AJIYA A DUHU BOOK1 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdul Category :  Romance

Chapter   37 / 77

108K to 111K   out of 230.9K words

ciwon zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa. Ji yake kamar ma nasa ciwon ya dawo sabo ne. Sai kuma gashi ya dawo a wannan bahagon halin yanzu.
         Da mamaki security daya buɗe masa ƙofa ke kallonsa. Sai dai shi ko kallon nasa baiyi ba ya wuce flat ɗinsa. A hankali ya maida ƙofar ya rufe yana sauke ajiyar zuciya ganin kowa bai gansa ba. Sai kuma ya dafe kansa dake matuƙar sara masa har yanzu tamkar zai cire. Yana shigowa falo na biyu yay wani irin turus ganin Mamy zaune. Zuba mata ido yay sai kuma ya ɗan wawwaiga kamar mai neman abu. Dan wani irin tsarga zuciyarsa kallon da take masa yake yi. Amma sai ya dake kamar yanda ya saba. Idanunsa ya maido kanta cikin sautin muryarsa mai fita ƙasa-ƙasa ya ce, “Mamy kina buƙatar wani abu n....”
     Hararar data wullo masa ta hanashi ƙarasawa. Sai ma duƙar da kansa da yay kawai.
          “Daga ina kake?”.
    Ta faɗa da kakkausar murya. Sam AA ya tsani ƙarya, baya sonta baya shiri da mai yinta. Gara idan bazai faɗi gaskiya akan abu ba ya gwammaci yin shiru kawai. Haushi ne ya turniƙe Mamy, cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya ta wani daka masa tsawa. “Ajwaad bada kai nake ba ne?! Kasan dai bana son wannan banzan halin naka na iskanci ko? Nace daga ina ka fito??”.
       “Mamy Please my head”
  Ya faɗa yana kai hannu a saman kansa. Harara ta balla masa duk da zuciyarta ta motsa da yanda yayi ɗin. Amma sai a faɗace ta ce, “A'a your heart ba head ba. Ni zaka rainama wayo kama pretending ko. To wlhy bara kaji, idan ma wani abu kuke ƙullawa kai da ita to ka dawo cikin hankalinka, in ba hakaba wlhy kaine masha wuya. Dan har yanzu har gobe kai har ƙarshen rayuwa ina akan bakana. Yanda ƴan uwanka suka auri zaɓina kaima dole hakan zakayi. Dan haka ka sani na zaɓa maka yarinyar da sukazo tare da Abdulhakeem ɗazun a matsayin mata, a cikin satin nan za'aje nema maka aurenta. Kuma wata biyu kacal za'a saka...”
     Ai da wani irin bala'in sauri ya kalli Mamyn, ta watsa masa harara cike da tabbatarwa........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖4️⃣9️⃣


______________


..........“Haka na faɗa kuma haka za'ai. Sannan wacece Maanal ɗin da wannan yaron Rafeeq ke magana ɗazun?”.
     Wani irin sake bugawa zuciyarsa da ƙirjinsa da kansa sukai a lokaci guda. Ya tsatstsareta da kaifafan idanunsa da suka gama jirkicewa gaba ɗaya kamar zai haɗiyeta da su. (Maanal! Waya gaya mata zancen Maanal? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un.....)
      “Sai ka gama tunanin zaka faɗa min wacece ita?!”.
    Ta sake faɗa a tsawace kamar zata falle fuskarsa da mari..
Da sauri ya kai duka hannayensa biyu ya dafe kansa. Sai kuma yay saurin zubewa a kujerar dake kusa da shi jin jiri na neman zubar da shi a wajen. Ɗan tsai tai tana kallonsa, kamar zata matsa garesa sai kuma, fuuu ta nufi hanyar kitchen tana faɗin, “Idan ka gama pretending ɗin iskancin kazo ka saman ka faɗa min wacece ita. In ba hakaba ni zan bincika, kuma ka bari har ya kaimu ga hakan wlhy sai ranka yay mummunan ɓaci a gidan nan. Zuwa safiya kuma idan ita uwar taka da uban naka suka tambayeka game da Nuratu da Huznah dan ALLAH kace baka so kaga yanda zan maka. Dan ko ka yarda ko baka yarda ba sai ka auresu dole su duka kuma a rana ɗaya”. Daga haka tai ficewarta ta kitchen ɗin dan dama tanan ta biyo....

    ______★

       “Jaan! wai ina kuma zaka naga ka ɗauka key?”.
     “Zan ɗan duba Ajwaad ne, dan tun fita sallar isha'i yay wani wajen. Kin san Oum akan Ajwaad dai, na tabbatar tana can zaman jiransa hankalinta a tashe. Ballan tana baida lafiyar nan”.
     Baki Nibras ta ɗan taɓe, tare da ballama Fawzan da yay gaba abinsa harara. Wani irin takaicin Oum na keta mata zuciya. Harta koma ta kwanta sai kuma ta miƙe zaram, sakkowa tai a gadon ta saka slippers ɗinta tabi bayansa batare data neman hijjab ta suturta jikinta ba duk da kasancewar kayan barci ne kuwa, dan ma dai sunada girma basa nuna mata ko'ina na jikinta. Tuni Fawzan har ya shige sashen AA, dan haka itama ta afka kawai. Isowarta dai-dai Fawzan ɗin na jijjiga AA cikin matuƙar tashin hankali da kiran sunansa. Sosai zuciyar Nibras ta motsa, tai mutsuwar tsaye tana kallon yanda mijin nata ya tallafi abin sonta da duka alamu suka nuna baya cikin ƙoshin lafiya. (A tabbas masoyi, dan kuwa da dukkan zuciyarta take jin ƙaunar ƙanin mijin nata kuma ɗan ƙawar mamanta. Mahaifiyarta da Mamy aminan juna ne shekaru masu yawa. Bata san komai daya faru ba wata rana mamanta ta bata umarnin shiryawa akan zatayi baƙo. Sam bata jayayya da ita, dan duk abinda take so itama tana so. Dan haka babu musu ta shirya tarba ta musamman ga wannan baƙo, duk da bata saka a ranta zata iya aminta da shi matsayin miji ba. Dan tana da nata tsarin itama akan mijin aurenta. Sai dai me, tana ganin Fawzan a matsayin baƙon nata duk ta rikice, dan guy ɗin it is hot kuma handsome. Bata wani ɓata lokaci ba ta miƙa wuya, kamar wasa soyayya ta ƙullu duk da ta fahimci shi ba wai hundred percent ya bata ammana bane. To amma mamanta ba Maman yara bace, tuni ta shirya mata duk ta yanda zata mallaki Fawzan ɗin har akai gagarumin biki na nunama tsara. Dan kowa yasan family na Ambassador Aliyu Darma ba gidan wasan yara bane. Bayan tashen dukiya da suna da yay Ƴaƴansa ma gwarazan kansu ne a fanin nema. Sai dai me, bayan aure da baifi wata ɗaya ba AA ya dawo Nigeria sakamakon jiyya da yay a ƙasar waje na tsawon shekaru biyu. Tun fa da Nibras ta ɗaura idonta akan AA taji komai ya ƙwace mata. Dan hundred percent shine irin zaɓin data jima tana ma kanta. Bawai dan Fawzan bashi da qualities ɗin AA bane. Kawai dai akwai abubuwa da yawa da suka bambanta su duk da a fuska suna kama da juna. Tayi iya bakin ƙoƙarin ta na ganin ta danne kwaɗayinta amma abu sai ƙara girma yake a zuciyar tata. Dan takai har siffanta kanta take tare da shi a lokacin da take tare da mijinta. Tabi hanyoyi da yawa akan AA amma ko kallo bata ishashi ba, dan yana da tsari akan mu'amularsa da matan yayyan nasa.......)
         “Nibras! Nibras!”. Kiran sunanta da Oum ke ƙwalawa ya maidota hanyyacinta. Sam bata san lokacin da Oum ɗin ta shigo sashen ba. Oum ɗin ce ta ƙara katse mata gajeren tunanin da faɗin, “Nibras ɗakko bowl a kitchen ki sawo ruwa a ciki. Kai kuma Fawzan ɗakko towel ƙarami a toilet ɗinsa”.
       Cikin rikicewa Fawzan ya amsa mata. Dan shi dama bai iya rikicewa ba. Har ya tafi Oum ta ƙwala masa kira. “Kaga dawo mu kamashi zuwa can sama ɗin zaifi”.
      “Oum kin san bazamu iya ɗaga shi ba. Auta bana wasa bane. Bari na kira Babban Yaya dai”. Oum bata musa masa ba, ya shiga kiran Babban yaya. Cikin ƴan mintuna kuwa sai gashi. Shima hankalin nasa a tashe yake. Da ƙyar suka kama AA ɗin su biyu suka miƙar zuwa upstairs. Dan gaba ɗaya jikinsa ya wani irin saki sai numfashi yake da ƙyar da kiran sunan ALLAH dana Oum yana faɗin Kansa kansa dai. Sai da suka shinfiɗesa a gadon sannan Fawzan ya nufi ɗakko towel ɗin, dai-dai da dawowar Nibras. Sai faman hawaye take, dan ji take kamar ta maido ciwon kanta ko zata ji sassauci. Babban Yaya ne ya amshi ruwan da towel ɗin yana faɗin, “Oum kuje falo bari nai masa. Dan jikin nasa ma ya ɗau zafi duka yana buƙatar ruwan sanyin”.
     Oum dake hawaye bata musa ba. Sai dai Nibras ba haka taso ba. Dan takaici har ɗan hararar babban yaya tayi ta gefen ido. Ganin yanda Oum ɗin ke hawaye Fawzan ya kama hannunta cike da lallashi, dole itama Nibras ɗin ta biyosu badan taso hakan ba. Sai dan tasan rijiya ba wajen wasa makaho bane ba. Shima babban yayan kamar AA yake baya ɗaukar raini..
     Tsaf babban yaya ya gogema AA jiki yana tofa masa addu'a, a hankali jikin ya dinga hucewa shi kuma yana sauke ajiyar zuciya. Sai da ya koma sanyi ƙalau barci ya fara ɗaukarsa sannan ya barsa haka. Kaya marasa nauyi ya ɗakko a closet ɗinsa ya canja masa, dan ya zame waɗan can duka da boxer kawai ya barsa sanda yake goge masa jikin. Koda ya sanar ma su Oum suka shigo itama zama tai a ta ɗayan gefen tana tofa masa addu'a, hakama Fawzan na daga wajen ƙafafunsa yana tausa masa su da tofa masa addu'ar kamar yanda babban yaya da Oum keyi. (😀AA ɗan gata kenan). Tsahon lokaci suna a hakan kafin barci mai nauyi yay awon gaba da shi, wannan addu'ar da suke masa ce kawai mafita, dan in irin wannan ciwon kan ya bugesa sam maganin asibiti baya masa. Ba kuma dan ciwon bana asibitin bane, kawai dai ita addu'a dabance, maganin kowacce irin masifa ce.. Yanda yake sauke numfashi kaɗan-kaɗan ya sakasu dinga sauke ajiyar zuciya suma. Yayinda Nibras dake ta hawaye ta kasa haƙuri sai da ta tambayi Oum cikin dauriya, dan ji take kamar ta shaƙeta kota tureta daga zaman datai kan AA a saman cinyarta. Kishin matar take ji, tsananin kishinta mai zafi. Bama ita ba, duk wanda zai raɓar mata AA bata ƙaunarsa sam musamman mace. Kai hatta Mamyn ma haushinta take ji, dan ta jima da fahimtar daga Mamy har Oum ɗin dukkan soyayyarsu akan AA tafi ƙarfi. Dan kowa nayi ne bakin rai bakin fama duk da Mamy na ɓoye kurwanta wa kowa sai su da suka sani ita da Saheeba da ƙalilan ɗin mutane......

_____________★

     WASHE GARI ba ƙaramin tashi hankalin RK yay da ganin yanda idanun Maanal suka kumbura ba. Gasu sunyi jazur. Amma koda ya tambayeta sai tace barci ne bata samu isashe ba sai gab da asuba. Badan ya yarda ba ya barta. Zama yay da kansa ya haɗa mata tea kamar yanda yay a kwana biyun nan, amma sai tace ta ƙoshi, ita so take dai su sallameta.
        “Karki damu in dai sallama ce in sha ALLAHU yau za'a sallameki. Amma dan ALLAH ina son muyi magana Maanal”.
    Yanda ya kira sunan nata in serious yasa ta kallesa. Sam kuwa babu wasan data sani akan fuskar tasa. Sai hakan ma yaso bata mamaki, kamar ba RK sarkin tsokana ba. Itama nutsuwar tayi yanda ya kamata. Kofin shayin ya miƙa mata, babu musu ta amsa. Tare da cema “Thanks” a hankali.
       “Karki damu wannan aiki na ne. Maanal ina son muyi magana akan lafiyarki. Dan haka a matsayin likitanki nake tare dake anan.”
     Kanta ta jinjina masa. Shi kuma ya sake gyara zama sosai da sake nutsuwa. Maanal kin yarda da ALLAH?”.
     Nan ma kanta ta jinjina masa.
Ya ce, “Alhamdullah, ina son yanda kika yarda da ALLAH shi kaɗai bashi da wani abokin tarayya ki yarda da cewar komai naki a hannunsa yake. Kuma shi mai iko ne akan komai. Maanal magana ta gaskiya ciwon dake tare dake baya buƙatar komai ƙanƙantar tashin hankali daga gareki, domin ciwo ne mai haɗarin gaske. Nasan rayuwa bata kasancewa sai da JARABAWOYI a cikinta, domin suna tafiya ƙafa da ƙafa ne da fitar numfashin mu. Amma duk sanda abu ya faru damu ya wuce yana da ƙyau mu manta da shi kamar ba'ayi ba. Tabbas ban san minene lulluɓe da rayuwarki ba, sannan ban san minene musabbabin ciwonki ba. Amma ina roƙonki ko sau ɗaya ki samu wani ki tattauna damuwarki da ita nauyin zuciyarki zai ragu. Sannan ki sake miƙa al'amuranki ga ALLAH, ki ƙara ruɓanya ibadarki da addu'oi muma in sha ALLAHU zamu tayaki kinji. Amma ki kwantar da hankalinki, ki daina barin damuwa na miki yawa akwai haɗari, dan ciwonki na neman kaiwa wani mataki musamman a tsakanin nan da yake yawan tashi. Dan ALLAH ki cire komai kinji. Ke mai haƙuri ce na sani, kuma jarumace dan a ɗan zamana dake na karanci ƙyawawan halaye daga gareki masu yawan gaske. Ƴan uwanki na sonki, ki daure ki bama kanki farin ciki, suma zasu samu farin ciki”.
        Murmushi tayi a karo na farko, sai kuma ta kallesa wani abu mai nauyi na narkewa daga cikin ƙirjinta. Tabbas zuciyarta bata son kowane ɗa namiji da sunan soyayya. Amma abubuwa da yawa daga RK na birgeta. Mutum ne shi mai sauƙin kai, sam bai ɗauki rayuwa da girma ba. Komai nashi so simple, burinsa ya bama kowa farin ciki koda shi bazai yi farin cikin ba, ko a wajen ma'aikatan asibitin nan takan ji suna hirarsa da yabonsa akan tausasawa kowa duk da kasancewar asibitin MALLAKINSA....
      “Nifa wannan kallon ALLAH narka ni yake yi Baby”. Ya faɗa yana wani karyar da kai. Murmushi ta saki a karo na farko, sai kuma ta kauda idanunta a hankali ta maida su ƙasa ta rissinar har lokacin da murmushi a kan fuskarta. Kusan minti ɗaya sannan tai magana batare data sake kallonsa ba.
      “Nagode sosai Yaya Rafeeq. Nagode da irin kulawar da kake bani batare da gajiyawa ba. Nagode da irin haƙurin da kakeyi da ni duk da abubuwa da nake maka da dama....”
    “No! no no please ni ban taɓa miki abu dan ki gode min ba. Dan haka kibar gode min. Kuma yaushe na zama Yayanki ne ma?”.
    “Yanzu mana”.
   Ta faɗa tana ɗan waro idanunta dake a kumbure sosai, gasu da ja har yanzu. Dariya sosai ya shiga yi, da sauran dariyar a fuskarsa ya ce, “A'a nagode a barni a matsayin da na kawo kaina dai. Ke duk tarin yayun nan naki. Ga Yazeed, ga Fadeel, Fawzan, AA, Uncle Sadeeq, Uncle Hamza haba ai sai daɗin ya miki yawa idan na ƙaru”.
            “Kai dai kace baka son yin ƙanwar da ni kawai na haƙura”.
      “Ni bance ba. Amma dai a barni a wancan matsayin, idan ma zan zama yayan a bari sai anan gaba kin shigo daga ciki”.
       “Hummm”.
    Kawai tace tana cigaba da juya spoon a cikin shayin daya bata. Fin minti ɗaya sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa. Ganin kallonta yake shima sai ta ɗan kauda idanun ta. “Yaya Rafeeq ka shirya yin aure yanzu?”.
       Mugun faɗuwa gabansa yay dan abin yazo masa a bazatar da baiyi zaton ji daga gareta haka cikin sauƙi ba, duk da bai san ma'anar yimasa tambayar ba. Cikin nutsuwar ban mamaki ya ce, “Miyasa kika mun wannan tambayar Maanal?”.
            Ƙasa ta ƙara yi da kanta, tana mai kokawar ƙarfafa kan nata da danne dukan abinda ke neman rinjayar shawarar data gama yanke ma kanta tun a daren jiya. Ajiyar zuciya taja mai nauyi kafin ta saki murmushi mai ciwo. “Ka amsa min kawai, ka shirya yin aure yanzu?”.
     “Ban san miyyasa kika min wannan tambayar ba Maanal, amma tabbas na shirya yin aure, dan na isa yinsa, da ban shirya yin aure ba ALLAH bazan tunkareki da sunan soyayya ba. Saboda alƙawari naima kaina bazan taɓa ɓatama kowacce yarinya lokacinta ba in har ba aurenta zanyi ba. Na daɗe ina addu'ar a duk sanda zan so wata ɗiya mace ya kasance aurenta nake so zanyi”.
       Sosai ta kafesa da ido, sai kuma ta wani lumshesu da sake buɗesu a kansa. Cikin son taushe muryarta dake neman fara yin rawa ta ce, “Ina son zuwa Kaduna a weekend ɗin nan. Kuma ina son na ɗan huta a can....” sai kuma ta ɗan yi shiru. Cikin zaƙuwa RK yace, “Uhumm ina jinki”.
       Murmushi ta sake saki mai ciwo idanunta dai na kallon ƙasa. “Na baka dama kaje ku gana da Daddy akan batun auren mu”.
      Ai ba zuciyar RK ba, hatta ɗakin ma ji yay yana masa girgiza. Yayinda wasu irin hawaye masu azabar zafi suka silalo da gudun tsiya a kumatun Maanal. Ƙarar tarwatsewar abu da basu san ko minene ba ta ratsa kunnunwansu. A tare duk suka dubi ƙofar, dan tanan ne abun yay ƙara. Plates ɗin abinci ne suka watse a ƙasa.
Dubansu suka maida ga wanda alama ta nuna daga hannunsa plates ɗin suka suɓuto...........✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_


🅿️➖5️⃣0️⃣


______________

.........“Subahanalillahi Naufal ya akai haka?”. Oum ta faɗa tana kallon Naufal first born ɗin babban Yaya kenan da a safiyar yau suka dawo daga Kano shi da sauran ƙannensa biyu ƴammata. Kafin Naufal da yay ƙwalƙwal da idanu alamar zai yi kuka ya bata amsa ta maida dubanta ga AA da yay tsaye a ƙofar duk ya tare ko'ina babu

37 / 77