Basariyya ta saki wayar dake a kunnen nata ta faɗo ƙasa ta tarwatse. Ita kuma tai baya sai gata jaɓar a saman gado ta zube...........✍️
☹️☹️😥😥🥲🤐
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣8️⃣
______________
.......Isowar labarin halin da AA ke ciki ya saka komai tsayawa cak ta kowanne ɓangare. Cikin ƙanƙanin lokaci mafi rinjayen manyan family ɗin suna a asibitin. Yayinda tuni RK, Abbu, da wasu likitoci suna a kansa anata ƙoƙarin ganin an ceto rayuwarsa.
Sosai Oum ke kuka, kuka mai ban tausayi, dan dole Abah ya dake tashi zuciyar ya kasance da ita. Dama yaranta Babban Yaya da Fawzan suna manne da ita. Abin mamaki a farko Mamy bata asibitin, sai dai ƴan uwanta suka tausheta dan da neman birkicewa tai zata tonama kanta asiri suka janyeta zuwa ɗaki. Sun nuna mata cewar tada hankalinta fa babu abinda zai janyo sai rushewarta a wannan zuri'a, amma idan ta cigaba da dannewa komai ya lafa sai ta ribantu da cikar burinta, saboda tabbas suna zargin akwai abinda ke faruwa tunda har ɗaurin auren yay wannan juyewar, gaba ɗaya kuma laifin sun maidashi ga Oum ne, acewarsu dama itace ta tura RK jikin Maanal ɗin domin hakan ta kasance ita a yaudare ta. To dan haka saita kwantar da hankalinta amarya ta tare a kumayi bikin Nuratu wani satin daga nan sai su san matakin ɗauka. Dan ko zasuyi yawo tsirara suma sai sun bata taimako na kashe wannan aure, acewarsu Nuratu bazatai rayuwa da kishiya ba. Da ƙyar dai suka tausheta ta haƙura suka shirya suka tafi asibiti, sai kuma da suka iso suka tarar da tashin hankali yafi wanda ma suke hasashe. Domin kuwa awanni sai shuɗawa suke babu wani bayani a game da samuwar AA ɗin.
Karo na farko da hankalin Mamy ya fara tashi, zuciyarta ta dinga raya mata kadafa ace rasa Ajwaad zatayi. Kai ina bata fatan haka, dan soyayyar da takema yaron daban take akan ta sauran yaran. Sai dai kuma abinda ya ƙona mata zuciya ganin yanda Abah da Babban Yaya da Fawzan keta dama-dama da Oum. Hakama sauran manyan kowa dai hankalinsa nakan Oum, ita aketa tausa da tunatar da ita tai masa addu'a. Dan ita ko kallonta kowa baiba a matsayin wadda tasha wahalar rainon cikin Ajwaad da naƙudarsa, da gaske dai ta tabbata sun ma manta da cewar itace mahaifiyarsa tarihi ya goge hakan....
Sai da su RK suka kwashe awa ɗai-ɗai har bakwai kafin su fara fitowa. Zuwa lokacin har anyi sallar magrib. Amma sai ƙalilan ne suka samun ƙarfin zuwa yinta. Kusan gaba ɗaya akai ca akansu, ALLAH sarki Abbu ga tsufa. Kaida ka gansu kasan su kansu sun jigata. Dan tuni babbar rigar saman kayansu duk sunyi fatali da su shi da RK. Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya bayan yace su sameshi a office. Bayan duk sun zauna a ƙaton haɗaɗɗen Office ɗin nashi cikin nutsuwarsa da Oum suka gado ya ce, “Kowa ya kwantar da hankalinsa tun awa biyu da kasancewar mu da shi aka samesa, bugun zuciyarsa ne yaƙi dai-daita tun ɗazun sai yanzu Alhamdullah. Amma duk da haka yana buƙatar addu'a, yaron nan ya jima a cikin ciwo, zuciyarsa ta kumbura a shirye take da komai ya iya faruwa. Amma Alhmdllh tunda har ankai ga wannan matakin muna fatan iyakar wahalar kenan dan gaskiya ya auna arziƙi. Yanzu za'a canja masa ɗaki domin hutawa, muna saka ran nan da awannin talatin numfashinsa zai dawo a gangar jikinsa in sha ALLAHU”.
Sosai kowa ya dinga sakin ajiyar zuciya da jerama UBANGIJI godiya. Harga ALLAH bayanin Abbu ya daki zuciyar Mamy matuƙa. Bayan kamar mintuna biyar aka fito da AA, babu wanda bai ji sabbin hawaye ba, wato ɗan adam ba'a bakin komai yake ba. Wlhy duk iskancin da muke ji a rayuwa da ciwo ƙalilan idan UBANGIJI ya so nuna ba komai bane mu a cikin sakan sai mun bayyana a ba komai ɗin ba. Cikin ƙanƙanin lokaci AA ya canja, kamar ba ɗan gayu ɗan kwalisar nan shugaban Mawaad Company ba ya arrahaman.....
________★
A Kaduna kam ai gidan gaba ɗaya ya hargitse, kafin kace mi dangin Hajiya Basariyya sun cika sashen Ammie. Wani irin harmutsi ne na tashin hankali daban mamaki. Dan faɗi kawai suke sai sun daki Ammie. Yayinda Huznah ke ɗauke da kakkaifar wuƙa tana rantsuwa da UBANGIJI sai ta kashe Maanal. Dole aka rufe Ammie da Maanal har ma da su Amaal a ɗaki. Kafin Nene ta kira Daddy ta tabbatar masa fa akwai matsala ya dawo Kaduna. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa da jin abinda ke faruwa, dole yay kiran CP na Kaduna yace a tura ƴan sanda gidansa. Wannan fa dabara itace ta kawo sassaucin al'amarin. Dan dole kowa ya nutsu kaf dangin Hajiya Basariyya aka korasu sashenta, saboda Daddy ya bada umarnin hakanne kawai bawai a ɗibesu zuwa station ba, sai idan sunyi gardama be. Sai a wannan gaɓar Huznah ta yanke jiki ta faɗi wai ita ta suma. Nan suka rufu a kanta Hajiya Basariyya na kukan idan har ƴarta ta mutu sai ta ɗaure Ammie. Dan sun tabbatar baƙin asiri taima AA Darma dan ya auri karuwar ɗiyarta ragowar wani...
Oho su Ammie bama su san anai ba. Dan su nasu hankalin na nan akan Maanal da aka samu ta farfaɗo a bisa taimakon likita da sukai gaggawar kira, abokin Yaya Yazeed kenan. Dole akai mata allurar barci mai ƙarfi domin samun nutsuwarta, Alhmdllh cikin ƙanƙanin lokaci barcin kuwa ya bugeta. Da wannan damar suka samu sukai zaman jimanta al'amarin, dan Ammie tayi matuƙar ƙagara Daddy ya iso, yace ya taho, saboda dole ya baro kano, ALLAH ma ya taimakesa ya samu jirgi. Suna isowa Kaduna yake samun kira daga Kanon akan halin da AA ke ciki, sai kuma hankalinsa ya ƙara tashi matuƙa. Dole yana isowa yace su Ammie su fara shirin wucewa Kano ɗin. A ɓangaren Hajiya Basariyya ma yace a shirya Huznah dan yau bazata kwanar masa gida ba a gidan mijinta zata kwana, Kanon kenan. Hajiya Basariyya ta birkice zatai masa hauka Yayanta ya wanke mata fuska da mari dan shi dama baya ɗaukar wargi. Ya kuma rantse mata idan ta sake cewa tak sai ya saka Daddy ya saketa. Wannan fa yasa dole ta nutsu, sai kukan baƙin ciki tana jin zuciyarta kamar itama zata fashe ɗin. Tana ji tana gani wasu dangin Daddy duka shirya Huznah dake